← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 110

Sashe 7

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya Karima ta kalli Mama ta ce, "yanzu daga unguwar ku nake kafin na zo, na haɗu da Atika da munafukar ƙawarta Safeera, kin ga kayan da aka basu na kyautar kai amarya? Kin ga kuɗi da kayan abinci? Ina gani na ce ba a banza yarinyar nan ta guji Saheer ba wallahi, ta bar halacci ta zaɓi kuɗi."

Mama ta kalli Saheer ta ce, "ka ji ko? Sai ka daina damun kan ka, ka daina saka damuwa a zuciyarka, daman ba ƙaunar ka take ba, kwantan ɓauna take yi maka, sai yanzu ta samu ta cika burinta. Da ita da mahaifinka sun haɗa kai sun aurar da ita a gidan kuɗi, kai kuma da yake baka da kuɗi sun cilla ka a bola.. Babban abin haushi da takicin ma mahaukaci ta aura ta bar ka."

Sadik da yake jinsu sai ya É—an fita, jim kaÉ—an ya dawo ya tsaya yana kallonsu ya ce, "Mama likita ya ce a ba shi lokaci ya huta, ba a son hayaniya." Jin haka duk sai suka yi shiru, sannan suka fita aka bar su su kaÉ—ai, Saheer yana zaune ya jingina da jikin gadon.

Bai san lokacin da hawaye ya fara ziraro masa ba, suka fara zuba wani yana bin wani kamar ba namiji ba, ya kasa dakatar dasu daga zubar da suke yi, ya bawa hawayen damar zuba yadda ya kamata, dan rashin zubar su matsala ce a gare shi. Babu abinda ya ke gani a idanunsa sai Islaha tana gidan wani namijin ba shi ba. Shi bai damu da kuɗin da suke ta zance ba, abinda idanunsa suke gano masa kawai Islahansa ta yi aure ta bar shi. Ya furzar da iska, ji yake gwara zaman wajan masu garkuwa da mutane akan raɗaɗi da ƙunan da yake addabar zuciyarsa.

Nana Haleema.

RDB3P005
Nana Haleema.

A hankali ya ji an zauna a kusa dashi, ya kalli Sadik suka haÉ—a ido sai ya É—auke kai, Sadik ya bi shi da kallon tausayi da rauni sannan ya ce, "Saheer!."

Bai iya magana ba sai hawayen da ya goge yana É—an girgiza kansa cikin rashin sanin abinda zai yi.

Sadik ya ce, "don Allah ka dawo hankalin ka, ka daure ka nutsu sai mu yi magana. Likita ya ce jininka ya hau sosai, in ba ka nutsu ba ya ka ke so abin ya zama?.”

Ya buÉ—e jajayen idanunsa ya kalli Sadik ya ce, "Aure ta yi fa Sadik, tana can gidan wani zata kwana tare dashi, a haka ka ke cewa na kwantar da hankalina?."

"Saboda lafiyar ka nake faɗa maka, dole ka sassauta wannan damuwar saboda jinin ka da ya hau a samu ya yi ƙasa, kuma har yanzu akwai sauran wahala a tare da kai, baka gama warware daga wahalar da ka sha ba.”

"Hmm! Ba ka san me nake ji bane Sadik, na kasa yarda Islaha zata yi min haka, na kasa yarda zata zaɓi kuɗi ta bar ni, na kasa yarda zata ci amanata har haka ba. Da abinda zata saka min dashi kenan, duk ƙaunar da na nuna mata, da zaman jiranta da na dinga yi, da wannan zata yi min sakayya? Mata nawa Mama ta bani naƙi aura saboda ita Sadik? Kai kanka har ƙanwar ka ka bani, amma naƙi na ce sai ita ɗin….”

Ya ɗan daki kansa a hankali sannan ya ce, “Wai tana gidan AbdulAziz Yola tana aure, tana can matsayin matar wani ba ni ba.”

Ya kalli Sadik suka haɗa ido sannan ya ce, "kuma ka ce min na kwantar da hankalina? Har abada hankalina bazai kwanta ba Sadik. Ka san ina son Islaha, bani da buri a duniya da ya wuce na mallake ta, itace kaɗaii abinda nake muradin mallaka a duniyata.”

Sadik ya dafa shi ya ce, "Na sani, na san kana jin zafi da ƙuna a ranka da zuciyarka, na san babu wanda ya san me ka ke ji sai Allah. Amma ka yi haƙuri, ka daure ka kawar da damuwar komai zai wuce."

"Komai zai wuce ko? Tana can gidan wani matsayin mata ka ce min komai zai wuce? Ta ya komai zai wuce?."

Cikin tausayi Sadik ya ce, "ina so ka warware ka samu lafiya sai na faÉ—a maka yadda za ka fahimta. Abu É—aya nake so ka sani, wallahi Islaha bata ci amnar ka ba, duk abinda ta aikata ta yi shine saboda kai."

Wani irin kallo ya yiwa Sadik, ya buÉ—e idanunsa sosai yana kallonsa ya ce, "saboda ni, auren wani ta tare a gidansa shine ta yi saboda ni?."

Sadik ya ce, "ka tsaya ka saurare ni ka ji dalilina kafin ka yanke min hikunci."

"Har abada bazan taɓa sauraren kowa akan maganar nan ba, bazan taɓa amincewa Islaha ta bar ni saboda ni ba. Ban da rainin hankali, ta ya za ka ce ta bar ni saboda ni, hankali zai ɗauki wannan ne?."

