Sashe 57
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saheer ya girgiza kai cikin wani irin yanayiya ce, "Ni bazan karɓi kuɗin nan ba, zan mayar mata da abinta, kamar yadda ka ce ba roƙa na yi ba, bana so."
Sadik ya ce, "da ka cika babban ajawo, da ka ciki cikakken mara hankali wanda yake buƙatar a fara ba sa magani. Wallahi in ka mayar da kuɗin nan ta tabbata kai banza ne, soloɓiyo wanda babu abinda zai iya yiwa kansa. Kai yanzu sai ka mayar dan shirme? In ma shi ɗin ne ya ɗauko kuɗin ya ba ka ai ba laifi bane, ya kai ya baka kuɗin ne, ya kai ya kira ka ya baka tunda yana da matsayi mai girma wanda mu bamu da shi. Balle ita tace Hamma ga kuɗi an bani na baka, sannan ta ga zata bani kuma zata bawa ƙawar ta. Meye naka da za ka ce baza ka karɓa ba?."
Saheer ya sauke numfashi ya ce, "kishi nake Sadik, bazan iya cin kuÉ—in aurenta ba."
"ai ba wani abun bane, tunda iyayensa ba su san auren da yake tsakaninsu ba, dole a bata irin wannan kuÉ—in."
Saheer ya sake kallon alert ɗin kuɗin, ya kalli Sadik ya ce, "Jikina ya yi sanyi, anya Islaha zata dawo gare ni, anya bata fi ƙarfina ba?."
Sadik ya ce, "bata fi ƙarfin ka ba, tunda tana sonka zata dawo cikin rayuwarka nan gaba. Amma kafin wata biyar, ka tabbatar ka gina kanka, yadda in ta dawo rayuwarka baza ta yi kewar rayuwar da ta yi a wata biyar baya ba."
Saheer ya yi shiru yana tunani zuciyarsa tama bugawa da ƙarfi. Shi kuwa Sadik murna yake yi, yana fatan Allah ya sa auren Islaha ya ɗore ko dan ta cigaba da tunawa dasu.
Islaha suna fita Napep suka kuma hawa bata ce komai ba, Safeera ta kalle ta ta ce, "Bazan gaji da faÉ—a miki gaskiya ba, batun auren da ki ke yi da Hamma Saheer haramci ki ke aikatawa, kuma wallahi mala'iku zunubi suke rubuta miki, amma na ga kamar kin raina zunubin ne shiyasa. In za ki yi maganar auren ki da shi, ki jira a raba wannan auren da yake kan ki, in ya so sai ki fara."
Islaha kamar jira take a taɓo ta ta fara masifa, "Ina ruwanki da ni? Kuɗin da na bashi Baffa ya bani su jiya, ki faɗa min me zan yi da waɗnanan kuɗin masu yawa? In ban bawa Hamma kuɗin ba me zan yi dasu, in ban baki na bawa Baffa da Sadik ba wa zan bawa? Me zan yi da kuɗin?."
Safeera sai ta yi mata banza bata tanka ba, dan in ta biye mata faɗa zasu kaca kaca, a yanayin da take ciki ta san halinta, bata jurewa ƙaramar magana, da ka taɓo ta sai masifa.
A haka ma bata daina mita ba, sai kuma ta fara hawaye tana murza ido.
Sai da ta gama kukan sannan Safeera ta sauka ta riƙe ƙarfen napep ɗin tana kallonta ta ce, "Da ki ba wa Saheer wannan kuɗin, gwara ki je orphanage ki ɗauki nauyin yara ƴan uwanki. Ban ce Saheer bai cancanci a ba shi ba, amma da niyar da ki ka ba shi kuɗin, da amfanin da ki ka ce a yi dasu ne babu lada sai zunubi mai girma, da kin je gidan marayu kin bayar da kin samu ladan da Allah zai kawo miki mafita cikin wannan ruɗanin da ki ke ciki. Ina sake tuna miki, magana da Saheer ma haramci ne a gare ki, domin kuwa ke matar aure ce!. Sai anjima" ta faɗa tana barin wajan ta bar Islaha tana kallonta.
Mai napep ya ce, "Hajiya ina muka nufa?." Ta É—aga kai ta faÉ—a masa sunan estate É—in suka tafi.
Kamar yadda tayi jiya daga farkon estate É—in ta sauka, ta ba shi kuÉ—insa ta kalli security da suke kallonta, dan tunda Jazy ya yi musu magana basu sake hanata zuwa ko ina ba.
Ta wuce ciki cikin ƙunar ran da bata san daga ina yake zuwar mata ba, gabaɗaya komai ba ya yi nata daɗi, komai ya tsaya mata tana buƙatar shawarar da zata kwantar mata da hankali, tana buƙatar rarrashin da zai saka zuciyar ta huta na wani lokaci. Bata da mai bata shawara balle ya rarrashe ta, sai dai ta yi kuka ta share hawayenta.
Mai napep ya na hango ta har ta É—an yi nisa, duk da ba ya gano gidan da ta shiga, dan daga farko zuwa ciki da É—an nisa kaÉ—an.
Ya kalli sigh board É—in sa aka rubuta AbdulAziz Yola Estate, ya É—auki waya yana danne-danne, kafin ya saka a kunne ya ce, "tabbas ta yi aure, sannan na sauke ta a estate É—in gidan AbdukAziz Yola. Kuma da ta zo shiga babu security É—aya da ya hanata, alamun sun santa ba yau ta saba zuwa ba. Sai dai kamar ba a son ranta ta yi auren ba, har yanzu tana shirin auren tsohon saurayinta in ta fito daga nan."
