Sashe 36
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Na yi magana da su, ana ta binciken waÉ—anda suka yi wannan aikin, in Allah ya yarda bazasu sha ba. An ba ka guda a abin sha ka sha kuma sun tsira, wannan baza su tsira ba in Allah ya yarda.
" Rehaan ya É—aga kai bai ce komai ba, dan har lokacin ba ya jin daÉ—i.
Abba ya ce, "ka ci abinci ka zo ku gaisa da mutanen gidan, kowa hankalinsa ya tashi."
Ray ya ce, "In sha Allah."
Abba ya ce, "ina matar ta ka, ance tare ku ka fita, ina fatan itama lafiya take?."
Rehaan ya ce, "lafiya lau."
"ta warware? An ce ta samu attack."
"Eh, ta samu lafiya.â€
Abba ya ce, "Ma sha Allah, ina zuwa" ya faÉ—a yana tashi ya sauka downstairs
Nana Haleema.
RDB3P29
Nana Haleema.
Mamy bata ce masa komai ba ta miƙe ta sauka, sai gata ta dawo da abinci a tray ta ajjiye a gabansa alamun ya ci. Daman yana jin yunwa, hakan ya saka ba ƙi ci ba ya sha tea sannan ya ci abincin kafin ya ajjiye alamun ya ƙoshi.
Mamy ta kalle sa ta ce, "Me ya kai ka gidan Riyya a daren jiya?."
Rehaan ya ɗago suka haɗa ido, sai ya sauke ido ƙasa bai ce komai ba. Mamy ta ce, "kai nake jira."
Ya langwaɓar da kai ya ce, "Mamy don Allah a bar maganar nan."
Mamy ta ce, "Allah ba za a barta ba, ka faÉ—a min meye fitar da kai zuwa gidan Jafar da daddare?."
"Mamy kawai na je na ganta ne."
"ban yarda ba, faÉ—a min dalilin."
Ya kuma kallon ta ya ce, "Mamy please."
Mamy ta haÉ—e rai ta ce, "Rehaan!."
Sai ya lumshe ido ya buɗe, yana tunanin ta ya zai faɗawa Mamy wannan abin kunyar? Allah ya sani yana jin kunyar faɗa mata abinda ya faru, amma kuma babu yadda zai yi dole ya faɗa mata tunda bazai iya yi mata ƙarya ba.
Ya rufe ido sannan ya ce, "Mamy ni ban san me zan ce miki ba."
"Baza ka faÉ—a min ba kenan?."
"Zan faÉ—a miki, kawai dai i'm shy."
Sai ta yi shiru bata ce komai ba, ganin ta share shi sai ya daure ya ce, "Mamy they had thier.....first....night...." Ya ƙarass faɗa a rarrabe har yana rufe idonsa ya buɗe saboda kunya. Ya cigaba da magana ya ce, "Shine na je for treatment."
Mamy bata nuna wani abu a fuskar ta ba ta ce, "meyasa ba a kai ka asibiti ba sai kai da kanka zaka je a daren?."
Cikin shagwaɓa ya ce, "Don Allah Mamy a bar maganar nan tunda na faɗa miki."
Mamy ta yi murmushi tana shafa kansa sannan ta ce, "When will you have your first night with your wife?."
Rehaan ya runtse ido yana jin kunyar kalamanta ya ce, "Mamy!."
"Ba wani Mamy, na ga kun fara shiri har fita ku ke yi tare."
Rehaan ya É—ora hannunsa akan goshinsa ya ce, "Mamy please!."
Ta sake yin murmushi tana cigaba da shafa kansa ta ce, "daman kana jin kunyata, i through ba ka jin kunya Rehaan."
Shi dai bai ce komai ba sai murmushi da yake yi. Ta riƙe kunnensa ta ce, "Kar na sake ji ka fita da daddare kai kaɗai, ka ji?."
Ya É—aga kai ya ce, "In sha Allah."
