← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 110

Sashe 73

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata jira umarnin Islaha ba ta kunna 17 É—in ta haÉ—a backcup da 12 É—in, ita dai Islaha kallonta kawai take yi ganin yadda take operating wayar alamun an saba dannawa.

Banisha ta ce, "bakya using wifi É—in Ray?" Islaha dai bata cekomai ba tana kallon yadda Banisha take sarrafa waya. Yadda ta ce Wifi É—in ma ya banbanta da yadda take faÉ—a, dan ita Wi fi take cewa, ita kuma Banisha Wayfay ta ce, kuma tana da tabbacin haka ne daidai tunda su turawa ne.

Cikin lokaci kaÉ—an ta gama yi mata backup ta cire sim card É—inta ta É—ora a kan sabuwar, ta goge komai na kan 12 É—in ta ajjiye mata sannan ta ce, "Welcome to latest iphone my Sis."

Islaha ta yi murmushi ta ce, "Thank you Bani."

Banisha ta yi dariya ta miƙe ta fita, Islaha ta bi wayar da kallo ta ɗauka wayar kiran Hamma ya shigo a sabuwar, bata ɗauka ba ta saka wayar a chaji sannan ta saka hijjab ta fita.

Ƙasa ta sauka ta nufi apartment Mamy da niyar ta yi mata godiya, bata same ta a falo ba ta bita har bedroom, ta same ta a tsaye tana shafe jikinta da turare, ga gahinta har baya ya sauka sai ƙyalli yake yi.

Islaha ta ɗan yi baya jin ƙhamshin har tsakiyar kanta. Mamy da ta lura da zuwanta ta ce, "sorry daughter, ƙhamshin zai yi affecting ɗin ki ko?."

Islaha ta yi murmushi ta ce, "Mamy an kai min waya, na gode Allah ya saka da alkhairi."

Mamy ta dafata ta ce, "Amin. Amma bani na siya miki ba, Rehaan ne. Gobe friday, suna zuwa shopping duk ranar friday, ki dinga binsu kina siyan abinda ki ke so, in kuma baza ki je ba sai a ba ki kuÉ—in ki."

Islaha ta ce, "To Mami, an gode." Mamy ta yi murmushi Islaha kuma ta koma apartment É—in Ray tana ta murmushi tana jin daÉ—in yadda Mamy take yi mata kirki.

Tana hawa upstairs ɗin ta same sa ya fito daga ɗaki, abinda bata taɓa gani ba shi ta gani, dan babu riga a jikinsa daga shi sai short. Kai tsaye idanunta ya sauka kan logon NIKE da yake rubuce a jikin small boxer da yake ta ciki, ƙaramin short shine mai logon Nike daga ciki, sai wani mai ɗan tsayi kaɗan daga sama.

Ita bata san me logon nan ya yi mata ba, kuma logon bana takalmi ko na riga ne yake ɗaukar hankalinta ba, na small boxer ɗinsa ne yake ɗaukar hankalinta, gashi ta lura komai nasa na Nike ne kamar mai yi musu advert. Ta ɗan kalle shi ta ɗauke kai, tana mamakin halittarsa ce a haka ta ga muscles ɗinsa irin na mazaje ko kuma gym ne? Ita dai ta san ba shi da ƙarfin da zai iya gym, wataƙila Allah ne ya yi shi a haka.

Ta yi tsaki ƙasa-ƙasa yadda ba zai ji ba ta ce, "mutum ya san yana tare da wacce ba muharramarsa ba ya dinga fitowa a haka, Allah ya kyauta."

Ba ta yi tunanin ya ji ba sai ta ji ya ce, "Yau ta saba ganin maza a haka?."

Islsha ta waiwayo ta kalle shi suka haÉ—a idanu, sai ta É—auke kai tana nuna shi da hannunta ta ce, "au wai kai namiji ne?."

Bai san ya buÉ—e idanunsa yana kallonta ba jin wata tambaya ta rainin hankali da ta yi masa, wai au kai namiji ne, to me ta ke É—aukarsa?.

Islaha ta taɓe baki ta ce, "Ni ban ga maza a nan ba, dan kai in ka saka kayan mata tsaf sajewa za ka yi dasu, daman ga gashi nan kana fama da shi. Don Allah ka daina saka kanka a jam'in maza, kana wulaƙanta mazan gaske. Dan banbancina da kai kaɗan ne, har na fika suffar jarumai wallahi" ta faɗa tana wani yamutsa fuska.

Rehaan bita da kallo dan ta kulle masa baki bai san me zai ce mata ba, ita kuma ta wuce ta shige É—aki bata sake kallonsa ba.

Tana shiga ta ɗauki tsohuwar wayarta ta tana juyawa taba murmushi ta ce, "wannan ta Hajiya Safeeran Saleem ce in sha Allah." Ta faɗa tana buɗe inda aka ajjiye mata kayan buɗan kan tana kallo, komai yana nan har kuɗin da aka bata bata taɓa ko sisi ba.

Ta ɗauki sarƙar gold ɗin tana kallo, sai kuma ta mayar ta ajjiye dan ba ta san me zata yi da su ba. Sai kuma ta ce, "ko na ɗauki kuɗin nan na haɗawa Safeera ta cika ta canja wayar ta siyi 14?." Sai kuma ta rufe bata ɗauka ba ta koma gefen gado ta zauna.

Kamar a mafarki aka buɗe ƙofar, ta waiwayo ta kalli mai shigowa suka haɗa ido da Salman da ya shigo nan take gabanta ya faɗi.

Ta miƙe tsaye tana kallonsa cikin firgici da tsoro, shi kuma ya shigo "Na zo mu yi wasa."

