← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 110

Sashe 2

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin É—aga murya ya ce, "Shiyasa me! Shiyasa za ka ce min na bari za ka yi min bayani ko? To bayanin me zaka yi min, me ka ke so na sani wanda ban sani ba?."

Sai kuma muryarsa ta yi ƙasa yana kallon idanun Sadik da jajayen idanunsa ya ce, "Aure fa ta yi, ba aiki ta tafi kamar wancan lokacin ba, ba sace ta aka yi ba, wani namijin ta aura har ta tafi gidansa zata tare. Kuma ka san da wannan maganar ka ɓoye min, Meyasa haka Sadik?."

Sadik ya ce, "na faÉ—a maka zan yi maka bayani, amma na yanzu."

Ya wara hannayensa ya ce, "bayanin me, me za ka faÉ—a min wanda ban gani ba? Ko za ka ce min auren ma haÉ—awa ta yi ba na gaskiya bane?."

Sadik ya kasa magana ya yi shiru, Saheer ya girgiza cikin wani irin yanayi ya girgiza kai ya ce, "Islaha! Islaha!! Islaha!!!."

Sai ya runtse ido ya kwanta da baya yana ji ina ma kawai ya suma ya huta, yadda yake jin azaba a ƙirjinsa so yake kawai ya suma, yadda zai daina fahimtar komai ko zai samu sassaucin raɗaɗin da yake ji a zuciyarsa.

Sadik cike da tausayinsa ya ce, "Islaha bata yi komai ba, bata cutar da kai ba, wallahi bata yaudare ka ba, komai ta yi shi ne saboda kai!."

Saheer ya buÉ—e ido ya kalle sa, kamar ya ji me ya ce sai kuma idanunsa suka rufe ruf, daga nan ya daina jin abinda Sadik É—in yake faÉ—a gabaÉ—aya.

Islaha har suka yi nisa bata daina kallon gidan tana hawaye ba, ta sauke numfashi mai ƙarfi ta sunkuyar da kai hawaye na bin kuncinta.

_i don't wanna go, but baby we both know, this is not our time, it's time to say goodbye, until we meet again, cause this is not the end, it will come a day, when we will find our way. Voilins playin and the angels crying when the stars align, then i will be there. No i don't care about them all, cause all I want is to be loved, And all I care about is you, you're stuck on me like a tattoo, no I don't care about the pain, I'll walk through fire and through rain just to get closer to you, you're stuck on me like a tattoo, I'm letting my hair down I'm takin' it cool You got my heart in your hand._

Waƙar tatto kenan da take tashi a motar kaɗan-kaɗan, ga wani sanyi da ƙhamshin turare da motar take yi mai tsayawa a rai.

Islaha ta yi tana jin waƙar na shiga jikinta har tsigar jikinta tana tashi, sai take ji kamar dan ita da Hamma akayi verse, musamman inda aka ce this is not the end, sai take tabbatarwa da kanta wannan tafiyar ba itace ƙarshen rabuwar ta da Hamma, akwai wata haɗuwar a gaba.

Ta rufe idanunta da suke ciwo saboda kuka ta ce, "this is not the end, zan dawo, wallahi zan dawo. Ni ƴar halak ce, duk in da naje zan dawo gare ka Hamma!" Ta faɗa tana curewa waje ɗaya zuciyarta tana yi mata zafin kewa da ƙauna da tunanin ta cutar da masoyinta...

Safeera ta juyo ta kalle ta, ta ga idanunta a kulle ta É—auke kai tana sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba. Jazy dai bai nuna komai ba, tafiya yake yi a hankali yana kallon gabansa babu wanda ya sake yiwa magana har suka je gidan.

Safeera kallon gidan take yi kawai, ta girgiza kai dan bata da tabbacin inda aka zo, gidansu ne ko kuma gidan Islahan ne bata sani ba.

Lokacin aka buÉ—e gate ya shiga da motar ciki, ta fara ganin mutane Æ´an biki ana ta shiga da fita, kasancewar gidan babba ne baza ka ce ma biki ake yi ba, sai dai ka ga wata ta wuce wata ta sake wucewa.

Har bakin apartment É—in Mamy ya kai motar, dan ya san yadda al'adar fulani take wajan uwar miji ake fara kai amarya.

Yana tsayar da motar ya kalli Islaha ta mirror ya ga fuskar ta a buÉ—e ta jinginar da kanta a jikin kujera, ya yi dariya a zuciyarsa yana mamakin wannan amarya mai buÉ—aÉ—É—iyar fuska, ko kukan ma ta daina. Ya buÉ—e motar ya fita bai ce komai ba

Yana fita Safeera ta juyo ta ce, "Islaha meye haka? Don Allah ki kulle fuskar ki, hakan ba al'ada bane, Mama don Allah ki yi mata magana."

A lokacin Atika ta ce, "Islaha ki rufe fuskar ki, kar ki saka a tafi da mu a baki." Kamar baza ta yi ba, sai kuma ta ja mayafin ta rufe fuskar ta har lokacin bata buÉ—e ido ba.

Shi kuwa Jazy ganin gidan shiru a nan ya tabbatar da duk suna ciki ana event É—in mother eve kamar yadda aka ce za a yi. Har zai shiga wajan Mamy ya ji ana kiran sa.

Ya waiwayo ganin Mama sai ya saka ya tsaya cak, ta ƙaraso ta ce, "Amaryar ce?."

Ya É—aga kai ya ce, "Itace."

"Kuma sai ka bar ta a mota? BuÉ—e ta fito mana."

"Daman ina so na tabbatar in Mamy tana ciki ne."

"Ai wajan Daada za a kai ta ba wajan Nadira ba, buÉ—e su fito."

