← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 110

Sashe 108

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hawaye ya ciwon mara ya zubo daga idanunta, ta runtse ido maimaikon ta ba shi amsa sai ta ce, "ni ban san dalilinsa na yin hakan ba, amma ba daga ni bane."

Saheer bai yi niyar yi mata maganar ba, amma jin ta kawo maganar sai ya ce, "Islaha ya faɗawa duniya ke matarsa ce, sannan ya pecking ɗinki a gaban kowa, ya yi holding hannunki yana kallon cikin idanun ki. Ni ban ce ya yi laifi ba tunda ke matarsa ce, amma batun dawowar ki na haƙura kawai, dan na san baza ki taɓa dawowa gare ni ba."

Islaha zuciyarta ta karye jin kalaman Saheer, tana tunanin shikenan zata tabbata ta zaɓi kuɗi akan halacci. Cikin gigicewa ta ce, "Kar ka sare, kar ka ji tsoro Hamma, na yi maka alƙawari zan dawo, bazan taɓa zama matar wani ba sai kai, kai ɗaya na shirya rayuwar aure da shi ba wani ba. Na aure sa saboda kai, kuma zan fito saboda kai, kuma na aure ka na zauna da kai."

"Islaha tsoro nake ji, gwara kawai na haƙura mu cigaba da kasancewa a matsayin Yaya da ƙanwa. Yana da kuɗi da ikon da baza ki iya ja da shi ba."

"kuɗinsa ɗin banza da wofi, ni kuɗinsa ba sa gabana, abinda yake gabana kawai na sani, kuma shi zan yi. Hamma kar ka yi tantama akan alƙawarin da na yi maka, wallahi sai na dawo gare ka a daidai lokacin da muka tsara hakan, zan aure ka a lokacin da da ka tsara auren. Abinda ya faru yau kar ya dame ka, in ma ya yi ne saboda wani dalili shi ya sani, ni dalilinsa ba ya gabana!."

Ya yi shiru kawai bai ce komai ba, dan da gaske hankalinsa ya tashi sosai, ya kasa zaman Niger jirgi yake nema kawai ya dawo nigeria, dan tunda aka É—auke su a hanya ya daina zuwa a mota sai jirgi, da ace ya samu jirgi a ranar zai dawo bazai cigaba da zama ba.

Ya kalli video ya fi sau babu adadi, babu abinda yake sakawa ya ji babu daÉ—i zuciyarsa kamar pecking É—inta da ya yi a kumatunta, faÉ—ar matarsa ce bai dame sa ba saboda yasan gaskiya ya faÉ—a, yadda yake kallonta ya É—aga masa hankali, dan kana ganin kallon ka san na soyayya ne zallah.

(kai ma dai Hamma kana tare da wahala).

Saheer ya sauke numfashi ya ce, "In ban yi haƙuri ba me zan yi? Haƙuri ya zamar min dole, amma...." Sai bai ce komai ba ya yi shiru.

"Hamma alƙawarin Islaha ne, babu mijin zata zauna dashi a matsayin mijinta sai kai, in na bar ka ban yi halacci ba, ni kuma bana so na zama butulu a duniya, ka yarda dani Hamma." Bai ce komai ba ya yanke wayar, ta yi tsaki tana danasanin zuwa wajan taron.

Facebook ta shiga ta ga yadda ake ta zuzuta maganar, ga mutane suna ta comments da Allahamumma bareek, ga masu cewa ta yi sa a suna yi, masu cewa basu dace ba suna faÉ—a, masu cewa sun dace suna faÉ—a.

Islaha ta yi tsaki ta ce, "ku ne ƴan wahala da ku ke ganin zama da wannan sa a ce, ni a gare ni babbar rashin sa a ce. Meye abin so a tare dashi oho, haushin matan da suke haukacewa a kanaa nake yi.”

Sai kuma ta kalli inda ya shiga ta ce, "ya zama dole na je mu yi ta ta ƙare, yana karya min rules, ko ya sake ni ko ya tsaya iya matsayinsa har kwanakin mu su ƙare" ta faɗa tana miƙewa ta shiga inda ta ga ya shiga.

Rehaan yana daga tsaye yana kallon ta, duk abinda ta faɗa ita da Saheer ya ji, ya cize lips ɗinsa ya koma ganin ta taho a fusace irin jaruman india nan. A tsaye ta same sa ya juya baya yana sanye da baƙar bathrub wacce ta tsaya a iya guiwarsa.

Tana shiga ta a ce, "Mr Rehaan na zo mu yi magana ta ƙarshe, don Allah mu kawo ƙarshen contract ɗin nan kowa ya huta."

Ya juyo ya kalle ta, yana jin kishin Saheer yana mamaye masa zuciya, kishi ya hana shi yi mata magana ya É—auke kai.

Islaha ta ce, "ina magana ka yi min banza, kana ta breaking rules É—ina bayan ba haka muka yi da kai ba, mu ajjiye abinda ya faru jiya a gefe. Meye naka na faÉ—awa duniya ni matarka ce bayan ka ce baka son kowa ya sani? Kai ka ce min auren sirri mu ka yi, meyasa za ka faÉ—awa Æ´an jarida da kanka?."

"Saboda ba na sirrin bane."

Ta shiga shock da kalamansa amma sai ta ce, "Dole ya zama na sirri, kamar yadda ka ɗora auren a kan haka dole ya cigaba da tafiya a haka. Ka ɓata min rai da abinda ka yi yanzu, ka ɓatawa......"

Sai harshenta ya sarƙe ta kasa faɗar sunan Saheer, sai ta canja maganar ta ce, "ka ɓatawa waɗanda nake tare dasu rai."