Islaha ta yi yaƙe wanda ya fi kuka ciwo ta ce, "To sannu."

Kafin ta yi magana ya ƙarasa ya zauna a gefen gadon yana taɓa lamp ɗin da take ajjiye a bedside drawer. Ganin ya zauna yana wasa da fitilar da ta ɗauki hankalinsa a guje ta fice daga ɗakin, kai tsaye ɗakin Rehana ta buɗe ta shiga.

A lokacin Rehaan ya fito daga wanka É—aure da towel a jikinsa, tana shiga suka haÉ—a ido ta yi tsaki ta juyar da fuska cikin nauyi da kunya ta ce, "please cover yourself."

Rehaan ya bita da kallo yana mamakin zuwan ta É—akinsa a firgice haka, sai ya zauna a stool da yake gaban mirror ya ce, "i was showering in my room, you did not even knock."

Islaha har lokacin bata juyo ba ta juya masa baya, ba dan Salman da yake ɗakinta ba fita zata yi, dan wani abu mai nayi take ji ya lulluɓe ta, ƙirjinta har ɗagawa yake yi sama-sama, tana ji kamar ana zuba mata ruwan sanyi daga kanta zuwa ƙafafunta.

Rehaan kallonta yake yi yana daga zaune, sai ya tuna da kalamanta da ta faɗa masa mintina kaɗan da suka gabata, ya miƙe ya matso kusa da ita ya tsaya bai ce komai ba. Islaha tsayuwarsa ta ji a kusa da ita, ta juyo bata yarda ta kalli jikinsa ba sai fuskarsa ta ke kallo, ta ɗan yi baya ganin kamar tsayuwar bata yi ba sannan ta ce, "Salman ne ya zo har ɗakin da nake, don Allah ka zo ka fita da shi, wallahi tsoro nake ji" ta faɗa tana cigaba da ja baya.

Bai ce mata komai ba sai kallon ta da yake yi, ita kuma sai ta rufe idanunta dan bata son kallonsa a haka ta sake cewa, "yana cikin É—aki, ka je ka yi masa magana."

Bai yi magana ba sai da ya zo daf da ita sannan ya ce, "sauran lokacin da ya ke zuwa ni nake yi masa magana, ko yau ya fara zuwa?."

Takaici ya saka ta yin tsaki ta juya zata nufi ƙofar da zata fita ya jawo hannunta da dawo baya.

A fusace ta fizge hannunta tana kallon idanunsa ta ce, "ka daina ƙoƙarin cewa za ka taɓa ni, ka daina riƙe min hannu bana son wannan ɗabi'ar. In baza ka je ka yi masa magana ba zan je mu kwana tare, daman ai ba yau muka saba kwanan ba."

Wani irin kallo yake yi mata wanda bata taɓa gani ba, tsakiyar idanunta yake kallo yana juya ƙwayar idananunsa a ciki. Kallon sai ya yi mata nauyi sosai, har ya saka jikinta ya yi sanyi, masifar da take yi ta gushe gabaɗaya. Ta sauke muryarta ƙasa ba kamar yadda ta yi magana a farko ba, tana ja da baya kaɗan-kaɗan ta ce, "ni dai zan je na yi magana da shi."

Zata fita ya sake riƙo hannunta, ya sake dawo da ita baya yana kallon fuskar ta. Islaha jikinta ya yi sanyi sosai, tana jin soft and smoothie palm ɗinsa yana ratsa cikin jikinta. Kafin ta yi magana ya lumshe ido ya buɗe ya ce, "i want to show you something."

Ta ƙarfafa jikinta ta ƙwace kanta ta ce, "ni babu abinda zan gani, ka ƙyale ni don Allah."

Islaha ta sake ja baya yana binta, Islaha ta girgiza masa kai ta ce, "Ni babu abinda zan gani, don Allah ka ƙyale ni, don Allah Mr Rehaan ka ƙyale."

Ya ce, "ina so na banbance miki namiji da mace."

Gabanta ya faɗi matuƙa, amma bata bari hakan ya yi tasiri ba ta harare sa ta ce, "ka jira mazan su zo sai su banbance, kai kam na faɗa maka banbancina da kai kaɗan ne, dan haka ba sai na ga komai ba dan ni da kai sammakal, ni ka ƙyale ni" ta faɗa tana niyar fita Rehaan ya finciko ta da ƙarfi ta dawo jikinsa gabaɗaya.

Idanunta suka fito waje saboda taoro da firgicewa, gashi ko hijjab babu a jikinta iya rigar bacci ce kuma bata da tsaho ko kaÉ—an.

Hannayenta suna jikinsa a zube a kan ƙirjinsa, saboda yadda ya jawo ta da ƙarfi bata san ta zuba hannunta a jikinsa ba. Ga shi jikinsa babu riga, hannunta ya sauka a kan ƙirjinsa da har lokacin ruwan jikinsa bai gama bushewa ba, ga gashin da yake kwance a ƙirjinsa hannunta yana taɓawa.

Islaha ta ƙwace kanta ta yi baya cikin masifa ta ce, "ni ka daina yi min irin wannan abu, ka daina faɗa ni, hannunka ya daina zuwa jikina, bana so."

Kallonta kawai yake yi bai cekomai ba, ta kawar da kai daga kallonsa ta ce, "Just beacuse we were under contract doesn't mean you can do whatever you want. Abin na ka ya fara yawa,ka dinga tunawa muna under rules ne, ka daina ƙoƙarin wuce gona da iri."

Maimakon ya ƙyale ta, sai ya miƙa hannunsa da hanzari ya riƙo waist ɗinta ya jawota jikinsa ya haɗe ta da jikinsa hannunta ya sake sauka a ƙirjinsa.
Chapter 73 · 0% Book details