Sashe 100
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai ta É—an ji wani iri a zuciyarta kamar bata kyauta ba ta ce, "ashe fa yana nan nake waya da Hamma."
Sai kuma ta ce, "to meye dan na yi wayar, ai ba wani abun nake faɗa ba gaisawa ce kawai."Da wannan tunanin ta share komai ta cigaba da harkokinta, ana ta yi mata waya ana yi mata murnar abinda ya faru tana jin daɗi. Bata yarda ta sauka ƙasa ba, kar ta haɗu da wani ɗan gidan a ɓata mata rai.
Shi kuwa Rehaan kai tsaye gidan Riyya ya wuce, ya samu bata nan amma jazy yana nan, ya zauna ya rufe ido bai ce komai ba.
Jazy ya share shi shima dan bazai kula shi ba ya san banza zai yi masa. Sai da ya gama zaman sannan ya ce, "a wanne date mu ka yi signing contract ni da c wife?.
Jazy cike da mamaki ya ce, "ikon Allah! Lokacin ma ni zan riƙe ma ka?."
"Jazy ka amsa min kawai."
"Ban sani ba, ai ba ni na ke zaune da ita ba balle na riƙe."
"Na ji tana saura one month fa."
"It can be possible ai."
Ya yi shiru sannan ya ce, "lokacin ya yi gudu sosai."
"Ba ka so ya yi gudun ne?."
"No, kawai dai..." sai kuma ya koma ya jingina da kujera bai ce komai ba.
Jazy ya É—an kall sa sannan ya ce, "so meye na damuwa dan lokacin ya zo, daman ba abinda ku ke jira kenan ba?."
Ya kalle sa ya É—afa kai ya ce, "yeah haka ne."
"So take a chill pill, lokacin da ka ke jira ya kusa, ku rabu ka huta da wannan tashin hankalin itama ta huta, ba shikenan ba?."
Wata irin bugawa zuciyarsa take yi, tana zafi-zafi kaɗan-kaɗan ba tare da ya san dalilin hakan ba, ya sake jingina da kujera ya ɗora ƙafa kan ɗaya ya sake rufe idanunsa.
Murmushinta na ɗazu ya gifta masa a idanu, ya buɗe idonunsa ya sake rufewa, ranar da ya kwance mata towel ya gifta a idanunsa, da yadda dogon gashinta ya mamaye fatar jikinta. Da sauri ya buɗe ido, yana jin wani irin shock mai ƙarfi har brain ɗinsa.
"Oh my god!"
Ya furta ba tare da ya sani ba yana sauke numfashi a hankali. Jazy ya kalle sa ya yi dariya bai ce masa komai ba.
Rehaan tunda ya yi shiru bai kuma magana ba, sautin bugun zuciyarss kawai yake ji, bai san abinda yake damunsa ba kawai ya san ba ya jin daÉ—i a jikinsa.
Sai kuma ya kalli Jazu ya ce, "a kan waye ma ta yi signing?."
Jazy ya kalle shi ya ce, "saurayinta Saheer. Yanzu haka suna shirye-shiryen aure, kana sakinta zai yi wuf da kayarsa, daman babu idda a kanta balle a ce sai an jira, kuna rabuwa a ranar zata faÉ—a gidan masoyinta."
Ya shafa kansa bai ce komai ba yana girgiza ƙafa, jikinsa har wani rawa yake yi saboda sabon yanayin da yake mamaye masa jikinsa gabaɗaya, yana ƙoƙarin ɓoyewa ne saboda kar Jazy ya tambayesa dalili shi kuma bai san me zai ce ba.
Jazy da yake kallonsa ta ƙasan ya ce, "Ai yaron nan yana matuƙar ƙaunar ta, kuma ya yi sa'a sosai, ya samu mai ƙaunarsa. Ta yi aure saboda shi, kuma zata fita saboda shi. Babban abinda ya saka nake taya shi murna shine a zaman auren da tayi babu abinda ya canja daga gare ta, yadda ta shiga haka zata fito, haka zai ɗauki kayyasa sabuwa dal."
Ya runtse ido yana jin wani abu yana sukar ransa, ya buÉ—e idanunsa cikin son kawar da wancan yanayin da son kushe ta ya ce, "Ita wannan har wata sabuwa ce? Ka manta wacece ita?."
Ya yi dariya ya ce, "kai a wajanka ta ke a haka, shi a wajansa sabuwa ce dal. Yadda ko wanne ango yake mararin amaryarsa, shima haka yake mararin matar da za ka saki."
Ya yi tsaki kawai bai ce komai ba, ya sake kallon sa kamar zai yi magana sai ya share ya rufe ido.
Jazy ya girgiza kai yana kallonsa yana dariya tare da godewa Allah, ko ba a faɗa ba ya san Rehaan ya faɗa tarkon love, Rehaan yana son Islaha, rabuwa da ita zai yi matuƙar wahala. Ita kuma har yanzu ba ya gabanta, Saheer ɗin ne a gabanta, dan shi ta auri shi. Ko ya wannan chakwakiya zata kasance?.
Nana Haleema.
RDB3P73
Nana Haleema.
Islaha ta koma wajan aikinta kamar yadda Rehaan ya bata ƙarfin guiwa ta yi amfani da kalamansa ta cigaba da harkokinta tunda ba a san matarsa bace har lokacin. Su Ummi kuwa suna prison an yanke musu hukunci, daga gidan kuma a ɓangaren Salman bata kuma jin komai ba, hasalima Umma da Salman ɗin ba sa nan. Sai dai yanzu babu magana ita da Mama, har Daadan ta daina zuwa gaishe ta. Da yake shine mai faɗa a ji a gidan babu wansa ya sake tayar da maganar balle a ce ta bar gidan, kowa ya shiga hankalinsa.
