Sashe 54
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ban ce sai an É—auke ni a mota ba, a napep na saba fita, kuma a nan zan cigaba da fita. Bazan ji haushi dan ya ce kar a kaini a mota ba, daman motarsa ce ba tawa ba, kuma bani na ce ina so ba. Amma wallahi Allah, bai isa ya ce bazan fita daga gidan nan ba, ba baiwa ya siyo ya ajjiye ba, balle ace sai lokacin da ya ga zama zan fita. Ka faÉ—a masa, in ya sake saka masu gadi suka hanani fita daga gidan nan, wallahi sai na haura katanga...."
Dariyar da Jafar ya yi ya hanata ƙarasa, ta lura tunda ta fara magana ya ke son yin dariya sai da ta zo gaɓa sannan ya yi. Jafar ya ce, "kuma za ki iya haura katangar Miss?."
Ta haÉ—e rai ta ce, "Ba wasa nake yi ba Mr Jafar."
"Oh sorry Miss, ina jin ki."
"Ka faɗa masa a rules ɗina da ya saka hannu a kai babu hanani zuwa duk inda zan je, ko zan je wani waje na kwana dubu babu ruwansa. Kar ya sake karya min rule, babu ruwansa da duk abinda zan je, ba a ƙarƙashinsa nake ba balle ya hana ni. Kuma daman na faɗa masa, in aka karya min ɗaya daga cikin rules komai ya ƙare. Sa a ɗaya ya ci a ɗazu Safeera ta zo, sai kuma na fara rashin lafiya, wallahi da sai na fita."
Jafar kallon ta kawai yake yi yana murmushi, dan shi mamaki ta ke ba shi sosai, in tana magana cikin faɗa da fusata kamar ba ita ba, sannan ya lura hanata fita ɗin da ya saka aka yi ya ɓata mata rai, kuma daman ranta a ɓace yake. Yadda ta raina Ray abin har tsoro yake ba shi, bata jin tsoronsa balle ya yi mata kwarjini, duk abinda ya zo bakinta faɗa masa take yi, bata jin nauyi kallon idanunsa ta faɗi magana son ranta.
Babu wata mace a duniya da ta ke yiwa Ray abinda ta ga dama kamar ta. In yana waje mata masa iya buÉ—e baki balle su yi magana, in ya basu damar maganar ma basa iyawa saboda tsoro da kwarjini, amma ita kullum abin nata sake gaba yake yi.
Jafar ya ce, "Shikenan, zan faɗa masa saƙonki Miss. Duk da in ki ka faɗa masa da kan ki sai ya fi fahimta, sai ya fi gane ya yi kuskurensa na sakawa a hanaki fita."
"Wallahi da ace ina da number wayarsa da É—azu sai na kira shi na faÉ—a masa, dan ya san ni ba irin macen da zai karyawa rule ya kwana lafiya ba ce."
Jafar ya ce, "ko na ba ki number?."
"bani da buƙatar magana da shi, bani da buƙatar ajjiye number sa a wayata, dan babu amfanin da zata yi min. Ni dai don Allah saƙona ya je inda nake so ya je."
Ya ce, "kar ki damu, zan faÉ—a masa."
Ta ce, "na gode."
Bai ce komai ba sai murmushi da ya yi, dan shi dramar ta dariya take ba shi. Ya fita daga falon ita kuma koma ta zauna, sai ta ke jin sauƙin ɓacin ran, sai take ji komai yana raguwa kamar Rehaan ɗin ta faɗawa abinda yake ranta, sai ta ɗan ji sauƙin ƙunar ran da ta dame ta ɗazu.
Islaha bata jima a zaune a falon Ray ba ta koma ɓangaren Mamy, ta shiga ɗakin da aka bata ta kwanta tana jin yunwa sosai.
Sai kuma ta miƙe ta dawo parlour har lokacin su Mamy suna inda suke suna hira, abinci take son ci amma ta kasa cewa zata ci.
Mamy kamar ta kula da abincin take son ci sai ta cs, "baza ki ci abinci ba?."
Islaha sai ta ji daÉ—i a ranta ta ce, "Zan ci."
Mamy ta ce, "ki ci ga shi nan akan dining, in kuma kina son wani abun sai ki saka a dafa miki."
Islaha ta ce, "To."
Mamy ta ce, "kar ki cuci kan ki, in akwai abinda ki ke so ki saka a dafa miki."
Islaha ta yi murmushi ta ce, "zan ci wannan ɗin ma." Mamy ta ce, "Shikenan." Islaha ta miƙe ta ƙarasa ta zuba tea, sai irsh da ta ci kaɗan, ta koma bedroom ta yi wanka ta kwanta.
Sai kuma ta tuna da sun yi da Hamma za su haɗu, ta miƙe ta jawo wayarta ta kira shi.
Yana ɗauka bata jira ya yi magana ba ta ce, "Hamma don Allah ka yi haƙuri, na so na fito sai na fara ciwon ciki."
Saheer da ya ke jinta ya yi shiru bai ce komai ba, jin bai ce komai ba sai ta ce, "Hamma."
Ya ce, "Ya jikin na ki?."
"Da sauƙi, har na kwanta."
"Allah ya ƙara lafiya."
"Amin Hamma."
"Ki kwanta ki huta."
"To, amma gobe in na dawo daga wajan aiki zan zo mu gaisa."
Ya ce, "Allah ya kaimu."
Har zai kashe wayar sai ta ce, "Hamma!."
Ya ce, "Islaha."
"Sai ji maganar ka kamar kana fushi."
