Sashe 29
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abba da ya dawo daga masallaci ya zo wucewa ya ji hayaniya daga ɓangaren baturen gidan, abin ya ba shi mamaki dan ko motsi baka ji daga ɓangaren Rehaan balle kuma hayaniya. Ganin ƙofar a buɗe ya saka ya shiga dan ya tabbatar ba lafiya ba.
"Me yake faruwa?" Ya faÉ—a yana kallonsu.
Salman ya ƙwace daga riƙon da Umma ta yi masa, ya ƙarasa wajan Abba yana kuka shaɓe-shaɓe kamar ƙaramin yaro ya ce, "Abba ni a wajanta nake so na kwana, Umma kullum sai ta zo ta tafi dani. Ni ina sonta, bana so na tafi."
Abba cikin mamaki da tsoron kalaman Salman ya ce, "wa ka ke so Salman?."
Ya nuna Islaha da take tsaye a wajan har lokacin ta kasa motsin kirki saboda tsoro da tashin hankali da ta ke ciki. Abba ya kalli Islaha sannan ya kalle shi ya ce, "Salman har ka san ka ce kan sonta?."
Shi dai bai amsa ba sai kuka yake yi sosai, Abba ya girgiza kai ya ce, "shikenan daina kuka."
Ya kalli Umma da take wuci kamar zakanya, kafin ya yi magana ta ce, "ka yi mata iyaka da ɗana, ban zan lamunci abinda take yi masa ba. Ya zata dinga saka min shi a ɗaki tana saka shi ya riƙe jikinta? Me Salman ya sani da zata dinga ƙoƙarin koya masa iskancin da da bai isa shi ba? In ba dan ta zo gidan nan ya aka yi Salman ya san ya ce ina sonta? Kai kanka yanzu da ya faɗa sai da ya ba ka mamaki da tsoro, saboda ka san bai taɓa faɗa ba sai da wannan annobar ta zo gidan nan. Zuwa na yi na same ta ta saka ya riƙe ta ta baya yana shafa jikinta."
Islaha ta lumshe ido jin sharrin da aka ƙulla mata wanda bata isa fitar da kanta daga ciki ba, ta kalli Umma da taƙe haƙiƙcewa tana faɗar ƙarya.
Abba ya kalli Islaha ya ce, "Ya aka yi?."
Islaha muryarta ta yi sanyi ta ce, "Wallahi bani na shigo da shi ba, kawai na ga ya shigo ne. Yana jin muyarta tana kiransa sai ya tashi ya riƙe ni wai na ɓoyesa, na so na ƙwace kaina amma na kasa" ta ƙarasa faɗa muryarta na cracking alamun zata yi kuka.
Umma ta ce, "ƙarya ki ke wallahi, meyasa bai taɓa yiwa ko wacce mace haka sai ke? Kwanan ki uku a gidan nan amma kin fara ƙoƙarin lalata min yaro. Bai taɓa cewa yana son wata ba sai ke, bai taɓa yiwa ko wacce mace haka ba sai ke, in ba koya masa ba ya aka yi ya sani?."
Abba ya ce, "ya isa haka, kar na sake jin bakin ki akan maganar nan."
Umma ta ce, "wallahi bazai yu ba, dole a yi min iyaka da ita, baza ta gurɓata min tarbiyyar yarona ba."
Abba ya riƙe hannun Salman ya ce, "mu je ka yi sallah."
Salman ya ƙi tafiya ya ce, "ni a wajanta zan zauna."
Abba ya ce, "zamu dawo, mu je. Kema fito..." ya faÉ—a yana kallon Umma.
Sai a lokacin Abba ya lura da Rehaan a tsaye a jikin ƙofar ya haɗe rai, bai ce masa komai ba ya fita da Salman.
Umma ta zo gifta Rehaan ta ce, "In baza ka iya tsare matarka ba ka sallamata ta je inda zata samu abinda take so, ta daina shafe min ɗana tana ƙoƙarin rage wani abun da shi."
Haka kwaai ya ji maganar ta da ki zuciyarsa, ya haɗɗiye yawu, apple adam ɗinsa yana up and down, ya ƙarasa cikin falon ya same ta a zaune ta rufe fuska da hannunta tana kuka.
Ya tsaya yana ƙare mata kallo, zuciyarsa tana wani irin tafasa cikin tsananin ɓacin rai da jin haushinta mai yawa. Yanzu yake danasanin yiwa Abba alƙawari akan aurenta, yanzu yake danasanin amincewa ya zauna da ita har na wata biyar. Tabbas ya cuci kansa, ya lalata backround ɗinsa ta ko ina.
A hankali ta É—ago ta kalle shi suka haÉ—a ido, idanunta ya yi ja sosai fuskarta ta sake tsukewa ta koma kamar ta fuskar yara.
Ganinsa a tsaye a kanta sai hawaye ya sake zubo mata, tana buƙatar wanda zai rarrashe ya bata gaskiya bata da kowa, muryarsa tana rawa ta ce, "Ni dai ka canja min gida, bazan iya zama a nan ba."
Wani irin abu yake ji yana caccakar zuciyarsa, ƙirjinsa yana bugawa da ƙarfi, ransa ya ɓaci jijiyoyin kansa suna harbawa. Cikin wata irin murya ya ce, "kin san yanayin ki, saba da aikatawa ko yaushe meyasa ki ka saka no intimacy a rules ɗin ki?....
Nana Haleema.
RDB3P24
Nana Haleema.
Da hanzari ta ɗago kai tana kallonsa, gabanta ya faɗi tana jin kalamans suna sukar ta kamar allura har cikin zuciyarsa. Ta goge hawayen idanunta ta miƙe tsaye tana kallonsa ta ce, "me ka ke nufi?."
