← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 110

Sashe 49

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daada ta harare ta ta ce, "Matar ɗan uwanki guda amma ba ki santa ba, kun raba kan ku da shi kamar ba jininku ba, kowa sai ɗan ɗakinsa yake zumunci da shi, kowa sai wanda babarsa ta haifa yake cewa shine ɗanuwansa. Duk son zumunci irin na Rehaan, kun saka ya ajjiye ku gefe kamar yadda ku ka ajjiye sa. Sai biki ya tashi, ka ga anyi anko ana hotuna kamar masu haɗin kai, nan kuwa kan ku a tarwatse yake. Sai ya yi aike da kuɗi kuma a amshe a saka a jaka a ƙara gaba. Duk abinda ku ka saka a ranku ku kuka sani, in Allah ya so ɗaukaka wani babu wanda ya isa ya hana, kuma da wahala a cikin dangi baka ga Allah ya ɗaga wani bar wani ba, ko da shine ɗan auta a dangin gabaɗaya. Shi Rehaan ta sa ƙaddarar sai ta zo akan ƴam uwa, musamman ku matan da ya fi sonku, amma ku ne ku ke watsa masa yaji a ido. Allah wadaran naka ya lalace."

Duk sai suka haɗe rai cikin danasanin shigowa ɗakin Daada, Abba yana ji bai ce komai ba dan ya san gaskiya take faɗa, Rehaan ya ce masa in aka cire Janan da ƙananun yara ƴaƴan amaryarsa guda biyu, mantawa yake yi yana da ƴan uwa mata yaye da ƙanne. Duk yadda ya so su sake da shi sun ƙi, sun watsar da shi shiyasa shima ya jingina su a gefe, kowa ya yi rayuwarsa yadda yake so. Kuma da ba haka suke ba, daga baya ne suka canja gabaɗaya, kuma kowa babarta ce take zugata.

"Ni fa Daada shiyasa bana son zuwa wajan ki wallahi. Kuma da ki ke zancen ba mu san matarsa ba ai ba a ɗauke ta an kai mana ita ba, tunda mu ne gaba da shi ba shine gaba damu. In da an kai mana ita har gida da mun santa har mun ƙulla zumunci."

Daada ta yi tsaki bata ce komai ba, Islaha dai tana ji tana sake tabbatar da kan ƴam gidan a watse yake gabaɗaya babu haɗin kai. Amma a social media in suna biki in ka ga yadda suke shan anko su yi kyau sai ka ɗauka akwai zumunci mai ƙarfi a tsakaninsu, ita dai tana ta ɗaukar darasi a gidan, ta gama na haddace na gidansu Saheer ga sabo ta samu.

Anisa da Sharifa suka fita daga falon Daada ba su sake kula ta ba. Bayan sun fita ta kalli Abna ta ce, "Laifin ka ne wallahi, kaine ba ka yi musu faɗa, kamar ba kai ka haife su ba, ko wacce tana iskancin da ta ga dama." Abba jin laifin zai dawo kansa sai ya miƙe ya yi mata sallama ya fita.

Daada ta kalli Islaha, "Ishlaya kaf gidan nan babu mai son mijinki a cikin ƴam uwansa, daga Janan sai na wajan amaryar babansa, su kuma yara ne basu girma sosai ba. Sun ɗauki wani abu sun saka a ransu, tun yana bibiyarsu akan zumunci har ya gaji. Mutum ne mai son ƴan uwansa, yana da son ya kyautata musu sosai, duk sati akwai kuɗin da yake warewa na zuwa siyayya, duk da suna da aure bai daina basu ba, duk juma'a sai an ba da wannan kuɗi. Kuma duk ranar da ɗaya a cikinsu ta yi niyar barin ƙasar nan, waya kawai take yi masa, babu ko sisinta za je ta dawo. Yana so ya yiwa ƴan uwansa alkhairi su ji daɗi, yana so ya ji suna alfahari da kasancewarsa ɗan uwansu, yadda duniya take faɗar sunansa su kuma su yi alfahari da shi. Amma baƙin hali ya hanasu, kowa da abinda ya ƙudurce a ransa, kamar shine ya bawa kansa arzuƙin."

