Sashe 91
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jazy ya É—aga kai ya ce, "In sha Allah Mamy."
Mamy ta riƙe hannun Islaha ta ce, "Mu je apartment ɗina ki huta." Islaha ta miƙe a hankali tana jin jiri yana ɗaukarta. Mamy ta kalli Rehaan ta ce, "a samo mata reliver inhaler." Bai ce komai ba suka fita daga falon.
A lokacin aka yiwa Rehaan waya, ya ɗauka ya ba da umarnin a shigo dasu inda yake. Ya koma ya zauna fuskarsa kwata-kwata babu walwala, kana kallonsa zaka san ba a hayyancinsa yake ba, ya haɗe rai kuma damuwa ta bayyana ƙarara akan fuskarsa. Shi dai Jazy bai ce komai ba yana daga tsaye yana kallon Oga Rehaan.
Shams ne ya shigo shi da wasu mutane guda biyu, suka ƙaraso suka gaishesa ya ja numfashi bai ce komai ba. Sai daga baya ya ce, "Case ɗin da yake trending a social media a yanzu, ina buƙutar a kawo ƙarshensa a daren nan."
ÆŠaya daga cikin Officers É—in ya ce, "wanne daga ciki." Ya kalle sa amma bai ce komai ba.
Ganin ya yi shiru sai Officer ya ce, "akan abubuwa biyu ne, akwai na wata yarinya Islaha da aka tashi dashi yau, sannan...."
Rehaan ya dakatar da shi yana sake haɗe rai ya ce, "Akansa nake magana. Ina buƙatar na san main account ɗin da ya fara fitar da pictures ɗin, sannan ina so a bani list ɗin sunayen duk wani blog da suka yi reposting video. A yau nake so case ɗin nan ya zo ƙarshe, bana so a ɗauki lokaci."
Officer zai yi magana Rehaan ya dakatar dashi ya ce, "kar ka ce min bazai yu ba, kawai a yi."
Officer ya yi murmushi ya ce, "wannan ƙaramin aiki ne, in sha Allah zuwa anjima zan yi maka bayanin komai." Rehaan bai ce komai ba ya ɗaga masa kai suka fita daga falon.
Jazy kanzil bai ce ba yana daga tsaye yana kallon Rehaan da mamakinsa, mutumin da yake ce mata mai bin maza meye nasa na É—aga hankali akan abinda ya same ta? Yana so ya yi masa magana amma ba ya so ya saka ya farka da shi a yanzu, shiyasa ya yi masa banza ya gama bidirinsa daga baya sai ya faÉ—a masa kuma ya tsokane sa.
Daada tunda ta koma ɓangarenta take ta sallallami tana mita akan abinda Islaha ta aikata, Mama tana gefe tana zugata ta ce, "Ai mun yi gaggawa Daada, wannan yarinyar sai yanzu nake jin asalin wacece ita. Tantiriyar ƴar iska ce, bata jin magana ko kaɗan, har ƙasashen waje ake fita da ita ana biyan ta. Ai daga kallon waɗanan hotunan kin san ta saba da bin maza, waɗannan video irin na turawa samari su bata kuɗi ne, kin san ƴan matan yanzu jikinsu ne jarinsu."
Daada ta ce, "ikon Allah! Ashe daman akuya ce da fatar kura, a haka kamar mai hankali har ina alfahari da ita ashe Æ´ar iska ce, haka kawai muna zaune lafiya na É—auko baragurbi na sakata a cikin ahlina. Bazai yu ba, kira min mijinki yanzu nan, dole a san abinda za a yi, in zan zauna da yarinyar da duniya ta gama ganin jikinta? Wannan ai babban abin kunya ne a wajan da Rehaan É—in babansa. Ba zai yu ba, kira sa yanzun nan a san abinda ya kamata ayi."
Mama ta kira Abba amma bai É—auka ba ta ce, "Bai É—auka ba Daada, amma na san zuwa anjima zai kira ni."
"Ai gwara ya kira É—in, bazan bar hakan ta cigaba da faruwa ba. In aka ga baragurbi cire sa ake yi, in ba haka ba sai ya lalata maka sauran. Ina ni ina cigaba da zama da yarinyar nan? Ai har abada."
A lokacin Abba ya kira wayar Mama sai ta miƙawa Daada tana sakawa a kunne ta ce, "Maza ka zo ina neman ka, sannan a kira kowa da kowa ina buƙatar ganinsa yanzun nan." Tana faɗa ta kashe wayar Mama tana ta girgiza kai, dan wallahi baza ta bar Islsha ta sarara a cikin gidan ba.
Mamy da Islaha tunda suka koma apartment tana zaune kusa da Islaha ta kwantar da kanta a kafaÉ—arta, Islaha ta yi shiru tana jin ciwo a zuciyarta, rarrashin da Mamy take yi mata yana sakawa ta ji daÉ—i, tana jin daÉ—in samun Mamy a gefenta, ta zamar mata jigo mai share mata hawaye, ta zamar mata bangon da ta rasa a shekarun da ta yi a duniya, yanzu ne ta samu bangon ya tsaya har ta jingina tana kuka.
A lokacin Abba ya kira wayar Mamy, tana É—auka ya sanar da ita umarnin Daada. Mamy ta kalli Islaha da ta yi lamoo a jikinta ta ce, "bata da lafiya, baza ta iya fitowa zuwa zaman meeting ba."
"Ya zama dole ta zo Nadira, saboda ita za a zauna."
"okay" ta furta tana kashe wayar.
Ta É—ago Islaha daga jikinta tana shafa fuskarta da ta kumbura sosai saboda kuka ta ce, "zamu je wajan Daada wai tana neman kowa, kuma kin san a kan ki za a haÉ—a meeting É—in. Kar ki damu, babu abinda zai faru, ni da Rehaan muna bayanki, babu wanda zai yi miki wani abun a gidan nan. Saka mayafin ki mu je."