Ya kalle ta ta gefen idanunsa ya É—auke kai cikin hausarsa da ba ko yaushe ya cika yi ba ya ce, "kin ji ai, no need na maimaita miki."
Islaha ta bi shi da kallo ta kasa magana sai ido da ta zuba masa dan bata san ma abinda zata ce ba. Inda zata samu yadda ta ke so da ta ce a jawo mata shi, ta dinga dukansa har sai ya daina numfashi.
Rehaan ya kalle ta ya ce, "look! Ni ban hana ki abinda ki ke ra'ayi ba, amma ina so na tuna miki nan gidanmu ne kuma nan apartment ɗina ne. Bazan yarda ki dinga ɓata min suna ko yaushe ba, in za ki yi abinda ki ke so ki bar gidan nan, in kin gama ko meye sai ki dawo ba abinda ya dame ni ba ne. Sannan ki ƙyale Salman, na faɗa miki yana da mental issue bazai taɓa rufa miki asiri ba."
Duk da ɓacin ran da ya danne mata ƙirji, takaici da haushinsa da suka tokare ta har take jin ta kasa numfashi yadda ya kamata, bai saka ta saurara masa ba ta ce, "ai na ji kana zancen na san ina so na saka bana so a rules ɗina, shine na ke so na na tuna maka…..kai dai!" ta faɗa tana nuna sa da yatsa irin up and down ɗin nan.
Kafin ta cigaba ya harɗe hannunsa a ƙirji ya ce, "ni dai me? Kin ji na ce miki da ba ki rubuta ba akwai wani abu ne?."
Sai ya yi murmushin takaici da baƙin ciki ya sake zuba masa ido, sai ya rasa me zai ce mata dan kamar zubar da class ne tsayawa yana faɗa tana faɗa. Sai ya ce, "i don’t have your time" ya faɗa yana hawa sama dan bai ga amfanin ya tsaya yana faɗa tana faɗa ba.
Takaici ya saka ta yi kuka mai yawa, a nan ta zauna ta ci kukanta son ranta. Buɗe ƙofar ta ji anyi ta san kuma Banisha ce, dan itace mai shigowa falon kai tsaye.
Banisha ta shogo ciki ta ce, "Sis Islaha me ya faru?."
Islaha ta girgiza mata kai bata ce komai ba. Banisha ta ce, "Daada ta ce na kira ki" tana faÉ—a ta wucewa sama wajan Rehaan.
Islaha ta ce, “Na shiga uku, ni fa bana so a ce na zo É—in nan. Da me zan ji? Da sharrin da aka yi min ko da zaunar da ni a gaban mutane?. Na baro gidan Maman su Hamma ma ban huta ba, har gwara can a kan nan.â€
Sai ta miƙe zaune har suka sakko tare shi da ita, Banisha ta ce, "mu je." Ko hijjab ɗin jikinta bata cire ba haka ta miƙe ta bi bayansu a sanyaye.
Bata kula da kowa a falon ba ta zauna dan kanta har ya fara ciwo saboda kukan da ta yi, ga shi ba wani abincin kirki take ci kwana biyu ba, har jiri take ji yana É—aukar ta. GabaÉ—aya bata lura da gabaÉ—aya matan gidan ne a zaune ba, ga Abba ga kuma Salman É—in.
Daada ta ce, "Ishlaya." Islaha ta É—ago ido a hankali ta kalli Daada.
Daada ta ce, "FaÉ—a min me ya faru?."
Islaha ta sunkuyar da kai muryarta a raunane ta ce, "bayan na bar nan na koma, sai na tuna na bar kaya a mota, shine na yiwa wanda ya kaini waya na ce ya kawo min. Yana kawo min sai ga shi ya zo wajan, kuma..." ta kasa ƙarasa tana dafe kanta cikin takaici.
Umma ta yi caraf ta ce, "ƙarya ki ke yi, ke ki ka neme shi ki ka kai shi har cikin falon mijin ki, in ba ki neme shi ba ta ya zai zo?."
Daada ta kalle ta ta ce, "ya isa, ba ke na tambaya ba ai ko?."
Daada ta ce, "Ina jin ki Ishlaya."
Islaha ta ce, "daƙyar ma na tuna lock ɗin da Banisha ta faɗa min, ina shiga ya bi bayana ya zauna. Sai ya ji muryarta tana nufo parlour, shine ya miƙe yana cewa na ɓoyesa kar ta tafi da shi. A haka ta shigo falon."
Daada ta sauke numfashi ta ce, "Ishlaya ke kin ce haka aka yi, ita tace ba haka bane."
Islaha ta ce, "Allah yana ganin duk abinda ya faru, bazan ɓoye gaskiya na faɗi ƙarya dan na burge wani ko dan na ɓoye laifina ba."
Rehaan ya bita da kallo jin tana tauhidi ita lallai ga mai tsoron Allah. Tsakin da ya yi ya saka kowa ya kalle shi, sai kuma ya ɗaure fuska ganin ana kallonsa, gabaɗaya zaman ƙasar ya ishe shi wallahi, yana da ayyukan yi shiyasa yake so ya tarkata ya koma inda ya fito ko hankalinsa zai kwanta da wannan ƙananun maganar.
Umma ta ce, "ni so nake yi a raba ta da É—ana, babu ita babu shi, kar na sake ganinsa a wajanta ko da wasa.
Ai ba dole sai ta kula shi ba, kuma yayan mijinta ne ba ƙani ba, babu ruwanta da shi."
Salman ya noƙe kafaɗa ya ce, "Abba ni dai ina sonta, don Allah ka ce Umma ta bar ni na zauna a wajanta, ni a wajanta nake so na zauna."