← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 110

Sashe 23

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jazy ya ɗora ƙafa kan ɗaya ya ce, "wai ko kana kishinta ne?” Ya faɗa yana kallonsa dan yanayin yadda ya damu da maimaita magana ɗaya a kanta sai zuciyarsa take faɗa masa kishi ne…

Nana Haleema.

RDB3P19
Nana Haleema.

Rehaan matcha ɗin da ya saka a bakinsa sai da ta dawo saboda yadda maganar ta dake shi, ya sarƙe yana tari kafin ya nutsu ya ce, "kishin wa? Ka taɓa ganin ana kishin irinsu ne daman?."

Jazy ya ce, "Abin ne da mamaki, ba ka da magana sai maimaita yarinyar Ubaid ce, in ba kishi ka ke yi ba me ka ke yi? Wanda ake kishi ake yiwa irin abinda ka ke yi a kanta.”

“Ba ka da hankali Jazy, yarinyar da har miscarrige ta yi na yi kishinta na ce ina kishin wa?.”

“Sai ka yi ai Rehaan, matar ka ce yanzu, in ma ƴar iska ce kaima ka zama mijin ƴar iska."

"Da na ga ranar da zan yi kishin wannan abin gwara na ga ranar mutuwata. Allah ba dan Abba ba, da yanzu bata cikin gidan nan. To na riga na yi masa alƙawari, da baza ta yi 48 hours a gidan nan ba. Bana son saɓa alƙawari shiyasa."

Jazy ya murmusa ya ce, "ka daina badmouthing É—inta, ba ka sanin a inda za ka amfana da wani a rayuwar ka."

"To ban da ita. Ya isa, mu bar zancen nan kawai."

Jazy ya yi shiru bai sake magana ba, amma a ransa yana fatan Allah ya kawo ranar da Ray zai yi danasani akan kalamansa. Dan shi ya yaba da Islaha sosai, yana yi masa fatan zama da ita, dan kowa ya san ba dan kuÉ—insa ko É—aukaka a auresa ba.

Jazy ya miƙe ya ce, "kai ka sani kuma, ni zan tafi wajan matata." Ray bai ce masa komai ba ya cigaba da kaɗa ƙafarsa.

A lokacin Islaha ta fito daga É—aki ta kalli Jazy ta ce, "Mr Jafar zan iya tambayar ka?."

"Ina jin ki Mrs Ray."

Ta wani kalle sa ta ce, "Islaha sunana, ko ka ce miss É—in, amma ka daina kirana da abinda ka ce, wallahi bana so."

Ya murmusa ya ce, "ina jin ki Miss."

"ina kana zargin wani abu mara kyau daga wani waje haka ina ake kai report?."

"Kamar wanne abu kenan? Kin san komai stage by stage ne, ko wanne da side É—insa."

"Kamar kana zargin cin zarafin mata, da safara dasu da sauran su dai.”"

"Okay. National angency for the prohibition of trafficking in person (NAPTIP). Su ake kaiwa irin wannan report É—in."

"Suna da office a nan Yola?."

Ya É—an yi shiru yana tunani ya ce, "gaskiya babu. Ina tunanin Abuja, kano, lagos etc. Amma babu a nan, but za ki iya kiransu a daga inda ki ke. Abinda ake so make sure kina da evideance akan abinda za ki yi reporting."

Ta É—aga kai ta ce, "na gode." Bai ce komai ba ya wuce ta ya sauka.

Sai kuma ta bi bayansa a last stair ta tsaya ta ce, "Mr Jafar."

Ya kalle ta ta ce, "Alƙawarin da muka yi dakai a farkon haɗuwar mu, shi nake so ka cika min."

"na me kenan?."

"Interview da Rehaan Yola."

Ya yi wata dariya yana kallon ta ya ce, "Miss Islaha, ai na fita daga wannan contarct É—in, yanzu kin fi ni kusa da shi."

Islaha ta haÉ—e rai ta ce, "Don Allah ka bar wasa, da gaske nake."

"nima da gaske nake Miss, kawai ki zaɓi rana ki zo gida ki saka masa camera shikenan fa."

"Please."

Ya sake yin murmushi ya ce, "Shikenan Miss, zamu yi maganar da shi."

"na gode. Amma don Allah kar ya san ni ce presenter sai ranar, bazan iya taking rubbish É—insa ba." Ya sake yin murmushi ya É—aga mata kai ya fita ita kuma ta koma sama.

Da ta koma É—aki laptop ta É—auko dan ta fara tura mails É—in da Chairman ya bata. Tana shigar da report É—insu na É—azu dan gobe za a gabatar da news É—in. ÆŠakin babu network yadda ya kamata, sai ta tuna bata gan shi a falo ba, ta saka hijjab ta dawo falon ta zauna tana aikinta.

Har ya fito ya zauna bata sani ba, aiki kawai take yi sai kuma ta dakata ta É—auki waya ta kira Saleem suka É—an jima suna magana, kafin ta kashe ta cigaba da danne danne ta. Ta jima a haka kafin ta É—an jingina da kujera tana jan numfashi na gajiya.

"Im so tired."

Islaha ta ji ya faÉ—a, da sauri ta kalle sa ta ga babu abinda yake yi amma wai ya gaji.

Ta yi ƙaramin tsaki ta ce, "ragon maza kawai, wannan shine ya rako maza duniya, komai nasa irin na mata ne, ko ni na fi sa ƙarfi da kuzari" ta faɗa ƙasa ƙasa tana cigaba da aikinta.

Wayarsa ta yi vibrating ya kalla ya ga Abba ne sai ya miƙe zaune sosai ya ɗaga, Abba ya ce, "Ta dawo?."

A ciki ya ce, "Eh."

"Kai da ita ku zo ina son ganin ku."

