← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 110

Sashe 102

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jazy zai yi magana ya dakatar da shi cikin wani irin yanayi mara daɗi ya ce, "ya ka ke min irin wannan maganar? Ka san wacece yarinyar nan Jazy, ta ya zan ka ce ina sonta? Aure contract ne a tsakanina da ita, lokaci mu ke jira komai ya ƙare. Wanne irin so zan yi mata haka? Dama haka ake jin son? A cikin raina ji nake kamar zai tarwatse. Haka son yake very cheap da zaka ce ina sonta? How comes?."

Jazy ya murmusa yana kallon yadda ya ruɗe lokaci ɗaya ya ce, "Haka ka ke gani, amma ni na san ba iya contract bane Rehaan, akwai abu mai ƙarfi da ya ke tsakaninka da ita. Shine ya canja maka yanayi, shine ya saka ka ke jin duk abinda ka ke ji a yanzu."

Ya girgiza kai cikin fitar hayyaci ya ce, "ba haka bane Jafar, ba abinda ka ke faɗa bane, ni ba wani love, babu shi a tsakanina da ita. Kar ka sake ɓata min rai akan wanda nake kai yanzu, ka bar maganar nan kafin kaina ya tarwatse...."

Sai kuma ya kalli sama yana furzar da iska mai ƙarfi yana girgiza kai ya ce, "gwara ma auren ya ƙare na koma England da zama, ba zan sake dawowa nigeria ba."

Jazy ya yi dariya ya ce, "well, we shall see." Ya faɗa yana ficewa ya ƙyale sa dan ya san daman bazai yi saurin karɓar maganar ba, sai ya fahimta da kansa sannan zai san gaskiya yake faɗa masa.

Jazy yana shiga wajan Mamy ya kalli Riyya ya ce, "Mu tafi?" Ya faÉ—a da sigar tambaya yana kallon ta. Mamy ta ce, "Jaafar baza ku zauna a nan zuwa gobe ba? Kana ji ance akwai matsalar rashin tsaro."

Ya yi murmushi ya ce, "Babu komai Mamy, zamu je lafiya."

Mamy ta É—aga kai ta ce, "Okay, kafin ku tafi É—in zo ka ji" ta faÉ—a tana tashi ta shiga ciki ya bi bayanta.

A tsaye ya same ta a parlour yana ƙarasawa ta kalle sa ta ce, "me ka fahimta daga yanayin Rehaan akan Islaha? Ba ka ga canji ba?."

Jafar ya yi dariya ya ce, "Mamy ko ke na san kin ga canji a tare dashi, ba ke kaɗai ba duk wanda yake tare da shi ya san ya canja. Mamy Ray yana son Islaha shi kansa ya fahimta, kawai ya ƙi yarda yana sonta ne saboda abinda yake tsakaninsu, amma wallahi ya san yana sonta."

Mamy ta yi murmushin jin daɗi ya ce, "na yi mamaki fa Jafar, yadda yake faɗa akan ta je inda ta samu attack ya bani mamaki shiyasa na tsaya ina kallonsa kamar tv. Ka san shi faɗa baya cikin halayensa, rabon da na ga yana irin wannan faɗan na manta, in na ce ban taɓa gani ya yi ba ban yi ƙarya ba. Amma ya za a yi da contract ɗin da yake tskaninsu kenan?."

Jazy ya ce, "contract yana nan Mamy, dan ita Islaha babu Rehaan a gabanta, shirin fita take yi ta auri saurayinta. Shi ne dai Allah ya kama sa ya saka masa soyayyarta har ta mayar da shk haka."

Mamy ta girgiza kai ta ce, "oh my God! Zan so na ga yadda wannan abu zai kasance, zan so na ga yadda za ayi da shi akan wannan maganar. Shi yana sonta ita kuma bata sonsa, ga shi kwanaki kaÉ—an ya rage su rabu."

