← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 110

Sashe 65

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Islaha ta ji gabanta ya faɗi sosai, ta tsaya tana kallon cup ɗin ba tare da ta karɓa ba, Mamy ta kalle ta suka haɗa ido sai ta karɓa Mamy ta fita tana amsa wayar. Islaha kalli ruwan hannunta, ta kalli Rehaan da yake kwance idanunsa a rufe, ta girgiza kai tana taɓe bakinta, dan gaskiya baza ta iya ba.

Ta kuma kallonsa ta kalli hannunta tana gwadawa, tana gwada ta ɗaga rigarsa da hannunta, sannan ta shafa ruwa a skin ɗinsa. Ta sake girgiza kai ta ce, "taɓɗijam, bazan iya aikin nan ba gaskiya, da dai mijina ne na gaske sai na yi, amma bazan iya aikata aikin nan ba."

A lokacin Mamy ta dawo ta kalli Islaha ta ga tana yadda ta bar ta, babu alamun ta tashi daga inda take zaune. Mamy ta ce, "ba ki iya ba?."

Islaha ta turo baki tana sunkuyar da kanta ƙasa, Mamy ta yi murmushi ta riƙo hannunta suka fito parlour dan kar su dame shi da magana sannan ta ce, "ba za ki iya ba?."

Da saurinta ta É—aga kai alamun eh, Mamy ta ce, "meyasa?."

Islaha ta kalli Mamy bata ce komai ba, Mamy ta ce, "ba mijinki bane?." Islaha ta kawar da kai bata ce komai ba, dan bata san wacce amsa zata bawa Mamy ba.

Mamy sake yin murmushi ta ce, "mijinki ne, yin hakan ba laifi bane Islaha. Ki je ki yi abinda na ce ki dawo."

Islaha ta shagwaɓe fuska tana kallon Mamy ta ce, "wallahi bazan iya ba."

Mamy ta dafa kafaÉ—arta ta ce, "za ki iya, je ki."

Islaha ta kalli ruwan hannunta bata ce komai ba, dan ita kanta ta san baza ta iya shafa masa ruwa a cikintsa ba, baza ta iya ɗaga rigarsa sama ta zuba ruwa a hannunta tana taɓa shi ba. Amma tana ganin girman Mamy, a cikin kwanakin ta yi mata abubuwan kirki sosai, kuma ko babu komai babbar mace ce wacce ta haife ta, zata iya yiwa duk wanda ta saka ta yiwa tunda neman lafiya ne. Matsalar da aka samu da ya zo akan Rehaan, da wani ne daban tsaf zata yi, amma Rehaan ɗin ne baza ta iya taɓa jikinsa ba.

Ganin Mamy ta zuba mata ido sai ta nufi ɗakin kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki tana tunanin katoɓarar da zata tafka. A yadda ta bar shi a haka ya ke, yana kwance yana kallonsa sama. Ta hararesa sannan ta ce, "da mutumin kirki ne da akwai sauƙi, amma ba na kirki bane."

Ta ƙarasa tana kallon fuskrsa ta ga idanunsa a rufe, gashin idanunsa sun sauka har akan fuskarsa, hancinsa ya sake yin tsaho, ga ƙaramin bakinsa a rufe. Ta ɗauke kai tana kallo ƙofar ɗakin da ta bari a buɗe, dan kar ta rufe a zo a same ta tana shafa masa ruwa a kan cikina ayi tunanin wani abun suke aikatawa da shi.

Rigarsa ta ke kallo tana tunanin yadda zata ɗagata sama, ba dan kar Mamy ta gane ba ai akan rigar zata kwarara ruwan kawai a huta. Ta sake matsawa gab da shi, ta saka yatsu biyu ta riƙe rigar kamar yadda ake riƙe abin ƙyama ta tsaya a haka, ita bata ɗaga rigar ba kuma bata saki ba.