Ya É—aga kansa sanann ya ce, "To." Daga haka ya kashe wayar.

Ya kalle ta ya ga ba shi take kallo ba ta mayar da hankali akan aikinta kawai.

Ya yi tsaki ya rasa ta ina ma zai iya yi mata magana, dan shi ko kallon ta baya so balle ya yi mata magana. Ya sake kallon ta ya ce, "let's go."

Ta kalle sa ta ƙasan ido suka haɗa ido, bata janye ido ba duk da yadda idanunsa yake rolling a kanta bai saka ta ɗauke ba. Ta mayar da kanta zuwa ga abinda take yi kamar bata ji ba.

Ya bita da kallo ganin ta raina masa hankali ya ce, "Ba ki ji ba?."

Islaha ta É—ago ta ce, "dani ka ke?."

Saboda takaici da rainin hankalin da ta yi masa bai san lokacin da ya ce, "A'a, da kaina nake."

Jin amsar da ya bata sai bata sake magana ba, ta cigaba da abinda take yi tunda ya ce da kansa yake.

Ray ya zuba mata ido kawai yana kallon ta, babu wata macen da ta take latsa shi kamar ta, tunda ya ke a duniya babu macen da ta ke mayar da shi kamar wani banza sai ita. Ita kaÉ—ai ce ta ke kallon idonsa ta faÉ—i duk abinda ya zo bakinta, ita kaÉ—ai ce yana magana tana mayar masa, ya rasa me ta gani a cikinsa da ta yi saurin raina sa haka.

Amma bazai yi mamaki ba, tunda ya san wacece ita, rashin kunya da raina maza a wajan irinsu ba komai bane, tunda ido ya buɗe ta saba da maza kala-kala. Jin shirun ya yi yawa bai ce komai ba sai ta kalle sa, ta ga ya harɗe hannu a ƙirji kawai yana kallon ta.

Islaha ta ɓata rai ta ce, "wannan kallo ya fita daga musulunci, a dinga sassautawa, ni ba maharramarka ba ce."

Ya buÉ—e ido kaÉ—an ya ce, "me zan kalla?."

"Abinda ka ke kallo yanzu."

"Na kalli me, abinda ya rage?."

Ta ɗaga ido tana kallonsa sai ta ga ya miƙe tsaye kamar ba shi ya yi maganar ba.

Ranta ya ɓaci sosai, dan tana jin haushi in ya ce mata ragowar nan, kalmar tana tsaya mata a rai sosai. Ta girgiza kai ta ce, "Ai ka san ragowar ma kala-kala ne, akwai ragowar da ta fi sabo daraja da ƙima, akwai ragowar da ta sabo tsada. Ko ban faɗa ba, ka san ni da nake ragowar na fi sababbi da yawa tsada. Shiyasa ka ke morewa lokacin ka da ƙaramar damar da ka samu ta kallona. Ban ga laifinka ba, ka kalla son ranka, lokaci kaɗan ya rage maka kallon ya gagari idanunka."

Bai amsa mata ba ya share ta magana da ita ma sai ya ji kamar yana zubar da class É—in da ya ke da shi ne, In ya tuna har zubar da ciki ta yi sai ya ji komai ya fice masa daga rai gabaÉ—aya.

Bai ɗauki wayarsa ba ya yi hanyar sauka, sai ta ji tsoro ya shige ta, kuma daman ya ce tazo su je. Ta miƙe da hanzari ta bi bayansa ta samu yana dab da fita daga apartment ɗin.

Islaha harare sa ta ce, "ji wata tafiya kamar ta mata, shi wannan gabaɗaya da mace ya yi kama, da zai saka kayan mata da ya saje damu, babu ƙarfi a tare dashi ko kaɗan." Yana fita ta bi bayansa a hankali har ya shiga ɓangaren Abba.

Ta ja ta tsaya bata shiga ba Abba yana kallonta ta window ya kalli Rehaan ya ce, "ka ce ta shigo."

Rehaan ya koma ya buɗe ƙofar sai ta ji muryar Abba ya ce, "shigo mana."

Ta shiga a nutse tare da yin sallama. Abba ya amsa yana nuna mata wajan zama ita kuma ta zauna.

Islaha ta ce, "Ina yini."

"lafiya lau amarya, ya gida?."

"Alhamdu lillah."

"Ina ki ka je da safe?."

"wajan aiki na je" ta faÉ—a a sanyaye.

"Meyasa ba ki faÉ—a za ki je ba ki ka hau napep?."

Ta yi shiru bata amsa ba dan bata san me zata ce ba. Abba ya ce, "Ko nan gaba kar ki sake, gidan nan ba a hawa napep, akwai direbobi da yawa da zasu kai ki duk inda ki ke so, kin ji ko?."

Islaha ta ce, "To, in sha Allah bazan sake ba."

"Yauwa haka nake so na ji."

Abba ya kalli Rehaan ya ce, "Kai kuma laifin ka ne, ka san ai tana zuwa aiki, na faÉ—a maka maganar nan tun ba yau ba, gudun maganar Daada sai ka samu wanda zai dinga kai ta yana dawowa da ita. Yanzu ga shi nan ka tarawa kanka baki da magana a gidan nan."

Ya kalli Abba ya ce, "Abba ni ban san da aikin ba, kuma ni na manta muna tare da ita."

Abba ya harari Rehaan jin abinda yake faÉ—a a gabanta, a ganinsa kamar cin fuska ne ya faÉ—i haka a gabanta.

Abba ya kalli Islaha da bata ɗago ba ya ce, "Jafar ya faɗa min ya nemi driver da zai dinga kai ki, gobe ƙarfe nawa za ki tafi?."

"ƙarfe bakwai."
Chapter 23 · 0% Book details