← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 110

Sashe 31

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokaci É—aya gaban Mamy ya faÉ—i sosai, ta É—an zuba mata ido na wani lokaci kafin ta janye idanunta ta ce, "Islaha sunan ki amma sun saka miki Islam, haka ne?."

Ta É—afa kai alamun eh, Mamy ta ce, "is okay, za ki iya tafiya"

Islaha ta miƙe ta koma ciki tana waiwayon Rehaan da ya ke wani narkewa a jikinta tana jin takaici yana mamaye ta kamar ta zo ta rufe shi da duka.

Mamy ta shafa kansa ta ce, "kamar tana da hankali."

Ya É—ago ya kalli Mamy ya ce, "a hakan?."

Mamy ta dungure masa kai ta ce, "meyasa baza ka nutsu ku zauna lafiya ba?."

Ya zaro ido ya ce, "da wannan É—in?."

"Ita É—in."

"Rashin kunya ta yi miki fa."

"Bani ta yiwa ba, kuma ko a lokacin laifin Ammi ne."

Ya yi shiru bai ce komai ba sai daga baya ya ce, "zan koma engaland."

Mamy ta miƙe ta ce, "ai an samu ka zauna ma, ina jin ba ka taɓa jimawa a ƙasar nan kamar yanzu ba, kullum kana yawo, amma nima zan je india."

Ya yi murmushi ya ce, "Kun yi magana da Riyya?."

Mamy ta yi murmushi ta ce, "mun yi É—azu." Ya É—aga kai bai ce komai ba, Mamy ta sauka daga saman.

Islaha tunda ta koma take saƙa da warware akan lamarin Zainab, sai kai kawo take yi tana so ta samu wani abu guda ɗaya da zata riƙe matsyin makami amma ta kasa. Tana so ta samu hujja mai ƙarfi da kai kokenta ma'aikatar da Jazy ya faɗa mata, kamar yadda ya faɗa mata sai tana da hujja zasu karɓi report ɗin, ita kuma hujjar ta rasa.

Ta yi ajiyar zuciyar rashin mafita, tana tuna abubuwan da suka faru tunda daga lokacin da aka goge hotunan Hafsa a wayarta, zuwa recording da komai da komai. Ta zauna ta yi tagumi ta rasa wanne irin tunani zata yi ta ji daɗi akan lamarin, tana buƙatar shawara, tana buƙatar ta yi magana da wanda zai fahimce ta har ya faɗa mata abinda ya kamata ta yi a wannan lokacin.

Ta cire hijjab É—in jikinta ta ajjiye, ta ja numfashi mai tsaho cikin tunani kala kala wanda bata da hanyar magance su a nan kusa.

Sai kuma ta miƙe tsaye a bayyane ta ce, "Ya zama dole na koma wajan Yafindo, ya zama dole na je na same ta duk abinda zai faru sai dai ya faru. Zainab ce kaɗai hujjata kuma ta ɓace, saƙon da ta bayar kuma yana hannunta. In na samu saƙon da ta bawa Yafindo, wataƙila zai iya taimaka min na je inda Jafar ya ce min, wataƙila ƙarshen matsalar ta zo."

Ta juya ta É—auki wayarta tana duba mail É—in da ta turawa mutanen da za su yi interview dasu, mutum É—aya ya yi approving saura biyu.

Haka kawai ta ji gabaɗaya bata jin bacci, ta zauna tana tunani akan gidansu Rehaan da matsalolinsu. Daga zuwanta zuwa yanzu ta fahimci babu haɗin kai a lamarin gidan ko kaɗan, kowa kansa ya sani. Sannan kamar Mamy ce ba sa so, shi kansa Rehaan ɗin ta fahimci ba kowa ne yake ƙaunarsa a cikin gidan ba.

A bayyane ta ce, "Amma kuma Mama tana da kirki sosai, har ta so ta fi Mamy kirki. Ina ganin girmanta sosai, dan tana sona."

