← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 110

Sashe 106

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya sake mayar da ido kanta, a lokacin suka haɗa ido da ita sai ta ɗauke kai tana jin gabanta yana faɗuwa ganin irin kallon da yake jifanta da shi wanda bata taɓa gani ba.

Rehaan ya miƙe ya ƙarasa inda ake magana ya yi magana cikin fulfulde, sannan ya ɗauki nauyin yaran dukkansu, ya ɗauki nauyin karatunsu daga matakin primary har phd, in ƙasar za su bari su yi karatu ya ɗauƙi nauyi, komai nasu ya dawo hannunsa. Sannan ya saka a bincika lafiyarsu indai akwai wanda zai iya warkewa ya ɗauki nauyin biyan kuɗin. Sannan ya yi musu kyautar kuɗi masu nauyi, kyautar da ko gwamna da yake wajan bai yi abinda ya yi ba.

Ana ta zuba masa video ana tafi, dan baƙon abu ne ka gan shi a taro, ba zuwa yake yi ba sai an ci sa a sosai, shiyasa ake ta yi masa hotuna da video.

Bayan ya dawo ya zauna, Jazy ma ya je ya yi nasa ya dawo ya zauna ya kallr shi ya ga yana kallon ta, ita kuma a lokacin tana yiwa yaran tambaya suna bata amsa, ga camera ana yi mata video alamun recording ake yi.

Jazy ya ce, "kana kishi ko?." Ya kalle sa ya É—auke kai bai ce komai ba.

Bayan taro ya tashi ana ta fita, ƴan jarida suka taho kansa amma aka hanasu zuwa, shine ya bada umarnin duk su ƙaraso inda yake zai amsa ko wacce tambaya, ai kuwa suka zagaye shi ana video ana miƙa masa speaker.

Ray ya miƙe tsaye yana kallonsu ɗaya daga cikin ƴan jaridar ya ce, "Yallaɓai a dah ba a ganinka a irin waɗnanan tarukan, amma kwana biyu muna yawan ganin fuskar ka a ko ina, ko zamu iya sanin dalili?."

Ya kalle shi ya ce, "na samu lokacin zuwa ne.”

“Ka daina zaman Engalaad kenan?.”

“ban daina ba.”

Wani ma ya ce, "ka ɗauki nauyin yaran nan gabaɗayansu, ya ka ke jin abinda suka ƙirƙira a ran ka?."

"ina alfahari dasu."

"Me zaka ce akan baiwar da Allah ya yiwa yaran nan?."

"Suna da baiwa ta musamman, in suka samu kulawa ƙasarmu zata samu manyan ƴan kimiya kamar su, zamu je inda ba mu yi tunanin zuwa ba saboda su."

Islaha tana kallonsa yana magana ta ƙi ta motsa, bakinsa kaɗai take kallo tana tuna abinda ya faru jiya. Sai taɓe baki take yi ganin kamar ba shine ya gama taɓa mata jiki ba, yanzu gashi ya zo an zagaye shi yana jin kansa shi wani ne. Inda zata faɗawa mutane abinda ya yi mata jiya cewa za a yi ƙarya take yi, wani ma sai ya ɗauka bata da hankali dan bai yi kama da wanda zai aikata ba ko kaɗan.

Chairman yana ta yi mata alama akan taje wajan Rehaan ta yi kamar bata gan shi ba, sai da suka haɗa ido sannan ta yi tsaki ta ƙarasa ta ɓuya a cikin mutane, sai voice ɗinta da speaker hannunta da ta miƙo inda yake ta ce, "Da gaske Mr Rehaan zai iya cika alƙawarin da ya ɗauka akan kula da yaran nan? Mun sha jin irin waɗannan alƙawarin daga bakunan mutane, alƙawarin na gaske ne ko irin wanda muka saba da shi ne?.”