Mamy ta kalli Safeera ta ce, "ki jira mu a nan."
Safeera ta ɗaga kai tare da yin tagumi, Mamy ta riƙe hannun Islaha suka nufi ɓangaren Daada, suka shiga suka tarar da kowa yana nan su kaɗai ake jira.
Suna ƙarasa zama akan carpet Daada ta ce, "Ni ban san haka Ishlaya take ba, da ban ɗauko ta na saka a cikin ahlin mu ba, na yi tunanin yarinyar kirki ce, ta gari wacce zata haifi yara na gari, ashe ita ɗin ta wuce tunanina a fannin tantiranci. Gaskiya bazan iya zama da ita a gidan nan, yarinyar da duniya ta gama ganin tsarsicinta ai ba abar so bace, kuma wannan ba ɗabi'ar fulani ba ce, ni kuma duk abinda ya saɓawa al'adarmu bana sonsa. Dan haka..." sai ta dakata tana kalle-kalle sannan ta ce, "ina yake?."
Sai a lokacin Rehana ya shigo falon jikinsa a sanyaye, tun kafin ya zauna ta ce, "Kai Rehaan! Ka saki yarinyar nan yanzun nan, tunda daman ba sonta ka ke yi ba, ka sake ta kawai ka huta da auren da na baka. Kuma daman duniya bata san ka yi aure ba, da ta ɓata maka suna."
Rehaan kalli Daada ya ɗauke idanunsa, ya kalli Mamy ya ga tana riƙe da hannun Islaha, ya kalli Islahan da kanta yake a ƙasa, ko ba a faɗa masa ba yasan kuka take yi, ya kalli Abba da yake kallonsa ya yi shiru bai ce komai ba.
Abba ya ce, "Ba ka ji abinda aka ce bane? Ka aikata kawai."
Rehaan ya cize bakinsa sannan ya ce, "ina bincike akan case É—in, a bani lokaci na gama komai sai ya biyo baya."
"Binciken me za ka yi? Ga zahiri kowa yana gani, yarinya a kwance da wani namijin da ba kai ba?. Ni daman na faɗa muku tunda ta zo gidan nan Salman ya canja ake ganin kamar ƙarya nake yi, ni da kaina na faɗa muku na ga abinda ban taɓa gani ba a tare da shi sai da ta zo gidan nan. Ni ban san Salman yana da lafiya irin ta ko wanne ɗa namiji ba sai da ta zo gidan nan, daga nan ya san rungume mace har yace yana sonta. In ba ƴar bariki ba wacece zata yi haka? Ni na fara zargin anya....."
"Umma please!"
Rehaan ya katse ta jin zata fasa masa zuciya da banzayen kalamanta, ya waiwayo suka haÉ—a ido da idanunsa da suka canja sannan ya ce, "na ce a bani lokaci, bana son wata magana kuma."
Daada ta ce, "anƙi a ba ka lokacin, na ga dai ni na haɗa auren ko? To yanzu na ce a raba bani da buƙatarsa ko kaɗan a cikin gidan, dan wallahi bazan zauna da wannan abin a gidan nan ba, ka ji na ce wallahi."
Rehaan ya kalli Islaha da kukan ta ya fara fitowa fili, ya kalli Mamy da ta yi shiru bata ce komai ba, sai ya girgiza bai ce komai ba.
Daada zata yi magana suka ga ya ƙarasa shigowa falon gabaɗaya, ya ƙarasa inda Islaha ta ke ya miƙa mata hannunsa yana kallonta alamun ta riƙe nasa. Islaha shadow ɗinsa ta gani a kanta a tsaye, ta ɗago jiƙaƙƙun idanunta ta kalle sa, ta ga ita yake kallo ga hannu ya miƙa mata yana jira ta ta saka nata a cikin nasa ya riƙe. Ta kalli hannun da ya miƙo mata tana kallonsa, fari tas dashi sai wani bracelet da yake zagaye a tsintsiyar hannunsa.
A hankali ta ɗora hannunta akan nasa, ya damƙe nataa cikin nasa sannan ya miƙar da ita tsaye, jiri ya ɗan ɗauke ta ya riƙe kafaɗunta sannan ya kalli Daada ya ce, "na ce a bani lokaci, zan yi abinda na ga ya dace" ya faɗa yana jan hannunta suka fara tafiya.
Sai ya ji Umma ta ce, "Wallahi sai ta bar gidan nan, bazai yu ta lalata min yaro ina kallo ba. Yarinyar da bata ji kunya buÉ—e jiki anyi mata video ba, ai lalata mutum irinsu Salman bazai mata wahala ba, sai ta bar gidan nan ai ba gidansu bane."
"Amma ni kin yarda gidanmu ne?" Ya tambaya yana kallon Umma.
Ta yi shiru bata amsa ba ya ce, "indai nan gidanmu ne itama gidansu ne. Babu inda zata je sai na gama abinda na ce ina yi!. Matata ce, ban yi niyar rabuwa da ita ba, kuma bazan yi ba."
Ya faÉ—a yana kallon Umma da mamaki ya daskarar da ita a wajen, bai sake kallonta ba ya ja hannun Islaha suka fita.
Daada ta fara tafa hannaye ta ce, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! AbdulAziz, haka É—an naka jinin indiyawa ya zama? Ina magana da shi zai ja hannun wannan yarinyar su fita, ni yake kallo yana cewa bazai yi abinda na ce ba a bashi lokaci?."
Abba ya ce, "ki yi haƙuri, zan yi magana da shi. Ina zuwa" ya faɗa yana miƙewa ya fita Mamy ma ta fita.