Jazy ya girgiza kai yana dariya ya ce, "Mamy kin san Rehaan ba ya bari ƙaaramar dama ta kubce masa, ko ya ya ƙaramar dama tazo masa yana amfani da ita koda bazai yi nasara ba. Rehaan bazai taɓa bari contaract ɗin nan ya ƙare ba, sai ya ƙirƙiri wani abun da Islaha bazata kubce masa ba, sai ya yi duk yadda zai yi ta zauna a gidan nan ko da bata sonsa."

Mamy ta ce, "zan fi kowa son hakan, zan fi kowa farin ciki in ya kasance suna rayuwa a inuwa É—aya matsayin ma'aurata.

Rehaan ya samu macen da na ke buri ya samu, ya samu irin wacce na jima ina yi masa addu'a da fatan ya same ta. Islaha zata zauna dashi ba dan ya isa ba, ba dan tana sona ba, ba dan kuɗinsa ko kyau da wani abun ba, zata zauna da shi da ra'ayin kanta ba dan an yi mata dole ba. Islaha itace matar da na jima ina yi masa addu'a akan Allah ya ba shi. Ga shi Allah ya amsa ya ba shi ita ɗin, kuma tana ƙoƙarin kubce mana."

Jazy ya ce, "sosai kam, Islaha ta haÉ—a duk abinda ki ka faÉ—a, babu macen da ta raina Rehaan kamar ta, baza ta zauna da shi saboda abubuwan da ki ka faÉ—a ba sai ta ra'ayi."

"Kuma gata marainiya, ina yi mata fatan ta rayu a gidan nan ko dan ta samu gatan da bata samu a rayuwarta ba. Zan zamar mata uwa, Rehaan zai zamar mata uba kuma mijinta. Kai kuma ka zama Yayanta, Riyya da Banisha su zama ƴan uwanta. Duk wanda yake yi mata kallon mara gata daga lokacin zai yi danasani akan kalamansa, zai san gata da kansa in ya ganta sai ya girmamata. Ina son Islaha Jafar, haka kawai Allah ya ɗora min ƙaunarta a raina."

Jafar ya ce, "Bata da damuwa ai, tana da kirki da hankali sosai."

"Ku je ku tafi, dare yana yi."

"Okay Mamy, sai da safe."

"Allah ya kiyaye hanya."

Ya amsa ya fita, Mamy ta zauna tana tunanin yadda wanann kwamacalar zata kasance.

Ray ko da ya koma Islaha bata nan, ya tsaya cak yana kallon inda ta zauna yana tuna maganar Jazy da ya ce yana sonta, ya jingina da ƙofa yana ji zuciyarsa tana bugawa, har sai da ya ɗora hannunsa akan ƙirjinsa saboda yadda take ɗagawa. Ya jima a haka a tsaye, kafin ya yi tsaki ya hau sama.

A lokacin ta fito daga É—aki da hijjab a jikinta, tana so ta yi masa maganar mahaifiyar Ummi da ta je har office tana kuka, dan ita har ranta ta yafewa Ummi saboda mahaifiyarta, tana so ta ce in zai yu a fito da ita amma kuma tana jin haushinsa. Ya zuba mata ido yana kallonta yana so ya gasgata maganar Jazy, ita kuma ta janye idanunta daga kansa, kamar zata yi magana sai kawai ta fasa ta juya ta koma É—akin.

Rehaan ya bi ƙofar da ta rufe da kallo, kafin ya ja ƙafafunsa shiga ɗaki ya jingina da bamgo ya ce, "me nake ji akanta ne, meyasa na damu haka? Na manta wacece ita ne?." Ya hargitsa gashin kansa, ya samu waje ya zauna yana tunanin abinda ya kamata ya yi da zai daina jin wannan tashin hankalin.

"Anya bazan kawo ƙarshen contarct ɗin nan na daina ganinta ba? In na daina ganinta maybe zan daina jin abinda nake ji a kanta."