Sai kuma ta yi tsaki ta ce, "Ina ruwana da tunanin akan gidan nan? Su kashe kansu mana, ina ruwana ni da ba zama nazo yi ba?" Sai ta watsar da tunanin ta cigaba da abinda yake gabanta.

Haka take zaune ita kaɗai, ta saka tashi ta kwanta har ƙarfe ɗaya na dare sannan ta fara jin bacci. Ta miƙe tsaye ta shiga banɗaki ta yi alwalar kwanciya bacci, ta fito tana gyara kan gadon da niyar kwanciya.

Kamar ance ta kalli window ta waiwaya tana kallon compound É—in apartment É—in Rehaan, ta gan shi a tsaye a kusa da mota, an buÉ—e masa bayan motar yana niyar shiga da alama fita zai yi.

Islaha gabanta ya faɗi, tsoron barin ta ita kaɗai ya mamaye mata zuciyarta, ta dafe ƙirji ta ce, "Ina zai je ya barni ni kaɗai a wannan gidan? Sai wannan mahaukacin Yayan nasa ya zo an sake ƙulla min wani sharrin?."

Ganin da gaske mota zai shiga kuma fita zai yi, bata san ta fizgi hijjab ta fita da gudu ba.

Tana fitowa inda motar ta ke a daidai lokacin ya kulle mota ana niyar jan motar su fira. Isaha ta tsaya tana kallon motar sa ta glass, shima ganinta a tsaye sai ya ba shi mamaki, yana kallonta ta glass kamar yadda take kallonsa.

Islaha ta miƙa hannunta yi knocking glass ɗin Rehaan sauke yana kallon ta. A karo na farko da Idanunsa suka yi mata kwarjini, kaifin idanunsa suka soki zuciyarta, lokaci ɗaya sai bakin ta ya yi nauyi sosai, ta sauke idanunta ƙasa tana turo baki ta ce, "ni gaskiya tsoro nake ji bazan iya zama ni kaɗai ba, zan bi ka duk inda zaka je."

Rehaan ya bita da kallo bai ce komai ba, ganin bai yi magana ba kawai sai ta zagaya ta buɗe back seat ta shiga kusa dashi ta rufe ƙofar.

Har a lokacin bai ce komai ba ya É—auke kai yana kallon gabansa. Sai kuma ya ce, "Shams me ka ke jira ne?."

Shams da mamakin ganin Islaha a kusa da Boss É—insa a zaune a back seat ya hana shi magana, jin muryar Rehaan sai ya ce, "Sorry Sir" ya faÉ—a yana kunna motar amma kallon Islaha yake yi.

Dan wallahi bai manta da fuskar Islaha ba, har gobe in ya tuna dramar da suka yi da ita a lokacin da suka sace ta yana dariya sosai.

Ganinta tare da mai gidansa a apartment É—aya ya ba shi mamaki, amma bai ce komai ba ya ja suka fita

       ***

"Ranka ya daÉ—e motar Rehaan ta fio daga gida yanzun nan, kuma daga shi sai matarsa da Shams, babu security ko É—aya, shi kaÉ—ai ne."

Daga can ɓangaren ya ce, "dakyau, ina zuwa."

Yana kashewa ya kira waya ya ce, "Rehaan ya fita, a san abinda za a yi, kar ɗayansu ya dawo da rai. Dukka su biyun bani da buƙatarsu, a tabbatar da anga bayansu."

Yana gama faɗar hakan ya kashe wayar, ya furzar da iska mai zafi ya ce, "Lokaci ya yi Rehaan, wallahi sai na bayanka, bazan taɓa bari ka rayu da rai da lafiya ba, sai na kashe ka. Matar ka da ta bi ka ku ka fita ka jawo mata, za a ɗauki gawa biyu. Mu je zuwa" ya faɗa yana lumshe ido cikin tsana da ƙiyayyar Rehaan wacce shi kansa bai san adadinta ba.

Nana Haleema.

