← Book details Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 110

Sashe 68

Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta ƙasa da muryarta ta ce, “Me za ki yi min dan na canja? Laifi ne dan na canja daga Islahan Hamma na koma Islahan Rehaan?....."

Saheer ya zuba mata idanu kawai yana kallonta ya kasa cewa komai ba.

Ta ce, "Kuma da ka ke cewa ba ka san me nake yi a tare da shi ba, in na yi É—in ina ruwanka Hamma? Babu ruwan ka a cikin duk abinda na yi da shi, tunda ka san shine mijina ba kai ba, zan iya yin duk abinda zuciyarka ta ke faÉ—a maka ina yi, ai ba laifi na aikata ba....sai ma lada da Allah zai ba ni."

Sai kuma ta dafe kanta tana wani jan numfashi mai ƙarfi, tana ji kamar zata samu attack a lokacin saboda takaicin maganar Hamma.

Ta cire hannunta daga kanta ta kalle shi shi ta ce, "Ka cigaba da kallona akan canjin da ka ga na yi, ka cigaba da kallona akan duk abinda ka ke kallona da shi, don Allah kar ka canja. In ka ga dama daga ka fara siyan kayan jariran, dan ƙanwar ka Islaha ta kusa haifo maka ƴaƴa da mijinta da take aure. Ka cigaba da kallona a yadda ka ke kallo, haka nake Hamma!" ta faɗa tana miƙewa daga inda ta ke zaune, ta miƙa hannunta sitiyarin motar ta danna lock ƙofar ta buɗe, ta fita ta bar masa motar hawaye yana zubowa daga idanunta.

A gefen titi ta zauna ta dafe kanta da duka hananyenta, kuka take yi mai matuƙar sauti, zuciyarta zafi take yi mata, damuwar rashin iyayenta ya fi mata komai ƙona a zuciyarta, ga kalaman Hamma mai nuni da bai yarda da alƙawarin da ta yi masa ba, sai abin ya haɗar mata goma da ashirin.

Saheer yana kallon ta har ta zauna, duk da kalaman da ta faÉ—a masa sun ba shi haushi ga kishin da ya mamaye masa zuciya, amma ya hakan bai saka ya iya tafiya ya bar ta a wajen ba.

Ya fito daga motar ya ce, "ki tashi mu tafi."

Islaha ta yi masa banza bata ce masa komai ba, ya riƙo hannunta ta fizge cikin tsananin fusata ta ce, "kar ka sake taɓa matar aure, ni matarsa ce ba matar ka ba, kar ka sake taɓa ni. In ka kuma taɓa ni sai na saka mijina ya kai ƙarar ka, kuma sai alƙali ya ɗaure ka wallahi.”

Haushi ya sake mamaye masa zuciya, amma haka ya daure dan ba ya so ya barta akan titi ya ce, "na ji, mu je."

"Wallahi bazan shiga ba Hamma, ka je kawai" ta faɗa tana fara tafiya ta ƙyalesa a tsaye a wajen.

A kan idanunsa ta hau napep ta tafi, ya hau motar ya tafi zuciyarsa tana yi masa zafi cikin kishi da haushinta mai matuƙar yawa.

Nana Haleema.

RDB3P52
Nana Haleema.

Islaha kai tsaye gidansu Safeera ta wuce, ta shiga É—akin Safeera ta faÉ—a kan gado ta fashe da kuka mai sauti. Safeera bata ce mata komai ba, tana tsaye tana saka kaya har ta gama shiryawa, ta zauna a kusa da ita ta ce, "Islaha meye?."

Bata iya bata amsa ba sai kuka take yi, Safeera ta yi shiru ta barta tana kuka son ranta. Sai da ta gama sannan ta miƙe zaune Safeera ta ce, "me ya same ki?."