Bai ce komai ba ya buÉ—e motar ya ce, "bismillah."

Safeera ta kalli Islaha da kamar bata ji me aka ce ba ta ce, "Islaha mu je."

Ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba, Mama Atika ta fita Safeera ta ce, "Don Allah mu je."

Kafin ta yi wani motsi Mama ta buɗe ɓangaren da Islaha take, cikin fara'a da sakin fuska ta ce, "Bismillah mana ɗiyata, ya za ki zauna a mota haka kamar ba gidan ku ba? Fito mu je ciki, ana ta zaman jiran zuwan ki."

Islaha ta kalli Mama ta cikin mayafin da ta rufe fuska, ta ji Mama ta riƙo hannunta dole ta motsa ta fito daga motar ba dan tana so ba.

Mama ta kalli Atika ta ce, "sannun ku da zuwa. Ku yi haƙuri, muna ta biki ne a ciki, shiyasa ba a yi mu ku tarba mai kyau ba."

Mama Atika ta ji daÉ—in yadda Mma ta tarbesu da sakin fuska sai ta ce, "Babu komai, hakan ma mun gode."

"A dai yi shiru kawai, amma ba haka muka so ba. Ina sauran mutanen kawo amaryar?."

"Mu ke nan."

Ta wara ido ta ce, "ku biyu? Amaryar Rehaan guda, ace mutum biyu ne suka yi rakiya?."

Mama Atika ta ce, "Baffa ta ne ya ce ba ya son taron mutane.”

Mama ta yi murmushi ta ce, "Allah sarki, Mu je." Har lokacin tana riƙe da hannun Islaha da ya ɗaukar ɗumi saboda tension.

Daada tunda ta hango su ta kasa rufe baki saboda murna, har suka ƙarasa aka zaunar da Islaha a kusa da ita.

Daada ta dafa kanta ta ce, "barka da shigowa dangina, barka da zuwa yarinyar albarka, sannun ku da hanya." Ta É—ago ta kalli su Safeera ta ce, "ku zauna mana, sannun ku da zuwa. Sadikka a kawo musu ruwa da abinci." Mama ta É—aga kai ta fita.

Safeera suka gaisa da Daada sannan ta ce, "Sallah zan yi."

Daada ta sake jin daɗi ganin dangin Islaha sun fara da sallah daga zuwansu cikin gidan, cikin jin daɗi ta ce, "ga banɗaki nan." Safeera ta miƙe ta shiga ta yi alwala.

Islaha a lokacin ta motsa kamar zata miƙe, Daada tana riƙe da ita ta ce, "ya dai ishlaya?."

Islaha duk da bata cikin farin ciki sai da ta yi murmushi jin sunan da Daada ta faÉ—a, a hankali ta ce, "Zan yi sallah."

Daada hakan ya sake yi mata daɗi, ta sake washe baki ƙaunar Islaha tana gudu a jininta ta ce, "to tashi mana, tashi ma za ki yi sallah. Ɗiyar albarka kenan, ranar da ta shigo gidan mijinta da sallah ta fara." Islaha ta miƙe ta shiga inda Safeera ta shiga domin yin alwala.

Tana shiga Daada ta kalli Mama Atika ta ce, "Yarinyar ku É—iyar albarka ce, ba dai tarbiyya ba."

Ta yi murmushi ta ce, "ba yabon kai ba, amma Islaha ba daga nan ba kam." Daada ta sake jin daÉ—i, a lokacin Mama ta shigo da masu aiki aka zube musu kayan ciye ciye da na sha.

Daada ta kalli Mama ta ce, "Ina Nadira take?."

Mama ta ce, "suna wajan biki."

Daada ta haÉ—e rai ta ce, "aje a tashi wajen bikin yanzu nan, sannan a sanarwa kowa ya hallara a wajan nan."

Mama ta ce, "to." Ta faÉ—a tana fita dan cika umarnin Daada.

Nana Haleema.

RDB3P002
Nana Haleema.

A lokacin Islaha ta fito daga yin alwala tana dafa bango saboda ciwon kai, ta tayar da sallah bata kalli kowa ba. Tana cikin sallah ta ji mutane suna ta shigowa, ta ja mayafi ta rufe fuskar ta dan Allah ya sani bata son ganin kowa, jiri take ji daƙyar ta iya sallar magrib a tsaye, magani take so ta sha ko zata ji daɗi, sannan ta kira Sadik ta ji ya Hamma yake.

Ta ja sallar ta yi tsaho da gangan, taƙi idarwa tana sane dan bata so ayi mata wata magana ko kaɗan. Daƙyar ta idar, ta zauna bata juyo ba dan bata san adadin mutanen da suka shigo ba.

Muryar Mama ta ji ta ce, "Amarya in kin idar duk ke ake jira." Gaban Islaha ya yanke ya faÉ—i, ta runtse ido ta sake jan mayafin ta rufe fuska sannan ta juyo a hankali.

Mama ta ce, "Amarya tasowa za ki yi ki dawo kusa da Daada."

Daada tana murmushi ta ce, "kema kin san ba iyawa zata yi ba, ki taimaka mata ta dawo nan É—in."

Mama ta ƙarasa wajan Islaha ta riƙo hannunta, ta miƙar da ita suka dawo tsakiyar falon Islaha ta zauna tana kallon mutane ta mayafinta, kowa ya zuba mata ido kuma dukkan su mata ne.

A hankali ta zauna kowa na falon kallon ta yake yi, musamman Janan da Ikram da Nana da kuma Banisha da sauran Æ´an uwansa mata.

Daada ta ce, "Sadikka a buÉ—e mana taron da addu'a."
Chapter 2 · 0% Book details