← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 110

Sashe 19

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ɗaga kai ta ce, "In sha Allah zan yi iya ƙoƙarina wajan ganin na gayyato shi."

Ya yi murmushin jin daÉ—i ya ce, "Na san za ki iya, za ku iya tafiya."

Tare suka fito da Safeera da take ta gimtse dariya, tsabar son tsokana har office ta bita, Islaha tana saka id card a wuya, sannan ta ɗauki recoder da handbag ɗinta, ta ɗauki laptop ɗinta ta ƙi kallon Safeera dan ta san tsokana ce.

Safeera ta ce, "Uhum, wai matar mutum ake cewa yaushe zata gayyato mijinta ayi hira dashi, Abin burgewa.” Islaha ta yi mata banza bata saurare ta ba, sai sake haɗe fuska da ta yi ko kallon inda take bata yi.

"Ke Islaha, auren nan da alama bazai zama na sirri ba fa, ga shi har maganar ta fara fita."

Islaha ta kalle ta ce, "Ni muslim ya tsare wai ance na yi aure, ina faɗa masa ƙarya ne yana cewa bai yarda ba. Ni dai na shiga uku, wannan dabara bata amfane ni da komai ba sai danasani, wanda na yi dan shi ɗin ma ko kallona ya ƙi yi.

Kin san Allah, wallahi Hamma ya bani haushi, na yi danasanin zuwa inda yake, ban yi tunanin zai kasa buɗe baki ya yi min magana ba, ko da gaske abinda ake faɗa akan na bar shi saboda kuɗi na ɗauka akwai zumunci mai ƙarfi a tsakanina da shi."

Safeera ta ce, "bai kyauta ba kam gaskiya, nima ban ji daɗin yadda ya yi shiru ba, ai ko sannu ya ce miki. Amma ta wani ɓangaren ba shi da laifi Islaha, yana sonki so mai tsanani, yana cikin raɗaɗi da ciwo, yana buƙatar hutu mai yawa."

Ta ɗaga kai bata ce komai ba sai kuma ta ja tsaki ta ce, "Zan sake yiwa Mr Jafar magana akan hira da Rehaan, ko dan Chairman ya bar ni na sha iska.”

"Rehaan gatsal, babu mai gida ko oga?."

"Safeera zan iya shaƙe ki wataran."

Safeera ta ƙyalƙyale da dariya ta ce, "Yi haƙuri matar oga, kuma amaryar Saheer, kai astagafirullah!" Ta faɗa tunawa da auren Islaha take haɗa ta da wani.

"Meye na tuban, ƙarya ki ka faɗa?."

"amma ba a daidai lokacin nan ya kamata na faÉ—a ba."

"Ke ki ka sani."

"Mu je na ta ke miki baya, na zama escord É—in ki kafin nan gaba na gasken su fara take miki baya." Islaha ta harare ta. Safeera ta sake yin dariya suka fito dan tana jin daÉ—in tsokanarta.

A tsaye suka samu Ummi ganin Islaha sai ta É—an yi murmushi ta ce, "Islaha ya ki ke."

Islaha ta bita da wani bad look tana frowning face É—inta ta ce, "Lafiya." Daga haka suka wuce ta.

Ummi ta ce, "akan me suke magana haka, matar wa ta zama, da gaske dai ta yi auren ko bata yi ba?." Babu mai bata amsa, hakan ya saka kai tsaye ta nufi wajan abokinta Muslim.

Kiran wayar Abba ne ya tashi Rehaan daga bacci, ya miƙe yana kallon agogo ya ga ƙarfe sha ɗaya na rana, ya yi tsaki dan ya jima bai yi bacci ba daren jiya, ya jima yana hidimar aiki, yana buƙatar yin bacci mai nauyi da safe.

Ya jawo wayar ya É—auka ya saka a speaker Abba ya ce, "Rehaan kana gida?."

