← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 110

Sashe 58

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ray sai ya yi masa banza bai kula sa ba, Jazy ya ce, "kai dai kana son tayar da rigima ne, in ba haka ba ina ruwanka da ita?. Ga shi nan ta ce na faÉ—a maka, wallahi duk ranar da ka sake karya mata rule ta gama zama da kai sai ka sake ta, kuma ta ce na faÉ—a maka, in ka sake hanawa ta fita ta gate, sai ta haura ta katanga ta gudu......."

Ya dakata da maganar yana dariya sannan ya ce, "abinda ya bani dariya kenan, ta ce in ka hanata fita ta gate sai ta haura ta fita, ba ka isa ka hanata fita ba. Kai yarinyar nan ƴar drama ce, can you imagine tun daga ranar da ka hana Lawal ya fita da ita bata saka hawa motar ba? Shekaran jiya da jiya duk bata hau ba napep ta ke hawa ta fita. Lawal ya kira ni yana faɗa min, na ce to ya zanyi mata, ƙyale ta."

"Mtsw! Bata da hankali fa, ni ban taɓa gani stupid girl kamar ta ba. Har na ƙagu wata biyar ɗin nan ya yi ta tarkata ta bar ni na huta, kamar a kan ƙaya nake haka nake ji wallahi, shiyasa zaman Nigeria ya fita daga raina."

"Ka faÉ—i gaskiya Malam, daman haka ka ke, ba itace ta saka baka son zaman Nigeria ba, daman in ka zo nan ba ka son komawa. Amma da gaske ni ban ga amfanin hanata fita ba, ka san tana aiki kuma tana zuwa inda take so, in wani abu mai mahimmacin ne ya saka zata fita a lokacin fa?."

Rehaan bai ce masa komai ba, Jazy sai ya yi nufin tsokana ya ce, "haka kawai bayan ka aure ta, ka rabata da masoyinta kuma sai ka hanata rayuwa da shi?."

"Ni na ce kar yi rayuwa da shi ne, ina ruwana da shi, ko na san shi ne?."

"Ba ka ce ba, amma auren ka ya ce."

"Ba aure bane, na lokaci ne kawai. Ta je ta yi duk abinda ta ga dama bai dame ni ba, daman ta saba, Salman ma ba ƙyalesa ta yi ba." Jazy ya yi tsaki yana girgiza kai bai ce masa komai ba.

Ray ganin kallon da Jazy yake yi masa sai ya ce, "kar ka yi tunanin na ce kar ta fita saboda wani abu ne, a ranar ma raina min hankali ta yi."

"Tana da number ka ne da zata kira ka ta raina maka hankali?."

"I was on video call with Kiddo, ban san ya aka yi na ganta apartment É—in Mamy ba, ka san Kiddo bata ji, kawai sai ta kai mata system É—in wai mu gaisa. Yarinyar nan tunda ta kalli screen sau É—aya ta É—auke kai ta cigaba da aiki da system É—inta, i was on the video call for over five minutes, but she didn't say anything to me. Sai kuma aka yi mata waya, ta É—auka tana cewa zan zo in anjima. Shiyasa na ce kar ya kai ta, kuma kar a bar ta ta fita."

Jazy ya buÉ—e ido cikin mamaki ya ce, "Wow! Haushi ka ji kenan dan bata kula ka?."

Ya wani kalle sa sannan ya ce, "Mamy ce?."

"Ba Mamy bace, amma....."

Ya dakatar da shi ya ce, "In ba Mamy ba, babu macen da zata ƙi kula ni na ji haushi."

"Kai a ganin ka ba haushi bane, ni a wajena haushi ka ji shiyasa ka saka a ka hanata fita."

Bai ce masa komai ba dan ba shi da amsar da zai basa, sai kuma ya ya tsaki ya ce, "Ni aure ma nake so na yi, na gaji da wannan wahalar."

Jazy ta yi dariya ya ce, "Wa zaka aura to?."

"Ban sani ba wallahi" ya faÉ—a yana rufe idanunsa a hankali.

Jazy ya ce, "ka san an yi attacking C wife É—in ka da mota?."

Ray ya buÉ—e ido ya kalle sa ya ce, "A ina?."

"Lawal ya ce min ya kai ta wani gida a cikin ƙauyen jimeta, tana fitowa aka yi kanta da mota za a taka ta, sai shi ne ya taimaka mata. Wannan firgici da tsoron da ta shiga sai da ya saka ta damu attack, daƙyar aka samu ta dawo daidai suka dawo gida. Abin tambayar a nan, waye ya yi attacking ɗinta, daga ɓangarenka ne ko daga wajanta?."

Ray ya harare Jazy ya ce, "Bata da ko sisi waye zai yi ƙoƙarin kashe ta? A kashe ta ace an kashe waye?."

Jazy jin da hausa Ray ya yi maganar sai ya yi dariya ya ce, "Matar Rehaan mana."

"ka manta, uwar matar Rehaan."

Jazy ya yi dariya sosai ya ce, "ashe ka iya zagi babu labari? Lallai Ray, baki yana ta buÉ—ewa. Kuma babarta dai ta yi maka rana, ta haifa ka aura."

"Yarinyar bata da hankali na faÉ—a maka, tsaf zata É—auko abinda wani zai ce zai kashe ta. Ni kaina ba dan ina tsoron Allah ba ai da yanzu babu labarinta."

Jazy ya ce, "In aka ce min akwai macen da zata raina ka kamar Islaha wallahi zan ce ƙarya ne, in aka ce min akwai macen da zata dinga faɗar maganar da ta ga dama a gaban idanunka zan ce ƙarya ne. Amma ga Miss Islaha ta goge min hadda, ta raina ka, raini na har abada. Tun kafin ta san waye kai take raina maka wayo, ko da ta sani ɗin ma bata daina ba."

