Sashe 43
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta É—auko a jakar ta ta matsawa Islaha a bakinta, suka cigaba da yi mata firfita. Sun É—an jima a haka kafin Islaha ta fara dawowa hankalinta, ta buÉ—e ido a hankali tana kallonsa, cikin lokaci kaÉ—an ta dawo daidai.
Wacce ta bata Inhaler ta ce, "Sannu baiwar Allah." Islaha ta É—aga kai kawai bata ce komai ba.
"Ina inher É—in ki?."
Bata iya bata amsa ba, sai lumshe ido da take yi kamar mai jin bacci.
Shi dai Lawal hamdala kawai yake yi, ganin ta dawo daidai da bai san ya zai yi mata ba. Matan ne suka taimaka mata ta shiga mota, sai da ta ja numfashi sannan ta ce, "Na gode."
ÆŠaya ta ce, "babu komai, nima ina da irin ciwo. Amma ki dinga yawo da inlaher, in ba haka ba za a samu matsala."
“In sha Allah, na gode.â€
“Babu komai†daga haka suka yi mata sallama suka tafi.
Lawal ya shiga motar ya ce, "Sannu Madam." Islaha ta amsa masa da kanta bata ce komai ba
Lawal ya kalli matan ta mirror, yana aiyana da suna tare da Rehaan da kakarsu ta yanke saƙa. Sai da ya ja motar sannan ta ce, "Ka rage ac don Allah." Da hanari ya rage yana tafiya a hankali kar a sake samun matsala.
Lokacin da suka je gidan har bakin apartment ɗinsu ya ajjiye moyar, ya sakko ya buɗe mata ƙofar ta sakko yana ta yi mata sannu.
Ta ɗaga kai ta ce, "Na ji sauƙi, na gode sosai."
"Amma Hajiya ya kamata a sanar da mutanen gidan nan abinda ya faru, mai motar nan da gangan ya yi ƙoƙarin taka ki, kamar daman jira yake ki fito daga gidan, dan na lura kamar bayan mu suke bi."
Islaha bata da lokacin yin tunani a wannan lokacin sai ta ce, "za a san abinda za a yi, na gode da taimakon da ka yi min, Allah ya saka da alkhairi" ta faÉ—a tana wucewa ciki.
Ta so ta shiga wajan Mamy da Daada su gaisa amma baza ta iya ba, ta zauna a falon ta cire É—ankwalin kanta ta kwance gashinta ta dafe kai da duka hannunta.
Ta jima a haka kafin ta miƙe ta hau saman ta kwanta a kan gado dan bata jin ƙarfi a jikinta ko kaɗam. A haka bacci ya ɗauke ta, sai la'asar ta farka ta tashi ta yi sallah ta yi wanka ta fito falon.
Har lokacin babu alamun Rehaan yana nan, bata damu da yana nan ko baya nan ba ta sauka ta É—an ci abinci kaÉ—an tana bin ko ina na falon da kallo.
A bayyane ta ce, "Ba dole Hamma ya ce na yi kyau ba, tunda nazo gidan nan ko tsintsiya da sunan shara ban É—auka ba, sai dai na zo na ga an gyara ko ina, balle kuma girki.â€
Sai da rana ta yi sanyi sosai sannan ta yafa mayafi akan ɗauraren gashinta ta fita zuwa wajan Mamy kamar yadda ta yi niya tun farko. Da sallama ta shiga cikin falon, sai da ta saka ƙafarta a falon sannan ta ɗago ido tana kallon mutanen ciki.
Rehaan yana zaune akan kujerar da take farko cikin manyan kaya, farin mace lace da hula wacce ta dace da kayan jikinsa, kayan sun karɓi jikinsa sosai. Dawowarsa gidan kenan dan ba a gida ya samu juma'a ba, ya fita ɗaurin aure da reception da aka gayyace shi, yana zaune yana ta ya Banisha game a wayar ta. Sai Mamy da ta ke zaune a gefe tana amsa waya, sai Ikram da take zaune tana cin abinci a ƙaramin bowl.
