← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 110

Sashe 39

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rehaan shima kallon mamaki yake yi mata, bai yi niyar fitowa ba sai ya shirya daga closet É—insa kamR yadda ya saba, hair burner É—insa ya manta a É—akin shiyasa ya fito ya É—auka sannan ya koma closet É—insa.

Islaha ta kasa kallonsa saboda kunya da danasanin shigowa É—akin sun gama mamaye mata zuciya, sai kawar da fuska take yi kamar munafuka, shi kuma ya tsaya cak yana kallonta dan bai san me ya kawo ta É—akin ba.

Cikin nutsuwa ya ƙaraso inda take, daga ɗan nesa da ita ya ce, "any problem?."

Islaha bata amsa ba, so take ta buÉ—e baki tayi magana bata san me ya rufe mata baki ta kasa cewa komai ba. Shi kaÉ—ai take hangowa a idanunta kawai, duk da kallo É—aya ta yi masa ta É—auke kai amma har lokacin shi take gani a idanunra. Hasken da fatarsa take dashi, da gashin jikinsa, da yanayin jikinsa, da yadda ruwa yake bin fatar jikinsa kaÉ—ai take iya tunawa a wannan lolacin, ta ruÉ—e ta rasa abinda ya kamata ta yi.

Rehaan dai ya zuba mata ido yana jira ya ji me zata ce masa, dan ya san akwai dalilin da ya kawo ta É—akin ba haka kawai ta zo ba.

Islaha daƙyar ta ce, "Daada.." sai bata ƙarasa ba bakin ya ƙame saboda ruɗewa.

Ya É—an yi tsaki cike da jin haushi ya ce, "Yau ki ka saba ganin namiji a haka?...Ki faÉ—a min abinda ya kawo ki, ina da aikin ki" ya faÉ—a a hankali yana binta da kallo.

Wani irin abu ya chaki zuciyarta, ta so ta daure ta ɗago ta kalli idanunsa amma sai ta kasa, tana so ta nuna masa ta saba ganin mazan a haka kamar yadda ya ce amma ta gaza aikata haka. Ji take ɗakin ya yi mata girma, kunya ta lalluɓe mata zuciya da idanunta.

Duk da haka bata ƙyalesa ba, ba ta bari kunyarsa ta rinjaye ta ba, bata bari kunya ta yi tasiri ba, kunya bata kashe bakin tsiwa ba ta ce, "fiye da haka ma saba gani. Allah na tuba me na gani yanzu? Ai ban ga komai ba tunda ba namiji ne a gabana ba, kuma ba dan ban saba gani bane ya saka na ɗauke idanuna daga kan ka, kawai akwai waɗanda basu cancanci a gansu a hakan bane, shiyasa bazan iya kallon ka. Ba wai dan ban saba ba, sai dan ba ka kai matsayin da idanuna za su........." maganar ta maƙale ganin ya matso daf da ita yana kallonta fuskar ta.

_Innalilllahi wa'inna ilaihir raji'un! Na shiga uku. Shi wai ba shi da kunya ne, bai san hakan bai dace bane, ni wallahi ƙarya nake yi, ko Hamma ban taɓa gani a haka ba. Na shiga uku ni Islaha._

Abinda take maimaitawa a ranta kenan, ta kasa ɗaga ido ta kalle sa har lokacin kuma bakinta yaƙi mutuwa.

Rehaan ita yake kallo da ta sunkuyar da kanta, ita kuma tana ƙoƙarin ɓoye tsoronta amma ta kasa, bata so ta nuna masa ta tsorata saboda kar ya daina yi mata kallon ƴar iska.

Ganinsa daf da ita ya saka ta matsa jikin bango ta ce, "Mr Rehaan....ka matsa don Allah."

Rehaan ya yi ƙasa da idanunsa, yana kallon fuskarta calmly ya ce, "Ba ko wanne ido ne ya cancanta ya ga ko wanne jiki ba, kin ji?."

Bata san ta É—aga amsa kai alamun eh ba saboda duk ta ruÉ—e lokaci É—aya. Ya yi murmushi yana ja da baya yana kallonta, rana ta farko da ya yi galaba a kan bakinta, har ya faÉ—i magana ta kasa mayar masa.

Da hanzari ta nufi ƙofa zata fice, sai da ta riƙe handle ɗin ta tabbatar ta kusa fita sannan ta ce, "Kakarka tana ƙasa tana jiran ka" tana faɗa ta fita da hanzari.

Ya yi tsaki ya ce, "Mara kunya" ya yi murmushi ya koma inda ya fito.

Islaha ta jima a falon a tsaye tana sauke numfashi har da ɗora hannunta a ƙirji kamar wacce ta yi gudu, tunda take a duniya bata taɓa jin kunya irin ta lokacin ba, bata taɓa zaton zai faɗi magana ta kasa mayar masa ba sai a wannan lokacin. Tana dafe ƙirjinta tana ji a ranta kamar bata kyautawa kanta ba, ta ya zata kalli wani namijin daga shi sai towel?. Ta yi tsaki mai tsaho mai nuni da jin haushin abinda ta aikata, sai kuma ta tuna da Daada a ƙasa ta sauka da sauri.

Tana zuwa ta ce, "Gashi nan." Daada ta amsa tana dafa ta cikin ƙaunarta.

Basu jima sosai ba ya sakko, sanye cikin riga da wando na kamfanin Nike baƙaƙe waɗanda suka yi masa kyau sosai. Tun kafin ya ƙaraso ƙhamshinsa ya cika wajan, ita dai bata ɗaga ido ta kalle sa ba har ya ƙaraso ya zauna.

Daada ta kalle sa ta ce, "Sannu Muhammad, ashe haka abu ya faru?."

Ya É—aga kai ya ce, "Barka da rana."

