Sashe 3
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mama ta yi addu'a kamar yadda ta saka ta, sannan Daada ta ce, "za a yi buÉ—an kai, ina Nadira?."
Mamy tana zaune bata ce komai ba, baza ka ce ma tana wajen ba, kallon Islaha kawai take yi tana ji ranta yana ɓaci sosai. Jin Daada ta neme ta sai ta ɗago a hankali fuskar ta babu walwala ta ce, "Gani nan."
Mama ta kalli Mamy ta ce, "ki ƙaraso." Mamy ta miƙe ta ƙaraso ta zauna daf da Islaha. Daada ta kalli Mama Atika ta ce, "za mu siyi fuskar amarya."
Mama Atika ta yi dariya ta ce, "ai ta ku ce yanzu."
Daada ta ce, "daman yanzu ai Æ´ar gida ce."
Daada ta juya ta ɗauko wata cover ta buɗe kowa ya ga ƙatuwar sarƙar gold mai nauyi da kauri sosai ta ce, "na siyi fuskar amarya da wannan."
Mama ce kaÉ—ai a cikin mutanen parlour ta ce, "Ma sha Allah! Amaryar Rehaan ta cancani haka" Bayan ita kowa É—uf ya yi, babu wanda ya nuna jin daÉ—insa a kan bajintar da Daada ta yi, sai masu aikin gidan da suke san barka suna guÉ—a.
Mama Atika ta murmusa ta ce, "Amarya ta gode sosai."
Mamy kamar baza ta yi magana ba, ganin irin kallon da Daada take yi mata ya saka ta É—an motsa baki kamar zata yi magana ba dan ta san me sata ce ba, dan ita bata shiryawa wani buÉ—an kai ba, dan ta manta da wannan culture É—in.
Sai Sanah Yayarta da take wajan ta ce, "Mahaifiyar Rehaan, gata nan a zaune" ta faÉ—a tana nuna Mamy.
Safeera da Mama Atika suka bita da kallo, fuskar ta gabaÉ—aya ba a sake take ba, ta haÉ—e rai kana kallon ta zaka fassara yadda ta É—auki auren ba sai ta buÉ—e baki ba.
Sanah cikin hausar ta da bata wani fita sosai ta ce, "ta siyi fuskar amarya da wannan" ta faɗa tana miƙewa a ƙarasa a hankali ta ajjiye basket ɗin kaba wanda aka yi masa ado mai kyau.
Daada ta kalli Mama ta ce, "buÉ—e."
Mama daman jira take ace ta buɗe dan ta ga abinda aka ɓoye a ciki, ta buɗe ta ɗauko rafar ƴan dubu dubu goma, sai awarwaron gold da zobe, da kuma english gold mai kyau, sai turare babba a cikin cover ɗinsa. Sai turaren wuta, da turaren ɗaki.
Masu aikin gidan da suke wajan suka saki guɗa mai ƙarfi, ana ta san barka dan kyautar Mamy ta yi. Ita dai Mamy kallon Yayarta ta yi kawai, dan ta san aikinta ne, ita bata yi wani shirin komai ba, dan ta manta shaf da wannan abun nasu.
Mama da take gefe ta ce, "Nima na siyi fuskar amarya da wannan." Ta faÉ—a tana É—auko leda a bayanta aka cire luxury lace, kai da ka gansa ba sai ance mata ya haura million ba, kallo É—aya zka yi masa ka san tsadarsa.
Aka sake yin guɗa a falon cikin murna, Umma dai bata shiryawa komai ba, amma ganin kishiyar ta yi sai ta ce, "Akwai kyautar turaren wuta da na saka a yiwa amarya daga ƙasar larabawa basu ƙaraso ba, amma za a kawowa amarya a har ɗakinta." Amaryar Abba dai bata ce komai ba, dan ita bata yi niya ba.
Daada ta kalli Mama Atika da ake ta ajjiye mata mata kaya a gabantq ta ce, "Yanzu za mu iya gamin fuskar amarya?."