Ray ya ce, "Tabbacin yarinyar su Ubaid ce, in da kamar su Riyya take baza ta yi ba.

Hmmmm! Yarinyar nan ni ta kalla ta ce min ta saba ganin maza da towel, ko babu towel É—in normal ne."

Jazy ya yi dariya son ransa dan shi da za a barsa da Islaha da ta zama maasa maganin damuwa. Ya ce, "Da ace ana saka mutum a pocket ko, Allah da ka ara min ita na saka ta a pocket, ta dinga bani nishaÉ—i ko yaushe."

"Ba abin dariya bane ba fa."

"To ko kaima ta ganka babu kayan ne? Ko daman shine silar rainin nan da ta yi maka?.."

Ray ya harare shi ya ce, "Allah ya kiyaye, da na ga wannan rana gwara na saka bindiga na harbe kaina. Ni da ita sai dai kallo, na fi ƙarfin irinta goma balle ita ƙaramar alhaki."

"Dama ta ce kai rago ne ai, maybe itama ba irin ka take so ba."

"Wai rago! Hmmm" ya faÉ—a yana shafa fuskarsa yana murmushi, dan shima sai ya ji nishaÉ—i a ransa, bai sani ba yadda Jazy ya mayar da abin wasa ne ya kawo haka, ko kuma ita É—in ce sila bai sani ba.

Jazy ya ce, "amma itace daidai da kai wallahi, gwara ta daina raga maka kana faÉ—a mata maganar da ka ga dama son ranka. Kuma wallahi, indai aka cigaba da irin wannan yanayin, akwai lokacin da za ka yi danasanin kiranta da karuwa."

Ray da mamaki ya kalle shi ya ce, "Wanne irin yanayi kenan?."

Jazy ya murmusa ya ce, "mu je zuwa dai." Bai ce masa komai ba ya É—auki waya yana dannawa shi kuma ya shiga inda Riyya ta shiga.

Nigeria.

Islaha tunda ta koma take bacci har bayan sallar magrib sannan ta tashi, ta yi wanka ta fito tana gyara kitson da Safeera ta yi mata. Ita ta riga ta saba, in tana period in ba a yi mata kalba ko kitso ba bata samun nustuwa, kuma guda biyu kacal ake yi mata irin na fulani.

Ta gama saka riga Mamy ta yi knock sannan ta buÉ—e ta shigo. Islaha ta kalli Mamy da take shigowa É—akin ta ce, "Sannu da zuwa Mamy."

Mamy da take kallonta ta ce, "ba ki da lafiya ne?."

"Lafiya lau Mamy."

Mamy ta harɗe hannu a ƙirji sannan ta ce, "Islaha meyasa ki ka fita a napep? Ba an baki driver da zai dinga kai ki aiki ba?."

Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, dan baza ta iya faÉ—awa Mamy hujjar ba, ko babu komai ta girme mata, kuma babu laifi tana yi mata kirki sosai.

Mamy ganin ta yi shiru sai ta ce, "Kar ki sake fita a napep, bana son yawan magana a gidan nan, na faɗa miki you are part of my family, ƙiris ake jira aka failure daga apartment ɗin nan ya zama abin magana."

Islaha ta É—aga kai ta ce, "In sha Allah bazan sake ba."

Mamy ta ce, "Good. Daada tana neman ki, in kin ci abinci sai ki je."

Islaha ta ce, "To Mamy."

Mamy har zata fita sai ta dawo ta ce, "wannan gashin ki?."

Islaha ta kali gashinta da jelar kitson da aka yi mata, wanda ta sauka har laps É—inta, ta kuma kallon Mamy ta ce, "Eh Mamy, nawa ne."

Mamy ta yi murmushi ta ce, "Ma sha Allah! Ga wacce ta fi Riyya" ta faÉ—a tana shafa gashin nata sannan ta fita daga É—akin.

Islaha ta ce, "ikon Allah, kamar basu saba ganin gashi ba, ita kanta Mamyn gashin ta mai tsaho ne dashi, amma nawa burge su yake yi" ta faÉ—a tana tattarewa kitson ta saka hula ta ta yafa mayafi a kanta sannan ta fito falon.

Bata samu kowa ba sai Banisha da sauran ƙannenta suna ta wasa. Ta ci abinci ta tafi wajan Daada kamar yadda Maamy ta ce.

Bata jima a can ba ta fito, tana fitowa suka yi kiciɓus da Salman. Gabanta ya faɗi matuƙa, kafin ta yi magana ya yi mata dariya ya ce, "ki ke guduwa bana ganin ki, ni na daina kula ki" ya faɗa kamar yaro cikin shagwaɓa sosai.

Sai ya bawa Islaha tausayi, ganin namiji babba kamar wannan rayuwarsa ta koma haka, gashi cikakken mutum, mutum mai kyau da suffar maza amma ƙwaƙwalwarsa irin ta yara ce.

Sai ta ji tausayinsa ya shiga ranta  ta ce, "Ka yi haƙuri."

Sai kuwa ya yi dariya ya ce, "Kin daina guduwa?."

Ta É—aga masa kai dan sai ta ji tsoron nasa yana barin zuciyarta.

Salman ya riƙo hannunta ya fara janta ya ce, "zo mu je mu hau mota."

Islaha ta turje ta ce, "A'a, ka cika ni."

Janta ya sake yi da ƙarfi ya ce, "mota zamu hau."
Chapter 58 · 0% Book details