"Safeera ina kewar iyayena, ina so na san inda suke, ina so na gansu, na fito daga can gidan nazo na samu Hamma na tambayesa ya faɗa min amma yake raina min hankali, wallahi bai taɓa faɗar abinda na ji ban yarda da shi ba sai ɗazu. Hamma ya san komai a kaina, meyasa yake ɓoye min!" Ta faɗa da ƙarfi tana hawaye.

"Relax! Ki daina kuka ki kwantar da hankalin ki, ya aka yi ki ka san ya san komai a kan ki?."

"A hannunwa ya karɓe ni ya kai ni gidan, a ina waɗanda suka ba shi ni su ke?."

"Meyasa bai faɗa miki ba, meyasa ba ki taɓa tambaya ba sai yanzu?."

"Na jima ina tambayarsa, sai ya ce min sai mun yi aure zai faÉ—a min. Yau kaÉ—ai na ji ina so na sani, na tambayesa amma ni yake kallo yana cewa na canja, har yana cewa wai bai san me nake aikatawa tare da Rehana ba. In na aikata abinda zuciyarsa take faÉ—a masa É—in ina ruwansa, ba mijina bane!?."

Safeera ta zaro ido jin abinda Islaha ta faɗa, tana girgiza kai tana aiyana lallai Hamma ɗan gold ya ɓata mata rai da yawa, tunda har tana cewa Rehaan ba mijinta bane. Safeera ta ji daɗi a ranta, dan wallahi bata jin daɗin biyewa Saheer da take yi tana ɗaukarwa kanta zunubi.

Ta ce, "Lallai Hamma bai kyauta ba, shi meye na sako maganar Rehaan dan kin yi zancen iyayen ki?."

"Oho masa, kuma na jima ina tambaya bai taɓa faɗa min, sai ya ce kaza in anjima ya ce kaza. Na gaji, na gaji da wannan rainin hankalin nan nasa, zuciyata tana faɗa min akwai wani abun a ƙasa."

"Kamar me?."

"Oho."

Safeera ta ce, "kema ke ce bakya jin magana, meye na hawa motar Saheer ku fita ke da shi don Allah?."

Islaha ta yi tsaki ta ce, "nima na yi danasani, da na san haka zai ɓata min rai da ban fara ba."

Safeera ta yi murmushi tana girgiza kai ta ce, "ki yi haƙuri, in sha Allah iyayen ki suna nan suna neman ki, in sha Allah Allah zai haɗa fuskokin ku a duniya."

Ta É—aga kai ta ce, "Allah ya sa." Ta amsa da amin bata ce komai ba.

Islaha cikin jin haushin kalaman Saheer ta ce, "Wai ni yake kallon yana cewa kuɗi sun canja ni, na rantse da Allah da ace kuɗi zasu canja ni ko kallonsa bazan yi ba. Ina ganin yadda ake wasa da kuɗi kamar ba nemansu ake yi ba, inda kuɗin suna gabana da yanzu na manta wani Hamma a duniya" ta faɗa tana miƙewa ta ƙarasa wajan kayanta tana buɗewa.

Safeera dai bata ce mata komai ba, ta yi shiru tana duba wayarta dan hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba.

Ta gama abinda zata yi ta dawo ta zauna, sai kuma ta kira Lawal ta ce ya zo su koma.

Safeera ta ce, "gabaÉ—aya kin canja yau, ki nutsu don Allah."

Ta ce, "Safeera ban taɓa jin ƙaunar rayuwa da mahifiayara kamar yau ba, kin ga yadda Mamy take nunawa Rehaan ƙauna, kin ga yadda take rikicewa akansa in ba shi da lafiya, kin ga inda ta ke riritasa tana ba shi kulawa kuwa?. Sun burge ni sosai, kallonsu ne ya saka min kewar tawa mahaifiyar. Yadda iyayenmu na fulani suke kunyar yaransu ita bata yi, kula da shi take yi da jikinta da zuciyarta kamar ta goya shi. Na yarda duk duniya babu kamar uwa, ya Allah ya haɗa ni da tawa in tana da rai."