Sadik zai yi magana Saheer ya dakatar daahi ya ce, "Ka ga Sadik, in tare da kai aka haɗa kai za a ci kuɗin da wanda ta aura wannan ba damuwata bane, amma ka daina faɗa kin abinda zan ji haushin ka a cikin zuciyata. Kar ka sake yi min zancen ta, ko sunanta bana buƙatar na sake ji a kusa dani, na yanke duk wata alaƙa da take tsakanina da ita, ta je ta yi duk abinda ta ga dama, bazan sake sauraren ta ba."

Sadik ya yi ajiyar zuciya dan ya san bazai fahimta a lokacin ba, amma zai saka ya fahimta wani lokacin in da rabon fahimtar, dan ba ya jin daɗin yadda yake zargin Islaha, bai so abin ya zo a haka ba, dan shi ya san sadaukar da kanta ta yi saboda shi, duk da ya san Saheer ɗin zai fahimta, naganganun su Mama yake tsoro. Sadik ya yi shiru yana kallonsa, sai kuma ya miƙe ya fita daga ɗakin jikinsa duk babu daɗi.

Da Islaha da Saheer É—in gabaÉ—aya tausayi suke ba shi, har ya fi jin tausayin Islaha akan Saheer, tunda ita aka jefa a cikin tsaka mai wuya. Ta sadaukar da farin cikinta da rayuwarta da duk wani burinta, ta kai kanta inda bata san abinda zata tarar ba, ta je can ta zauna a matsayin matar aure saboda shi. Babban abin takaici da tausayin shine wanda ta yi dominsa ya gaza fahimta, yana ganin kamar ta ci amanarsa. Amma zai san abinda zai dan ya gyara wannan matsalar, in bai gyara matslaar ba ba a yiwa Islaha adalci ba:

Kiran sallar asuba ne ya farkar da Islaha daga baccin da ya É—auke ta a kan kujera.

, ta miƙe a firgice tana zare ido ganin haske a kanta, bata san ta yi bacci ba, ta dai san ta jima a haka a zaune tana saƙa da warwarewa. Kukan ɗawisu take ji kaɗan kaɗan, ta kalli window ta hangosa yana ta yawo a tsakanin falon zuwa baya.

Ta lumshe ido ta buɗe, ta kalli wayarta ba tare da tunanin komai ba ta kira number Sadik. Har ta katse bai ɗauka ba, ta miƙe ta shiga banɗaki tana sake kallon sink dan bata san ya zata kunna tap ɗin ba.

Ta ta dafe kanta jin har lokacin yana ciwo, ta fito ta ɗauki wayarta ta ɗauki hoton sink ɗin ta turawa chatgpt tana tambayarsa yadda ake amfani da shi. Cikin sakanni ya faɗa mata, tana kallon wajan ta ga inda zata taɓa.

Bata ɓata lokaci ba ta yi alwala ta fito ta tayar da sallah a inda ta ke, bayan ta idar ta jingina da kujera tana tunanin masoyinta bata san a halin da ya ke ciki ba, a haka bacci ya sake ɗaukar ta bata san ta yi ba.

Sautin kocking ne ya tashe ta, ta miƙe zaune tare da taɓa wayarta, gabanta ya faɗi ganin sha ɗaya na safe, ta zabura tana kallon wayar cikin mamakin gudun lokacin. Ta kalli ƙofar jin ana sake danna door bell, ta miƙe cikin bahagon yanayi ta ƙarasa ta buɗe. Tana buɗewa suka haɗa ido da Mama, Mama ta yi mata murmushi ta ce, "Amarya Islaha ko na ce Islam, na tashe ki ko?."

Islaha ta É—an murmusa kaÉ—an ta ce, "daman na tashi, sannu da zuwa."

Mama ta ce, "yauwa amarya, ku shiga ku ajjiye mata" ta faɗa tana kallon na bayanta tana kallon matan da suke riƙe da breakfast. Suka shiga suka ajjiye.

Islaha ta kalle su ta ce, "ku tafi da wannan ma, jiya aka kawo ban iya ci ba." Suka É—auko wanda Daada ta kawo suka fita.

Mama ta bita da kallo ganin kayan jiya ne a jikinta, har mayafin yana jikinta alamun dasu ta kwana. Islaha tana kallon Mama suka haÉ—a ido alamun daman kallon ta take yi.

Mama ta murmusa ta ce, "Ba dai a nan ki ka kwanta ba?."

Islaha ta ce, "ban san na yi baccin ba, sai asuba na farka."

Mama ta ce, "Ai da kin sani sama ki ka tafi ya fi, nan sautin wannan kayan kiwon nasa ma ya tashe ki." ÆŠan murmushi ta yi kaÉ—an amma bata ce komai ba.

Mama ta ce, "zan koma, in kina buƙatar wani abu duk wanda ki ka haɗu da shi a ma'aikatan gidan ki ce a raka ki wajan Mama."

Islaha ta É—aga kai ta ce, "to Mama, An gode."

Mama ta yi murmushi ta ce, "kar ki damu." Ta faÉ—a yana juyawa ta bar wajan.

Islaha ta rufe ƙofar tana sauke numfashi ta ce, “tana da kirki sosai, babu ruwanta" ta faɗa tana kallon stairs ɗin da zai kai ta sama.

Ta ɗauki wayar ta sannan ta fara hawa saman kamar mai jin tsoron taka ƙasa, ta buɗe ƙofar falon tana kallon falon kamar jiya bata gan shi ba, ko ina da duhu sosai, ko ina haskensa a kashe ya ke, ta ƙarasa ɗakin da suka shiga da Safeera.
Chapter 7 · 0% Book details