← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 110

Sashe 74

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Islaha cikin firgici da wani irim yanayin da bata saba da shi ba ta ce, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Mr Rehaan ka bari don Allah, bana so!"ta faɗa cikin sanyin murya tana ji kamar ta yi kuka, tana jin wani abu yana shiga cikin jininta, ga shi ya haɗe jikinsa da nata ya riƙe ƙugunta ya matse ta a jikinsa.

Rehaan ya kalli fuskar ta ya ga ta firgita sosai idanunta a rufe kamar zata yi kuka. Rehaan ɗage gira sama yana sake tamke fuskarsa, ya kai bakinsa daidai kunnenta hancinsa yana ɓata kunnenta, gashinsa ya sauka a gefen fuskar ta yana taɓa jikinta sannan ya ce, " i set the rule......"

ya sake yin ƙasa da muryarsa sannan ya ce, "now."

Nana Haleema.

RDB3P56
Nana Haleema.

Tashin hankali ya yiwa Islaha dirar mikiya, yadda ya yi maganar a daidai kunnenta ya saka ta ji wani irin yarrrrrr har gashin kanta sai da ya amsa, ta ji wani abu zirr a ko ina na jikinta, ƙofofin gashin jikinta suka buɗe suka firfito suka miƙe. Zuciyarta ta harba cikin wani irin yanayin da ya zamar mata baƙo a cikin duniyar ta, jikinta ya fara rawa saboda ta rasa inda zata saka ranta ta ji daɗi. Idanunta a rufe suke ruff, ta kasa motsi fuskar ta ta canja zuwa yanayin tsoro kamar zata fashe da kuka.

Rehaan ƙhamshin turaren da ya ke wuyanta yake ji a hancinsa a hankali, ya kai hancinsa wuyanta ya shaƙi ƙhamshin har hancinsa yana taɓa wuyanta, ta firgita jin kamar ya tsira mata allura, fuskar ta sake canjawa zuwa wani irin yanayi.

Bakinta yana rawa ta ce, "Mr Rehaan don Allah ka bari, wallahi bana so!" Ta faÉ—a kamar zata yi kuka har lokacin idanunta a rufe yake

Rehaan ya yi murmushi yana bin fuskar ta da kallo, musamman bakinta da yake moving kaÉ—an-kaÉ—an, yana tuna yadda bakinta ya ke da laushi da santsi a lokacin da ya yi kissing É—inta.

Ya kai hannunsa kan lips É—inta ya shafa yana kallon idanunta sannan ya ce, "Namiji da mace nake so ki banbance."

Bata san ta rungume shi ba jin maganar a tsakiyar kanta, jikinta ya fara rawa ta kasa cewa komai ba kuma ta kasa guduwa.

So ya ke ƙure rashin kunyar ta, so ya ke ya ga a cikin barikin a wanne stage ta tsaya, so ya ke ya ga rashin kunyar ta ta a wanne matakin ta tssya. Sai gashi tun ba a je ko ina ba ya ga bata yi nisa a harkar ba, barikin nata a baki yake, bai kai matakin da yake so ya ga ta kai ba, tunda ga shi abu kaɗan ya firgita ta.

Rehaan ganin idanunta a rufe sai ya hura mata iskar bakinsa, ta buÉ—e ido a hankali ta kalli fuskarsa ya sake É—aga rigarsa sama. Islaha ta yi hanzari zata gudu, kawai ta ji saukar bakinsa a wuyanta ya yi kissing.

"Na shiga uku! Mr Rehaan...!" Ta faÉ—a zata fara kuka saboda tashin hankali.

Bakinta kaɗai yake kallo, so yake ya yi kissing ɗinta amma ya kasa samun courage ɗin hakan, ganin ya gama firgitata sai ya sassauta riƙon da ya yi mata, ta ƙwace kanta ta ja baya, bata ce komai ba ta fita da gudu tana hakki.