"Amin" Safeera ta amsa tana jin kewar Umma sosai, sai ta ce, "Rehaan É—in ya dawo ne?."

Ta ɗaga kai ta ce, "jiya na koma daga wajen aiki na gansa a kwance babu lafiya, wani ciwon ciki yake yi da ban taɓa ganin irinsa ba, har ciwon ya kai sai an jiƙa towel da ruwan sanyi an ɗora a cikinsa, magana ma daƙyar ya ke yi. Mtsw! Duk da dai yana da raki, shi fa wannan bai yi kama da maza ba wallahi, gabaɗayansa rago ne."

Safeera ta yi dariya ta ce, "Bai yi kama da maza ba sai dake ya yi kama?."

"Ai gabaÉ—ayansa mace ne, bai yi kama da maza ba ko kaÉ—an, ba shi da wata alama da zata nuna shi É—in namiji ne. Rago ne, ga raki, ga iyayi."

Safeera ta yi dariya tana girgiza kai ta ce, "Ni dai ina roƙon Allah ya nuna min ranar da Rehaan zai banbance miki tsakanin mace da namiji."

"Kamar ya?."

"Kamar yadda ki ka ji, daga ranar da ki ka tabbatar shi namiji ne, daga rana za ki daina yi masa kallon mace ki koma yi masa kallon namijin gaske. Kuma duk jarumtar ka ciwon ciki ba abin wasa bane."

Ta taɓe baki kawai bata ce komai ba, tana ji kamar ta bata labarin kwanciyar da ya yi jikinta, da shafa cikinsa da ta yi amma tana jin kamar kar ta faɗa. Sai ta share ɗin bata faɗa ba, dan ta san iskanci zata yi mata a kan hakan.

"Amma dai kina ce masa ya jiki ko?."

"Ni wallahi ban faÉ—a ba."

"Ai kuwa ba ki kyauta ba, ko babu komai kuna tare, yana ba kici da sha da wajan kwana, kuma Mamy tana yi miki kirki sosai."

Islaha ta ce, "to zan gani in zan iya. Ke rainin hankalinsa ne bana so, shiyasa bana shige masa, dan in ya É—ura min wani takaicin tsaf in na yi tsalle zan tsinkesa da mari."

"Mijin naki?."

"Ubana ne?." Safeera ta yi dariya bata ce komai dan ta san a fusace take.

Islaha sai kuma ta tuna da abinda ya faru jiya, ta ja tsaki bata ce komai ba. Safeera ta yi dariya son ranta, dan ita bata fatan auren nan ya rabu, tana so ta ga idanun Islaha a lokacin da Rehaan zai nuna mata shi namiji ne ba mace ba.

A lokacin Lawal ya zo Safeera ta raka ta har mota ta saka mata kayan da ta É—auka sannan suka tafi.

Rehaan yana zaune yana waya da Ubaid kamar ba ya son maganar, daƙyar yake amsa maganar alamun ta dole yake yi masa. Sai daga baya ya kashe wayar ya cillar da ita akan kujera ya ce, "wannan yarinyar ta cuci kanta, bana so Ubaid ya san ta a matsayin C wife ɗin."

"Ray kai da wa ka ke magana kai kaÉ—ai?" Jazy ya faÉ—a yana shigowa.

Ray ya ɗaga ido ya kalle shi dan bai san ya dawo ƙasar ba ya ce, "kai kuma yaushe ka dawo?."

"Da safe."

Ray yana harararsa ta ƙasan idanu ya ce, "har honeymoon ɗin ya ƙare?."

Jazy ya zauna yana dariya ya ce, "honeymoon ai ba ya ƙarewa, dole ce ta dawo dani, amma jibi zamu koma mu ɗora daga inda muka tsaya."

Rehaan bai tanka ba Jazy ya ce, "Ya jiki?."
Chapter 68 · 0% Book details