Sashe 52
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wulaƙanci kawai, dan ya nuna musu ƙasƙantacciya ce a gidan shiyasa ya yi min haka. Ya kira driver da aka saka ya dinga kai ni unguwa ya ce masa kar ya kai ni ko ina, sannan ya kira masu gadi ya ce wai kar a barni na fita. Ki ji fa rainin hankali, wai ni za a hana fita. Hmmm! Na rantse da girman Allah, ba dan wanda ya ce na yi haƙuri ya yi sa'an Baffa ba, wallahi sai na fita in ya so su ɗauko ni su dawo dani!."
Safeera ta ce, "baza ma ki yi hakan ba, amma meye dalilinsa na hana ki fita?."
Ta wara hannayenta ta ce, "shi ya sani. Saata ya ci kin zo, wallahi da ko....?" Dai ta kasa ƙarasawa saboda takaici.
Safeera cikin son kwantar mata da hankali ta ce, "Wataƙila yana da dalili."
"Dalilin me yake da shi? Ba ya ƙasar nan fa."
"Shi da ba ya nan ta ya aka yi ya san za ki fita, ko kin kira sa kin tambaye sa ne?."
Islaha ta bita da banzan kallo ta ce, "a matsayinsa na wa zan kira shi na tambaya dan zan fita?."
"Mijinki" ta bata amsa kai tsaye tana kallon ta.
"Dallah malama ki gyara kalaman ki, contract Husband."
Safeera ta harare ta ta ce, "ke dai ki ka sani. To ke ban da rigima me za ki fita ki yi da ranar nan? Nima sai da na fito na yi danasani saboda rana."
"Hamma ne ya kira ni ya ce yana so mu haɗu, ni yanzu ban san me zan ce masa ba....." sai kuma ta yi ƙwafa ta ce, "Ke sai ma na fita, in ya ga dama ya saka a kashe ni. In ban fita daga gidan nan ba ya yi galaba a kaina, ni kuma ban shiryawa hakan ba."
Safeera ta ce, "gwara hakan, ya yi min daidai da ya hanaki wallahi. Bakya jin magana, na rasa ina iliminki ya tafi, na rasa gane canja ki aka yi ko wani abun ne ya shiga kan ki dai ban sani ba, ko kuma daman addinin na ki a baki yake bai kai zuciya ba dai duk ban sani ba. Kina matar wani, igiyar aure uku cif a kan ki, amma ki dinga biyewa wani namiji har yana cewa zaku haÉ—u da shi waje? Kina manta haramcin da yake cikin hakan, saboda Saheer ya rufe miki ido."
"Safeera ya kamata ki gane ba da wani nufi nake zuwa mu gaisa ba, ya kamata ki tuna waye Hamma a gare ni. Ina jinsa kamar jinina saboda kusancinmu, akan me dan na je wajansa zai zama laifi?."
"Inda da zuciya É—aya ki ke zuwa wajansa babu laifi, amma kina zuwa wajensa a matsayinsa na wanda ki ke so kuma wanda za ki aura. Wallahi ina guje miki fushin Allah, ana ta rubuta miki zunubi lodi lodi."
Islaha ta ce, "A'a wallahi, tunda muka yi maganar nan na daina zuwa wajensa da wannan niyar, ina zuwa mu gaisa ne saboda shi É—in É—anuwana ne, ko maganar auren ya kawo min bana son amsawa."
Safeera ta ce, "wataƙila a jikinsa ya ji za ki je wajan Saheer, shi kuma yana kare martabar aurensa shiyasa ya hana ki fita."
Islaha ta buÉ—e idanu waje ta ce, "shi É—in ne yake kare martabar aure? Shi É—in da yake turo min É—an uwansa mahaukaci har yana cewa nima ina son mahaukacin, wannan ne kare martabar auren?. Shi bai ma san meye martaba ba balle ya kare ta, wanda bai san martabar mace ba ta ya zai san martaba aure?. Kuma kawai dan zan fita sai ya ji a jikinsa saboda ni É—in tasa ce?."
"Tasa ce mana, matarsa ce ke fa."
"Mtsw! In kina cewa matar nan sai na ji kamar na rufe ki da duka....In ba dan ke É—in ba ce babu wanda ya isa ya dinga faÉ—a min maganar nan."
Safeera ta yi dariya bata ce komai ba. Islaha ta ce, "Na fi tunanin a wayar da nake yi da Hamma ne ya ji, dan lokacin ƙanwarsa ta ajjiye min laptop ɗina suna video call, ni kuma aka kira ni, tabbas a nan ya san zan fita."
Safeera ta yi dariya cike da tsokana ta ce, "gaisawa ku ka yi kenan?."
"Na gaisa da wa? shi É—in? Allah ya raba gatari da saran shuka. Yadda ta ajjiye haka tazo ta É—auka, ko kallo bai ishe ni ba wallahi.."
Safeera ta ce, "to ai ba burgewa ki ka yi ba ai, dan ko babu aure ya girme miki." Islaha ta yi tsaki ta zauna a akan kujera ta yi mata banza.
Safeera ta zauna ta ce, "Ba ki kyauta ba dai, ko irin ka je lafiyan nan ya kamata ki ce masa. Ke ki ke kallon aurenku a matsayin na yarjejeniya, amma a wajan Allah ba haka abin yake ba. Kuma haÉ—uwar ki da Saheer ba daidai bane, in dai ki ka haÉ—u da shi wallahi sai an rubuta miki zunubi."
