← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 110

Sashe 15

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"In ba za ki je ba Labiba ki sauka lafiya, Wallahi Jedda ba garin zama babu visa bane balle ki samu mafaka. Makka kuwa akwai inda zamu shiga, za ki manta a ƙasar ki ke saboda waɗanda za ki gani. In za ki je in anjima zamu hau mota, in baza ki ba ni kam zan wuce."

Labiba ta ce, "dole na na je ai, Allah ya kaimu" ta amsa da amin suka fara haÉ—a kayan da zasu wuce garin makka.

*Madina.*

Umma ta rame, ta yi duhu saboda wajigata da mutanen gidan suke yi, ta fita daga hankalinta saboda rashin ishashen hutu da rashin bacci.

Tana zaune a kan kujera tana gyangyaɗi, ta ji an kira ta da ƙarfi ta zabura ta miƙe tsaye tana goge idanunta.

Zuwa yanzu tana fahimtar abubuwa sosai a kalmomin larabci, itama su yalla, mafi, la la la, na'am duk sun zauna a bakinta sosai. Irin su zo, zauna, tashi, duk da larabci take faÉ—a saboda da zama kuma tana chuÉ—anya dasu.

Matae gidan ta ƙaraso ta nunawa Mama tulin  kayan wanki da akace ta wanke. Umma ta kalli kayan, bata zaɓi haka ta kwasa ta tafi ɗakin wankin ta zuba a washing machine tana yi gyangyaɗi.

Jiri ya ɗauke ta bata san ta zube a wajan ba sai da ta jita a ƙasa a kan tiles. Ta dafe kanta, ta kwanta ta huta kafin wankin ya gama bacci ya ɗauke ta.

Ruwan sanyin da aka watsa mata shine ya tashe ta, ta tashi a firgice a gigice tana jan nunfashi daƙyar ta zauna. Tana ji matar tana yi mata masifa amma ba fahimta take yi, ta gama ta fita Umma ta bi jikinta da kallo ganin yadda aka jiƙa ta sai kawai ta fashe da kuka. Ta haɗa kai da guiwa tana kuka sosai, ba komai take hange ba sai mijinta da yaranta da ta bari a gida ta taho tana bautar yaran wasu.

Kanta ya yi nauyi, ga ciwo ga jirin da take ji. Ta miƙe tsaye ta cigaba da wankin tana ji zazzaɓi yana rufe ta. Kafin ta gama wankin zazzaɓi ya rufe ta ko buɗe ido bata yi, bata sake sanin inda kanta yake ba sai buɗe ido ta yi ta ganta a asibiti an saka msta ruwa.

Tana buɗe ta ji babu ciwon kan, ya tafi gabaɗaya kanta ya daina yi mata nauyin. Ta kalli agogon asibitin ta ga ƙarfe bakwai na safe alamun ta jima tana bacci har gari ya waye. Ta mayar da ido ta rufe dan bacci ya kuma ɗauke ta, so take bacci ya sake ɗauke ta gwara ta fanshe baccin da ya tarar mata. Bata iya baccin ba ta miƙe, a lokacin wani likita ya shigo da sallama, kallo ɗaya ta yi masa ta san wannan ɗan ƙasar su ne dan ya yi kama dasu sosai.

Ya ƙaraso ya ce, "Hausa?."

Mama ta ji daÉ—i ya kamata ta ce, "Eh."

Ya yi murmushi ya ce, "Sannu Mama, kin farka?."

Umma ta miƙe ta ce, "na tashi."

Ya yi murmushi ya auna bp ta ya kalle ta ya ve, "Mama ya aka yi bp ya hau haka? Bakya samun bacci ne?."

Umma ta É—aga kai ta ce, "bana samun bacci ko kaÉ—an."

Ya É—aga kai ya ce, "meyasa bakya yin baccin?."

"Aiki nake yi."

Ya É—aga kai ya cigaba da abinda yake yi kafin ya ce, "waÉ—anda suka kawo ki suna ta zuwa kina bacci, in sun zo zance musukin tashi. Zuwa nan da azahar za a iya baki sallama ki koma gida. Amma ki gujewa rashin bacci da damuwa, in ba haka ba jininki zai dinga hawa ko yaushe."

Umma ta ce, "Don Allah kar ka ce musu na tashi, ka bar ni na yi bacci yadda nake so, don Allah."

Ya yo murmushi bai ce komai ba, dan ya fahinci aiki ta zo yi daga ƙasa nigeria, ya kashe ruwan ya fita ita kuma ta koma ta kwanta. Sai kuma ta tuna da sallah, ta miƙe ta shiga banɗaki ta yi alwala ta yi sallar da take kanta.

Kamar yadda ya ce bayan ssllar azahar aka sallameta suka koma gida. Ta shiga É—akinta a sanyaye ta zauna tana kallon maganin da aka bata.

Ta yi tagumi tana tunani, ko haihuwa bata taɓa sakawa jininta ya hau ba, amma yau ga aikin wahala ya saka jininta ya hau har ta samu.

Ta sauke numfashin nadama ta ce, "dole na nemi afuwar Baban Safeera, ya zama dole na nemi hanyar da zan koma gida, ya zama dole na bar gidan nan na koma nigeria."

Ta tuna abubuwan da suka faru, ta buÉ—e jakar ta tana kallon Æ´an kuÉ—in da tara wanda basu taka kara sun karya ba ta ce, "Ga shi dai na zo dan na tara kuÉ—i amma kuÉ—in basa taruwa, a magani ma kaÉ—ai suke tafiya, ya zan yi?."

Ta yi shiru babu mai bata amsa, amma ta yi ƙudurin ko me zata aikata yi zata yi indai zata bar ƙasar Jeddah ta koma ƙasar ta cikin ƴaƴanta da mijinta.