Ya kwanta da baya yana kallon sama, ya yi shiru yana tunani kala-kala wanda ya rasa mafita a cikin tunaninsa, ya juya ya yi ruf da ciki yana so ya gano abinda yake addabar zuciyarsa amma ya kasa. Gabaɗaya zaman ɗakin ya ishe shi, duk inda ya waiga ita yake gani a yanayi daban-daban, jin yana neman haukacewa sai ya miƙe ya ɗauki waya ya kira Shams ya ce ya zo su fita, a daren suka bar gidan dan gabaɗaya gidan ba ya yi masa daɗi ko kaɗan.

Shi da ya bar gida dan ya daina tunaninta amma sai tunanin ya fi na gidan yawa, duk inda ya juya ita ya ke kallo, in ya rufe ido murmushinta yake gani, a kunnensa kuwa muryarta yake ji lokacin da ta yi masa godiya.

Ya É—auki pillow ya cillar cikin É—aga murya ya ce, "Jazy why!....."

Sai kuma ya yi sanyi ya É—ora hannayensa a kansa ya ce, "Meyasa ka ce ina sonta? Meyasa ka faÉ—a min, meyasa ba ka yi min shiru ba?..."

Ya koma da baya ya kwanta yana rufe ido ya ce, "gashi na rasa nutsuwata, na rasa hankalina, na rasa tunanina, komai ya daina yi min daÉ—i. Jazy why...!" Ya sake faÉ—a kamar zai yi kuka, ya rasa inda zai saka ransa ya ji daÉ—i, duk inda yake zaune sai ya ji baya jin daÉ—i.

Bacci ya ke so ya yi amma ya kasa, in ya rufe ido ita yake gani, ya buɗe ita yake gani, muryarta yake ji a kunnesa, zatinta yake gani a ƙwaƙwalwarsa, ƙhamshin turarenta yake ji a hancinsa, taste ɗin bakinta yake ji a cikin bakinsa, laushin fatar ta yake ji a tafukan hannunsa. Gabaɗaya ya haukace, ya fita daga hayyancin gabaɗaya, ta ko wanne ɓangare Islaha ta yi masa kane-kane ta hana shi sakat, ko bugun zuciyarsa da sunanta yake bugawa.

Washe gari ko baccin safe na ƙa'ida bai yi ba, ya dinga kiran Jazy babu ƙaƙƙautawa.

Shi ba mai son tarawa mutane kira bane, ko Mamy in ya kira sau É—aya bata É—auka ba baya sake kiranta, amma yau shine yake jerawa Jazy kiran da bai san adadi ba, har sai da ya Jazy ya zo gidan.

Yana shigowa ya kalle shi ya ce, "Ray bashi ka ke bina ne ko ina da wata agender da kai da za ka takura min da waya? Ba ka san safiya bace, ina tare da matata gabaÉ—aya ka É—aga min hankali sai da na fito. Me zan yi maka?."

Rehaan ya kalli Jazy da idanunsa da suke lumshewa, cikin raunin zuciya da ya bayyana a tare da shi ya ce, "Meyasa za ka ce ina sonta? Jazy ka faÉ—a min na kasa nutsuwa, na baro gidan na dawo nan shima ban samu nutsuwa ba...."

Sai ya yi shiru kafin ya ce, "Na kusa haukacewa Jazy, ban san me yake damuna ba, ko in na juya ita nake gani, maganarta nake ji, na rasa ya zan yi na daina ganinta."

Jazy jin Rehaan ya yi rauni da yawa sai ya zauna a kusa da shi ya ce, "wannan shine love É—in Ray, ka yarda kana son Islaha."

"Ta ya zan yarda? Bayan ka san wacece yarinyar nan..." sai miƙe zaune sosai ya ce, "Yarinyar Ubaid ce, bayan nan bata daina duk abinda take yi ba, har Salman bata ƙyale ba."
Chapter 102 · 0% Book details