Islaha tana jin Daada tana mamakin yadda ƴan gidan ba sa iya riƙe sirrinsu, komai faɗa suke a gabanta, basa tunanin ita baƙuwa ce a cikinsu.

Islaha ta ce, "Allah ya kyauta."

Daada ta ce, "Amin Ishlaya. Ke dai ki riƙe mijinki, ki zama masa inuwar da zai sha iska in ya kwaso rana."

Islaha jin an fara yi mata wa'azi akan abinda baza ta iya ba sai ta miƙe ta ce, "Daada zan koma, sai anjima." Suka yi sallama ta nufi apartment ɗin har lokacin ko jikokin gidan babu kowa bacci yake yi.

   Mama tana kallon fitowar Islaha ta window, tunda apartment ɗin Daada yana kusa da nata.

Ta yi tsaki ta ce, "Shegiyar yarinya ƴar bariki, da iyayin tsiya da yauƙi kamar wata kuɓewa, ko waye ya aike ta ta je ta gaishe da Daadan oho.

Na lura Nadira so take ta ɓata min gari, ta fara jan yarinyar nan a jikinta, billahillazi bazai yu ba, ba a banza na bari auren nan ya yu ba sai dan ƙudirina. Dole na san abinda ya kamata na yi, dole na yi abinda kowa zai farka daga dogon baccin da yake yi."

"Mama."

Kiran sunanta da ya saka ta ta juyo ta ta ga Æ´arta ta biyu mai bin Zayyad ta ce, "Ke kuma lafiya ki ka fito da safiyar nan?."

Anisa ta zauna tana haÉ—e tai ta ce, "in dai na zo gidan nan na je gaishe da Daada shine damuwata, mun shiga ni da Sharifa dan mu gashe ta, mu ka tarar da matar yaron nan Rehaan. A gabanta kin ji abinda take faÉ—a mana? Wai ba ma son Rehaan, kuma Allah ya É—aukaka shi....."

"Mama dama ana iya ɗauke ɗaukaka, da na ɗauki ɗaukakar nan na dawo da ita kan Hamma, ko Sameer ko Daady ko Amir. Haba, wannan baƙar magana har ina?."

Mama ta gyÉ—a kai ta ce, "Shi ma É—aukakar zata gushe Anisa, É—aukakarsa zata gushe indai ina da rai."

"Daman wannan itace wacce aka aura masa, ai na santa sosai. Babansu Khalifa yana son program É—inta, Indai zata yi program ko ya yi missing a tv sai ya bibiya a youtube."

"Shegiyar yarinya mai iyayin tsiya ba, itace matar da aka aura masa. Mai buÉ—aÉ—É—en ido, karuwa mai lasisi."

"Karuwa kuma Mama!."

"Ita fa, har aikatau ɗin ƙasar waje ta yi. Kuma gidan da ta ke zaune woman leader ake ceewa matar gidan, tantiriya ce lamba ɗaya."

"Amma aka auro ta gidan nan?."

"Ni na saka a yi hakan."

"Akan me kenan?."

"Akan Rehaan mana, da ita zan yi amfani na lalata rayuwarsa."

Anisa ta ce, "ta wacce hanya kenan?."

"Ta hanyar ta yarda dani, ni kuma zan bata abinda zata dinga ba shi kullum har ya bi jikinsa."

Anisa ta ce, "amma kin san Mamy baza ta yarda ta amince da ke ba."

Mama ta murmusa ta ce, "Ke dai mu je zuwa, Nadira É—in banza da wofi, wallahi sai na ga bayan Rehaan. Ni ba kisan kai zan yi ba, amma wannan É—aukakar sai ta gushe, sai an daina jin labarinsa, sai duniyar ta tsaya masa cak. Anisa in kina musu ku rubuta ki ajjiye!."