_Ke Islaha ba wani abun bane ba, ba shi da lafiya taimaka masa za ki yi, ko babu komai za ki samu ladan taimakon mara lafiya. Ki shafa masa kawai._

Abinda zuciyarta take faÉ—a mata kenan, sai ta samu courage ta É—an janye rigar kaÉ—an, kai tsaye idanunta suka faÉ—a kan logon Nike da yake jikin short É—in jikinsa. Ta runtse ido ta ce, "Innalillahi! Na shiga uku, me yake kai idanuna wajan nan ne? Logon Nike É—in ne ban sani ba koma meye?."

Ta yi tsaki ta ɗaga rigar ta zuba ruwan a hannunta tana tunanin ta ina zata fara.Ganin tana ɓata lokaci sai hankali ta fara zuba ruwan a kan cikinsa, sannan ta kai hannunta zata taɓa ruwan da ta zuba, kamar mai jin tsoro ta tsayar da hannun a tsakiya, ita bata ɗora akan skin ɗinsa ba ita bata ɗauke ba.

Ta runtse ido kamar wacce zata taɓa wuta a haka ta kai hannunta, sai ta yi saurin ɗaukewa kamar wacce wutar lantarki ta ja, ta yarfe hannu ta sake rufe idanu sannan ta shimfiɗa palm ɗinta a akan cikinsa.

Wani irin shock ta ji ya ja ta a jikinta, ta daure bata ɗauke hannun ba ta ɗan shafa cikinsa a hankali. Santsi da laushin skin ɗinsa ya saka hannunta ya zame ya yi ƙasa sai jin hannunta ta yi akan nalve ɗinsa.Ta daure bata buɗe ido ba, ta yi ƙoƙarin daidaita hannunta yadda bazai sake zamewa ba, ta cigaba da shafe ruwan tana yi tana salati.

Tana jin yadda cikinsa yake ɗagawa a hankali, ga zafi da cikin ya yi kamar mai zazzaɓi. A haka ta janye hannunta daga cikinsa, har lokacin bata buɗe idanunta ba, kuma yanayin da take ji har lokacin bai bar jikinta ba. Kafin ta ƙarasa janye hannunta ta ji an riƙe hannunta, hakan ya saka ta firgita ta buɗe idanunta tana kallon hannunta.

Hannunsa ta gani riƙe da wrist ɗinta, ta wara idanu waje tana tunanin daman ba bacci yake yi ba kenan? Daman yana ji tana taɓa masa ciki bai hanata ba?. Ta kalli fuskarsa ta ga ya buɗe ido, ta ɗauke kanta saboda takaici, dan da ta san idanunsa biyu bazata aikata ba.

Kamar mai raÉ—a ya ce, "Please don't stop, it makes me feel better" ya faÉ—a a hankali yana lumshe idanunsa kuma bai saki hannunta ba.

Islaha ta ji abinda ya ce amma sai ta yi kamar bata ji ba, ya mayar da hannunta a kan cikinsa, stilt bai saki hannun ba.

Ta bi hannunta da kallo ta buÉ—e baki zata yi magana sai kuma ta yi shiru, ta haÉ—e rai kamar yana kallonta. Sai sannan ya saki hannunta, kuma ta kasa É—auke hannunta daga cikinsa, sai kallon hannun nata take yi kamar mai ganin wani abun a hannun.

Mamy tana tsaye a bakin ƙofa tana kallon duk abinda yake faruwa, da yadda ta ɗaga rigar, da yadda ta ke shafa masa ruwan duk ta gani, tana daga tsaye tana kallonta bata sani ba. Duk tsaki da harararsa da ta ke yi tana gani.

Ta yi murmushin jin daɗi, dan a ranta take jin Rehaan ya samu daidai shi, wacce bata aure sa dan kuɗinsa ko wani abu ba, ya auri wacce bata raga masa saboda yana da abin duniya, ya auri wacce bata san kara ko ɗaga ƙafa akan abinda ta saka a gaba ba. Tabbas Islaha ce daidai da Rehaan, bata aure shi da wani abu nasa ba, beside ta fi ko wacce mace raina shi a duniya. Mamy ganin Islaha ta zauna sai ta ƙarasa rufe ƙofar a hankali, ta juya ta sauka tana ji a ranta ta samu wacce zata maye gurbinta wajan kula da Rehaan.

