← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 110

Sashe 45

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yanzu kuma kin aikata, a cikin garin nan da unguwar nan da kin aikata wannan abun ba komai bane, yawancin matan da ki ke gani suna fantamawa da kuɗi harkar nan suke yi, ɗaiɗaiku ne ba sa yi. Kuma ba daina bin mazan za ki yi ba, za ki cigaba da yin duk abinda ki ke so normal ne, in kina son larabawa kamar su Ubaid duk samu. Labiba tunda ki ka zo nan baza ki samu matsalar kuɗi ba, in dai za ki bayar za a ba ki. Kawai ki ɗaura belt, in macen ce ta zo ki karɓe ta hannu biyu, in namijin ne ya zo shima ki karɓe shi hannu biyu, in duka ne suka zo lokaci ɗaya ki haɗa."

Labiba ta É—ago ta kalle ta ta ce, "Na haÉ—a fa?."

"to sai me? Gajiya kawai za ki tarawa kan ki, da kin watsa ruwa kin yi bacci shikenan komai zai wuce. Sau nawa muna haÉ—a mata biyu lokaci É—aya? Sau nawa muna haÉ—a maza biyu lokaci É—aya?. "

"Ban kai nan ba Aisha."

"Za ki kai ne, ai tunda ki ka zo nan a hankali idanunki za su buÉ—e. Ni ma da haka nake faÉ—a, amma yanzu ga shi na waye, ko maza biyar ne zan iya dasu lokaci É—aya. Burina kawai a bani, indai za a bani na cika jakata an wuce wajen."

Labiba ta yi shiru bata ce komai ba Aisha ta ce, "Ki miƙe ki nemi kuɗi, ko a gidanku sai kana da kuɗi ake yi da kai."

"Kuɗi na zo nema, amma gwara na fara sana'a kamar yadda kowa yake yi, akan na sake anincewa da wannan ƙazantar."

"kina tsaka soyawa ko dafawa za a zo a tashe ki, in aka yi rashin sa'a aka cafke ki sai nigeria, abinda ki ka tara ya tashi a banza da wofi. Labiba ban da ke ban taɓa kawo wata gidan nan ba, amma ke saboda akwai amana na kawo ki  saboda a amfana." Labiba ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba.

Aysha ta ce, "Ki É—auki abinci ki ci, ki yi wanka ki zo ki raka ni kasuwa na yi siyayya. Ki saki jikinki, ba wani abu mai muni ki ka yi ba, neman kuÉ—i Mama ta turo ki, kuma ga shi kin samu. Ki duba account É—inki, na mayar miki da kuÉ—in zuwa naira na saka miki. WaÉ—anan da suke hannun ki tunda suna da yawa za a iya mayar miki dasu naira ki saka a bank É—in ki ko ki tura gida."

Bata ce komai ba, Aysha ta fita tana ji suna larabcin da itama yanzu tana fahimta.

Bayan fitar Aysha ta ɗauki wayar ta ta duba kuɗin  da Aisha ta ce ta canja zuwa naira, ta ga naira dubu ɗari uku ne. Ta yi ajiyar zuciya tana kallon kuɗin, dan bata barin kuɗi account ɗinta sai zata turawa Mama take canjawa ta tura mata.

Cikin sanyin ta turawa Mama dubu ɗari biyu, ta bar dubu ɗari a ciki ko amfaninsu zai ta so. Ta kalli agogon wayar ta ga su ƙarfe tara na dare, nigeria kuma ƙarfe bakwai kenan.

Saitabkira layin Mama, tana ɗauka ta ji Mama ta ce, "ƴar albarka gaba da baya, Allah ya tsare min ke, Allah ya ba ki nasara akan duk abinda ki ke yi. Yanzu na ga kuɗi sun faɗo, daman ɗazu nake zancen ki, nace baiwar Allah nan kwana biyu ban ga saƙo ba, ashe kina tafe."