Duk da akwai hayaniya a wajen bai hana ya ji zaƙin muryarta har tsakiyar kansa ba, ya kalli inda ta ke tsaye, yana kallon hannunta da ya ɗan leƙo ta cikin mutane, sai ya yiwa mutanen wajen alama da su buɗa wajan, aka buɗa wajen Islaha tana tsaye tana kallon gefe har lokacin bata ɗauke hannunta da ta miƙa masa speaker ba.

Ta juyo ta kalle shi, ya yi mata alama da ta zo da hannunsa. A take idon mutane ya dawo kanta, kowa ya zuba mata ido ana jira a ga zata je ɗin ko baza ta je ba. Saboda gudun abin magana sai yi ƙaramin tsaki ta ƙarasa zuwa wajan tana kallonsa.

Rehaan kallonta yake yi yana jin nishaɗi mai yawa yana ratsa shi, in yana kallonta sai ya ji kamar babu wanda ya kai shi farin ciki a duniya. Sai da ta ƙaraso sannan ya kalli cikin idanunta ya ce, "Maimaita, me ki ka ce?."

Ba tare da shakka ba Islaha ta ce, "Da gaske Mr Rehaan zai cika alƙawarin da ya ɗauka ko kuwa ya faɗa ne saboda idanun mutane?.”

Ray ya kalli Jazy da yake wani smiling daga tsaye, ya kalle ta amma bai ce komai ba.

Ɗaya daga cikin ƴan jaridar ya yi caraf ya ce, "ƴar jarida Islaha ce ta fara hira da kai da harshen hausa a kaf nigeria, kowa ya ga yadda hirar ta kasance da duk abinda ya faru. Mutane suna ta yaɗawa akan akwai ɓoyayyiyar alaƙa a tsakaninka da ita, zamu so mu ji daga bakin ka, da gaske akwai alaƙar ko babu?."

Gabanta ya faɗi sosai amma bata nuna ba, ta kalle shi suka haɗa ido sai juyar da kanta gefe, dan wani irin kallo yake yi mata wanda yake yi mata nauyi, sai ta ji ta kasa jurewa sai ta ɗauke idonta daga kansa. Ita kuma in ta kalle shi daren jiya take taunawa, shiyasa bata yarda su haɗa ido, kuma bata damu da tambayar da aka yi masa ba, dan ta san ba faɗar alaƙarsu zai yi ba.

Rehaan da yake kallonta ya yi murmushi ya ce, "yeah akwai alaƙa a tsakaninmu!."

Islaha ta zaro idanu waje, da hanzari ta juyo suka haÉ—a ido, idanunta suka firfito waje tana girgiza masa kai alamun kar ya faÉ—a don Allah.

Rehaan ya yi wani irin murmushi yana bin fuskarta da kallo, yana rolling idanunsa a fuskarta yana jin nishaɗi a zuciyarsa. Sai ya zura yatsunsa a cikin nata, ya sarƙe hannunsu waje ɗaya yana kallon fuskarta.

Ta so ƙwace hannunta amma ta kasa, babban tashin hankalinta a gaban ƴan jarida ga shi ana ta ɗaukarsu hoto, kar ta yi wanj abin da zai jawo mata ɓatawar suna, ta haƙura da ƙwace hannunta ta kalli ƴan jaridar ta ce, "he is my...."

"she is my wife.....”

Ya dakata yana kallon idanunta sannan ya ce, “my secret wife" ya faɗa yana kallon idanunta da suka firfito waje, kafin ya duƙa ya yi picking ɗinta a kumatu. Islaha sai ta ɗan firgita lokacin da ta ji bakinsa a cheeck ɗinta, ta daskare a wajan idanunta suna waje ta zazzaro su saboda tashin hankali......

Nana Haleema.

RDB3P78
Nana Haleema.

Islaha kallon idanunsa take yi idanunta a waje saboda tsoro da tashin hankali, kwata-kwata bata taɓa zaton zai furta wannan maganar ba, ba taɓa tunanin zai amsa shine mijinta a gaban ƴan jarida ba. Ta zuba masa ido tana kallonsa cikin tashin hankali, sai da ya murza yatsunta sannan ta dawo hankalinta ta kalli yadda idanun mutane yake a kansu gabɗaya, sai ta ji kunya ta lulluɓe ta kamar ta nutse a wajan.

