Sashe 90
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai kuma ta buɗe ido suka haɗa ido da Rehaan da ya kafa mata idanu yana kallonta ya kasa janye idanunsa daga kanta. Ganin sun haɗa ido sai ya sake ɗaukar ruwan miƙa mata alamun ta kuma sha, sai ta miƙe zaune tana riƙe kanta saboda ciwo. Ta karɓi ruwan ta sha, ta jingina da bango kanta yana sarawa sosai, zuciyarta tana bugawa, tana ji kamar ba a duniya take ba. Shiru ya ratsa wajen, babu mai magana a cikinsu sai numfashi da take yi a hankali a hankali.
"Salama alaikum ina Ishlaya? Abinda zata yi mana kenan tsakani da Allah? Ina yabonta sallag sai na samu ta da kasa alwala?." Daada ta faÉ—a tana shigowa wajan, Mamy da Mama da Abba suna bayanta.
Duk suka bita da kallo, kana ganinta ka san bata da lafiya kuma bata cikin hayyacinta. Daada ta ce, "me nake gani haka a duniya, ƴar nan dama fuska biyu ce dake?." Islaha ta runtse idanunta, hawaye ya sake sakkosa daga idanunta.
Daada ta ce, "Duk soyayyar da na nuna miki ashe daman ke ba ta gari ba ce? Iskancin ki ya kai har a yi video da ke ana aikata alfasha? Ina kunyar fulanin da na gani a tare da ke har na yi ƙwaɗayin a auro ki?."
Ta kalli Rehaan da har lokacin yana tsugune yana kallon Islaha, yana ji kamar zuciyarsa kalaman Daada suke shiga. Daada ta ce, "daman shi ba so yake yi ba, ƙwadayin tarbiyya ya saka na ɗauko ki, ashe ba ki samu tarbiyyar ba ko kaɗan, kallon kitse nake yiwa rogo, tarbiyyar ta ki a baki take bata kai zuciya ba. Bana son wanda bai girmama kansa ba, bana son wanda ya watsar da alkunya da ɗabi’un fulani. Dan haka ni bazan zauna da ke a matsayin matar jikana ba, bazan iya cigaba da zama dake ana zuba hotunanki tsiarara a duniya ba, ina ni ina ke Ishlaya? Kin fi ƙarfina. Gwara kawai a rabu lafiya, tunda daman ba so yake yi ba."
Mama ta ce, "gwara haka, zubar da ƙimar gidan nan ne ace wannan tana cikinsa ko da a matsayin mai aiki ne balle kuma matar Rehaan. Gwara a yi ta ta ƙare, na ji daɗi da ya kasance babu wanda ya san da auren nan a waje, da mun shiga uku."
Mamy da Abba dai basu ce komai ba sai Jazy ne ya ce, "Daada wannan hotunan haÉ—asu aka yi, ba ita bace."
Daada ta juyo a fusace ta ce, "na saka ka a ciki ne? Uban ƴan iyayi, magana nake yi akan jikana da matarsa ba kai ba, ban saka ka a ciki ba. Kar na sake magana ka saka min baki, ban saka da kai ba balle na kwashe da kai. Auren nan dole a raba shi, bazai zauna da irin wannan matar a cikin gidan nan ba."
Daada ta kalli Abba ta ce, "Ashe da gaskiyar babar Salmanu, da take cewa zata lalata mata ɗa mu ke ganin ƙarya take yi, yanzu na yarda zata aikata."
Sautin kukan Islaha ya saka kowa ya kalle ta, Islaha ta saka yatsunta ta toshe kunenta tana kuka jikinta yana karkarwa.
Safeera itama kuka take yi ta ce, "ba halin Islaha bane, kuma wallahi ba ita bace."
Daada zata kuma magana Rehana ya miƙe tsaye ya kalli Daada, fuskarsa ta canja cikin yanayin da ba su taɓa gani ba ya ce, "Daada ku je waje, don Allah!."
