← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 110

Sashe 93

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abba ya girgiza kai ya ce, "Bazan hana ka bin umarnin babar ka ba, dan a wancan lokacin ka yi min biyayya har ka ka zaune da ita a matsayin matar ka, a wannan lokacin kuma bazan hana ka yiwa babar ka biyayya ba.

A yi binciken, nima zan so a ce ba ita bace ko dan zargin da duniya take yi mata."

Ya É—aga kai ya ce, "in sha Allah." Abba ya juya ya fita shi kuma ya lumshe idanunsa."

   Sai dare Safeera da Islaha suka koma apartment ɗin Rehaan, zuwa lokacin taji sauƙin ciwon kan da yake damunta. A ɗakin babu mai cewa komai, Safeera bata ce mata komai ba ta shirya ta kwanta ita kuwa kaya ta canja kawai ta kwanta ta yi shiru tana tunani.

Har safeera ta yi bacci ita ta kasa yi, ta tashi ta ɗauki wayar Safira ta sake kallon video tana kuka. Sai kuma ta tashi ta fita daga ɗakin, ta ƙarasa ƙofar ɗakin Rehaan tana tunanin ta shiga ko kar ta shiga, sai ta yanke hukuncin shiga kawai.

Tana shiga ya É—ago ido ya kalle ta, yana zaune a gefen gado ya kasa bacci, shiyasa ya tashi ya kunna hasken É—akin ya zauna yana tunani. Islaha ta shiga tsakiyar É—akin tana kallonsa, sai kuma ta sunkuyar da kanta ta rasa me zata ce masa.

Shima shiru ya yi bai ce mata komai ba yana kallonta, sai ta É—ago suka haÉ—a ido ta ce, "Ka kalli videon ko?."

Bai bata amsa ba sai lumshe ido da ya yi ya buɗe akan fuskar ta da ta kumbura saboda kuka, ta sake sunkuyar da kai tana kallon ƙasa muryar ta tana rawa ta ce, "Kuma ka kalli jikina a ranar da na yi wanka a public bathroom, ka kalla ko?" Ta faɗa bata ɗago kanta ba tana kallon ƙafafunta.

Rehaan ya ta so ya matso kusa da ita yana kallonta, bata É—ago kanta ba muryarta ta fara rawa sosai, ta buÉ—e baki zata yi magana amma ta kasa saboda kuka.

Sai da ta tsayar da kukan tana jin ciwon kai ya dawo sabo a lokacin, muryar ta tana cracking ta ce, "Don Allah ka banbance min, da jikina da jikin ta cikin videon nan iri É—aya ne? Na ruÉ—e, na kasa banbance kaina da.........."

Sai ta kasa ƙarasawa ta durƙushe zata zube a ƙasa Rehaan ya taro ta ya riƙe duka hannayenta, ta ɗaga ido ta kalle shi ta ce, "Na kasa ganewa, kuma ina so na gane dan na fita daga halin da nake ciki. Ka taimaka ka faɗa min, don Allah!."

Rehaan bai san ya yi hugging ɗinta ba da ya ji ta sake fashewa da kuka a ƙirjinsa, ya riƙe ta sosai a jikinsa yana runtse ido kukanta yana yin nutso a cikin jikinta.

"Ni na kasa ganewa, ka faɗa min ka ji!" Ta sake faɗa tana jikinsa shi kuma ya kasa ce mata komai, kawai ji ya yi yana buƙatar rungumeta shiyasa ya yi, amma ba dan ya yi magana ba.

Jin kukan nata ya yi yawa sai ya ce, "na faÉ—a miki, ina tare da ke. Calm down!."

"I can't...."

"Stop crying."

"I can't..." ta kuma faÉ—a tana kuka a jikinsa ya lumshe ido yana sake hugging É—inta.

Ta jima a haka a jikinsa, kafin ta zare jikinta tana ja da baya yana kallonta, sai kuma ta buɗe ƙofar ta fita ta sauka ƙasa ta rasa inda zata saka ranta. Daga ƙarshe ta kwanta akaan carpet, ta rasa inda zata saka ranta ta ji daɗi.

A haka bacci ɓarawo ya fara ɗaukar ta, sai ta ji kamar da mutum a kusa da ita a kwance, da farko ta share saboda ta san da Safeera suke kwance, amma tunawa a falo take sai ta buɗe ido a firgice tana so ta miƙe ta kunna switch amma ta kasa. Da ƙarfi aka jawo ta, sai kuma ya yi dariya ya ce, "Hooo ta ji tsoro, in gari ya bar duhu sai kin bani alawa na bata tsoro."

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Ta furta tana so ta ƙwace hannunta daga riƙon da ya yi mata  amma ta kasa.

A daidai lokacin aka kunna hasken falon gabaɗaya, lokacin ta yi nasarar ƙwace hNnunta ta koma gefe tana hakki, dan ƙiris ya rage tashin hankali ya saka ta samu attack.

"Laa ila'ha illalahu, muhammadur rasulillah S.A.W!."

Salatin da ta ji an yi ya saka ta buÉ—e ido a firgice tana kallon mutanen da suke tsaye suna kallon ta......

Nana Haleema.

RDB3P68
Nana Haleema.

Umma ta ƙarasa cikin zafin nama ta ja hannun Salman ta yi gefe da shi ta ce, "Na faɗa miki lalata min yaro ta ke yi, yanzu ba dan Allah ya kawo ni ba me zata yi masa?" Ta faɗa tana kallon Mama da ta ke tsaye daga bayanta.

Umma ta juya ta chakumi wuyan Islaha ta miƙar da ita tsaye ta ce, "na rantse da girman Allah sai kin bar gidan nan, bazan zuba ido ki lalata min yaro ba, abin har ya kai ki dinga gayyatarsa nan? Na shiga uku! Tun yaushe ki ka saba gayyato shi nan ɗin?."

