← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 110

Sashe 21

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Islaha basu gama aikin da zasu yi ba sai bayan sallar la'asar, duk ta gaji kuma ko abinci bata ci ba. Haka suka rabu da su Saleem ta wuce orphanage. Kamar ko yaushe da ta je kai tsaye wajan girki ta wuce dan Yafindo take so ta gani. Tana shiga suka haÉ—u da Baba Tabawa, Islaha da murmushi ta ce, "Baba ina yini."

Ta yi murmushi itama ta ce, "Lafiya lau Islaha, kwana biyu kin ɓuya ba a ganin ki kwata-kwata."

Islaha ta ce, "aiki ne ya yi min yawa, yanzu ma daga can nake. Yafindo ta dawo kuwa?."

Baba ta ce, "ta dawo."

Islaha ta ji daÉ—i ya mamaye mata zuciya ta ce, "Tana ina?."

Kafin a bata amsa Yafindo ta shigo tana magana. Islaha ta ce, "Hajiya Yafindo ina yini." Da sauri ta kalli Islaha, gabanta ya yanke ya faÉ—i, ta É—auke kai kafin ta ce, "Lafiya lau."

Islaha ta ƙarasa inda take tsate ta ce, "Wajan ki nazo."

Yafindo jikinta ya fara rawa ta girgiza kai ta ce, "aiki nake yi yanzu."

Islaha ta bita da kallon mamaki ganin ta tsorata sosai, kafin ta ce, "Ai iya maganar baki ce, ba wani abun ba."

"ni dai bazan saurare ki ba, dan Allah ki ƙyale ni na zauna lafiya."

Islaha ta dinga karanyar yanayinta kafin ta ce, "Yi min magana zai hana ki zama lafiya ne?."

Yafindo ta fara hawaye ta ce, "Dan Allah ki ƙyale ni, ki tafi kafin a ganki a wajena don Allah."

Islaha ta girgiza kai ta ce, "Yi haƙuri ki daina kuka, zan tafi. Amma ki bani saƙon da..." bata gama ji ba ta cillar da ludayin hannunta ta fita da gaggawa.

Baba ta kalli Islaha ta ce, "Nima na rasa me yake samunta, tunda ta dawo take a É—arare gabaÉ—aya bata sakewa."

Islaha ta ce, “Baba kina da waya?."

"Ina da ita."

"Don Allah bani lambar ki, zan dinga kira ina tambayar ki." Ba musu ta bata lamba ta yi saving Islaha ta fito daha kitchen É—in tana tunani.

Karo suka yi da mutum akan hanyar ta, Islaha ta kalli wacce suka yi karo suka haÉ—a ido, sai da gabanta ya faÉ—i ganin Hafsa ce.

Islaha ta bita da kallo ganin yadda yarinya ta canja, ta yi haske ga wata kiɓa ta musamman da ta ƙara. Hafsa ta ɗauke kai kamar bata gane Islaha ba ta raɓa zata wuce.

Ta riƙo hannunta ta dawo da ita baya ta ce, "In fuskar ki bata nuna kin sanni ba zuciyar ki ta nuna Hafsa. Irin rayuwar da aka ɗora ku kenan, a haka ake so a ga kun rayu? Kuna lalata rayuwarku su kuma kuna tara musu kuɗi, kun ɓata tarbiyar ku saboda abinda za ku tafi ku bari a duniya. Tunda haka ki ka zaɓa ya yi kyau, je ki" ta faɗa tana sakin hannunta sai Hafsan ta kasa motsawa.

Fadwa ta ƙaraso wajan ta ce, "Hafsa me ki ke yi a nan? Zo mu wuce" ta faɗa tana jan hannun Hafsan da ƙarfi suka bar wajan.

Ta office ɗin Mama ta zo wucewa, ta ga yadda yara suke shiga ciki sai kawai ta buɗe ƙofar itama ta shiga.

Ganinta ya saka Mama ta miƙewa tsaye babu shiri, Islaha ta kawar da tashin hankalin fuskar ta tana kallon yaran ɗaya bayan ɗaya.