Labiba sai ta ji daÉ—i a ranta ta yi murmushi ta ce, "Amin Mama. Ina nan ta faffukar aiki dan na turo miki kuÉ—i."

"Na san da haka Labiba, ki cigaba da dagewa in dai za ki samo mana kuÉ—i ko wanne aikin ne ki yi. Yanzu maganar da nake miki daga tafiyar ki zuwa yanzu kuÉ—in da ki ke aikowa har an kusa siyin babban fili, kin ga kuwa tafiya ai ta yi riba."

Labiba ta yi murmushi ta ce, "Gaskiya ne Mama. Ina Hanan?."

"Yanzu ta fita, amma nasan bazata jima ba zata dawo."

"Baffa fa?."

"Yana nan, kin san dai ba dai na ce miki komai a kansa ba."

Ta yi dariya ta ce, "Gaskiya ne."

"Kar ki dinga tunanin dawowa gida, ki yi zaman ki a nan sai kin zama hamshaƙiyar mai kuɗi sannan sai ki dawo. Cikin satin nan akwai waɗanda zamu aiko dasu in Allah ya yarda."

Labiba ta ce, "To Mama, sai anjima."

"Allah ya yi miki albarka." Ta amsa da amin ta kashe wayar.

Aisha da take tsaye a kanta kafin Labiba ta yi magana ta ce, "Kina jin yadda take saka miki albarka, kuma ki ce ke za ki bar gidan nan, to ki je ina?."

Labiba ta kalle ta ta ce, "Ni ban saba da harkar nan ba, shiyasa gabaÉ—aya na takura."

Ta dafata ta ce, "Kar ki damu, za ki saba a hankali, nan gaba za ki fi amincewa da ita fiye da wanda ki ka yi a baya."

Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Shikenan, Mu je." Aisha ta bata hannu hannu suka tafa ta ce, "ko ke fa yar gari, mu je." Labiba ta yi dariya sannan suka fita tare.

****

Mama tana kashe wayar ta yi baƙi suka shigo da sallama, ta amsa tana bisu da kallo ganin ƴan mata ne guda biyu kuma bata san su ba.

Suka gaisa sannan ta ce, "Ban gane ku ba."

ÆŠaya ta ce, "nan ne gidan woman leader ko?."

Mama ta ce, "Gani a zaune ina kallon ki."

Ɗaya ta ce, "Sunana Ikilima, wannan ƙawata ce sunanta Ma'arufa. Mun zo ne muna so a yi mana hanyar barin ƙasar nan, muna so mu je saudia aiki."

Mama ta bi su da kallo ta ce, "To ai ba haka kawai ake tafiya aikin ba, ba haka kawai ake kwaso jiki ace ana so a tafi aiki ba Æ´an mata. Ina iyayen ku?."

ÆŠaya ta ce, "Ba ma so su sani, muna so mu samu kuÉ—i ne kawai."

Mama ta taɓe baki ta ce, "Yanzu aikin saudia ya zama na ƙa'ida, sai kina jin larabci ko turanci, sun daina karɓar waɗanda basa jin yarensu, saboda wahala ake sha wajen fahimtar maganar su. Kun iya?."

Iklima ta ce, "Na iya turanci sosai, larabcin ma ina ji, amma ba sosai ba."

Mama ta kalli É—ayar ta ce, "kefa?."

"nima na iya, babu yaren da ba ma ji."

Mama ta ɗaga kai tana binsu da kallo, daman ana neman ƴan matan da za a kai aiki, amma bata sani ba ko sun yi daidai da waɗanda ake nema ko ba su yi. Ita bata damu da amincewar iyayensu ba, indai su sun amince zance ya ƙare.

Mama ta ce, "ku bani lambar waya, in na gama komai zan kira ku." Jikinsu har rawa yake suka bada lamba saboda suka yi mata godiya suka fita.