Rehaan ya yi tsaki yana murmushi duk a lokaci É—aya ya ce, "shirme! Sai na koya mata hankali, ina so ta banbance namiji ne ni ko mace" ya yi murmushi yana shafa gashin kansa cikin sabon yanayi ya ce, "matsoraciya!" Ya faÉ—a yana koma closet É—insa

Islaha a falon ta tsaya tana sauke numfashi tana ƙoƙarin daidaita nutsuwar ta ta dawo daidai. Sai da ta nutsu zuciyarta ta daina bugawa da ƙarfi, ta kalli ɗakinsa sai ta ga bai biyota ba. Ta kai hannu ta shafa wuyanta daidai inda ya yi kissing, ta runtse ido tana jin abun baƙo a gare ta.

Ta girgiza kai cike da jin kunyar abinda ya yi mata, ta kalli hannunta tana tuna a kan fatar ƙirjinsa ta ɗora tafin hannunta, ta yi tsaki cike da takaici abinda ya farutsaki ta ce, "Wallahi sai na tuna masa, ya kamata ya san a matakin da mu ke kai nida shi."

Bata san adadin lokacin da ta kwashe a wajen a zaune ba, jikinta ya gama mutuwa, sai ta nutsu sannan zata iya miƙewa tsaye. Tana zaune ta ga wucewarsa ya buɗe ɗakinta ya shiga ya samu Salman a zaune yana ta wasa da duk abinda ya gani.

Ganinsa sai Salman ya miƙe ya ce, "Na zo wajan ta mu yi wasa."

Rehaan ya haɗe masa rai ya ce, "not now, zo mu je wajan Daada" ya faɗa yana riƙo hannunsa.

Salman ya turje ya ce, "ni dai a'a, a nan zan zauna." Rehaan ya bi shi da kallo yana tunanin waye ya buɗe masa ƙofar har ya shigo.

Ya sake jan hannunsa ya ce, "yanzu zamu dawo." Bai ce komai ba suka sauka bai ko kalli Islaha ba, dan ya gama da ita tunda ya fahimci mara kunyar ƙarya ce. Islaha ta harare sa ta ce, "mai taɓa mata kawai."

Saboda firgicin abinda ya yi mata ko barin wajan bata yi ba, har ya dawo ya sake wuce ta, ta sake hararaesa sannan ta shiga ɗakin tana dafe ƙirjinta dan har lokacin bugawa ya ke yi.

Islaha tana shiga ta buÉ—e jakarta ta É—auko contract agreement É—insu tana dubawa, ta girgiza kai ta ce, "ya fara wuce iyakarsa, ya zama dole na tuna masa a ina muke, bazan yarda ya sake kai hannunsa jikina ba, daman bamu tsara da hakan a zaman mu ba."

Da wannan abun ta kwana a ranta, amma ko ya ta motsa jikinta sai ta dinga jin jikinta a haɗe da nasa, ga shi babu kaya a jikinsa, tana jin yadda hancinsa ya taɓa wuyanta, da yadda gashinsa ya dinga taɓa fatar jikinta, da yadda ya yi kissing wuyanta. Ta miƙe zaune tana tsaki kamar ta yi hauka saboda tunani, ta sake kwanciya ta runtse ido tana so ta kawar da tunanin amma ta kasa, a haka bacci ya kwashe ta.

Washe gari friday, a zaman da ta yi a gidan ta ga suna hidima a duk ranar juma'a, sadaka ake yi babu kama hannun yato, na abinci na kuÉ—i da sauransu.

Duk da sai yamma zasu yi interview, amma dole zata shiga wajen aiki da wuri a shirya abubuwan da ya kamata a shirya. Bayan ta gama shiryawa cikin black abaya cikin irin wanda Hamma yake kawo mata, har zata fita sai ta dawo ta É—auki takardun contarct É—in ta fita.