"Yallaɓai tun yaushe hakan ya faru?."

"Kenan da gaske itace matar sirrin da aka ce ka yi?."

"Daman ita ce wacce ka aura?."

"Meyasa da ta yi hira da kai bata faÉ—a ba?."

Tambayoyin da ake ta yi masa kenan, shi kuma idanunsa yana kanta yana kallon yadda ta firgita da kalamansa, kafin ya juyo ya kalli Æ´an jarida, sai ya kalli Jazy da ya yi clapping hannunsa alamun ya kyauta.

Ya ɗauke kansa yana riƙe da hannunta bai saki ba, ya ja hannunta zasu tafi ya ji ta turje, ya kalle ta suka sake haɗa ido ya sunkuya ya kai bakinsa kusa da kunnen ta ya ce, "mu tafi, ko in ɗauke ki."

Islaha ta sake kallonsa dan gani take kamar an canja shi, ba Mr Rehaan ɗin da ta sani ba, wani ne daban a gabanta ba wanda suka saba kafsa faɗa bane ba. In kuwa shine to ciwon kan da ya yi jiya ya taɓa masa ƙwaƙwalwa, ko kuma ya manta wacece ita shiyasa yake yi mata waɗannan abubuwan da bata taɓa zato ba. A ganinta inda ya san itace bazai yi ba, shiyasa ta saka a ranta bai fahimci ita bace.

Jin ya ce zai ɗauke ta sai ta yi sanyi sosai, dan bata shiryawa faruwar hakan ba, ya barta ta ji da abinda ya faɗa a gaban mutane ba sai ya sake ƙara mata wani tension ɗin ba. Rehaan ya ja hannunta suka tafi, ita dai ta san an karɓi loudspeaker da take hannunta bata san waye ba.

Har suka je wajan mota yana riƙe da hannunta, sai da suka je wajen motar sannan fizge hannunta zata fara yi masa masifa ya kalli fuskarta ya ce, "Calm down! Akwai securities a nan, ki bari mu koma gida."

Wani irin wuci ɓacin rai take yi wanda Jazy ya lura da shi, ko ba a faɗa ba ya san Rehaan ya ɓallo ruwa mai kwarara daga sama, dan ya san bata yi tunanin zai faɗi alaƙarsu a wajan ba, ya san ko da wasa bata yi hasashen zai bayyanawa duniya uta matarsa bace. Shi kuma ya ji daɗi da ya faɗa ɗin, ko babu komai Poor Saheer zai san ta fi ƙarfinsa, zai daina hangenta har ya saka a ransa zata dawo. Matar da Rehaan ba matarsa bace, koda Rehaan ya rabu da Islaha a ganinsa ta fi ƙarfin Saheer. A haka suka shiga mota shi da ita aka ja motar suka tafi.

Maimakom ta ga an wuce gida sai ta ga sun nufi ɗaya daga guest house ɗinsa, ta yi shiru ta daure bata ce komai ba, ga shi ya riƙe mata hannu ya hanata ƙwacewa, ta juya tana kallon window tana jira su sauka daga motar.

Sai da zasu fito daga motar sannan ta fizge hannunta, ya sake riƙo hannunta yana yi mata magana da ido, kamar wacce ya yiwa asiri sai kawai ta dakata yana jan hannunta har suka shiga parlour.

Suna shiga ta ƙwace hannunta cikin masifa ta ce, "meye naka na faɗawa duniya ni matarka ce, meye na yi hakan?.”

Ya waiwayo yana kallonta yana cire hular kansa, Islaha ta ce, "Na ga a cikin rules ɗinka da ka rubuta min ka ce baka so duniya ta san ni matar ka ce, meyasa ka ke breaking rules ɗinka da kan ka?.”
Chapter 106 · 0% Book details