Tana fita Baffa ya shigo ya kalle ta ya ce, "ki cigaba Zulaiha, wata rana za ki yi danasanin tura yaran mutane wata ƙasar aiki, za ki ɗanɗana irin abinda iyayensu suke ɗanɗanawa. Zulaiha wallahi za ki yi kuka da idanunki, a lokacin da kuka bazai yi miki amfanin komai ba, baza ki taɓa cin ribar haka ba."

Mama ta haÉ—e rai tana kallon Baffa ta ce, "Ni fa ba karuwanci nake tura su ba aiki ne." Baffa ya yi murmushi kawai ya fita.

Mama ta fara mita tana ta bala'i ita kaÉ—ai har Hanan ta shigo ta same ta sai mita take yi, bata ce komai ba ta wuce, jim kaÉ—an ta dawo ta ce, "Mama kin san me?."

Bata kalle ta ba ta ce, "Sai kin faÉ—a."

"Kin ga ƙatuwar motar da ake yawo da Islaha kuwa?..."

"Mtsww!" Ta yi tsaki bata ce komai ba.

Hanan ta ce, "Ni na ji labari daga bakin masu aikin gidan, na ji ana cewa Rehaan yola aka aura mata."

Mama ta kuma yin dogon tsaki ta ce, "Shine me? Ko shi Rehana É—in ta aura sai me?."

"Ta samu cigaba a rayuwarta fiye da yadda ki ke tunani."

"Ta samu mana ina ruwana? Ni daman bance kar ta samu ba, ɗana ne bazata aura ba wallahi. Ta je ta auri ɗan ƙaruna ma ƙarewar kuɗi, ita ta ga zata iya. Ni fa ba dan kin yi zancen ta ba ni na manta da shafin rayuwarta." Hanan bata ce komai ba ta koma ciki.

Washr gari.

Saheer yana fitowa daga gida ya ga mota ta tsaya a kusa dashi, a tunaninsa Islaha ce a bayan motar amma sai ya ga maza biyu sun fito.

Duk suka ba shi hannu suka gaisa, sannan É—aya ya ce, "na san baka san mu ba."

Saheer da ya ke kallonsu ya ce, "gaskiya ban san ku ba."

ÆŠaya ya yi murmushi ya ce, "In baza ka ba mu dama da mun shiga mota mun tattauna na mintina biyu."

Saheer da yake yi musu kallon mamaki ya ce, "A kan me kenan?."

"Akan wani abu mai mahimmaci, wanda zai sa ka ka ƙaru sosai."

"Meye shi?."

"Inda zaka shiga motar zaka ji. Ba sace ka zamu yi ba, magana ce kawai zamu yi da kai, in ka amince shikenan."

Ya É—an yi jim yana tunani, sai kuma ya shiga gaba É—aya ya shiga baya É—aya maxaunin driver.

Saheer ya ce, "Ina jin ku."

Wanda yake zaune a mazaunin driver ya kalli na bayan, shi kuma ga É—auko jaka a gefensa ya buÉ—e, ya nunawa Saheer ya ce, "Miliyan biyu ce cash."

Da mamaki ya ce, "ta meye?."

Na gaban ya ce, "Mun zo ne akan Islaha, yarinyar da ta rabu da kai ta auri Rehaan Yola."

Saheer ya nutsu sosai sannan ya ce, "Me ta yi?."

Ya girgiza kai ya ce, "Wani aiki mu ke so saka ta ta yi mana akan Rehaan, aiki ne ba na cutarwa ba, sai na son sanin wasu abubuwa akan cinikaiyyarsa. Tunda ita tana tare da shi a matsayin matarsa, kai kuma kana tare da kai a matsayin wanda take so, har yanzu tana girmama ka kuma tana jin maganar ka, shiyasa mu ka zo gare ka akan maganar."

Saheer dai kallonsu yake yi sannan ya ce, "Ban gane ba."
Chapter 45 · 0% Book details