"In sha Allah zai yafe min, in Allah ya yarda zai yafe min ya mayar dani É—akina ko dan su Safeera. Da wannee ido zan kalli mutanen Katsina?."

Sai kuma ta sake yin tagumi da hannu ta ce, "na tafka babban kuskure a rayuwata, na bar halak na taho ina aikin da babu lada, na bar sharar masallaci na zo nan ina yin ta coci." Umma ta kwanta ta rufe ido cikin tunani da neman mafitar da zata koma gida ta riƙe yaranta?.

Washe gari....

Nana Haleema.

RDB3P12
Nana Haleema.

Islaha daƙyar ta iya yin bacci mai tsaho, tunda ta farka sallar asuba bata koma ba, tana idar ta miƙe ta shiga wanka, bayan ta shirya cikin abaya dan duk su Safeera ta zuba mata a cikin kayan da ta haɗa mata. Kayan ma gabaɗaya kala biyar ne sai undies na bacci, ta yi tsaki ta gama abinda zata yi ta zauna tana jiran bakwai na safe ta yi ta fita daga gidan.

Gajiya ta yi da zaman ta miƙe ta ƙarasa windwow ta buɗe tana kallon kyawawan ɗawisun da suke yawo a compound ɗin apartment ɗin. Murmushi ta yi dan ɗawisu suna burge ta sosai, akwai kyau da ɗaukar ido ga kuma tsada.

Kamar ance ta kalli gefen daga compound É—in ta hango Rehaan a tsakiyarsu yana basu abinci, ga tattarbu a gefe suna ta cin abinci da ya zuba musu.

Islaha ta taɓe baki tana hararasa kamar yana kallonta a bayyane ta ce, "Ni dai ban ga abinda mutumin nan zai yi ya burge ni ba wallahi, kalle shi don Allah, kamar wani na kirki har ciyar da dabbobi yake yi.”

Sai kuma ta ga ya ɗauko roll ɗin chocolate ya buɗe yana zubarwa a ƙasa. Islaha ta gyara tsayuwa a bayyane ta ce, "me zai da wannan kuma?."

Bata gama mammaki ba ta ga yana ɓarewa yana cillarwa a ƙasa, ta zuba ido tana jira ta ga abinda zai faru. Sai ta kuma ganin ya buɗe sweeted hollandia milk, itama ya zubar a ƙasa ya koma gefe ya tsaya ya harɗe hannu a ƙirji yana kallon wajen. Abin mamaki house flys ta gani sun hau kan alawar da holladia milk ɗin da ya zubar.

Islaha ta buɗe ido cikin mamaki ta ce, "kenan house flys yake ciyarwa ko kuma dai iskanci ne? Su ma flys ɗin in aka ciyar dasu lada za a samu?.”

Sai kuma ta ce, "Astagafirullah! Su ma halittar Allah ne. Amma dai wannan iyayi ne kawai, lallai sai ya nunawa mutane shi bature ne.”

Islaha tana tsaye tana kallonsa shi kuma ya jima a wajan a tsaye, kafin ta ga ya bar wajem ya shigo cikin gidan. Tana tsaye tana kallo sai ga mai gyara wajan yazo yana gyarawa, lokaci ɗaya komai ya dawo tas kamar ba shi ya ɓata wajan ba.

Islaha ta kulle window É—in ta ce, "É—an rainin sense."

Ƙarfe bakwai tana yi ta ɗauki jakarta da wayarta ta fito falon, galon shiru babu kowa, ko haske babu balle ta ga wani a zaune, ta buɗe ƙofar ta sauka daga saman, ko abinci bata tsaya ci ba ta buɗe ƙofar ta fita.

Gidan ma shiru kamaar ba monday ba, babu kowa sai masu aiki da suke ta kai kawo, ana ta hidima sa É—ore É—oren abinci. Bata cewa kowa komai ba ta nufi gate da sassarfa ta fita daga gidan bata cewa kowa komai ba.

Kai tsaye gidansu Safeera ta wuce, tana shiga gidan ta tarar da Safeera a tsaye ta juye ruwan wanka zata yi wanka. Ganin Islaha sai ta buÉ—e ido cikin mamaki ta ce, "ke meye haka?."

Islaha bata ce komai ba kawai ta shiga É—aki bata kula ta ba, Safeera ta bi bayanta da hanzari, ta same ta a tsaye tana kwance rolling É—in kanta tana cewa, "Bani tea na sha, yunwa nake ji." Safeera bata ce komai ba, ta fita ta kawo mata iya tea dan ta san bata cin abinci da sassafe.

Islaha ta zauna tana shan tea É—in a hankali, har lumshe ido take yi saboda jin daÉ—in tea É—in dan yunwa take. Safeera bata ce komai ba sai da ta gama ta ajjiye cup É—in, sannan Safeera ta ce, "ke kuwa kamar wacce aka koro, da sassafe ki ka fito daga gidanki?."

Ta É—ago ido ta kalle ta bata ce komai ba, Safeera ta ce, "lafiya na ga idanun ki sun kunbura haka Me ya faru?."

“Meye ma bai faru ba? Ki yi wankan mu shiga gida wajan Hamma, abinda ya fito dani kenan."

"Islaha na faÉ—a miki ki bari a kwana biyu, a yanzu babu lallai ya saurare ki."

"Ni a yanzu zan yi magana da shi, ki shirya kawai."

Safeera ta ce, "shikenan ai. Ga kayan ki nan, Mama ce ta tattaro komai na ki na cikin gidanta ta bayar aka kawo min, ina niyar na samu mai napep ya kai miki can, tunda yanzu kin zo sai ki wuce dasu."
Chapter 15 · 0% Book details