Mamy ta ajjiye wayar ta amsa sallamar tana kallonta ta ce, "Islaha shigo mana."
Islaha ta ƙarasa tsakiyar falon da ƙhamshinsa ya cika ko ina. Kamar bai san ta shigo ba, ya mayar da hankalinsa wajan Banisha gabaɗaya.
Islaha itama bata nuna ta gan shi ba, tafiya take yi da niyar ƙarasawa kusa da Mamy. Gab da zata gifta shi ta ji an ja mayafinta da ƙarfi ta bayanta, jan mayafin da aka yi sai ya taho da ribbon ɗin kanta, zafin jan mayafin da ya haɗo da gashinta ya saka ta yi ƙaramar ƙara a lokacin mayafin da ribbon ɗin suka zube a ƙasa, gashinta ya warware ya sauka a fuskar Rehaan gabaɗaya.
Kafin su farga da wanda ya janye mata mayafin ya damƙi gashinta da ƙarfi ya ce, "Lahh wannan duka gashinki ne?."
Islaha ta runtse ido jin zafin yana ratsa kanta da ƙwaƙwalwar, daman ga ciwon kan da take fama dashi, ga shi ana sake ja mata gashinta.
Mamy cikin faÉ—a ta ce, "Salman meye haka?."
Sai a lokacin ya sa ki gashin Islaha ya kalli Mamy ya ce, "Mamy ni wajanta nazo, tun É—azu nake nemanta an ce bata nan, shine nake murna da na ganta."
Kafin Mamy ta sake magana Salman ya nufo wajan Islaha kamar zai riƙe ta, babu shiri ta buga tsalle ta yi bayan Mamy a guje.
"Meye haka ka ke yi!?" Rehaan ya faɗa cikin tsawa yana riƙe sa.
Salman ya kalli Rehaan ya ce, "Ni wajanta na zo, kuma kaima ka ce ai tana sona ko?."
Rehana ya yi tsaki ya ce, "Ka bar wannan shirmen" ya sake faÉ—a yana jan hannunsa ya zaunar dashi a kusa dashi.
Islaha gabaɗaya ta tsorata da abinda ya faru, Mamy ta riƙo hannunta ta zaunar da ita a kusa da ita sanann ta ce, "Ikram bani ribbon da mayafin ta."
Ikram kallon gashin Islaha kawai take yi, itma tana da gashi sosai amma ko rabin na Islaha bai yi ba, na Islaha baƙi ne sosai, ga yawa da tsaho.
Ta ɗauke kaita miƙawa Mamy ribbon da mayafin, Mamy ta karɓa da kanta ta ɗaurewa Islaha gashinta, ta yafa mata mayafin a kanta ita dai satar kallon Salman take yi.
Islaha tana zaune a kusa da Mamy bata ce komai ba, Rehaan shi kam kamar bai san da ita a wajan ba. Salman ya taɓa Rehaan hakan ya saka shi ya kalle sa ya ce, "Za ka bar min ita mu dinga wasa? Daada ta ce wai matar ka ce, kuma na san kai kana sona, za ka bani ita ko? Ni ina sonta kamar yadda nake son cartoon ta cikin tv."
Reahan ya É—an kalli Islaha da take kallon Salman, ya kalli Salman ya ce, "Ka je masallaci ka yi sallah?."
Ya É—aga kai ya ce, "tare muka yi da Abba."
Sai ya yi shiru bai ce komai ce masa komai ba, dan bai san me zai ce masa ba.
Salman ya sake cewa, "za ka bani?."
"Zan bar maka ita, ba haka ka ke so ba?." Ya É—aga kai da sauri yana dariyar farin ciki.