Ta yi murmushi ta ce, "a guje, an ba ku dama."
Daada ta gyara zaman glasses É—inta ta ce, "Ina Banisha?."
Banisha ta taso Daada ta ce, "zo ki buɗe mana fuskarta, sannan ki zaɓa mata suna."
Banisha ta zo kusa da Islaha da ko motsin kirki bata yi, tana zuwa ta fara leƙa mayafin suka haɗa ido da Islaha, ta yi murmushi itama dai Islahan ta yi murmushi dan ta gane fuskar ta.
A hankali Banisha ta ce, "ya sunan ki?."
Islaha a hanlali ta ce, "Islaha."
Banisha ta É—ago ta buÉ—e fuskar sannan ta ce, "i chose Islam, as her new cultural name
Daada ta harare ta ta ce, "dallah can iyayen iyayi, ku duk abinda aka haÉ—a da Æ´an É—akin ku sai kun yiwa mutane iyayin banza da wofi. In za ki yi hausa ki yi hausa, waye yake jin yaren da ki ka yi magana?. Kin ga na yi kama da ba'indiya?."
Banisha ta turo baki ta ce, "na zaɓa mata suna, Islam." A take waje ya ruɗe da guɗa, Daada tana ta saka mata albarka.
Islaha ta yi ƙasa da kai taƙi ɗagowa Mama ta ce, "tunda mun siyi fuska ya kamata a ɗago ko?."
Islaha bata ɗago ba, sai sake sauke kanta ƙasa da ta yi tana wasa da abin hannun da Hammanta ya bata. Duk da ciwo kanta yake yi sosai, ta shanye ciwon saboda kar ta ɗago.
Daada ta bita da kallo tana murmushi sannan ta ce, "Kunya take ji, kun san jinin fulani ba dai kunya ba."
Mamy dai tana zaune bata ce komai ba, Daada ta fara yi mata nasihar zaman aure ita duk ba ji take yi ba.
Sai da Daada ta gama sannan ta kalli Mamy ta ce, "baza ki ce komai ba?."
Sai a lokacin Mamy ta buÉ—e baki kamar bata so ta ce, "Allah ya saka albarka." Duk mutanen É—akin suka amsa da amin.
Daada tana murmushi ta ce, "A rakata ɓangarenta ta huta" ta kalli su Safeera ta ce, "ga wannan na masu rakiya ne" ta faɗa tana basu ƙatuwar jaka cike da kaya da kuɗi. Su Mama Atika suka yi godiya suka miƙe dan raka Islaha ɓangaren ta. Kowa ya bita da kallo dan duk so suke su ga fuskar Islaha da ta ƙi ɗagowa.
A hankali ta É—an waigo suka haÉ—a ido da wata mata da take kusa da Mamy, ta janye idanunta sai suka haÉ—a ido da Mamy. Ta É—auke kai da sauri dan ko ba a faÉ—a mata ba ta san itace mahaifiyarsa, yanayinta ya gwada hakan ba sai an yi maka dogon bayani.
Ƙirjinta ya buga da ƙarfi, ta shiga tunanin a ina ma ta san fuskar amma ta kasa tunawa. Ta ja mayafin ta sake rufe fuskar ta, a lokacin aka tashi dan rakata inda zata zauna, ita dai tana kusa da Safeera tana tafiya kamar bata so.
Banisha ce ta buɗe ƙofar falon, suka shiga a hankali aka zaunar da ita a falon Rehaan na downstairs.
Sanah Yayar Mamy ita ta zaunar da ita sannna ta ce, "amarya nan ne ɓangaren ki" ta faɗa cikin hausar ta da bata fita yadda ya kamata.
Bata ce komai ba ita dai ta zauna É—in kawai, idanunta yana kan hannunta tana kallon hannunta. Kowa ya fita daga apartment É—in falon ya rage daga ita sai Safeera da Mama Atika.