Rehaan da ya ji kamar ya yi ta dukan kansa har aai ya fitarwa da kansa jini, ya cize bakinsa cikin yanayin kishi ya ce, "Nawa za a biya shi ya yi farin ciki?."

Ta sake kallon sa ta ce, "what! Kana tunanin akwai abinda za ka basa ya yi farin ciki da ya wuce ni? Ko kana tunanin ina zaune da kai a nan saboda kuÉ—i ne?."

Sai kuma ta dafe kai ta ce, "ai baka da kuɗin da zai karɓa daga gare ka ba, ba ka da kuɗin da zaka iya siyana daga wajensa. Kuma inda ace na san kallon da ka ke yi min kenan, da duk abinda na yi maka wallahi sai ka biya ni, ina so mutum ya cigaba da kallona a yadda yake kallona, bana so na canjawa mutum fahimtarsa a kaina. Har jinyarka da Mamy ta dinga saka ni, da wacce ta wuce da ta jiya wallahi da sai ka biya."

Rehaan ya yi murmushi yana mamakin ko yaushe ya ce mata tana zaune da shi dan kuÉ—insa oho. Ya waiwayo yana kallon ta yana takawa zuwa inda take ita kuma tana yin baya kaÉ—an-kaÉ—an tana cewa, "ka daina bana so, ka dakata don Allah."

A daidai lokacin suka zo kusa da gadon, ya saka hannu guda É—aya ya turata ta faÉ—a kan gadon, ya kwance igiyar gaban rigar wankansa ya buÉ—e ta ba tare da ya cire ba, ya bi bayanta ya dafa hannayensa a kan gadon yana kallon idanunta.

Islaha yadda ta faÉ—a kan gadon ya tsorata ta, ga shi ta ga yana kwance riga ya buÉ—e ta ya saka ta yi saurin rufe ido gabanta yana faÉ—uwa amma ka kasa magana.

"Kina magana akan kissing É—in ki da na yi jiya?....." ya faÉ—a yana É—ora yatsansa akan lips É—inta yana zagayawa da shi.

Ya sake sunkuyowa yana kallon bakinta kamar zai É—ora nasa akan nata sannan ya ce, "Fine! One million to whatever you want, is enough to buy you again?."

Nana Haleema.

RDB3P80
Nana Haleema.

Islaha ta tsorata sosai musmaman da ta ji maganarsa daf da ita, kuma ga shi ya ɗora yatsansa akan bakinta. Ta wuntsila ta juya ta sauka daga kan gadon, cikin masifa da tsiwa ta ce, "You treat me like i'm just some toy, that you can wind up and toss aside. Na fi ƙarfin ka yi wasa da hankalina, kuma ka tsaya a inda ka ke tun farko, ka daina zuwa inda baka da hurumi a kai. Ka yi min jiya na yi shiru ban ce komai ba, ba dan ka yi nasara ba sai dan saboda wani dalili nawa shiyasa na share maganar ban ce maka komai ba..”

Daga jiya ya zama na ƙarshe, kar hannunka ya sake zuwa jikina, ko da wasa kar ka sake kuskuren cewa zaka taɓa ni. Ni matar yarjejeniya ce, ina da hujjar da zan kai ka court akan taɓa min jiki, tunda ina da shaida ka saka hannu kuma ka amince baza ka taɓa ni ba. Ka dakata haka don Allah, ka jira lokacinmu ya ƙare kowa ya kama gabansa.”

“In na tafi sai ka manta ya kalar fuskata take, ni daman ban riƙe kamaninka ba balle har na tuna. A zamana da kai babu wani abu mai amfani da zan dinga tunawa dashi lokacin da na bar gidan. Sai sharrin ƴan gidanku da sunayen da ka dinga kirana da shi, ni bani da lokacin tunawa da kai kaima ka daina, mu jira lokaci ya ƙare kowa ya watse” ta faɗa tana fita daga ɗaki.

Ya yi murmushi yana shafa fuskarsa cikin nishaÉ—in da yake ji yana ratsa shi, in ya tuna ita matarsa ce ta aure farin ciki yake ji, iya hakan sai ya dinga kore masa tunanin Saheer da tsiyarsa. Ya sake yin ya ce, "C wife! you make me joy."

   Islaha haka ta dinga hauka tana buge-buge a ɗaki ga ciwon mara da ya fara damunta, ga damuwar Rehaan da take nema ta saka maganar su Adda ta tabbbata a kanta. Gabaɗaya ta fita daga hayyacinta saboda takaicin da ta ɗorawa zuciyarta, tana ganin Safeera tana yi mata waya ta kasa ɗauka, haka ta gama haukanta ta kwanta a kan gado ta fashe da kuka saboda ciwon da ya fara damunta.

Rehaan bai sake ganinta ba har dare ya yi, bai san a wanne ɗaki ta shiga ba dan ɗakunan gidan suna da da yawa. Yana so ya je dubata amma zuciyarsa tamna hana shi yin hakan, tun yana daurewa har ya kasa ya miƙe ya nufi ɗakin da ya ke kusa da wanda yake ciki amma bai ganta ba, ya rufe ya tafi wani nan ma bai ganta ba, ya sake duba wani nan ma bata nan.

Sai ya ji gabansa ya faÉ—i, duk ya san bazata fita bai sani ba amma sai ya ji tsoro, da hanzari ya hau painthouse ya buÉ—e É—akin, ga mamakinsa tana ciki a kwance a kan tiles tana kuka. Ya yi ajiyar zuciya yana girmama girman taurin kan Islaha, duk É—akunan da suke gidan sai ta hau sama na uku sannan ta kwanta.
Chapter 108 · 0% Book details