Rehaan ya ce, "amma sai ka daina abinda ka ke, ka ji?." Ya É—aga kai alamun to ya daina sannan ya ce, "To ta zo mu tafi wajan Umma ta zauna a can, ka ga cartoom É—im ma a tv Umma na ke gani, itama sai na dinga ganinta a tv Umma ko?."
Rehaan ya ce, "In na koma england shikenan na bar maka ita."
Cikin zumuÉ—i ya ce, "yaushe za ka koma?."
"Na kusa" ya faɗa cikin ƙoasawa da maganar yana ɗan lumshe idanunsa.
Salman ya ce, "to zan je na faÉ—awa Umma, ta siya mata kayan wasa irin nawa ko?.
" Ya ɗaga masa kai shi kuma ya miƙe ya fita da hanzari.
Sai a lokacin Islaha ta yi ajiyar zuciya ta kalli Mamy da take kallon Rehaan. Mamy ta ce, "Ba hankali ne da shi ba, ka daina biye masa Rehaan." Ray bai ce komai ba sai waya da ya É—auko yana dubawa.
Islaha ta ce, "Mamy daman nazo na gaishe ki."
Mamy ta yi murmushi ta ce, "Na gode Islaha. Ni bazan ce Islam É—in an da Bansha ta saka miki ba, sunanki ya fi daÉ—i."
Islaha ta yi murmushi bata ce komai ba, amma tana mamakin yadda Mamyn ta canja lokaci É—aya, ta daina haÉ—e mata rai har take yi mata magana haka.
Islaha ta miƙe ta ce, "Zan koma."
Mamy ta ce, "to na gode.†Islaha ta nufi hanyar fita tana tafiya a hankali ta fita daga falon.
Bayan Islaha ta fita Mamy ta taɓa Rehaan da ko hanyar da Islaha ta bi bai kalla ba ta ce, "kai lamarin Salman ba abin zuba masa ido bane ba, matar aure yake yiwa mata wannan shirmen?."
Rehaan ya kalli Mamy cikin ko in kula ya ce, "ni me zan yi? ÆŠan uwana ne."
"dan É—an uwanka ne matarsa ce? Kar abin ya yi nisa ya zarce tunanin mu fa, kar nan gaba ka zo kana danasani akan wannan alaÆ™ar da ka haÉ—a.â€
Sai ya miƙe ya ce, "Mamy na gaji" ya faɗa yana fita daga apartment ɗin gabaɗaya.
Mamy ta yi tsaki ta ce, "Rehaan yana da shirme wallahi, zan yiwa Jafar magana ya san yadda zai ɓullowa lamarin, wannan abun ba abinda za a yi shiru bane tunda Salman ba shi da hankali. Abin ya fara yin yawa, tunda har ya fara cire mata mayafi a gaban mutane" ta faɗa tana miƙewa ta shiga ciki.
Ikram dai bata ce komai ba ta yi shiru, yanayin yadda Rehaan ya yi wa Islaha ya tabbatar mata da gaske ba ya sonta, dan in akwai so tabbas akwai kishi. Ita bata ga alamun kishi ko kaɗan a tare da shi ba, kamar bai san abinda ya faru ba, bayan matarsa aka cirewa mayafi. Sai ta tafi tunanin itama in ya aure ta ba ya sonta haka ne zai faru? Da wannan tunanin ta miƙe ta shiga ɗakin da Riyya ta bari.
Islaha tana fita Mama ta hangota ta kira sunanta hakan ya saka ƙarasawa apartment ɗin Mama. Mama ta dafata ta ce, "Da ban gan ki baza ki shigo ba?."
Islaha ta yi murmushi dan matar tana burge ta sosai ta ce, "Daman zan zo mu gaisa."
"Ya na ji maganar ki haka, ba ki da lafiya?" Ta faÉ—a lokacin da suke shiga falon Mama.
Islaha ta ce, "kaina ne yake ciwo."
Cikin nuna kulawa ta ce, "Subahanallahi! Kin sha magani kuwa?." Islaha ta É—aga kai alamun eh.