"How was Islaha?."
Ya ce, "ban sani ba, tashina kenan kuka shigo."
Mamy ta ce, "You didn't go check on her?."
Ya É—aga kai ya ce, "Maybe bacci take yi."
Mamy ta miƙe tsaye ta ce, "in Jafar ya zo ka turo min shi."
Rehaan da sauri ya É—aga kai ya kalle ta sai ta haÉ—e rai tana kallonsa ta ce, "ba ka ji ba?." Rehaan ya É—aga kai bai ce komai ba Mamy ta sauka.
Mamy bata jima da sauka ba Jafar ya shigo da sallana ya ƙaraso ya ce, "Ya ka ke?."
Ya gyara zama sannan ya ce, "i'm okay, ya Riyya?."
Bai ce komai ba ya zauna sai ya kira Riyya video call ya ba shi. Rehaan ya karɓa yana kallonta ganin fuskar ta har lokacin bata dawo daidai ba, amma daga gani ka san ta ji sauƙi.
Ya ce, "Riyya."
Riyya ta ce, "Ray ina fatan kana lafiya, ina ta kiran ka bana samu."
"Wayar ta ƙone a mota Riyya, amma ina lafiya. Kin ji sauƙi?."
Sai ya bata kunya dan sai a lokacin ta ke jin kunyarsa sosai, ta sauke idanunta ƙasa ta ce, "i'm feeling well, but...." Sai ta yi shiru bata ce komai ba.
Ray ya ce, "But what?."
"I'm dizzy."
"Kin ci abinci?."
"Na ci."
"Ki sha pcm ki kwanta ki sake yin bacci, za ki daina ji, sannan ki sha ruwa, kin ji?."
Ta É—aga masa kai sannan ta ce, "byee." Daga haka ta kashe wayar.
Jazy ya ce, "Ya jikin Islaha, ina tunanin ta samu lafiya?."
Rehaan ya ce, "ban sani ba."
Jazy ya kalle sa ya ce, "ya kamata ace ka sani." Bai ce komai ba ya yi shiru.
Jazy ya ce, "ya aka yi aka samu labarin ka fita daga gidan nan?."
Ya kalle sa ya ce, "ban sani ba, tunda aka bani pioson a cikin gidan nan, sanin na fita bazai gagara a sani ba."
Jazy ya ce, "yana da kyau a bincika sosai, dan ni a jikina yana bani akwai munafuki a gidan nan."
Ray ya ce, "azo ayi min sim card swap, sannan ina buƙatar sabuwar waya ka saka a kawo min. Sim card ɗina na Uk ban san ya zan yi ba, dole sai na je can."
Jazy ya ce, "Okay zan saka a kawo in na fita." Rehaan ya amsa da kansa bai ce komai ba.
Sai kuma ya tuna da abinda Jazy ya yiwa Riyya, ya harare shi, shi kuma ya yi dariya dan ya san hararar ta meye.
"Mamy tana nemanka."
Ya wara ido ya ce, "wa take nema?." Rehaan bai amsa ba Jazy ya ce, "kar ka ce min ka faÉ—a mata abinda ya faru."
Rehaan ya ce, "tana ta tambayar me ya fita dani, na ce a bar maganar amma ta ƙi, shine kawai na faɗa mata."
Jazy ya É—ora hannunsa a kai ya ce, "Na shiga uku! Kenan ta sani?."
Ya É—aga masa gira alamun eh ta sani, sai kuma ya ce, "Ray ka kashe ni" ya faÉ—a yana dafe kansa bai ce komai ba.
Ray ya murmusa ya ce, "Kasan kana jin kunyar ka aikata?." Bai ce masa komai ba ya yi shiru yana ji kamar Mamy É—in tana wajan.
Sautin buɗe ƙofa ya saka duka suka kalle ta, sai ta yi turus ganin suna kallonta ga shi bata saka mayafi ba. Fittrd gown ce a jikinta a cikin waɗanda ta ɗauko a wajen Safeera,ta yi mata kyau ta fitar da ko ina a jikinta.