Shiru ya yi alamun ana ba shi amsa, sannan ya ce, "Za a yi hakan, sai ka ji ni" ya faÉ—a yana kashe wayar yana sake kallon estate É—in kafin ya juya kan machine É—insa ya fita.....
Nana Haleema.
RDB3P45
Nana Haleema.
*Englaand.*
Rehaan yana zaune a parlour yana shan ruwa, dawowarsa gidan kenan cikin gajiya ta tsata yake sosai, hutawa yake so ya yi dan ya gaji. Da ya gama shan ruwa É—aki ya shiga ya yi wanka ya canja kaya sannan ya kwanta.
Sallah ce kaɗai ta tashe sa, yana tashi ya duba wayarsa ya ga kiran waya da messages da yawa. Bai bi ta kai ba ya sake yin wanka, sannan ya yi sallah ya sakko ƙasa ya samu an yi masa girki, ya zauna ya ci ya ɗauko ipad yana duba abubuwan da ya kamata ya yi.
Door bell aka danna sai ya kalli ƙofar yana tunanin waye zai zo masa yanzu, ya san shi bai yi da kowa zai zo ba, daman Alma yake tunani kuma itama tunda ya zo bai ganta ba. Sai ya yi tsaki dan shi ya tsani buɗe ƙofa a rayuwarsa, yadda yake a gajiyen nan ba yaso ya miƙe ko kaɗan, abincin ma da zai yu a baki za a bashi. Daƙyar ya miƙe ya buɗe, kafin ya gama tantance waye aka rungume shi
Sai ya yi murmushi ya yi hugging É—inta back ya ce, "Riyya, yaushe ki ka zo?."
Ta É—ago daga jikinsa ta ce, "kwana biyu kenan."
Ya É—aga kai ya shafa fuskarta ya ce, "Welcome."
Ya faɗa yana riƙe da hannunta suka shiga falon, Jazy ya ƙaraso ya rufe ƙofar sannan ya ce, "da yake ka ga Riyya ni na zama banza kenan ko? Kamar ba ka ganni ba."
Ray bai kula sa ba Riyya yake kallo ya ce, "i hope kina lafiya, sai na ga kin rame, me ya kawo clavicle" ya faɗa yana taɓa clavicle ɗinta.
Kafin ta yi magana ya sake cewa, "ba ya ba ki abinci ne ki ka rame?."
Riyya ta yi dariya ta ce, "Ban fa rame ba, kaine ka ga haka, but am gaining weight, ƙiris na ƙarasa kiddo."
Ray ya yi murmushi ya ce, "ba ya takura miki? Ba ya yi miki faÉ—a da shouting?."
Riyya takalli Jazy da yake kallonsu yana murmuahi, ta kalli Rehana ta ce, "ba ya yi min komai."
"Kar ki kare sa, ki faÉ—a min gaskiya."
"Allah da gaske."
"Good."
Sai kuma ta kalli Jazy ya ce, "Meyasa ba ka kawo min ita ba sai yau? Meyasa bata zauna a gidan nan ba?."
"Me zai kawo ni gidan nan? Ango ne ni, bana buƙatar wanda zai takura mana ni da matata. Hotel ya fi daɗin honeymoon, dan bana son takura na gida."
Rehaan ya taɓe baki bai ce komai ba yana harararsa, ita kuma Riyya sai ta ji kunya ta rufe fuskarta. Ray ya kalle ta ya ce, "me ki ke so?."
Riyya ta É—ago kai ta ce, "Babu komai" ta faÉ—a tana tashi ta shiga ciki ta bar su a falon.
Jazy ya kalli Rehaan kafin ya yi magana Rehaan ya ce, "Ya batun mutanen nan kuwa, bayan na taho nan an samu feedback?."
Jazy ya ce, "eh an samu, Cctv ta ɗauki fuskarsa, amma dukkansu sun rufe fuska, mutum ɗaya ne bai rufe ba, shi kuma an tabbatar mana da baya garin nan. Amma in dai ba lahira ya tafi ba Allah sai an nemo sa."
Rayya ce, "Thank you for that."
"Alma ta zo?."
"kai nima abin ya bani mamaki fa, ban yi tunanin zan yi kwanakin a gidan nan Alma bata zo ba."
"Kuma ta san ka dawo?."
"ni na san ta sani, sai dai in akwai abinda take shiryawa. Amma Alma ta san ina ƙasar nan, definitely."
Jazy ya yi shiru bai ce komai ba, sai kuma ya tuna da saƙon Islaha ya ce, "Kai C wife ɗin ka ta bani saƙo na ba ka."
Rehaan ya ɗago ya kalle sa alamun wanne saƙo ne, kafin ya yi magana da ya yi dariya son ransa sannan ya ce, "ta ce na ce maka she loves you."
Rehaan ya harare shi dan ya san ba ƙarya yake yi, Jazy ya yi dariya ya ce, "Yadda ka ɗago ido kana jiran na faɗa maka saƙon ne ya bani mamaki, kamar daman jira ka ke acr ta bada saƙo. To bata ce tana sonka ba, kuma ka san baza ta ce ba. Wait! Kai meyasa ka saka aka hanata fita? Ina ruwanka da ina zata je za ka ce masu gadi kar su barta ta fita?."
Ray ya ɗora ƙafarsa ɗaya akan table sannan ya ce, "Ra'ayin hakan na yi."
"Amma ka san a cikin rules É—inta da ka yi signing babu hanata fita ko? Ina ruwanka da duk inda zata je da za ka ce kar a kaita kuma kar a barta ta fita?."