Anisa ta yi murmushi t ce, "ni na san za ki iya Mama, É—aukakar nan tasa da Æ´aÆ´anki ta cancanta ba ahi ba. Yadda gidan nan yake a hannunki, Abba ma a hannunki, babarsa ta ke a hannuki, kishiyoyin su ke a hannunki, dukiyar mai gidan ta ke a hannun Æ´aÆ´an li. Kamata ya yi ace sunan É—akin ns ya yi tambarin da sunan da na Rehaan ya yi, É—aukaka da ke ta dace ba da Rehaan ba."

Mama ta yi dariya ta ce, "da zarar Rehaan ya yi ƙasa, to tabbas na ci gari."

"Ki buÉ—e wuta Mama, dan kullum kasuwancinsa sake gaba suke yi, in ba mu farga ba sai dai mu buÉ—e ido mu ga mun zama ma su goge masa takalmi."

Mama ta yi murmushi tana girgiza kai cikin mummunan ƙuduri ta ce, "a yi dai mu gani........

Nana Haleema

RDB3P39
Nana Haleema.

Saheer yana zaune a falon Mama yana cin abinci, gabaɗaya ba shi da walwala ko kaɗan, a hankali yake cin abincin kamar wanda aka yiwa dole, duk loma ɗaya da zai bakinsa Sudaisa yake ganowa a idanunsa, yana tunanin tana can suna bata abinci mara tsafta suna dukanta. Yana tunanin ko ya suka ƙare da black, ko ya suka ƙare da Arɗo bai sani ba. Wani lokacin sai ya ji kamar ya koma ya gano halin da take ciki.

Baffa da yake zaune ya kalle sa ya ce, "Saheer yaushe za ka koma aiki?."

Saheer ya kalli Baffa ya ce, "Na kusa in sha Allah, ina so a gama haÉ—a gidan can gabaÉ—aya, in ya so sai na koma."

Mama ta yi caraf ta ce, "Abinda ba aure za ka yi ba, gidan me za ka takura kanka sai ka gama?. Ko ka kai kuÉ—in aure an saka rana ne?."

Ya kalli Mama ya ce, "So nake na kammala gabaÉ—aya na huta kawai."

Baffa ya ce, "ya kamata ka koma wajan sana'arka, ka cigaba da addu'a, Allah ya cigaba da kiyayewa." Ya amsa da amin ya ajjiye abincin ya fita.

Haka kawai yake jin kewar Islaha a zuciyarsa, idanunsa ita suke so su gani, kunennsa suna so su ji muryarta, yana son ganinta matuƙa, kewarta ta dabaibaye masa zuciya da gangar jikinsa.

Ya shiga É—aki ya dafa bango yana ji zuciyarsa tana harbawa sosai, ya kasa cire son Islaha daga ransa, duk da ya san akwai auren wani a kanta, son da yake yi mata zunubi yake É—aukarwa kanaa amma ya rasa yadda zai yi da zuciyarsa. Zuciyarsa itace take sarrafa shi ba shine yake sarrafata ba.

Yana ji wayarsa tana ringing har ta katse bai É—auka ba, aka kuma kira a lokacin ya É—auka ba tare da ya duba ya ga waye mai kiran ba.

Daga can ɓangaren aka ce, "Saheer ka shirya karɓar kuɗin ko ba ka shirya ba?."

Ya É—an yi jim yana tunanin su waye haka, kafin ya gama tunani aka kuma cewa, "Naira miliyan biyu taka ce, indai ka amince da abinda za ka yi mana."

Saheer ya yi tsaki ya datse kiran, ta ya zai iya wannan abun mai kama da ganganci? Haka kawai ya jefa rayuwar Islaha cikin hatsari bata ji ba bata gani ba. Kuma in ya yi hakan kamar ya ci amanar ta ne, shi kuma bai shiryawa hakan ba.
Chapter 49 · 0% Book details