Islaha dai bata ce komai ba, tana tsaye kawai dan ta ruÉ—e bata san abinda ya kamata ta ce ba.

Mama ta ce, "na jima da dawowa daga rakiyar yarinyar nan ai, ki duba iskanci da ta yia waya, babu kunya babu tsoron Allah. Bayan hotuna da videon ta da suka gama yawo a duniya, bata haƙura ba sai da ta jawo yaro har ɗaki tana yi masa iskanci, abin kunya mijinta yana sama ita kuma tana ƙasa. Daman haka ki ke?."

Umma ta ce, "wallahi sai na faÉ—awa Daada, dole yarinyar nan ta bar gidan nan, bazan iya zama da ita tana cutar dani ba."

Salman da yake gefe yana ta taɓa wannan da wancan ya ce, "Umma tsorata ta nayi tana bacci." Umma saboda fusata bata san ta juya ta mare sa ba, ta nunasa da yatsa ta ce, "yi min shiru, in ka sake magana sai na fasa maka baki."

Mama ta ce, "ya za ki dinga yi masa faÉ—a? Kin manta lalurar da yake da ita ne? Ga wacce ya kamata a yiwa faÉ—a nan a tsaye tana kallon ki."

Umma ta sake riƙe rigar Islaha ta ce, "na rantse da Allah sai na koya miki hankali, sai na kore ki daga gidan nan wallahi tunda ba gidan ubanki bane."

Rehaan yana tsaye a kan stairs yana kallon komai, ya harɗe hannu a ƙirji yana kallon duk abinda yake faruwa. Ya tashi zai yi sallah kenan ya ji hayaniya dole ya fito ya ga abinda yake faruwa. Takaici kamar ya kashe shi, duk abinda Islaha take yi bai taɓa jin haushi kamar ranar ba, bai san dalilin da ya saka ya ji ransa ya ɓaci ba, haushinta da takaicin wannan ɗabi'a'un nata sun tsaya masa a rai, bai ce komai yana tsaye yana kallonsu su kuma ba su kula da shi ba.

Umma ta ce, "mu je wajan Daada, a daren nan sai ta bar gidan nan wallahi. Iskanci ya yi yawa, abin ya kai har tana gayyato shi ɗaki da daren nan? Kuma saboda rashin tsoron Allah mijinta yana sama ita tana ƙasa tana iskanci?. Bazai yu ba wallahi, dole a bar gidan ta je ta samu ƴan uwanta yan iska su cigaba daga inda suka tsaya."

Mama ta yi caraf ta ce, "ni abinda yake É—aure min kai, ya aka yi ya san lambobin falon nan in ba buÉ—e masa ta ke yi ba?."

Mama ta sake fusata Umma, ta fusata sosai ta ce, "ko yarinyar nan ta bar gidan nan, ko kuma ni na bar shi, dole a yi É—aya dan bazan zauna tana lalata min yaro ba."

Islaha ta kasa cewa komai, bata da bakin da zata kare kanta shiyasa ta kama bakinta ta yi shiru kawai. Tana cikin damuwa mai yawa, bata da lokacin da zata buÉ—e baki ta yi magana akan abinda bazai amfane ta da komai ba.

Mama zata yi magana Rehaan ta ga Rehaan, ya sanya hannunsa duka biyun a cikin pocket ɗin pyjamas ɗinsa fuskarsa a ɗaure, babu alamun wasa ko sassauci a tare da shi. Yana ƙarasowa ya kalle su ɗaya bayan ɗaya sannan ce, "Mama dare ya yi a bar maganar nan."

Mama ta nuna islaha da ta zauna ta dafe kanta ta ce, "kamata muka yi dumu-dumu tana yiwa Salman fyaÉ—e, kuma ka ce a bar maganar?."

Wani irin abu ya ji ya da ki zuciyarsa da ƙarfi, amma bai nuna ba sai ya daure ya ce, "dare ya yi yanzu, hayaniyar ku ta hanani bacci, ku je kawai."

Umma ta kalle sa a fusace ta ce, "dole ka ce haka ai, dole ka ce mu je tunda ba ka da bakin da zaka kare ta. To wallahi da safe sai an yita ta ƙare, ko ta bar gidan nan ko ni na bar shi, dan ta gama zama a gidan nan, baza mu zauna da karuwa tana bin yaranmu tana lalatawa ba. Ta je ta yi a wani gidan, amma ban da nan wallahi."

"Fine! Ku je" ya faÉ—a cikin gajiya da maganar.

Hakan da ya faÉ—a sai ya sake fusata Umma da Mama, suka taso masa da faÉ—a kowa yana faÉ—ar abinda yake bakinsa, shi dai yana tsaye ya yi shiru, dan sun bar kan Islaha sun dawo kansa suna yi masa faÉ—a kamar zasu da ke sa.

A lokacin aka shigo falon duk suka juya suka ga Mamy ce ta shigo sanye da dogon hijjab a jikinta. Umma kamar jira take yi Mamy ta shigo ta nuna ta ce, "Ki faÉ—awa É—an ki, dole karuwar matarsa ta bar gidan nan wallahi."

Mamy cike da damuwa ta ce, "me ya faru? Ana jin maganar ku har apartement É—ina, dare ne fa."

Mama ta nuna Islaha da bata ɗago kai ba ta ce, "wannan karuwar...! Ita mu k kama dumu-dumu  tana ƙoƙarin zugewa Salman zip ɗin wandonsa."

"Hasbunallah! Ya Salam! Ya Salam!._
Chapter 93 · 0% Book details