← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 110

Sashe 95

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya kalli Islaha ya ga har lokacin tana yadda ta ke, ya ɗauke kai yana jin wani irin zafi a fatar jikinsa, ya yi ƙaramin tsaki ya ce, "Don Allah ku je, sai da safe" ya faɗa yana juyawa ya hau sama da sauri.

Bai san ya suka ƙare ba ya ji shiru ɗuf babu motsin kowa a falon. Yana tsaye ya jingina da bango yana ajiyar zuciya sai wayar ta yi ƙara, ganin Mamy ce sai ya ɗauka abinda ta ce ya saka ya sakko ƙasan ya ganta a zaune kusa da Islaha ta kwantar da kanata a jikinta tana ta kuka.

Mamy ta kalle sa bayan ya ƙaraso ta ce, "ban yarda ba Rehaan, wannan maganar shirya ta aka yi, ina so wannan ma ta shiga cikin maganarmu ta ɗazu, a warware komai Rehaan. A samo wanda yake buɗe ƙofar parlour nan, dan na ga kamar camerar bakin ƙofar ta daina aiki. Na tabbatar aiko Salman ake yi yana zuwa apartment ɗin nan, wani lokacin ba zuwan kansa bane aiko shi ake yi."

Ta shafa fuskar Islaha tana goge mata hawaye ta ce, "Bana so na ga tana kuka, ina jin zafin kukanta a cikin zuciyata, ka yi min abinda zan daina ganin hawaye a idanunta Rehaan."

Rehaan bai iya cewa komai ba, itama Mamy ganin yanayinsa bata yi tunanin zai yi magana ba, dan fuskarsa ta canja sosai ta nuna alamun ɓacin rai da damuwa. Sai ta miƙe ta fita ta bar Islaha a zaune tana jan nunfashi. Yana tsaye yana kallon ta, yana jin takaici da baƙin ciki suna zagaye ilahirin jikinsa, yana hango zubar da cikin da ta yi a Jeddah a idanunsa.

Ga shi dai yana jin tausayinta sosai, amma bai taɓa jin haushinta kamar lokacin ba, bai taɓa jin yana danasanin haɗa ido da ita ba sai a lokacin, bai san meyasa abinda yake ji ya rinjayi tausayin ba, ya san dai zuciyarsa tana yi maza zafi da ƙuna amma bai san dalili ba.

Har cikin zuciyarsa ya ke jin abinda ta aikata, yana daurewa ne bai nuna ba saboda mutanen gidan, amma in ya tuna yayansa ne, kuma ta buɗe masa ƙofa ya shigo sai ya ji takaici yana mamaye masa zuciya. Tambayar da yake yiwa kansa me ya sakko da ita? Dan ya san ƙawarta tana tare da ita, me ya sakko da ita ta bar ƙawarta a sama?.

Islaha bata san yana tsaye ba ta ɗago a hankali tana buɗe idanunta da suka yi nata nauyi, ta kalli inda yake sai suka suka haɗa ido, ta sake rufewa ta buɗe ta miƙe zaune sosai tana kallonsa.

A zuciyarsa yake ji yana faɗar maganar bai san ta fito fili ba ya ce, "Me ki ka aikata haka? Ki bari a gama da case ɗin ɗazu mana, ki bari saka wanda ki ka kai wajensa har ya yi miki ya goge video da ya yi miki, sannan a sauke shi da media kafin ki ki cigaba. Har cikin apartment ɗina, bakya jin kunyar Allah ki ka gayyato Salman har nan?. Oh shiyasa ki ka sakko nan, saboda ƙawarki tana sama ko? Meyasa baza ki jira a gama case ɗin da yake gaban ki ba?."

Islaha ta ɗago iso ta sake kallonsa ta buɗe baki zata yi magana sai ta ji ta kasa, ta miƙe tsaye ta tsaya tana dafe kanta, dan bata san me zata ce ba gwara ta yi masa shiru.

