← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 110

Sashe 48

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mamy ta buÉ—e idananu ta ce, "Lah! Kai ma ba ka san ya gudu Uk ba kenan?."

Jazy cikin mamaki ya ce, "bai faÉ—a min ba Mamy."

Mamy ta yi dariya ta ce, "Ai yanzu haka ma bacci take yi, na tabbatar ya jima da shiga England."

Jazy ya zauna ya ce, "Ya kyauta, tare fa nace za mu tafi, shine ya gudu." Mamy bata ce komai ba sai murmushi da ta yi.

Jazy ya kalli Islaha suka haÉ—a ido, sai ta ce, "Ina yini, Mr Jafar."

Jafar ya ce, "Hajiya Islaha, ya ki ke?."

Islaha ta sake kallonsa jin ya saka mata hajiya a gaban sunanta, sannan tana mamakin yadda dukkansu suka saba da faÉ—ar ya ki ke ko ya ka ke, har Mamy. Ta ce, "Lafiya lau."

Mamy ta ce, "tana jin tsoron can, shiyasa na ce ta zo nan ta kwanta kafin ya dawo."

Jazy ya ce, "hakan ya yi kyau."

Mamy ta kalli Riyya tana nuna mata Islaha ta ce, "Riyya ga Islaha, sunan da suka mata kuma Islam, matar Yayanki."

Riyya ta kalli Islaha sannan ta ce, "na san fuskar ta, amma na manta a ina."

Jafar ya ce, "zaki santa, tana aiki a gidan tv."

Riyya ta ce, "Sannu Sis, ya ki ke?."

Islaha ta kalli wacce ake kira Riyya ɗin, sai ta tuna yadda Rehaan ya dinga yiwa Jafar masifa akan abinda ya yi mata. Ita yadda ya dinga masifa ta yi tunanin Riyya ɗin yarinya ce ƙarama, irin wacce bata wuce shekara sha bakwai ɗin nan ba, sai ta ga zata kai age mate ɗinta. Duk da bikinta ya yi trending a social media, amma da makeup a fuskarta bata gane ta ba sai yanzu da ta ganta babu kwalliya, tana ta girmama kyaun da iyalan Mamy suke da shi.

Islaha ta ce, "Lafiya lau Sis" ta faÉ—a dan ta ga sun mayar da faÉ—ar sis kamar ruwa a bakinsu.

Shigowar Janan ya sake hargitsa wajan, suna ta ihun ganin juna kafin su shiga É—akin Riyya gabaÉ—ayansu. A lokacin aka gama gyaran É—akin, Islaha ta shiga É—akin dan zaman falon takura mata yake yi.

Bayan ta shiga ɗaki Mamy ta kalli Jafar ta ce, "Tunda ka faɗa min wacece yarinyar nan sai nake jin sauƙin haushin auren da nake ji, sai na ke ji tana shiga raina sosai har na ke burin Rehaan ya karɓe ta a matsayin matarsa, dan na lura bata da hayaniya."

Jazy ya ce, "Mamy islaha bata da damuwa ko kaɗan, kuma a kwanakin da zata yi a nan, zaki fahimci wacece ita, za ki iya sakawa ayi miki ɓoyayyen bincike a kanta, zaki fahimci abinda ta saka a gaba, wanda ko kaɗan babu Rehaan a ciki."

Mamy ta É—aga kai ta ce, "Zan yi hakan, kafin ya dawo ina so na tabbatar da wacece ita."

Jazy ya ce, "Hakan ya yi kyau Mamy" daga haka ya miƙe ya fita.

Su Riyya kuwa suna É—aki sun saka Ikram a gaba akan soyayyar da take yiwa Rehaan, Riyya ta ce, "Ikram ya dai, har yanzu da batun Hamma Ray É—in?."

Ikram ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Riyya ban san ya zan yi ba, amma ina sonsa sosai, gashi kuma ya riga ya yi aure."

Janan ta ce, "Ina ruwan mu da aurensa, in dai zai aure ki ba shikenna ba?."