Islaha bata ce mata komai ba, dan ta riga ta bata wannan amsar tun farko. Safeera dai ta kawar da zancen ta ce, "na kawo miki ziyara, ba ruwa balle abincin ƴan gayu." Islaha ta yi tsaki ta ce, "Ya ɓata min rai ne wallahi, kuma ni marata ciwo take yi."
Safeera ta ce, "ko ba ki faÉ—a ba ai, fuskar ki ta nuna kina kan hanya."
Ta miƙe ta ɗauko nata ruwa da lemo ta ajjiye mata. Safeera ta ce, "Abinci fa?."
Ta kalle ta ta ce, "ke ni ba a nan nake kwana ba, a ɓangaren Babarsa nake kwana, tsoron nan nake ji. Na san wannan wahalallen chef ɗin nasa baya nan, kuma ni wallahi bazan iya girki ba, ban taɓa shiga kitchen ɗin nan ba balle na yi girki, in za ki iya bismillah.
Safeera ta ce, "inye ka ga matar mai kuɗi, ki ce sai dai a dafa a baki, a ɗauke miki kuma a wanke? Shiyasa har ƙiba ki ka yi."
Ta harare ta, Safeera ta yi dariya ta sha ruwan tana cigaba da janta hira, dan ta ga yanayinta yana canjawa alamun ta fara jin ciwon sosai.
Sama-sama suka yi hira, ta lura har lokacin bata huce ba ga ciwo, a nan suka yi sallar la'asar. Bayan sun idar da sallah Islaha ta miƙe tana yamutsa fuska ta ce, "na fara jin ciwon nan sosai, ina da pcm a ɓangaren babarsa."
Safeera ta ce, "ke kuwa ba Mama sai babarsa? Ke wacce iri ce ne?."
Bata ce komai ba, Safeera ta ce, "mu je ki ɗauko." Bata musa ba, suka fita zuwa ɓangaren Mamy, suna shiga suka haɗa ido da Ammi da Mamy a zaune suna hira.......
Nana Haleema.
KRBBK:
RDB3P41
Nana Haleema.
Islaha ta ɗauke kai daga kallon Ammi suka ƙarasa cikin falon ta kalli Mamy ta ce, "Mamy ga ƙawata, sunanta Safeera."
Mamy ta kalli Safeera da fara'a ta ce, "Sannu Safeera, ya ki ke?."
Safeera ta gaishe da Mamy ta amsa tana ta murmushi, Ammi ta kalli Islaha ita kuma É—auke kai bata ce.
Mamy ta ce, "ku je ciki mana." Islaha ta riƙe hannun Safeera suka wuce Mamy da Ammi ba tare da sun kula ta ba.
Suna wucewa Ammi ta kalli Mamy ta ce, "Ban gane ba, kin yi accepting yarinyar nan kenan?."
Mamy kai tsaye ta ce, "Na ga bata da wani problems."
Ammi ta buÉ—e idanu cikin mamaki ta ce, "wannan za ki cewa bata da matsala, kin manta abinda ta yi mana a asibiti, ko kin manta abinda ta yi min a gidan nan?. Har kin saki jiki da ita tana zama a apartment É—in ki?."
Mamy ta ce, "A asibiti kuskure aka samu, sannan na gidan nan ma duk kuskure ne."
Ammi ta girgiza kai ta ce, "Kina bani mamaki, a haka ki ke cewa za ki kare Rehaan? Bayan ga wacce ta shigo da niyar ganin bayansa kin bar ta a zaune a ɓangaren ki? Gaskiya kin bani mamaki Nadira, ban yi tunanin za ki yi saurin yarda da ita akan Rehaan ba.
Mamy ta yi shiru bata ce komai ba, dan ita har ranta a yanzu bata ga laifin Islaha ba, duk da har lokacin tana kan gwadata, amma bata ga wani kuskure a tare da ita ba, amma sai ta gama gwajin zata tabbatar da ita É—in wacece.
Ammi ta ce, "Me zai yi da yarinyar nan, kallle ta fa kaf in laws É—in gidan nan farare ne, ko kunya bakya ji a ga wannan a matsayin sirikar ki?."
Mamy cikin rashin damuwa ta ce, "Skin type É—inta yana da kyau, ni sai nake ji kamar na cire nata na bata nawa. Kuma Rehaan irin skin type É—inta yake so, ya jima yana faÉ—a min shi bazai auri farar mace ba, kin ga an yi eqaul."
Ammi zata sake magana Mamy ta dakatar da ita ta ce, "Ina kan bincike a kanta, in na gama da kaina zan saka ya sallame ta." Ammi ta yi shiru bata ce komai ba, baƙin ciki kamar ya kai ta lahira, tana ji a ranta in ta bar Islaha kamar ta yi nasara a kanta, sai ta yi maganinta.
  Islaha suna shiga ɗakin Safeera ta ce, "kai! Kuɗi suna inda suke, kalli wani haɗɗɗen falo da Mamy take zaune. Gaskiya Mamyn nan kyakykyawa ce, dole kishiyoyinta su dinga kishi da ita. Ki kalli gashi har baya kamar ba babba ba, ga maganarta kana ji ka san ba ƴar nan bace."
Islaha ta ce, "Wannan wacce suke tare munafuka ce, bata ƙaunata."
Safeera ta ce, "Na ga alama, sai hararar ki take yi. Amma itama Mamy ranar buɗan kanki ranta a ɓace yake, ya aka yi ta sakko haka?."