Gab da zata tashi daga aiki su gama gaisawa da Hamma a da ya koma Niger yana gab da dawowa, ta gama haÉ—a kayanta kenan aka shigo da wata mata cikin office É—in.
Islaha ta kalli matar ta ce, "sannu baiwar Allah."
Matar ta ce, "Yauwa Islaha. Ya aikin?."
"Alhamdu lillah! Ki zauna."
Ta zauna sannan ta ce, "na san ba ki sanni ba. Sunana Hajara, ni ce mahaifiyar Ummi da aka kai gidan yari."
Islaha ta ce, "Ayya, ban san ki ba."
Hajara ta ce, "alfarma nazo nema a wajan ki, don Allah don girman Allah ki yi haƙuri a fito min da Ummi daga gidan yari, Ummi budurwa ce bata taɓa aure ba, zamanta a gidan yari zai lalata mata rayuwa gabaɗaya. Don Allah ki ji ƙaina, a matsayina na mahaifiyarta ki saka a fito min da ita."
Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, matar ta fara yi mata kuka. Islaha sai ta ji hankalinta ya tashi ta ce, "Mama don Allah ki daina kuka."
"Dole na yi kuka, zaman gidan yari ga mace bashi da daɗi. Na san ta yi kuskure, ta aikata babban laifin da ya kamata ace an kama ta, amma ki yi min wannan alfarmar dan matsayin annabi, ki saka a fito mun da ita. Na yi miki alƙawarin zan ɗauke ta ta koma zamfara can wajan dangina, baza ki sake ganinta ba har abada."
"Mama bani na kulle ta ba, bani da ikon da zan saka a fito da ita."
"Kina da shi, tunda case É—in ki ne, don Allah taimaka min don Allah."
Islaha ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Mama ban yi miki alƙawari ba, amma zan san abinda zan yi in sha Allah."
"Ki taimaka min don Allah."
"In sha Allah."
Daga haka suka yi sallama ta fita duk ta kashewa Islaha jiki, ta ta fito Lawal ya É—auke ta zuwa gidansu Safeera da aka kawo lefen aurenta.
Rehaan yana zaune a gida aka kira shi a waya ya É—auka aka ce, "Sir akwai matslaa, akwai matsalar tsaro. Kar a bar kowa ya fita, in an fita a dawo."
Abinda aka faÉ—a kenan sai ya kashe wayar ya kira su Mamy ya tabbatar kowa yana gida, har janan sai da ya hana fita da su ikram. Can kuma sai Islaha ta zo ransa, ya kalli Jazy da yake kallonsa kafin Jazy ya ce, "C wife É—inka ya kamata ka fara kira ba su Janan ko Riyya ba."
Bai ce komai ba ya kira number Islaha amma ba a ɗauka ba, ya sake kira ba a ɗauka ba dole ya haƙura dan shi ba ya son a tara masa kira, shima kuma ba shi da lokacin tarawa wani kiran.
Jazy ya ce, "ya kamata a san inda ta ke fa, tana cikin familyn nan a yanzu, ta fi kowa kusa da kai, ita za a fi saurin cutarwa fiye da kowa."
Rehaan sai ya ji hankalinsa ya tashi sossi ya ce, "waye ya ke fita da ita?."
Jazy ya ce, "Lawal ne, ka kira shi yanzu nan."
"Bani da number, kira shi please."
Jazy ya ɗauko waya yana yanga kamar bazai kira ba, yana danna wayar kamar ba ya so dan ya ƙular da Rehaan ya ga yanayinsa.
Ray bai san ya karɓi wayar daga hannunsa ba ya ce, "Ana sauri ka tsaya kana yiwa mutane iyayi? Sai wani abun ya same ta?" Ya faɗa yan kiran Lawal. Yana ɗauka ya ce, "kana ina?."
Lawal ya ce, "na kai hajiya gidansu ƙawarta, yansu haka tana ciki."
"Ka kira ta da gaggawa ku dawo, bana son ɓata lokaci ku dawo yanzu."
Tana gama faɗa ya cillawa Jazy wayar shi kuma ya chafe yana kallon Rehaan ɗin da hankalinsa yake a tashe sosai. Jazy ya ɗaga gira sama yana murmushi, sai ya miƙe ya fice bai ce komai ba.
Islaha kuwa tana can wajan Safeera, tana ganin kiran Rehaan bata É—auka ba, bata san lambar waye ba ta ga dai ana yi mata waya kuma bata É—auka ba.
Sai bayan sallar magrib sannan suka taho gida, tun daga farkon estate ɗin ta san akwai wani abu, dan an ƙara tsaro mai yawa kamar gidan shugaban ƙasa.
Suna shiga kai tsaye ɓangarensu ta nufa ta hau sama sai ta tsaya cak ganinsa a tsaye yana kallonta kamar jiranta yake yi.
Rabon da su haÉ—a ido da shi tun ranar da ya yi mata maganar aiki, daga nan ta daina ganinsa ko a wajan Mamy, Mamy ce take faÉ—a mata aiki ne ya yi masa yawa shiyasa ba ya zama a gida.
Haɗa ido da shi ya saka jikinta ya yi sanyi sosai, a hankali ta ƙaraso inda ya ke kafin ta yi magana har ya ƙaraso daf da ita yana kallon idanunta, ya girgiza kansa ya ce, "so i called you, and you were not picking my call."