Riyya ta ce, "Kuma ba son auren nan yake yi ba, sannan matar ba type ɗinsa ba ce. Ƴaƴan gidan nan, da matan gidan nan, da sirikai gabaɗaya dukkansu farare ne tas, ita kaɗai ce mai irin wanann skin type ɗun, kin ga bata dace da shi ba."

Ikram ta ce, "Amma tana da kyau, tana da kyaun da ni kaina na gani kuma na tabbatar. Ga wani gashi da take dashi, mai yawa da tsaho. Riyya duk gashin ki, kin ga dai kaf gidan nan kin fi kowa gashi ko? To ko ke baza ki nuna mata yawan gashi ba. Wani irin gashi ne da ita mai kyau, ga tsaho har baya."

Riyya ta buÉ—e ido ta ce, "Da gaske?."

"Wallahi, ni na gani a falon Mamy. Ta zo gaishe da Mamy Hamma Salman ya shigo ya ja mata mayafi har ribbon É—inta ya faÉ—i. Kin ga yadda gashin ya buÉ—e har fuskar Hamma Ray ya sauka. Hmm! Ni na fara giving up, duk da na san ba sonta yake yi ba, amma tana da qualities É—in da zai iya sonta nan gaba."

Janan ta ce, "Ai Mamy a ɓangarenmu ta ke, zaki iya aurensa ko dan ita."

Ikram ta ce, "Mamy ta fara sakkowa, da dai bata son auren, amma yanzu kamar ta yi accepting."

Riyya ta ce, "Gaskiya Daada bata kyauta mana ba data ƙaƙaba masa wannna auren, yanzu da ke ya aura ba shikenan ba?." Ikram ta yi shiru kawai bata ce komai ba, suka cigaba da tattaunawa kafin su fito daga ɗakin.

Nana Haleema.

RDB3P38
Nana Haleema.

Da suka fito ta ƙofar ɗakin da Islaha take suka zo wucewa, ta saka doguwar riga ta bacci wacce ta wuce guiwa da kaɗan, rigar tana da shape dan bata buɗewa, bin jiki take yi ta kwanta a ko ina. Ta saki gashinta har baya, tana tsaye ta juya baya bata san suna kallon ta ba.

Ikram ta ce, "Kun gani ko, na faÉ—a muku daman ta haÉ—u."

A lokacin Islaha ta juyo suka haɗa ido dasu, sai suka basar kamar ba kallonta suke yi na, Riyya ta shiga ɗakin ta ce, "Ma sha Allah, Sis kina da gashi mai kyau" ta faɗa tana taɓa gashin dan ya burge ta sosai.

Islaha ta murmusa tana saka hula bata ce komai ba, ta zauna a gefen gado bata ce komai ba.

Riyya ta ce, "Bara mu je wajan Mamy." Da kai ta amsa suka fita ta bisu da kallo ta sauke ajiyar zuciya kawai.

Washe gari Islaha bata farka ba sai ƙarfe goma na safe, ta tashi ta yi wanka ta yi alwala ta yi sallar walha, ta ɗauki wayarta ta kira Barr Suraj bai ɗauka ba, ta ajjiye wayar kawai ta yi shiru.

Apartment ɗin shiru, babu motsin kowa alamun bacci suke yi, sai ta miƙe dan tana so ta je apartment ɗin Ray ta ɗauko laptop ɗinta, ta saka hijjab akan doguwar rigar jikinta ta fito. Ko ina ƙhamshi yake yi, ta ƙarasa falo na biyu kafin ta fito main parlour ɗin.

An gyara shi ya yi tas sai ƙhamhasi yake yi, ko ina haske babu alamun kowa bacci yake yi a ɓangaren.

Motsi ta ji a bayanta sai ta juya sai ta ga Mamy ta fito daga kitchen, duk da sun gaisa da asuba sai da ta sake gaishe ta.

Mamy ta amsa ta ce, "Har kin tashi?."

Islaha ta ce, "Eh."

Mamy ta ce, "Ga breakfast nan in kina so."

Islaha ta ce, "To Maamy."