RDB3P26
Nana Haleema

Tunda suka tafi Islaha bata yi magana ba, tana jikin ƙofa ta jingina tana kallon window. Ac motar ta dame ta, da motar ta yi wani irin sanyi mai ratsa jiki, ga turarensa ya gama mamaye ko ina a cikin motar. Ta ɗan ja numfashi jin kamar numfashinta ya fara tokare ta, ta saka hijjab ɗinta ta toshe hancinta jin sanyin zai yi mata illa.

Shi kam Rehaan kamar bai san da ita ba, waya yake amsawa tunda suka fara tafiya har suka tsaya bai daina magana a waya ba. Ta É—an kalle sa ta ga sai yatsina yake yi kamar wanda ya yi doguwar tafita, ta É—auke kai tana jan siririn tsaki tana ji kamar ta gaggaura masa mari saboda takaici.

Kallon gidan da aka buÉ—e musu take yi, ta buÉ—e ido kawai tana kallo ganin girman gidan da yadda aka tsara shi ya burge ta. Harabar gidan kanta abin kallo ce, ga haske ko ina kamar ba É—aya da wani abun na dare ba.

Shams ya tsayar da motar, har lokacin Rehaan bai gama waya ba, sun yi minitina biyar da tsayawa sannan ya kashe wayar ya buÉ—e motar ya fita. Tana ganin ya fita itama ta fita, har lokacin bata lura Shams ne yake driving motar ba.

Inda ya nufa take nufa yana gaba tana binsa a bayan, har suka shiga main parlor mai kyau da girma. Maimakon ta ga ya tsaya sai ta ga ya nufi stairs kai tsaye ya hau sama. Kamar ta bi sa sai kuma ta tsaya dan kar ta zaƙe da yawa, ta tsaya tana kallon falon.

Rehaan yana shiga first parlour É—in da yake upstairs É—in ya jiyo kukan Riyya daga cikin bedroom. Rehaan ya kalli Jazy da yake zaune a kan kujera ya dafe kansa da hannu biyu, bai san Rehaan yana tsaye a kansa ba sai ji ya yi ya ce, "Jazy me ka yi mata haka da ta ke wannan kukan?."

Jazy ya firgita jin maganar Rehaan a sama, dan bai dan ya zo ba kawai ya ji magana ne. Ganin Rehaan sai ya miƙe tsaye ya ce, "zo mu je don Allah, na rasa abinda ya kamata na yi mata, sai kuka take yi tun ɗazu, daƙyar na samu nunfashinta ya dawo daidai."

Ray ya ƙi binsa ya daƙire ya ce, "ƙoƙarin kashe ta ka yi ne ko me? Me ya same ta haka?."

Jazy ya ja hannunsa ya ce, "ka zo mu je ka gani." Rehana ya bi bayansa ya shiga É—akin dan bai san me ya samu Riyya É—in ba.

Rehaan da hanzari ya ƙarasa inda Riyya take ganin tana kuka sosai, ya riƙo ta jikinsa ya ce, "Riyya me ya same....." bai ƙarasa maganar ba jin jikinta ya yi zafi sosai.

Rehaan a rikice ya ce, "Oh my god! Wnnan fever daga ina kuma, me ya same ki Riyya?."

Riyya jin muryar Rehaan sai ta buɗe ido daƙyar, ganin yadda idanunta suka yi ja suka kumbura sosai sai hankalinsa ya sake tashi, cikin faɗa ya kalli Jazy ya ce, "wai me ka yi mata haka, me yake damunta da za ka bar ta a gida baza ka kaita asibiti ba?......"

Ya sake kallon Riyya ya ce, "Riyya me yake damun ki, ina ne yake yi miki ciwo?."

Riyya ta riƙe hannun Rehaan cikin muryarta da ta dashe ta koma ta marasa lafiya ta ce, "ka tafi dani gida, bazan iya zama a nan ba, wajen Mamy zan koma."
Chapter 31 · 0% Book details