Cikin muryar bacci ya ce, "Uhum Abba, ina kwana."

"Lafiya lau. Ana ta knocking ƙofar shiru, Daada ta ba da abinci a kawo ba a buɗe ba."

Cike da mamaki ya ce, "Abinci Abba? Daman ana kawo min abinci ne?."

Abba ya ce, "matarka aka aikowa ai."

Ya runtse ido cike da takaici da ɓacin rai, dan shi wallahi ya manta da ita a tare da shi, sai kawai ya yi shiru bai ce komai ba.

Abba ya ce, "ku zo ku buÉ—e, ana tsaye ana jira."

Rehaa ya bi wayar da kallo, ya yi tsaki ya kira number Banisha dan ta zo ta buÉ—e amma har ta katse bata É—auka ba ya san bacci take yi.. Ya yi tsaki ya fi sau goma, ya sauka daga kan gadon a hankali, ya saka takalminsa ya fito daga É—akin.

Falon yana nan shiru babu kowa kamar yadda ya bar shi, ya kalli ƙofar ɗakinta dan shi bazai iya sauka ya karɓar mata abinci ba, in ba abincin Mamy ba babu abincin wanda yake ci sai na chef ɗinsa, bata isa tana bacci ya sauka ta karɓar mata abinci ya ajjiye ba.

Slowly yake takawa yana nufar ƙofar ɗakinta, ya buɗe yana kallon ɗakin ganin komai a kashe yake alamun babu kowa. Ya ja numfashi ya jawo ƙofar ya rufe ya fito daga ɗakin yana kiran wayar Abba.

Abba yana ɗauka ya ce, “Abba su koma da abincin kawai, na ga kamar bata nan."

Cikin mamaki Abba ya ce, "ka ga kamar bata nan kamar ya? Kana so ka ce ta fita ba ka sani ba?."

"Abba ai ba sai na sani ba, amma dai ni ban ganta ba."

Yana jiyo salatin Daada daga waya, sai ya yi saurin katse kiran ya shiga É—aki yana faÉ—in, "wannan tsohuwa tana takura min sosai, ta saka ni a gaba kamar itace ta haife ni, ina ruwana dan bata nan?" Ya faÉ—a tana shiga bathroom dan shikenan an katse masa bacci.

Bayan ya fito ya tsaya a gaban mirror, ya ɗauki hair burner yana burning gashin sa da lafiyayyen scent mai daɗi. Burner ɗin bata fi girman brush ba, zaka jona ta a jikin socket, sannam ka zuba turaren da ka ke so a cikinta, ka ɗaure saman ta da comb, hayaƙin turaren yana shiga gashi kuma kana taje gashin.

Bayan ya gama ya fara shafawa fuskarsa skin care, tun daga kan su oli cream babu abinda bai saka ba. Lokaci ɗaya fuskarsa ta fara fitar da kyau fiye da na baya. Ya miƙe ya ɗauki ƙananun kaya ya saka, ya ɗauki band ya ɗaure kansa a lokacin aka fara kiran wayar.

Yana kallon wayar ya yi ya ga chef Yola, ya É—auke kai bai É—auka ba.

Wani kiran ya sake shigowa ya ga cleaner nan ma ya ɗauke kansa. sai da ya gama tsaf, sannan ya kira chef da cleaner ɗin ya basu umarnin shigowa. Duk suna da access key ɗin da suke buɗe ƙofar, kowa ya fara aikinsa.

Ba jimawa Chef ya kawo masa ice matcha dan ya san fav ɗinsa ne musamman da safe. Ai kam ya sha macha ɗin sosai, kafin ya miƙe ya sauka dan yana so ya shiga wajan Mamy.

Yana fitowa Abba ya fara kiransa a waya ya É—auka Abba ya ce, "Ka zo wajan Daada ina son ganinka yanzun nan."