Kamar ta juya ta ɗauko mayafi sai kuma ya fasa ta ƙaraso ta ce, "Mr Jafar."
Ya ce, "Miss ya jikin?."
Ta ɗan girgiza kai ta ce, "Na ji sauƙi."
"Allah ya ƙara lafiya."
"Amin ya rabbi."
Ta ɗan kalli Rehaan da yake kallonta, suna haɗa ido sai ya ɗauke idonsa ban san meyasa idanunsa suke kallonta a lokacin ba, musamman bakinta a da ya san ya ɗuminsu yake, da yadda laushi da tsantsinsu yake a cikin na sa. Islaha bata ce masa komai ba ta sauka ƙasa dan yunwa take ji.
Jazy ya kalli Ray da ya wani basar kamar bai ganta ya ce, "a cikin kwana huɗu har yarinya ta fara fuskarta barazana ga rayuwarta, gaskiya zama matar mai kuɗi irinka ba abu ne mai sauƙi ba."
Bai ce masa komai ba ya yi shiru Jazy ya ce, "meyasa ba ka ce mata ya jiki ba? A motar ka ta samu attack Rehaan, a kanka aka kusa kashe ta. Ya kamata ace ka ce mata ya jiki, ko babu komai zata ji daÉ—in ka kula da lafiyar ta."
Ray ya yi masa banza bai amsa ba sai daga baya ya kalli Jazy ya ce, "da ta fito ka ji ta yi min magana ne?."
"Ka damu da ta yi ma ka ne?."
"Ta damu da na tambayi lafiyarta ne?" Ya ba shi amsa kai tsaye yana kallonsa.
Jazy ya murmusa kawai kafin ya miƙe ya sauka ƙasa dan ya je wajen Mamy kamar yadda aka ce tana kiransa. A zaune ya same ta tana cin abinci a kan dining, bai ce mata komai ba ya fita.
Bayan ta gama cin abinci sama ta dawo ta tarar da Rehaan a inda yake, ta tsaya tana kallonsa dan tana so ta yi masa warning akan kar ya sake tafiya da ita inda za a kashe ta. Ta gyara tsayuwa ta ce, "Da yake ka san za a kai maka attack, shiyasa ka bar ni na shiga motar ka, wato in aka kashe ni an kashe banza ko?."
Rehaan a saman kansa ya ji maganar ta dan bai yi zaton tazo wajen ba. Ya É—ago ya kalle ta ga tana kallonsa, ya É—auke kansa daga kallonta, dan suna haÉ—a ido sai ya tuna kissing É—inta da ya yi a mota wanda ita bata san ya yi ba. Ya kasa mantawa da abinda ya yi, har lokacin yana ji kamar bakinta yana cikin nasa.
Islaha bata san tunanin me yake yi ba ta ce, "Haka kawai sai ka saka na mutu da wannan ƙaddararren auren na ka a kaina? Dan ba ka ƙaunata sai ka bari na kai kaina inda za a kashe ni ko? Ni daman tunda na ga ka bari na shiga motarka ba tare da ka yi wani complain ba nasan da wata a ƙasa. Yanzu da na mutu fa?."
Rehaan murmushi ya yi ba tare da ya waiwayo ba, dan haka kawai ta ba shi dariya jin wai da ta mutu fa, sai ka ce ba tare suke a cikin motar ba. Sai kuma ya É—ago ya kalle ta ya ce, "in kin mutu waye ya damu?."
"Mutane da yawa zasu damu, su za su damu in na mutu. Su na ƙaunata, suna burin rayuwa na yi rayuwa a duniya kamar kowa, su ka yiwa asara kuma ka cuta. Kuma duk baƙin cikin ka sai na rayu a duniyar nan, sai na tsufa sannan zan mutu in sha Allah."