← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 110

Sashe 22

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"kya tambayi kaza hanyar rafi? In za ki saka min wuƙa ki ce min ya sunan unguwar wallahi ban sani ba."

Safeera ta yi dariya ta ce, "ni Safeera na ga ta kaina, wannan wacce irin amarya ce da bata san sunan unguwar da aka kai ta ba?."

Islaha ta yi shiru bata ce komai ba, tana ji Safeera tana tsokanar ta amma bata tanka ba. Safeera ta tare mata napep ta faÉ—a masa sunan unguwar ta shiga ta tafi ita kuma koma tana yi mata dariya.

    A farkon estate ɗin akwai security barrier gate, irin ƙarfen nan da ake rufe hanyar, wanda sai an ɗaga maka shi sannan za ka wuce, kuma napep ba ya shiga wajan sai in kana ɗaya daga cikin ƴan estate ɗin, kuma gabaɗaya estate ɗin daga Abba sai yaransa, kuma duk sun girmi hawa napep.

Mai napep ya ce, "Hajiya a nan babur yake tsayawa, ba ya ahiga ciki." Islaha bata ce komai ba ta sauka ta ba shi kuÉ—insa ta fara takawa a hankali zuwa wajan.

Yadda take tafiyar sai ka ɗauka bata da gaskiya, tana tafiya tana waiwayon bayanta, sannan a hankali take tafiyar kamar bata so. Bata yi zato ba ta ga security da ƙatuwar bindiga a tsaye a gabanta.

Gabanta ya faɗi sosai, amma sai ta yi ƙoƙarin danne tsoron ta ta tsaya cak tana kallonsa, shima ya bita da kallo ya ce, "Hajiya cire facemask ɗin."

Bata ƙi ba ta cire shi ya bita fuskar ta da kallo dan shi dai bai santa baya ce, "ina za ki je?."

"Zan shiga gidan nan" ta faÉ—a tana nuna gidansu Rehaan su da hannunta.

Ya kalli gidan sannan ya kalle ta ya ce, "wajan wa za ki je?."

Islaha ta lumshe ido cike da takaici ta ce, "Daada."

"Ta san da zuwan ki?." Ta É—aga kai alamun eh.

Ya ce, "mu bata sanar mana zata yi baƙuwa ba, ki kira ta a waya mu ji in da gaske ki ke."

Ɗayan da suke tare daga gefe ya ce, "Ƙarya suke yi fa, sun ga an yi biki ana ta shiga da fita, shine yau ma suka dawo."

Islaha ta juya ta kalle sa jin abinda ya ce, sai ta É—auke kai bata ce komai ba dan bata san me zata ce musu ba, gwara ta yi shiru tunda da almajira ta yi musu kama.

Wanda yake gabanta ya ce, "Ki kira ta mu ji in da gaske ki ke, gidan nan ba a yin baƙi masu zuwa a napep. Kuma kaf masu aikin na san su, babu ke a cikin su."

"Ka ga na yi maka kama da mai aiki?" Ta faÉ—a tana kallon sa cike da takaici.

Ya kalle ta ya ce, "Masu aikin gidan basu da kama, haka suke kamar ki."

Ta yi tsaki a ƙufule ta ce, "in za ka bari na wuce ka bari, in baza ka bari ba na koma inda na fito. Ka tsare ni a hanya kana yi min tambaya kamar wacce zata shiga gidan tuba?."

"Ke ni ki ke faÉ—awa haka?."

"Na faÉ—a, don Allah ka saka bindigar hannunka ka harbe na mutu."

Zai yi magana suka ji horn ɗin mota daga bayansu, yana ganin motar ya gane suka ɗaga masa ƙarfen dan ya wuce. Yana zuwa kusa da Islaha ya sauke glass ƙasa yana kallon ta ya ce, "Miss Islaha."

Jin an kira sunanta sai ta kalli motar, ta ga Jafar ne a ciki ya yi kwalliya cikin manyan kaya, kansa É—auke da hula ya yi kyau kana ganinsa ka ga ango. Kafin ta yi magana ya ce, "me ki ke yi a nan a tsaye?."

Wanda suke magana dashi ya ce, "Oga ba mu santa ba, ta sauka daga napep zata shiga cikin, mun ce wajan wa zata je tace Daada, mun ce ta yi mata waya taƙi. Har tana yi min rashin kunya, wai na harbe ta."

Ya murmusa dan ya san zata aikata ya ce, "Kar ku sake tare ta, ko sau nawa za ku ganta kar ku ce mata komai."

"Okay Sir" suka amsa gabaÉ—ayansu.

Jazy ya kalli Islaha ya ce, "Zo mu ƙarasa." Kamar baza ta je ba sai kuma ta shiga motar Jazy ya ja motar suka shiga.

Kasa cewa komai ta yi, dan a fusace take sosai zuciyar ta a sama take akan wukaƙancin da aka yi mata. Bata so ya yi magana ta sauke masa kwandon masifa shiyasa ta kama kanta.

Jazy ya ce, "Miss Islaha me ya fito dake daga gidan nan ke kaÉ—ai? Babu mota babu security? Ba ki san matsayin ki ya wuce haka ba?" Daidai lokacin da yake danna horn ama buÉ—e masa gate É—in gidan.

Islaha ta ce, "na je wajan aiki ne."

"Aiki! A yau É—in?."

Ta yi shiru bata amsa ba ya ce, "kin manta ke amarya ce?."

Ta kalle sa ta ga ba ita yake kallo ba glass ɗin gabansa yake kallo. Islaha ta yi ƙaramin tsaki cikin ko in kula ta ce, "amaran dai suna inda suke, ni kam wannan suna bai dace dani ba."