Saheer ya yi murmushi ya ce, "Ba fushi nake yi ba Islaha, na yi tunanin daman ba ki da lafiya, na san lokacin rashin lafiyar ta ki ya yi. Ki kwanta ki huta, Allah ya kaimu goben." Ta amsa da amin sannan ta kashe wayar ta kwanta a hankali.
*
A daren Barr yana tsaye a ƙofar wani gida ƙarami, ya yi sallama aka amsa ya shiga gidan, ya kunna hasken wayarsa ya haska gidan suka haɗa ido da Yafindo.
Yafindo a firgice ta miƙe ta ce, "Suraj me ka zo yi nan?."
Cikin sigar kwantar da hankali ya ce, "Kwantar da hankalin ki Yafindo, ni kaÉ—ai na zo nan. Kar ki É—aga hankalin ki, koma ki zauna."
Yafindo ta zauna ta ce, "Don Allah ka tafi, ban shirya salwantar da rayuwar yarana ba. Ya aka yi ka san na dawo nan?."
Suraj ya zauna a gefen ta ya ce, "na yi bincike na gano kina nan, shiyasa na zo. Ni ba Islaha ba ne, dan na tabbatar ba a hana ki magana dani ba, kuma babu wanda ya ganni lokacin da na zo nan."
Yafindo ta grigiza kai ta ce, "Islaha tana ƙoƙarin ganin ta gyara abinda yake faruwa, amma da ta fara zata kasa, saboda wasu dalilai da suke tare da ita. Tana son ganin rayuwar yaran gidan ta fita daga hatsari, amma yadda mutanen nan suka ƙeƙashe zuciyarsu basu imanin da za su ƙyale ta ba."
Barr ya ce, "Ranar da ta je gidan ki karo a na biyu ki ka ƙi yin magana da ita, har ƙoƙarin taka ta da mota aka yi, kai tsaye kashe ta suka so yi."
Yafindo ta ce, "za su iya, yadda suka É—auki lamarin nan za su iya kashe rai wallahi."
Barr ya sauke nunfashi ya ce, "Yafindo ki faɗa min ya ku ka yi da Zainab kafin ta gudu, ina ta ce miki zata je, wanne saƙo ta ba ki ki bawa Islaha?." Yafindo ta yi shiru bata ce komai ba.
Barr ya ce, "Yafindo yin shiru nan na ki ba mafita bane, muna zargin gidan nan da safarar mata, muna zarginsu da lalata rayuwar mata, mu na zargin suna ɗaukar marayu suna rabawa masu kuɗi su kuma suna ba su kuɗi. So mu ke mu kai maganar inda za a daƙile wannan ɓarnar, kuma hakan bazai faru ba sai mun samu hujja, kuma a yanzu Zainab ce kaɗai hujjar mu. Duk hujjar da Islaha ta samu sai an tabbatar ta rasata, suna bibiyarta sosai, suna ɓatar da duk wata hujja da Islaha ta samu. Shiyasa na karɓi lamarin na zo nan ko ita bata sani ba, tunda ita suke bibiya bani ba, kin ga zan yi abinda ya kamata ba tare sa hankalinsu ya zo kain ba. Yafindo, ki taimaka ki faɗa min abinda Zainab ta ce miki, shirun ki bazai yi amfanin komai ba."
Yafindo ta sauke numfashi ta ce, "sun ce indai na yi magana sai sun ga bayana, kuma sai sun kashe Æ´ar dana mallaka a duniya."
"Kina da hujjar da za ki ƙi magana Yafindo, amma da Islaha su ka hana ki magana ba ni ba,
kuma ni a yanzu babu wanda ya san nazo gare ki."
Ta ɗan yi shiru kafin ta ce, "zan faɗa ma ka Suraj, ko da zasu kashe ni ka kula da rayuwar ƙanwarka gata tana bacci" ta faɗa tana nuna masa ƴarta da take bacci.
Suraj ya riƙe hannunta ya ce, "Babu abinda zai same ki in sha Allah, zan killace ki, ki zauna a ƙarƙashin inuwa ta in sha Allah. Bazan taɓa bari wani abun ya same ki ba, zan ba ki kariya ko da zan rasa raina."
Yafindo ta ce, "Tabbas Zainab ta same ni kafin ta bar gidan, kuma mun yi magana da ita. Takardar ta bani tana nan" ta faɗa tana miƙewa ta shiga ɗaki, ba jimawa ta dawo ta miƙa masa.
Har zai karɓa sai ta ɗauke takardar ta ce, "Amanar yaran suna hannunka a yanzu, kar a haɗa baki da kai a cutar da yaran nan. Ban sani ba ko a tsaginsu ka ke ko a tsagin Islaha, amma ga shi zan tamƙa amanar a hannunka, in ka ci amana Allah yana kallon ka."
Duk da yadda ya ji maganar ta soki zuciyarsa amma bai nuna mata ba ya ce, "Baza a taɓa haɗa kai dani a cutar da marayu ba, nima maraya ne, zan so ƴan uwana marayu su girma cikin tarbiyyar da kyakykyawar rayuwa kamar yadda na tashi a ciki."
Yafindo ta ba shi takardar ya karɓa sannan ta ce, "Mun yi magana da ita kamar yadda na faɗa ma ka. Da farko ta fita a gigice, daga baya ta dawo ta ba ni wannan."
Suraj ya gyara zama ya tausasa muryarsa ya ce, "Me ta ce miki? Sannan ina ta tafi?."
Yafindo ta yi ajiyar zuciya ta É—ago ta kalle shi, ta yi shiru ta kasa magana. Suraj ya ce, "bazan ci amanar yara ba, baza a haÉ—a kai da ni a lalata rayuwar yara marayu ba."
Yafindo ta É—aga kai cikin gamsuwa ta ce,..........
Nana Haleema.
RDB3P43