Safeera sai da kowa ya fita sannan ta ce, "Islaha kinga girman falon nan kuwa?."
Islaha ta yi tsaki ta murguÉ—a baki bata ma buÉ—e fuska, sai kuma ta dafe kanta da hananyenta dan ciwo yake yi mata sosai.
Tana ji su Mama Atika suna ta yabon kirki Daada da Mama, ita dai bata ce komai ba dan ta ƙi buɗe fuskarta, Allah kaɗai ya san me take ji, Allah kaɗai ya san me zuciyarta take yi. Har ɓangaren aka kawo musu abinci, a nan suka saki jiki suka ci suka sha.
Islaha ta kalli Safeera sannan ta buɗe fuska ta ce, "bani wayata." Safeera ta bata wayar ta karɓa ta kira Sadik amma bai ɗauka ba, sai ta kira Hamma shima bai ɗauka ba, ta yi tsaki ta ajjiye wayar ta ce, "Zazzaɓi nake ji, kaina kamar zai rabe biyu."
Mama Atika ta ce, "Ai dole, wanann kukan da ki ka sha ai dole ki yi ciwon kai. Sai kin yi bacci sannan za ki ji daÉ—i, dan fuskar ki ta kumbura sosai."
Safeera ta ce, "Ni tsoro nake ji kar ta samu attack, kuka kamar an kunna fanfo?."
Mama Atika ta ce, "Ita kaÉ—ai ta san me take ji. Islaha ga kyautar ki, a ina za a ajjiye miki?."
Islaha daƙyar ta ce, "ku je dasu, Safeera ta ajjiye a wajenta."
Safeera ta buɗe ido ta ce, "wa, ni Safeera ni zan kai wannan dukiyar gidan mu? Haka kawai a shigo a yanka min wuya Ki ajjiye abin ki, ni wallahi bazan ɗauka ba" ta faɗa tana miƙewa a lokacin Banisha da Janan da Ikram suka dawo.
Janan ba yabo babu fallasa ta ce, "Amarya mu je mu nuna miki bedroom É—in ki."
Islaha ta kalle su duk suka haÉ—a ido dan fuskar ta a buÉ—e take. Ganin babu wani mai sakakkiyar fuska a tare dasu sai ta sake kama kanta. Ikram wani irin abu ta ji ya tsaya mata rai, kishi ya taso mata ganin wai matar Rehaan ce a zaune a gabanta.
Islaha ta ƙi miƙewa balle ta bi bayansu, yadda fuskarsu take a ɗaure in suka raina mata hankali tsaf zata mare su, zuciyarta a kusa take, baza ta juri raini daga wajen na ƙasa da ita ba.
Safeera ganin yanayin ƙawar ta ta sai ta ce, "Bata jin daɗi, mu je ku nuna min." Suka wuce sama Safeera ta bi bayansu, basu jima ba suka sakko suka fita.
Sai da suka fita sannan Safeera ta koma saman ta saka mata kayan da aka bata a É—akin sanann ta sakko ta ce, "mu je na raka ki saman."
Zata yi musuSafeera ta ce, "Dob Allah mu je." Islaha ta miƙe suka hau saman sannan ta ce, "ki daina wanann halin a gaban Mama, ita bata san komai ba." Islaha ta yi mata banza Safeera ta ce, "Kai amma ɓangaren nan ba dai kyau ba, kamar a aljanna."
Islaha tsaki ta yi tana so ta nemi hanyar kushe apartment amma ta gaza, dan duk hassadar ta ƙarya take yi ta ce bai yi kyau ba. A haka suka shiga falon saman, suka fara haɗa ido ƙaton hotonsa yake jikin bango, Islaha ta kalli hoton ta ja tsaki sannan suka shiga ɗakin.
Safeera ta ce, "gaskiya ke kam Allah ya taimake ki....." bata ƙarasa ba Islaha ta wani kalle ta, Safeera ta toshe baki tana dariya.