← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 110

Sashe 13

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammi ta harari Islaha da ba ita take kallo ba ta ce, "Shashasha mara tarbiyya" ta sake faɗa a ƙufule cike da jin haushin sunan matar Rehaan da Islaha take amasa.

A fusace Islaha ta ɗago suka haɗa ido, sai kuma ta fasa magana ta sauke kai ƙasa bata ce komai ba. Shiru ya ratsa falon sai yara da suke game suna ihu kaɗan kaɗan.

Ganin Mamy ta ƙi magana sai Sanah ta ce, "Allah ya ba ku zaman lafiya, Rehaan ku je ku huta dare ya yi."

Sai a lokacin Mamy ta ce, "Ita ta je, ina son magana da shi......."

Ta kalli Rehaan ta ce, "Rehaan follow me" ta faÉ—a tana tashi ta shiga ciki dole ya bita bayanta shima.

Suna shiga ɗaki ta kalle sa ta ce, "Rehaan bana son yarinyar nan ko kaɗan, bata yi min ba kwata-kwata, bana jinta a raina balle na karɓe ta a matsayin inlaw.

Bata da kunya, bata girmama na gaba da ita, rashin kunya take yiwa waÉ—anda suka haife ta, kad ka saki jiki ka zauna da ita, ka dinga baya-baya kar ta cutar da kai."

Rehaan sai ya ji babu daɗi a ransa, jikinsa ya yi sanyi sosai, haushin Islaha ya sake ninkuwa a ransa, ya ji ina ma bai taɓa sanin mai irin sunanta ba.

Ya kalli Mamy ya ce, "To Mamy."

Mamy ta ce, "Kuma ka shirya aure next month, ni Ikram nake so ka sake aure Rehaan."

"Mamy mun gama maganar nan da ke, bazan iya aurenta ba. Amma zan yi aure nan kusa, amma ba Ikram ba."

Mamy ta ce, "bana son ka É—auko wacce zata cutar da kai."

Ya riƙe hsnnunta ya ce, "zan kasance cikin ƙoshin lafiya ko yaushe."

Ta shafa kansa ta ce, "Allah ya sa."

Ya yi murmushi ya fito daga ɗakin, a nan ya tarar Islaha bata nan ya wuce ɓangaren Abba kamar yadda ya ce ya same shi.

A zaune ya samu Abba kamar ɗazu, shima ya zauna Abba ya ce, "na kira ka dan na tuna maka alƙwarin da ka yi min akan auren nan, kana sane dai ko?."

"ina sane Abba."

Abba ya ce, "ka yi haƙuri ka riƙe auren, bana so a samu wata damuwa ka ji?."

"In sha Allah babu abinda za a samu daga ɓangarena, zan yi komai saboda kai."

"Haka nake so na ji, ka yi haƙuri ka kawar da kai kafin ka samu wacce ka ke ra'ayin aure."

"To" ya amsa a taƙaice.

Abba ya ce, "Tashi ka je, Allah ya yi maka albarka."

"Amin Abba, sai da safe" ya faɗa tana miƙewa ya fita daga ɓangaren ya koma ɓangarensa.

Yana shiga falon Islaha da take zaman jiran shigowarsa ta miƙe tsaye ta kalle shi ta ce, "ina so a yi cancelling contract ɗin nan, bazan iya zama a gidan nan a matsayin matar ka ba...."

"Na gaji wallahi, iya kwana ɗaya da na yi a gidan ku na ji bazan iya zama, ina buƙatar komawa gida wajan Hamma, bazan iya zama a nan ba. Dan haka a soke shi, na yi alƙawarin zan biya ka kuɗin ka, kawai ka sake ni na kama gabana, in dai kuɗi ne zan san duk hanyar da zan bi na nemo su na ba ka abin ka, zaman gidan nan bai yi daidai da ra'ayina ba. Ni da Hamma za mu san duk hanyar da za mu nemi kuɗi mu ba ka, amma bazan iya zama a gidan nan gaskiya...."

Rehaan ya tsaya cak jin maganarta a bayansa, ya waiwayo yana bin ta da kallon ba ki da hankali......

RDB3P10
Nana Haleema.

Rehaan ya yi holding hannunsa a cheast ɗinsa yana kallonta jin tana maganar a soke yarjejeniya, bayan alƙawarin da ya sake yiwa Abba ko mintina goma ba a yi ba ta kawo masa shirme.

Islaha ganin yana kallon ta sai ta ce, "zan yi ko wanne irin aiki ne a ƙarƙashinka, har sai ka fanshe kuɗin da ka bani, amma bazan iya zaman gidan nan a matsayin matar ka ba, ina buƙatar komawa wajen Hamma."

Rehaan ya É—an girgiza kai yana blushing sannan ya kawar da kansa daga kallonta, ya sake waiwayowa ya kalle ta ya ce, "A yi cancelling?."

Islaha ta É—aga kai alamun eh tana kallonsa, dan da gaske baza ta iya zama a cikin gidansu ba.

Ya kalli ƙasa kamar mai neman wani abu kafin ya sake kallonta, ya saka hannu aljihu sannan ya ce, "So you have my account details, right?"

Ta É—ago ta kalle shi jin abinda ya ce, Rehaan ya É—aga gira sama ya haÉ—e fuska kamar ba shine yake murmushi ba.

Islaha cike da damuwa ta ce, "bani da ita, kuma bani da kuɗin da zan biya ka a yanzu balle har na tura maka. Amma na yi maka alƙawari zan yi aiki a ƙarƙashin ka har sai na biya ka kuɗin ka, ko wanne irin aiki ne zan yi indai zan samu kuɗin da zan ba ka, ko da ba za a dinga bani salary ba na yarda, ni dai burina a soke yarjejeniyar nan na kama gabana."