Bata same shi a parlour ba dan ta ganshi ta window yana bawa dadbobinsa abinci, ta san ya kusa shigowa ita kuma so ta ke su haÉ—u.

Downstairs ta koma tana kallon breakfast ɗin da aka haɗa, ta ƙarasa kan dining ɗin tana kallon madarar nido da take a babban gwangwani a ajjiye. Ita daman Allah ya yi ta da son madara, ko ba a tea ba in ta gani zata ɗauka ta sha.

Ta É—auki tea spoon ta buÉ—e madarar ta zuba a hannunta, ta rufe madarar sannan ta É—ora lips É—inta a kan madarar tana sha, sai ta manne mata a bakinta gabaÉ—aya, ita kuma saka harshenta tana lashewa a hankali.

A daidai lokacin Rehaan ya shigo parlour suka haɗa ido, ya dauke idanunsa ƙasa ya kalli bakinta ya ga duk madara ɓata ta har a mayafinta. Ya ɗauke kansa ya wuce ta ya hau sama, ita kuma madarar da ta ke bakinta ne ya saka bata yi magana ba, sai da ta gama ta karkaɗe jikinta, ta wanke hannunta da bakinta ssnnan ta bi bayansa.

A falo ta same shi a tsaye yana É—aukar wayarsa akan center table ta ce, "Mr Rehaan, ina so na tuna maka wani abu guda É—aya...."

Sai ta warware takardar contract ɗin da ya sama hannu ta nuna masa ta ce, "a ciki rules ɗina dana rubuta maka, na ce maka bana so wani abu ya haɗa ni da kai. Stop trying to create a bond between us, kar ka sake ƙoƙarin kai hannunka jikina, in ba haka ba ths contract will be cancelled!."

Ya waiwayo ya kalle ta cikin mamakinta, ita kuma ta sake nuna masa takardar ta ce, "bana so ka sake ƙoƙarin taɓa ni, bana so hannunka ya sake zuwa jikina. Babu ruwanka dani, ka bar ni na ji da waɗanda suka saba taɓa ni a waje, amma kai ban da kai. Ka yi jiya kuma ya wuce, kar sake!."

Shi wallahi mamaki take bashi, yarinya sai  magana ga rashin kunyar tsiya, ko kunyarsa bata ji take tsayawa a gabansa tana faɗa masa haka, har tana ba shi umarnin kar ya sake kamar wata Mamy.

Ya ajjiye wayar ya harɗe hannu a ƙirjinsa yana kallonta, yana so ya tuna me ya faru jiyan da har zata so tana yi masa warning?. Ya ce, "Is that a command... or are you just trying to advise me?"

"Umarni nake ba ka ba shawara ba! Ban yi signing akan takardar nan da sunan hannun ka zai zo jikina ba, kai kuma ka yi signing akan babu wata alaƙa makamanciyar ta jiya da zata haɗa ni da kai, meyasa tun kafin zaman ya yi nisa za ka fara ƙoƙarin karya min sharuɗa bayan ni ina ƙoƙarin kiyaye na ka?."

"Mr Rehaan...kawai kar a sake, bana son abinda ka ke yi min, kuma bana buƙata, ka bari mu rabu lafiya don Allah" ta faɗa tana ninke paper da hannunta.

Ta ku ɗaya biyu ta yi ya riƙo hannunta, dan in bai nuna mata bata isa ta ba shi umarni ba kwana zai yi yana tunanin maganar ta.

Islaha ta rufe ido ba tare da ta juyo ba, ta buÉ—e idanunta a fusace ta juyo ta ce, "Mr Reh...."

Maganar ta tsaya cak jin hannunsa a waist ɗinta, ta ɗaga ido tana kallonsa tana ta ga shima ita yake kallo, ta tafi tunanin me waist ɗinta ya yi masa ne da ya ke yi masa daɗin riƙewa? Abu kaɗan ya riƙe mata ƙugu?.
Chapter 74 · 0% Book details