"barkan ka, Allah ya kiyaye gaba."

"Amin."

"Ka cigaba da addu'a, ka cigaba da sadaka ka ji."

"In sha Allah."

"Allah ya ƙara kiyayewa."

"Amin."

"Iyayenka mata sun ahigo kuwa?."

Ya girgiza kai ya ce, "Ban sani ba ko da ina bacci sun zo."

Daada bata ce komai ba, ta miƙe tana kallon Islaha ta ce, "Ishlaya in kina son abinci ki dinga aikawa a karɓo miki, wannan abincinsa gabaɗaya na ƙasar waje ne, in kina son na gargajiya ki snaar dani." Islaha ta yi murmushi tana miƙewa tsaye.

Daada ta ce, "Ke da ba ki da lafiya, yi zaman ki ba sai kin raka ni ba, akwai ƴan rakiyata a waje." Islaha sai da ta rakata har bakin ƙofa, sannan masu aikin suka riƙe ta suka tafi ita kuma ta rufe ƙofar ta dawo ta zauna.

Yana inda ta bar shi bai motsa, sai ɗora ƙafa kan ɗaya da ya yi yana kaɗa ƙafa kamar basarake. Islaha ta saci kallonsa ta gefen ido, gashinsa ya sauka har wuyansa, tana kallon gashin tana aiyana ko ya irin gashin nan nasu yake, dan gashinsa gabaɗaya bai yi kama da na fulani ba, da irin na su Banisha ya yi kama, tana so ta ji gashin ya irin nasu yake mai laushi ne ko ya ya.

Ƙofar aka buɗe aka shigo tare da sallama Banisha da Janan da Ikram suka shigo falon.

A guje Banisha ta ƙaraso ta zauna a kusa dashi, ya yi murmushi ya riƙe hannunta ya ce, "Kiddo ya school."

"lafiya lau, gobe zan yi presentation."

Ya ja kunatunta ya ce, "all the best."

Itama ta rama ta ce, "thank you."

Ya kalli Janan da Ikram ya ce, "Na manta rabon da na gan ku, bakwa nemana."

Suka yi dariya Ikram ta ƙarasa ta ba shi hannu suka gaisa sannan ta ce, "ka san mun yi busy, har yanzu ba mu huta da gajiyar biki ba."

"Uhum i see" abinda ya faÉ—a kenan, ya bawa Janan hannu suka gaisa.

Janan ta kalli Islaha ta ce, "Hii Sis Islaha."

Islaha ta yi fara'a ta ce, "Hi Janan."

"Ya jikin ki?."

"na ji sauƙi."

"Allah ya ƙara sauƙi."

"Amin, na gode."

"Let me introduce Ikram to you, Sister Hamma Jafar ce, inlaw É—in Riyya."

Ikram dai kallon Islaaha take yi har Islaha ta kalle ta suka haÉ—a ido, Ikram ta murmusa ta bata hannu suka gaisa.

Janan ta ce, "Hamma Jafar ne ne ya kira ni ya ce na zo na faÉ—a maka, Bilal yana waje da masu sim swap É—in."

Ray ya gyara zama ya ce, "Okay su zo." Janan da Ikram suka fita.

Babu jimawa suka dawo gabaɗaya da baƙin, Islsha tana zaune bata motsa ba tana kallon ikon Allah. Ganin kamfanin layin waya guda a gabanta, a take aka yi capturing ɗinsa aka yi masa sim swap cikin mintina ƙalilan.

Bilal ya ba shi sabuwar waya a kwalinta, ya ajjiye a gefe bai ce komai ba Banisha sai surutu take yi masa. Sim swap É—in gabaÉ—aya bai wuce mintina goma ba aka gama suka fita, ya rage daga shi sai su Ikram.

Ikram sai satar kallon Islaha take yi da take ta ta danan waya kamar bata san dasu a wajen ba. Ƙare mata kallo take yi tun daga sama har ƙasa. tana so ta hango aibunta ko muninta amma ta gaza, kyau take gani mai ɗaukar ido da ɗaukar hankali, babu abin burgewa sai bakinta, da zananniyar gira da Allah ya bata.

Islaha tana lura da kallon da Ikram take yi mata wanda bata san dalilinsa ba, ta basar kamar bata sani ba tana ta danan waya suna magana da Brr.

Rehaan ya miƙe ya hau sama da wayar a hannunsa bai ce musu komai ba.

Janan ta taɓa Islaha ta ce, "Sis bakya magana?."

Islaha ta É—ago ido ta yi murmushi ta ce, "Ina yi mana."

"Amma ki ka yi shiru?." Murmushi ta kuma yi kawai bata ce komai ba, basu jima a zaune ba duk suka fita daga falon. Islaha ta miƙe ta hau sama, bata same sa a falo ba ta wuce ɗaki ta rufe ƙofar.

      ***

Sai zagaye yake yi a cikin falon hankalinsa a tashe, ya kasa nutsuwa tunda ya ji an matsanta binciken akan waÉ—anda suka kai wa Rehaan hari, ba ya so sunansa ya fito, ba ya so a ce shine ya saka a kashe Rehaan.

Ya kalli yaran da suka yi aikin ya ce, "Ba ku taɓa yin aiki daidai ba, ko yaushe sai kun ɓata komai. Yanzu da kun kashe shi da hakan ai bai faru ba."

"Ranka ya daÉ—e motar bullet prove ce, babu harbin da ba mu yi mata ba amma bai same su ba."

Cikin faɗa ya ce, "Amma kun san babu ta yadda za a yi ya hau motar da ba bullet prove ba ko? Meyasa ba mu fara ƙona motar ba tun farko?. Wancan kun ba shi guba ƴar kaɗan, wannan kuma kun kasa aikata komai."
Chapter 39 · 0% Book details