Daada ta kalle shi tana harararsa ta ce, "bazan tafi ba, sai an warware auren nan."
Ya lumshe ido yana jin sautin kukan Islaha yana ratsa jininsa, sai ya rikice ya rasa me zai yi ya ce, "Daada don Allah ki je, zan yi komai da kaina."
Daada ta ce, "ai daman duk mai kishin kansa bazai zauna da wannan ba, kai É—in ne nake tantama a kanka, dan na san ba dukkan ka ne fulani ba, tsaf zaka ce zaka zauna da ita tunda ku Æ´an Æ™asashen waje ba kunya gare ku ba.â€
"Daada ki je!"
Ya faɗa cikin wata irin murya mara sauti amma ami amo yana runtse ido da ƙarfi, dan ji yake yi kamar ana zuba masa ruwan zafi.
Daada ta dinga binsa da kallo ganin canjin da bata taɓa gani ba ta ce, "Ka tabbatar za ka yi ɗin?."
Ya É—aga mata kai, sannan ta kalli Abba da Mama ta ce, "mu je mu tattauna akan maganar nan..." ta waiwayo ta kalli Rehaan ta ce, "kai kuma ka kawo mana takardar sakinta yanzun nan." Daga haka suka fita Daada tana mita.
Suna fita Rehaan ya kalli Mamy da take kallonsa, ta yi masa nuni da Islaha da idanunta, ya kalli abinda ta nuna ya sake kallonta, ta sake yi masa alamar da shi ya fahimta sannan ta fita.
Islaha ta É—ago ido tana kallonsa kamar yadda yake kallonta, hawaye yana zuba daga idanunta, ko buÉ—e idanunta bata iya yi, saboda nauyin da kanta ya yi. Idanunta ya yi luu kamar zai rufe saboda kuka, muryarta ta dashe bata fita yadda ya kamata ta ce, "Kowa bai yarda dani ba, nima ban yarda da kaina ba, kuma bani da kowa a duniya, Allah kaÉ—ai nake da shi."
Rehaan yanayin da yake ciki ya ta'azzara, jikinsa ya fara rawa yana daga tsaye. Ya kasa jure ganin tana kuka cikin fitar hayyaci, ya kasa riƙe kansa kamar yadda ya saba, ya ƙarasa inda ta ke zaune ya tsuguna a kusa da ita ya riƙe kafaɗunta, yana kallon idanunta bai ce komai ba.
Slowly ya jawo hannunta ya kwantar da ita a ƙirjinsa, ya sanya hannayensa duka biyun ya zagaya dasu bayanta, ya yi tapping bayanta da sigar rarrrashi, ya kai bakinsa kunnenta ya ce, "Waye ya ce ba ki da kowa? Ba gani nan ba..."
"Stop crying, i'm here for you."
Islaha ta saki jikinta a jikinsa sosai, ta lumshe ido tana jin sautin bugun zuciyarsa a kunnenta, ta yi luf tana hawaye tana jin yadda yake tapping bayanta cikin rarrashi da nuna tsantsar kulawa a gare ta.
Nana Haleema.
RDB3P66
Nana Haleema.
Islaha a yanayin da ta ke ciki na ƙunar zuciya da nauyin kai, bata san ta kwantar da kanta a jikinsa tana kuka ba, ta riƙe shi sosai tama zubar da hawaye.
Rehaan ko gajiyar durƙusawar da ya yi bata damunsa, yana riƙe da ita ya ɗora haɓarsa a gashin kanta ya rufe ido ya yi shiru cikin wani irin yanayi. Sun jima a haka kafin ya ja numfashi sannan ya ɗago kanta, ya ɗora hannunsa akan fuskarta yana goge mata hawayen fuskarta yana kallon jajayen idanunta, ya girgiza mata kai ya ce, "ina tare da ke, babu wanda zai wulaƙanta ki ya zauna lafiya. Ki daina kuka" ya faɗa yana shafa kumatunta.
