← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 110

Sashe 66

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Islaha ta tsaya cak jin maganarsa mai haɗe da godiya wacce bata yi tunani ba. Ta juyo suka haɗa ido, yadda ya rame lokaci ɗaya sai ya sake bata tausayi sosai, duk da ta san akwai rakinsa amma da alama ya ji jiki. Ta ɗage gira sama tana yi masa sani kallon up and down, dan ita tunda ta ga yana wannan langwaɓewar ta sake raina shi ta ce, "for what?."

Bai san me ya ba shi dariya a kalamanta ba, ya yi murmushi yana kallonta sannan ya ce, "ask me" ya faɗa yana miƙewa tsaye yana yamutsa fuska ya ɗan ɗaga hannunsa yana stretching slowly.

"Wayyo Allah!."

Isɓaha furta ba tare da ta shirya ba, ganin idanunta sun sake janta inda suke fara janta jiya. Ita ta rasa meye a logon nan da take kallon, bata san meyasa idanunsa suke kallon logon ba.

Jin abinda ta ce sai ya kalle ta ya ga idanunta a rufe, bai ce mata komai ba ya dama slippers ya shiga bathroom bai kuma kallonta ba.

Islaha fitowa parlour ta tarar da Mamy a zaune, har ta haɗo masa breakfast daga ƙasa ta ajjiye. Mamy ta kalli Islaha ta ce, "zo ku yi breakfast."

Islaha ta zauna a kusa da Mamy, da kanta take haÉ—a mata tea kafin ta kalle ta ta ce, "kina son milk?."

"Ina so."

"Okay my love" ta faɗa tana haɗa mata da kanta ta miƙa mata.

Islaha ta ce, "thank you Mamy."

Mamy ta zauna sannan ta ce, "enjoy your breakfast."

Islaha ta fara shan tea É—in, ta É—auki two slices bread tana ci.

Wani irin maiƙo ne da bread ɗin ga laushi da daɗi, daƙyar za ka iya cinye guda biyu saboda maiƙon da ya ke da shi. Daƙyar ta iya cinye ɗaya, sai ta haɗa da lamb pepper soup ta ci.

Mamy ta ce, "ke kina shan madara, ga Rehaan ba ya son madara, in dai ya sha sai ta dawo, sai ya ce ƙarni take yi. Kuma zai sha a drink ko smoothie, amma bazai sha a tea ba.”

Islaha ta yi murmushin da ya tsaya a kan laɓɓanta kawai, tana mamakin labarin da Mamy take bata, tana tunanin ko ina ruwanta oho.

Sai da ta gama breakfast É—in sannan Mamy ta ce, "Thank you Islaha." Islaha ta kalli Mamy tana ajjiye kofin hannunta tana murmushi bata ce komai ba.

Mamy ta ce, "na gode da ki ka kula da Rehaan, in ba ke ba babu wanda zai kula da shi da zuciya É—aya a cikin gidan nan, daga ke sai Dear, i mean Abbansu."

Mamy ta ce, "akwai lokacin da ya yi irin wannan ciwon, na bar shi a hannun wani a gidan nan, wani yayansa Sameer na gidan nan, kafin gari ya waye an buÉ—e wayarsa an É—auki document, an É—auki kuÉ—i. At the end an ba shi abinda sai da ya kwana biyar yana ciwo bai san inda kansa yake ba. Amma ke da zuciya É—aya na bar ki da shi, ga shi na same sa lafiya babu abinda ya same shi."

Islsha ta yi murmushi kawai bata ce komai ba, dan ita bata san me zata cewa Mamy ba. Mamy ta dawo kusa da Islaha ta riƙe hannunta ta ce, "Islaha a kaf gidan nan, kar wani ya baki magani ya ce ki bawa Rehaan na ciwon ciki ko na wani abun ki karɓa ki ba shi, ko da an matsa sai kin karɓa, ki karɓa amma kar ki basa. In Daada ce ta ba ki ki karɓa da zuciya ɗaya, kar ta yi miki aike a kawo miki ki yo amfani da shi. Kaf gidan nan ba ƙaunarsa suke yi ba, masu sonsa kaɗan ne. Rehaan yana da son ƴan uwa, amma sun ware sa gefe saboda suna ganin shine ƙarami kuma ya fi su ɗaukaka. Ƙaramar hanya ake nema da za a cutar da shi, ƴar ƙaramar ƙofa ake nema a shigo a yi masa kisan gilla. Lokacin da muka taɓa haɗuwa da ke a asibiti, yana kwance an ba shi poison, har yanzu ba a san wanda ya bayar ba."

Islaha jinta kawai take yi bata ce komai ba har ta je ƙarshe sannan ta ce, "In sha Allah Mamy."

Mamy ta ce, "da farko ban karɓi auren ki ba saboda ba ya so, ni kuma duk abinda Rehaan yake so shi nake so. A zaman three weeks da na yi da ke sai na fahimci ki, sai na fahimci da Rehaan da babu shi duk ɗaya ne a wajan ki. Sai hakan ya yi min daɗi, saboda na san ba ki zo nan dan ki cuce shi ko dan kuɗinsa ba, dan na ga ke gabaɗaya ma haushi yake ba ki, ko?."

Islaha ta zaro ido waje cikin jin nauyin Mamy ta rufe fuska da hannunta. Mamy ta yi dariya ta ce, "haka ne Islaha, haushinsa ki ke ji a yanzu, amma ina fatan nan gaba ki so shi."