Rehaan ya ce, "Lokacin da ki ka yi signing kin ce kin taimaka min ne, meyasa ki ke neman a soke?."

"Saboda Hamma, saboda shi na saka rayuwata a cikin ta ka, duk abinda na yi saboda shi nayi, ba dan shi ba da baza ka sake ganin fuskata ba har abada."

Rehaan ya taɓe baki yana girgiza kansa cikin ko in kula da kalamanta ya ce, "Okay ki je ki faɗa masa ya biya ni kuɗin da na ba ki, once i receive my money, we can cancel the agreement. But if my money is not paid back, don't bring up canceling the contract again.

Ya juya zai bar wajan sai kuma ya kalle ta ya ce, "fifty millions naira, not fiffty thousands" ya faÉ—a yana hawa sama yana ciro waya daga aljihu ba tare da ya kuma kallonta ba.

Islaha ta yi shiru cike da damuwa, ta zauna tana tunanin Hamma yana wani waje ba shi da lafiya bata san halin da yake ciki ba, ta fashe da kuka mai taɓa zuciya, tana ji kamar haɗɗiye zuciya ta mutu saboda tunanin Hamma. Ta runtse ido cikin ƙunci da takaici, kamar ta dinga dukan kanta haka zuciya take raya mata, ta ɗauki waya ta kira Safeera.

Safeera tana É—auka ta fara yi mata masifa ta ce, "tun É—azu nake jiran ki har yanzu ba ki ce min komai ba, kin koma wajan Hamman ko ba ki koma ba?."

Safeera cike da gajiya da maganar ta ce, "wai sau nawa zan faÉ—a miki ne, na je yana bacci ya ki ke so na yi miki?."

Sai ta tuna ashe sun yi magana ta faÉ—a mata ta je yana bacci, ita ta manta sun yi magana, damuwa da tunanin Hamma ya saka ta manta.

Jikinta ya yi sanyi ta ce, "Safeera ban san ya zan yi ba, na rasa abinda yake damuna, ina so na ga Hamma, ina so na yiwa Hamma bayani, ina so Hamma ya san ban yaudare sa ba."

Safeera ta ce, "don Allah ki nutsu, ni na san Hamman ya san ba ki yaudare sa ba, meyasa ki ke takura rayuwar ki haka?." Islaha ta sauke numfashi irin na wacce ta yi kuka bata ce komai ba. Safeera ta ce, "don Allah ki nutsu, wannan abinda ki ke yi ba shine mafita ba."

"Ina a soke yarjejeniyar nan, ina so na dawo na kula da Hamma, ko ban koma gidansu da zama ba ni dai na bar gidan nan."

"Kina da miliyan hamsin kenan?."

"Bani da ita."

"To ki bar batun za ki soke contract, ko da kina da kuɗin a hannunki dole sai kin zauna da shi tunda kin riga da kin amince akan za ki zauna dashi in ya ba ki kuɗi, kin yarda shima ya yarda, ki ka saka hannu shima ya saka. Ya ba ki kuɗi dan ki zauna da shi, ki ka karɓa dan ki karɓo Hamma kuma buƙatar ki ta biya. Saboda ke ki ka fi kowa son kai sai burin ki ya cika sai a soke contract ɗin? Ki zama wayayyiya wacce ta san shari'a mana Islaha."

Ta lumshe ido ta ce, "bazan iya zama ba, ji nake zan iya mutuwa wallahi."

Safeera cikin rarrashi ta ce, "baza ki mutu ba, kuma Hamma zai fahimce ki yadda ya kamata. Kawai ki nutsu, ki shirya tunkararsa kawai."

Ta girgiza kai kamar Safeera tana kallon ta ta ce, "Kunyarsa nake ji."

"Ki adana kunyar, ki É—aura É—ammarar yi masa bayani yadda zai fahimta." Ta yi ajiyar zuciya kawai ta yanke wayar ta kwanta a kan kujera.

Islaha yunwa take ji sosai, yunwa take ji tana yamutsa cikinta, dan rabonta da abinci tun tana gidansu Safeera. Tea kaɗai ta iya sha a gidan, bayan nan bata kuma cin komai ba. Ta kalli manyan flaks ɗin da suke ajjiye akan center table, ta miƙe daƙyar ta buɗe ɗaya ta ga kaji ne da dankalin turawa. Ta ɗauki mini plate ɗin ta zuba dankalin ta ci kaɗan, ta sha ruwa ta koma ta yi shiru a wajan.

Knocking ƙofar ta ji ana yi, gabanta ya faɗi ta kalli agogo ta ga ƙarfe sha ɗaya na dare, ta sake kallon ƙofar sai kuma ta ji an buɗe ƙofar an shigo ta zubawa ƙofar ido.

Banisha ce ta shigo ita da Janan da kuma Ikram, fuskarsu É—auke da makeup da alama dawowarsu kenan daga gidan bikin Riyya. A tare suka yi sallama, ta amsa tana É—ago ido suka haÉ—a ido da Banisha.

Banisha ta yi murmuahi ta ce, "Hiii Sis." Islaha ta É—an murmusa ta gyaÉ—a kai ta ce, "Hello Banisha."

Janan ta ce, "Hiii." Ta É—an É—aga kai bata ce komai ba tana kallon ta kawai.

Ikram ta ce, "Hamma Rehaan yana nan?."

Banisha ta ce, "Yana sama, ku zo mu je." Ta gabanta suka wuce suka hau sama bata sake kallonsu ba, dan gani ta yi suna da jin kai ga wani iyayin da suke ji da shi.
Chapter 13 · 0% Book details