Ciki yake shiga da motar har aparment É—in Ray sannan ya kalle ta ya ce, "Ke kuwa sunan ya dace dake Miss, ko na ce Mrs Rehaan, yanzu Miss ba na ki bane."

Bata ce komai ba ya ce, "Seriously fita ke kaɗai bai dace dake ba, yanzu ba dah bane, kina da buƙatar a killace ki. Ki duba abinda aka yi miki yanzu, in wani ya ji an yiwa matar Rehaan haka babban abin kunya ne.”

"Bani da wannan buƙata Mr Jafar, ni ba ƴar gwamna ba, ba matar shugaban ƙasa ba, killace ni ɗin me za a yi? Wani na kashe da sai na fita da security saboda kar a ɗauki fansar kisan a kaina?. Wallahi bazan lamunci fita da wasu mutane ba, ban ce ina so ba, a bari duk ranar da ya ɗauko original wife sai a bata su dan su kula da lafiyar ta, ni kam bana so."

Ya kashe motar sannan ya ce, "ke fake wife ce?."

"Ni na fi fake wife zama fake."

Ya yi dariya ya ce, "Islaha kenan, kina da drama" ya faÉ—a yana buÉ—e motar ya fita itama ta fita daga motar.

Shine ya yi unlocking ƙofar, dan ita in za a kashe ta bata san me suke dannawa ba, ya buɗe falon suka shiga dogon corridor ɗin da yake falon kafin ka shiga.

Ƙhamshi ya mamaye ko ina a falon, sai ƙhamshi yake yi kuma ko tass musamman tiles ɗin har fuskar ka kana gani.

Basu same shi a falon ƙasan ba, Jazy ya hau saman tana bayansa. Suna shiga falon suka same sa yana danna waya ga laptop a gabansa yana video call, ga takardu a jibge a gabanda.

Jazy aya ƙarasa falon ita kuma ta karya kwana inda ɗakinta yake.

Jazy ya ce, "Mr Busy." Bai ko kalle sa ba ya cigaba da magana da english, ana faÉ—a masa yana jotting a wayarsa kafin ya gama a katse kiran.

Ya ja numfashi ya ce, "zan je englaand in sha Allah." Sai kuma ya kalli Jazy suka haÉ—a ido ya ce, "sai kawai ka fito ka bar Riyya ita kaÉ—ai?."

Jazy ya ce, "Janan da su Ikram suna can."

Ya ɗan yi murmushi ya ce, "ta ya zan iya auren ƙannena? Sune fa ƙawayen matar tawa."

"Sai me?."

"sai rashin class."

"A wajan ka kenan. Bilal ne ya kira ni, yace yana ta neman ka baya samu. Akwai waÉ—anda suka kawo kaya mall, kayan sun yi yawan da dole sai da kai."

Ray ya harare sa ya ce, "kai ko ni?."

Shima ya rama hararar ya ce, "kai dai."

Ray ya koma kalar tausayi ya ce, "Jazy ba ka tausayina, dame ka ke so na ji? Kaina ya kusa ya yi bindinga Allah."

"Zama billionaire ai ba wasa ba, haka zaka cigaba da haƙuri. Matarka ce ma abin tausayi, yanayin yadda ka ke aikace-aikace nan ba ka da lokacin ta."

Bai amsa ba Jazy ya ce, "ga asibiti ma ana neman ka." Ya yi masa shiru bai ce komai ba, sai kuma ya É—auki ice matcha É—insa yana sha yana shafa kansa.

"Ray barin Islaha ta fita ita kaɗai bai dace ba, kana taƙamar auren sirri ka yi amma ka san bana sirri bane, tunda jama'ar gidan nan kaf sun sani. Ɗazu ma a news an yi maganar auren nan naka, ana so a gasgata da gaske ne ko ƙarya. Barinta ita kaɗai ba daidai bane, yanzu na haɗu da ita a farkon estate ɗin nan an hanata shigowa, yanzu hakan siyawa kai mutunci ne? Matarka guda ace security sun hana ta wucewa?.”

"Kai baza ku takura min akanta ba fa, ni na ce ta fita ita kaÉ—ai É—in? Meyasa bata nemi wani a gidan nan ya fita da ita ba?. Ya ku ke É—ora min laifin da ba nawa ba?."

"kai ya kamata ka samar mata driver É—aya da zai dinga kai ta inda zata je, matarka ce fa."

"Point of correection! Ka kira ta da C wife, a haka nake kallonta ba mata ba” ya furta yana hararsa.

Jazy ya ce, "Koma dai meye matarka sunanta, ban damu da wani C wife ba, tunda an bada sadaki an shaida sunanta matar ka. Ni zan yi magana da Shams, ya bani mutum É—aya a ajjiye mata duk inda zata je su dinga comminicating a waya."

Ray ya taɓe baki bai ce komai ba yana jinsa yana waya da Shams har ya ba shi number Lawal driver, ya kira ya ce yazo ya same sa.

Sai da ya gama wayar sannan ya kalle shi ta ƙasan idanu ya ce, "amma in za ka yi aure na biyu da ita za ka yi ko?."

Jazy ya kalle sa ya ce, "Eh mana, jira nake ka sake ta sai na É—auka, ai ba haramci a ciki ko?."

"I see, zaƙewar ka akanta ya yi yawa, kamar wata mai mahimmaci a gare ka. Amma ka sani sai dai ka rabu da Riyya, baza ka haɗa min ƙanwa da wannan gurɓatacciyar ragowar su Ubaid ɗin ba."
Chapter 22 · 0% Book details