Ya ce, "Duk abinda zaki yi ki yi, amma ban da ɗan uwana, sai lokacin da ki ka zo gidan nan sannan ya zama haka, ki ɗauke ido daga kansa. In masu gadin gidan nan za ki nema wannan ra'ayinki ne, amma wani daga cikin gidan nan kar ki sake wannan kuskuren. Ki je can ki ƙarata da mazan da ki ka saba bi suna recording ɗin ki, amma a cikin gidan nan bazan yi tolerating wannan shirmen ba."

Islaha duk da bata jin daÉ—i kwata-kwata, tana ji kamar zata sume a wajen amma hakan bai saka ta buÉ—e baki ta ce, "Mr Rehaan!."

Ta ku uku ya yi ya ƙaraso daf da ita, ta buɗe idanunsa a cikin mata ya ɗora finger ɗinsa akan lips ɗinta ya ce, "shiiiiii!."

Ya girgiza kai ya ce, "kar ki ƙara faɗar sunana, i saw anythings, i heard anythings, ba ki da abinda zaki faɗa min abinda na gani ko na ji."

Ta zuba masa ido kawai tana kallonsa, ƙirjinta yana ɗagawa saboda numfashin da take yi. A kunnensa yake jin yadda numfashinta sauka, kana ji ka san bata da lafiyar numfashi, kuma tana fama da lalura a lokacin.

Sai ya ja baya ya ce, "saboda Mamy, saboda ita kaÉ—ai zan tsaya a goge pictures É—in nan, in ba dan ita ba babu dalilin da zai saka na saka hannuna a case É—in ki...."

Ya kuma ja da baya yana tafiya ya ce, "saboda Mamy kawai!" ya faɗa yana juyawa zai hau sama, su ka haɗu da Safeera tana sakkowa. Kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai, ta ba shi hanya ya wuce ita kuma ta ƙaraso wajan Islaha.

Islaha bata san ta ƙaraso ba sai da Safeera ta dafata ta ce, "Islaha meye kuma ya sake faruwa cikin daren nan? Kin ga yadda fuskar ki ta sake komawa? Me ye ya faru?."

Islaha ta kalli Safeera ta ce, "zaki iya yi min wani taimako?."

Safeera ta ce, "me zai hana, faÉ—a min ko meye ina jin ki."

Islaha tana riƙe da kanta ta ce, "ina zuwa." Ta faɗa tana shiga kitchen, ba jimawa ta dawo ɗauke da sabuwar wuƙa sai ƙyalli take yi.

Ta miƙawa Safeera ta ce, "Don Allah ki kashe ni, ki kashe ni na huta Safeera. Bana so na mutu kafira, da yanzu na jima da bugawa kaina wannan wuƙar kowa ya huta. Tunda bani da kowa, bani da mai saurarena, bani da wanda zai fahimce ni."

Safeera da ta daskare a tsaye saboda mamaki ta ce, "Islaha kina cikin hankalin ki kuwa, me ki ke faÉ—a haka?."

"Safeera ya zan yi, ni kaÉ—ai na san abinda nake ji a zuciyata, so nake na mutu, gwara ki kashe kawai."

Safeera ta ce, "dan ƙaddara ta same ki sai ki gaza karɓarta, dan Allah ya jarabce ki sai ki kasa cin jarabawar?. Abinda za ki sakawa wanda ya halicce ki da shi kenan, da irin waɗanann kalaman za ki karɓi ƙaddarar ki Islaha?. Musulma ce ke, kin yi imani da ƙaddara mai kyau da mara kyau, masu kyau sun zo miki sau babu adadi, kin karɓa kin gode kina farin ciki, kina alfahari da kasancewar ki a inuwar musulunci. Yanzu dan akasinta ta zo sau ɗaya tak sai ki juya baya? Zai ki rufe ido ki manta da Allah ne ya yi nufin hakan?."