Mama ta ce, "Islaha ke ce da yammar nan?."

Islsha ta É—aga kai ta ce, "Ni ce. Sannu ya aiki?."

"Lafiya lau. Kwana biyu bakya shigowa."

"Aiki ne yake yi min yawa. WaÉ—ananan sababbin zuwa ne?."

Mama ta kalli yaran ta ce, "wannan ne sabon zuwa? Da yawa duk kin san su."

Ta É—aga kai ta ce, "meeting ku ke yi kenan?."

Mama ta ce, "a kan dai sana'arsu ne kawai." Ta É—aga kai tana sake binsu da kallo kafin ta ce, "Shikenan, sai anjima" ta faÉ—a tana fita daga offife É—in.

Mama da gaggawa ta ce, "ku je, zan neme ku." Duk suka tashi suka fita.

Ta ɗauki waya ta kira ana ɗauka ta ce, "Kaza ta dawo gidanta tana tone-tone. A harbe ta ko a yanka ta. Aikin nan da na ce a dakata da shi, a aiwatar da shi a yanzu. Kamar yadda ba faɗa, bana so kowa sani.” Ta faɗa tana yanke wayae tana bin bayan Islaha da kallo.

Islaha tunda ta bar wajan take tunanin ya kamata ta É—auko mataki kafin abin ya sake yin girma.

Ta da ki hannunta tana dafe kai ta ce, "Hujja mai ƙarfi ce babu, Zainab ce hujjata ban san inda take ba, a ina zan ga Zainab? A ina zan nemo ta? Ina ta shiga?."

"Dole na san abinda zan yi, ya zamar min dole na san abimda zan yi" ta faɗa tana shiga lambar zainab tana scrolling ɗin recording ɗin da ta taɓa tura mata lokacin da tana a Jeddah har recording ɗin ya fita.

Baki buɗe Islaha take kallon wayar, wayar ta suɓuce a hannunta ta faɗi ƙasa. Audio ɗin ta ga babu shi a kan chat ɗinsu, an goge shi daga kan wayarta an goge shi daga chat ɗinta da Zainab.

A bayyane ta ce, "innalillhi wa'inna ilaihir raji'un!" Ta faÉ—a tana sake É—auko wayar ta cigaba da scrolling amma babu komai.

"Waye ya goge, ina ya shiga, yaushe aka goge shi?!" Ta faÉ—a tana cigana da bincika wayar amma babu.

Sai ta shiga lambar Hamma dan a lokacin tura masa, hannunta yana rawa take dubawa, ga maganar da ta yi masa akan audio É—in amma babu audio É—in.

Kanta ya sara ta shiga lambar Barr shima an goge daga kan wayarta, ta shiga Safeera itama an goge.

Bata san hawaye ya fara sakko mata ba ta runtse ido ta ce, "a ina aka goge? Yaushe aka goge min, waye ya goge?."

Sai kuma ta share hawaye ta ce, "Su waye suke yi min haka, waye yake tare dani da fuska biyu?."

"Ya zama dole na gano inda Zainab take, na gamo dalilin da ya saka Yafindo ta kasa yi min magana, sannan na gano munafukan da suke tare dani. Ni wayata babu security, kowa yana iya É—auka ya yi amfani da ita. Amma waye ya san na turawa Hamma, Safeera da Barr a lokacui É—aya da har ya bi lambobinsu ya goge?."

Kanta ya kulle ta rasa abinda zata yi wanda zai kawo mata mafita, ta jingina da bango tana jan numfashi, a lokacin aka fara kiran sallar magrib, cikin ta ƙulle saboda yunwa mai tsanani, ta runtse ido ta fito ta hau napep ta nufi gidansu Safeera.

Na ce waye ne yake fitar da sirrin Islaha? Mu je zuwa

Nana Haleema.

RDB3P18
Nana Haleema.

Islaha da sallama ta shiga gidansu Safeera ta tarar dasu suna zaune a tsakar gida gabaÉ—ayansu suna cin abinci. Duk suka amsa suna kallon ta Baba ya ce, "Wa nake gani kamar amarya Islaha?."