_Ba amin ba, har abada Mamy, ina da wanda na ke so, me zan yi da wannan ragon?._

Abinda ta faɗa a ranta kenan, amma a zahiri ba ta ce komai ba sai yaƙe da take yi.

Mamy ta ce, "ki yi min alƙawarin za ki kula da shi kamar yadda nake kula da shi."

Islaha ta buɗe fuska zuciyarta tana bugawa, bata son ɗaukar alƙawarin da bazata iya ba, dan gaskiya bazata iya kula da Rehaan ba.

Kafin ta yi magana ya buɗe ƙofa ya fito, suka kalle shi yana sanye da jallabiyya black blue mai dogon hannu, gashinsa a ɗaure yana tahowa a hankali.

Mamy ta miƙe ta riƙo hannunsa ya riƙe hannunta ya zauna a kusa da ita, ta ɗauki wani ruwa a kofi ta ce, "karɓi ka sha" ta faɗa tana ba shi glass cup ɗin. Bai ce komai ba ya karɓa ya sha, ruwan zamza ne da aka sauke masa alkur'ani, indai yana gida dashi yake fara breakfast sai dai in Mamy bata nan.

Ta miƙa masa tea ta ce, "ka sha, za ka ji daɗi."

Rehaan ya ajjiye tea ɗin da ya karɓa akan table, ya yi pecking goshinta sannan ya ce, "you are the best mother in the world, i love you so much Mamy."

Mamy ta shafa kanta ta ce, "and you are the best son in the world, take your tea and enjoy, kafin ya yi sanyi." Ya wani shagwaɓe fuska yana kallon ta ya ce, "you can't say you love me?."

Ta yi dariya tana jan hancinsa ta ce, "i love you." Ya yi murmushi ya kai tea É—in bakinsa ya sha a hankali.

Islaha kallonsu take yi cikin burgewa da ban sha'awa, bata san idanunta sun cika da hawaye ba sai da ta ji saukarsu a kan fuskar ta.

Kewar mahaifiya ta ji tana tasowa a zuciyarta, sai ta ke gani ina ma tana da uwa da zata dinga kula da ita a duk lokacin da bata da lafiya, Ina ma tana da uwa irin Mamy da zata dinga rarrashinta har ta ba ta abinci a baki. Rashin uwa shine yake sakawa ta yi kuka mai ƙarfi a duk lokacin da take cikin wannan yanayi, bata da gatan da za a bata abinci a baki a rarrasheta kamar yadda Mamy take yiwa Rehaan. Babu wanda ya taɓa tsayawa akan nema mata maganin ciwon da take fama dashi a cikin ko wanne wata, duk da Hmma ya yi ƙoƙari akan hakan, sun je asibiti kala-kala amma bata daina ba. Amma ta san da mahaifiyarta tana nan da yanzu tana nema magani ko da ta san bazai yi amfaniba.

Dafa kafaɗarta Mamy ta yi ta ce, "Islaha!..”

“Me ya faru ki ke kuka?."

Sai a lokacin ta farga kuka take yi, ta goge idanunta bata ce komai ba.

Mamy cikin kulawa ta ce, "faÉ—a min, meye ya faru ki ke kuka?."

Islaha ta goge ido ta ce, "ina tunawa da Mamana, ina so na tuna da fuskarta amma na kasa. Na rayu babu ita, ban san inda ta ke ba, tana da rai ko ta mutu ban sani ba. Iyayen gidan marayu kawai na sani, sai su Baffa da nake kallo a matsayin iyayena, amma ba mahaifa ba" ta faÉ—a hawaye yana sake sakkowa daga idanunta.

Mamy ta yi hugging É—inta tana shafa bayanta a hankali cike da tausayi da raunin da ya mamaye mata zuciya. Islaha jin ta samu gatan da wata mace ta rungumeta da fuskar rarrashi sai kawai ta fashe da kukan da yake damun ranta.

Mamy tana shafa bayanta a hankali cikin wani irin yanayi, ƙirjinta yana bugawa da sauri, tana jin wani irin abu yana shiga jikinta a game da Islaha. Bata san meye, amma tana jinsa baƙo wanda bata taɓa ji ba. Soyayyar Islaha ta gama kamata lokaci ɗaya, ta gama shiga zuciyarta da jininta, yanzu kuma ga tausayinta da ya ke sake samun muhalli mai kyau a zuciyarta.

Rehaan ma kallon ta yake yi, rana ta farko da zuciyarsa ta yi sanyi da rauni a kanta, ko lokacin da ta samu attack ta silarsa bai ji irin wanann yanayin ba. Sai ya tafi tunanin da shine babu Mamy wanne hali zai shiga? Wanne irin halin kewa zuciyarsa zata kasance a ciki?.

Ya sake kallon Mamy, ya kalli Islaha da ta ɗago kanta tana share hawayenta. Ya ɗauke kai daga kanta jin zuciyarsa tana bugawa da ƙarfi, ya ja numfashi mai tsaho, duk da ciwon da yake ji a cikinsa bai hana shi sauke numfashim da ƙarfi ba. Tabbas ya ji tausayinta sosai, lokaci ɗaya tausayin ya samu gurbi mai girma a zuciyarsa....

Nana Haleema.
KRBBK:
RDB3P51
Nana Haleema.

Mamy ta gogewa Islaha hawayen da take yi sannan ta bata ruwa ta sha sannan ta ce, "Ki daina kuka, kowa da yadda Allah ya tsara masa rayuwarsa, ke maraici shine jarabawar ki."

Mamy ta kuma cewa, "a da kin san iyayenki?."
Chapter 66 · 0% Book details