Mamy ta kira mai aikinta ta ce, "Ki gyara min irish É—in nan, kafin na fito a gama, bana so Dear ya ta shu ban gama breakfast ba."

Islaha ta zaro ido jin wai Dear, ta kalli Mamy tana girgiza kai cike da mamakin sunan, dan dai ta san iyaye da an girma za a koma cewa abban wance.

Mamy ta kalli Islaha ta ce, "in akwai abinda ki ke so ki ki faÉ—a musu sai a dafa miki." Islaha ta amsa Mamy ta juya ta shiga ciki.

Islaha ta fita zuwa apartment É—in tana fatan kar Allah ya haÉ—ata da Salman, har zata wuce sai ta fasa ta nufi wajan Daada da niyar gaishe ta.

Tana dhiga ta same ta tana shan tea a zaune akan kujera, tana ganinta ta sjjiye cup É—in tana tafa hannu ta ce, "Ga islama, ga Ishlaya."

Islaha ta yi murmushi ta ƙarasa har ƙasa ta gaishe ta, ta kalli Abba da wani babban mutum da yake zaune, ta gaishe su da girmama suka amsa.

Abba ya nuna ta ya ce, "Itace matar Rehaan, na san baka santa ba."

Yayan Abba ya ce, "Allah Sarki, kamar na san ki."

Daada ta yi caraf ta ce, "Æ´ar jarida ce, ana haskota a ko ina."

Ya É—aga kai ya ce, "Tabbas a nan na santa kam,
Allah ya taimaka."

Daada ta ce, "ance min a wajan Nadira ki ka kwana ko?."

Islaha ta ce, "eh Daada, ina jin tsoron can ne, shine ta ce na je na kwanta a wajenta."

Daada ta riƙe baki ta ce, "Tunda nake da ƴar indian a gidan nan bata taɓa yin abinda ya burge ni kamar wannan ba, ashe su ma indiyawan sun san ya kamata, ba a yawon tsafi suka tsaya ba."

Yayan Abba ya ce, "Haba Daada, ki bar wannan maganar mana."

"Ƙarya na yi? Ai halinta ne. Farkon aurensu da ƙanin ka a ƙasar waje ta riƙe sa ya daina zuwa gaishe ni, sai da na miƙe tsaye da addu'a na ƙwato shi."

"Daada ai kin ƙwato ɗin ko?."

"Gashi a gabana kana gani."

"Hakan ma mun gode Allah" ya faɗa yana miƙewa ya ce, "Daada zan koma, ya sunanki?" ya faɗa yana kallon Islaha.

Maimakon Islaha ta amsa sai Daada ta ce, "Sunanta Islama."

Abba ya yi dariya ya ce, "Sunan al'ada ne wannan, amma sunanta Islaha."

Ya É—aga kai ya ce, "Ma sha Allah, ya kamata a kawo ta ga Æ´an uwa, na tabbatar bata san kowa ba."

Daada ta ce, "kai da yake babansa ne sai ka faÉ—a masa ya amince, amma ni ai ya raina ni. Yanzu ba ya ganin darajata, ban isa na faÉ—awa Rehaan magana ta ji ba. Wacce ni, ni kaza?." Bai ce komai ba ya murmusa ya fita.

Mata ne guda biyu suka shigo falon da sallma hannun ɗaya riƙe da yaro. Kana kallon fuskar ɗaya ba sai an ce maka jinin Umma ba ce, kamar su ta fito da Umma sosai, hannunta riƙe da hannun yaro guda ɗaya.

Tun kafin su ta ƙaraso Daada ta ce, "Bana neman ku, ku koma."

Mai kama da Umman ta ɗan ɓata rai ta ce, "Daga zuwa abin kirki."

Sai kuma suka kalli Abba suka gaishe sa, ya amsa sannan ya ce, "Ya gidan da masu gidan?."

"Suna lafiya lau, Wannan wacece?" Anisa Æ´ar Mama ta faÉ—a tana nuna Islaha.
Chapter 48 · 0% Book details