Islaha ta shiga ciki ta ce, "Ni ce Baba. Ina yini."

Baba ya ce, "Lafiya lau Islaha. Allah ya sanya alkhairi ya zaunar daku lafiya, Baffa ai ya faÉ—a min komai, na ce gwara hakan, Allah ya sa hakan alkhairi ne."

Mama ce kaɗai ta amsa da amin, ta ɗora da faɗin, "Kai ba ka ga yadda iyalan gidan suke ƙaunarta ba, abin ya burge ni sosai."

Islaha yaƙe kawai take yi wanda ya fi kuka ciwo, sannan kalli Safeera ta ce, "Sallah zan yi." A tare suka shiga ɗaki Islaha ta yi alwala ta tayar da sallar magrib bayan ta idar ta ce, "Yunwa nake ji Safeera."

Safeera ta ce, "bara na kawo miki." Ta fita ta kawo mata abinci, ta ci kaÉ—an ta ajjiye, dan yunwar ta yi mata yawa har ta kasa cin abincin.

Safeera ta ce, "na ganki wani iri, wani abu ya faru ne?."

"Meye ma bai faru ba, neman chaja min kai ake yi, ana so a tarwatsa min ƙwaƙwalwata kawai."

"Meya faru?."

"In ka ga ɓarna kana so ka kai ƙara don a gyara wajan wa ake zuwa? Police, Dss, ko kotu kai tsaye?.

Safeera ta ce, "bana ce ba gaskiya, amma zan tambayar miki na ji inda ake zuwa. Wani abu ne ya faru?."

Islaha ta ce, "komai ma ya faru, na gaji da ajjiye maganar nan ta gidan da na tashi, lokacin da zan bayyanata ya yi, ko kashe ni za a yi sai a kashe ni. Ina so na san inda Zainab take, ina so na san waye a jikina yake ƙoƙarin kaini ƙasa."

Safeera ta zauna a kusa da ita ta ce, "kamar ya a kai ki ƙasa, ban gane ba?."

Islaha ta ce, "mu bar maganar nan kawai."

Safeera ta ce, "Ai shikenan. Wai sai yanzu ki ka ci abinci tun tea É—in nan na safe?."

"Sai yanzu wallahi, shiyasa gabaÉ—aya cikina babu daÉ—i abincin ma na kasa cin mai yawa."

"Ai dole. Ki daina yiwa kan ki haka, kar ki sake jawowa kan ki wata matsalar."

Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, suna zaune har aka yi sallar i'sha suka yi sallah a É—akin Islaha ta koma ta jingina da wardrobe É—in Safeera kamar ba tafiya zata yi ba.

"Ba yanzu za ki wuce ba?."

Ba tare da ta kalle ta ba ta ce, "Ina?."

"Gidanki mana."

Ta É—ago ido ta kalle ta ta ce, "ina da gida ne?."

Safeera ta gyara kalamanta ta ce, "gidan mijin contract." Ta yi ƙaramin tsaki ta kulle idanunta ta ja numfashi sai kuma ta buɗe ido ta ce, "ni bana son tunawa zan koma wallahi, bana son komawa gidan nan."

"Haka za ki yi haƙuri ki koma, ke ki ka ce min so ki ke ya karya rule ɗaya dan ki samu mafaka. Ke kuma ga shi kina ta karya masa rule bakya tunanin shima zai samu mafaka a kanki?."

Islaha ta kalle ta ta ce, "bana so komawa ne, wallahi ko ganinsa bana ƙaunar yi, bana son tunawa ina tare da shi balle har na je gidan."

Safeera ta ce, "haƙuri za ki yi, ki tashi mu je na raka ki ki hau mota ki koma."

Kamar bazata tashi ba ta yi mata shiru, sai daga baya dai ta jure ta miƙe suka fito, ta yiwa Mama sallama suka fito kan titi.

Safeera ta ce, "meye ma sunan unguwar?."
Chapter 21 · 0% Book details