Ya zubawa wayar ido ganin Abba ya kashe wayar, ya fita daga inda yake ya nufi zuwa, ya nufi wajan Daada ransa a ɓace, dan ya san maganar bazata wuce ta yarinyar da ba shi yace a ɗaura masa aure da ita ba....

Nana Haleema.

RDB3P16
Nana Haleema.

Tunda ya shiga ya haɗe rai, ganin kowa yana zaune harda Mamy, bazai ba da fuskar da Daada zata faɗi wani abin da bai yi masa ba. Ya ƙarasa ya zauna a inda ya saba zama indai za a zauna a parlour Daada nan ne wajansa, kafin ya gaishe su Daada ta ce, "ina ƴar mutane ta tafi?."

Ya yi shiru bai bata amsa ba kamar ba da shi take magana ba. Daada ta ce, "da kai nake magana fa, ina Æ´ar mutane ta tafi tun safe ba ka sani ba?." Nan ma ya share bai ce komai ba.

Mama ta ce, "Rehaan da kai ake magana fa, ina islaha ta tafi?."

Ya É—ago kansa yana kallon Daada ya ce, "Wace Islaha?."

Daada ta yi masa daƙuwa ta ce, "uwarka Nadira, itace Ishlaya." Ya wani kalle ta kamar zai rama zagin da ta yi masa, sai kuma ya yi shiru.

Daada ta ce, "kalle ni da kyau, in za ka rama sai ka rama tunda na ga tashin rashin kunya ka ke ji dashi."

Abba da ya san yadda yake bi da Rehaan É—in a tausashe ya ce, "Rehaan ina yarinyar ta tafi tun sassafe ba ka sani ba?."

Ray ya kalli Abba ya ce, "Abba duk inda zata je sai na sani? Ina ruwana da inda zata je ko zata zauna? Yarinya ce ita da in ba a ganta ba za a yi tunanin wani abun ya same ta?. Kuma ni meye ya kawo ni a cikin maganar dan kawai ta fita?."

"Saboda a waje ɗaya ku ke kwana, kuma matar ka ce ta aure” Daada ta bashi amsa tana harararsa.”

Rehaan ya kalli Daada ya ce, "dan a waje ɗaya mu ke kwana ba hakan yana nufin duk inda zata je sai na sani ba, ba hakan yana nufin dan ta fita a dinga tambayata ina ta je ba. Tana da right ɗin zuwa duk inda ta ga dama, zan ɗaure ta ne ko kuma ita baiwa ce?…..”

Daada zata yi magana ya riga ta ya ce, “Daada don Allah ki daina ɗaga min hankali akan abinda bai kamata ba, ko bacci ban samu na yi yadda ya kamata ba, kin saka an tashe ni."

Daada ta ce, "rayuwar turawa za ka fara yi mana a gidan kenan, ka ga abinda uwarka ta ke yi shiyasa za ka ɗora matarka a kan hakan ko?.”

Ya sake kallon ta Daada ta ce, "Eh mana, itama ai ba tambayar babanka take yi in zata fita ba, kai kuma ka tashi a wajenta ka ga yadda take tafiyar da rayuwar aurenta, sai ka ɗauka hakan abin arzuƙi ne shiyasa kaima ka ke ƙoƙarin ɗora matarka akan haka. To wallahi Allah bazan lamunci wannan iskancin ba, bazan ɗauki wannan rashin tarbiyyar a cikin jikokina ba, in ita ta yi daman ba jinin mu bace, amma kai jinin mu ne, matarka ma ta mu ce. Mu jinin fulani ne, babu wani jini da ya gurɓata mu balle a canja mana al'ada."

"Itama Mamy babu wani jini da ya gurɓata ta, in ma ta gurɓace ɗin sai dai in jinin fulanin ne suka mayar da ita haka" ya bata amsa kai tsaye yana kallon ta.

Abba ya buÉ—e baki cike da maamkinsa ya ce, "Rehaan...!"
Chapter 19 · 0% Book details