Ita da shi ne kaÉ—ai suka ji me yake faÉ—a, yadda yake yin maganar ko Jazy da Safeera baza su ji ba, suna dai kallon bakinsa yana motsawa amma ba jin sauti. Ya shafa gashin kanta, ya sake goge mata hawayenta ita kuma ta sunkuyar da kanta.
Ya miƙe tsaye ya kalli Jazy da yake kallonsa, ya ƙarasa inda yake ya ce, "Jazy!..."
"A saka DSS su yi aiki a kan case ɗin nan, ina so a nemo min main account ɗin da aka fara posting pictures ɗin, sannan a rubuta min sunayen duk wani blog da ya yi reposting. A yau nake so a yi binciken ba gobe ba, a yau nake so na san su waye suke da hannu a case ɗin, a yau nake so komai ya ƙare, bana son ɓata lokaci!."
Yadda Rehaan yake maganar cikin ba da umarni ya saka Jazy ya buɗe ido ya ce, "Okay Sir! Za mu yi duk yadda ka ce, zamu tabbatar sun san wacce suka taɓa."
Yanayin da Jazy ya amsa ya saka Ray ya yi tsaki, ya É—auki waya ya kira É—aya daga cikin DSS É—in da ya sani.
Safeera ta koma kusa da Islaha tana rarrashinya, Jazy dai yana tsaye yana kallon ikon Allah ganin Mr Rehaan an faɗa tarkon love, shi kuma ya saka waya a kunne yana magana cikin ba da umarni, kuma a ranar yake so a kama su, ba ya son ɓata lokaci.
Jazy ya murmusa kawai bai ce masa komai ba ya kalli Islaha ya ce, "Miss ki daina kukan nan, in sha Allah duk wanda ya ke da hannu a aikata wannan abun zai zo hannu, tunda har Ogan ki ya shiga maganar ki É—auka an gama."
Islaha ta kallesa da jajayen idanunta da suka yi nauyi ta ce, "da gaske ni ce a jikin hoton?."
"Ki daina kuka, kin ga kin samu attack bai kamata ki dawo da maganar ba. Safeera ki je da ita sama ta huta."
Tana niyar ɗagata Mamy ta shigo falon ta ƙarasa inda islaha ta ce, "Sannu Daughter..." sai kuma ta kalli Rehaan ta ce, "Rehaan!."
Ya kalle ita ta ce, "ina so ka saka a yi bincike akan wanda ya yi posting hotuna da videos É—in nan, ni na san ba Islaha ba ce, haÉ—awa aka yi."
Islaha jin muryar Mamy sai ta sake fashewa da kuka ta ce, "Mamy da gaske ni ce ko?."
Mamy ta shafa kanta ta ce, "in ma ke ɗin ce duk wanda ya yaɗa dole ya shiga hannu, muna da ikon yin shari'a da shi akan hakan, balle ba ke ba ce. Ki daina ɗaga hankalin ki, babu abinda zai same ki. Ina tare da ke, Rehaan yana tare da ke, Jafar da ƙawarki duk muna tare da ke. In kaf gidan nan zasu juya miki baya, mu zamu riƙe ki hannu biyu, babu wanda zai wulaƙanta ki ya zauna lafiya, kuma babu wanda zai saka Rehaan ya sake ki matuƙar ina da rai. Waɗanda suka haɗa kuma zasu yi danasani, sai sun san wacece ke, sai sun san kina da gata, sai sun san sun taɓo wacce ta fi ƙarfinsu wallahi."
Mamy ta sake kallon Rehaan da yake tsaye ta ce, "Ka yi abinda ya kamata, Jazy please, don Allah kar ku bar kowa a cikin case É—in, ina so su san wacece Islaha a cikin garin Yola. Jafar ko cikin mahaifiyarsu suka koma, ina so a fito dasu a nuna musu wacece Islaha!."