Nana Haleema.

RDB3P50
Nana Haleema.

Islaha kamar robbot haka ta zama, tunda ta ƙame haka bata motsa ba, ko hannunta bata motsawa, tunda ya mayar da hannunta kan cikinsa bata kuma motsi ba kuma bata janye hannunta ba kuma bata cigaba da shafa ruwan ba. Tunani take yi ta ya shafa masa ruwa a ciki ya zama yana jin daɗin hakan? Har ya kasa haƙuri ya riƙe hannunta ya cr kar ta daina?. Ita kaɗai take tunaninta ta ɗauke kai daga kallonsa. Sai daga baya ta kula ya yi bacci, numfashinsa ya yi daidai sannan ya saki jikinsa.

Ta janye hannunta ta miƙe tsaye tana kallon yadda yake baccin a nutse. Goshinsa ta kalla sai ta ga kamar yana gumi, ta ɗauki remote ta ƙara ac ɗakin, sannan ta kashe sauran hasken da ya rage ta fita daga ɗakin.

Da ta koma ɗaki itama bacci ta yi, ba wajan aiki zata ba je shiyasa bata yi ƙoƙarin tashi ba. Sai ƙarfe sha ɗaya na safe ta farka, bata fito ba sai da ta yi wanka ta canja kaya.

Kayanta ta ke kallo ganin duk ta saka, daman kaɗan take ɗaukowa daga gidansu Safeera ta mayar dasu, ta mayar dasu ta ajjiye sannan ta fito parlour. Parlour shiru babu motsin kowa, komai na parlour a a kashe alamun bai tashi daga bacci ba kuma Mamy bata zo saman ba. Ta kalli ɗakinsa tana ji kamar ta je ta ga ya yake, dan ya bata tausayi, bata taɓa ganin ciwon ciki irinsa ba, sai kuma ta fasa ta juya zata sauka.

Haɗuwa suka yi da Mamy tana tahowa upstairs ɗin ita kuma zata sauka, Islaha ta tsaya tana jira ta ƙaraso su gaisa. Mamy tana ƙarasowa kusa da ita ta yi murmushi tare da hugging ɗinta ta ce, "Good morning Islaha."

Islaha ta yi murmushi ta ce, "Good morning Mamy."

"Ya ki ka kwana?."

"Lafiya lau."

"ya jikinsa?."

Islaha ta ce, "da sauƙi, bacci yake yi."

Mamy ta gyaÉ—a kai ta ce, "let me check on him." Ta faÉ—a tana wucewa, sai kuma ta juyo ta kalli Islaha ce, "na san ba ki je kin duba shi ba kema, zo mu je tare" ta faÉ—a tana yin gaba, Islaha kamar zata yi kuka amma haka ta bi bayanta.

Suna buɗe ƙofar ɗakin ya buɗe ido, Mamy ta kunna hasken ɗakin ta ce, "Good morning my love." Ya miƙe zaune yana yamutsa fuska saboda haske ya ce, "Morning Mamy."

Ta ƙarasa ta zauna kusa a da shi ta ce, "Ya jikin?."

"ya yi sauƙi."

Ta riƙe fuskarsa ta ce, "Ya daina ciwon?." Ya ɗaga mata kai yana ajiyar zuciya.

Mamy ta ce, "ka yi wanka, ka zo ka yi breakfast."

"Okay." Ta yi pecking ɗinsa a goshi ta miƙe ta fita ta bar Islaha a ciki har da rufe ƙofar.

Sautin rufe ƙofar ya saka Islaha ta juya tana kallon Mamy, a ranta tana ayyana wai me matar nan take nufi da ita ne da zata fita ta barsu su biyu harda rufe ƙofa?. Ta juya zata fita bata ce masa komai ba, kamar yadda shima bai ce ba, gab da zata ƙarasa ƙofar da zata kai ta parlour ta ji ya ce, "Thank you."
Chapter 65 · 0% Book details