Islaha ta ajjiye wuƙar hannunta ta zauna akan kujera ta ce, "Safeera hotunan tsaraicina ne suka yawo a duniya, ga wani abinda da akace na sake yi, ance na gayyaro namiji har parlour nan, kuma bani da bakin kare kaina, dan kowa ya ganni. Safeera ina ji in ban mutu ba bazan samu sassauci ba."

Ta zauna kusa da ita cikin rarrashi ta ce, "ki tuba ga Allah, ki nemi yafiya akan kalaman nan na ki yanzun nan."

Muryarta tana cracking ta ce, "astagafirullah!."

Safeera ta dafata ta ce, "Allah bazai taɓa bari ki wulaƙanta ba, zai shige miki gaba a duk lamarin da ki ka saka a gaba, zai ba ki kariya a lokacin da ki ke buƙatar kariyarsa, abu ɗaya kawai za ki yi, ki yarda da shine mai yi kuma shine mai yayewa, ki roƙesa zai amsa miki. Waɗanda suka yaɗa hotunan nan zai yi maganinsu, zai tona musu asiri a idannun duniya. Ki yi haƙuri, ki dinga maimaita innalillahi wa'in a ilaihir raji'un, ki dinga maimaita la'ilaha illahu azimul halim, la'ilaha illahu rabbil arsil azim, la'ilaha illahu rabbu samawati wal arabi wa rabbul arshil kareem, komai zai tafi yadda ki ke so."

_(A duk lokacin da ɗayanmu ya shiga matsala, damuwa ko ya faɗa hannun ɓarayi ko mutane masu cutarwa, ya dinga maimaita wannan addu'ar bazai gushe ba sai Allah ya kawo masa mafita.)_

Islaha ta ce, "to Safeera, zan yi."

Safeera ta dinga rarrashinta har ta daina kukan, ta ɗauke wuƙar ta mayar da ita mazauninta, kafin ta taimaka mata su koma saman, ta saka ta suka yi alwala ta tayar da sallah, Islaha ta yi sallar a zaune dan baza ta iya tsayuwa ba saboda ciwon kai.

Rehaan tunda ya shiga ɗaki yana sauke ajiyar zuciya, a jikin mirror ya zauna idanunsa suna ƙasa yana furzar da iska mai zafi, tausayin Islaha ne yake mamaye masa zuciya, har ya fara jin haushin kansa akan abinda ya faɗa mata, yana ji kamar ya sauka ya rarrasheta har sai ta daina kuka. Ba dan cin fuska ko wulaƙanci ya faɗa mata ba, ya faɗa ne dan ya kore yanayin da yake addabar zuciyarsa, ya faɗa dan ya samu mafaka ya kushe ta ko zai daina jin abinda yake ji, amma bai daina ba sai ma hauhawa da yanayin yake yi. Sai kuma ya yi tsaki ya haɗɗiye yawu yana lumshe idanunsa ya ce, "Oh my god! Ya Allah me nake ji haka, meyasa raina ya ɓaci?."

Sai kuma ya tuna da Mamy ya ce, "Saboda Mamy, saboda Mamy kaÉ—ai nake yi, Itace ta saka ni, dole zan yi saboda ita" ya faÉ—a yana É—aukar waya maimakon ya kira Dss É—in da ya bawa aiki sai ya kira Jazy.

Jazy yana zaune akan sallaya shi da Riyya sun idar da tahajjud ya ji wayarsa tana vibrating, ya jawo ya duba ya ce, "Ray kuma! A daren nan?" Ya faÉ—a tana É—auka ya saka a speaker.

Jazy ya ce, "Ray ya aka yi, wani abu ya faru ne?."

Bai iya magana ba sai numfashi da yake saukewa a hankali.

Jazy ya ce, "dare ne fa Ray, ka kira ni ka yi shiru."

Cikin wata irin murya mai nuni da raunin zuciyarsa ya ce, "ka yi mgana da mutumin nan?."

Da mamaki ya ce, "ikon Allah! Ka rasa lokacin tambayata wannan maganar sai yanzu? Ka jira gobe mana, ba da kai aka zauna dasu ba?."
Chapter 95 · 0% Book details