Sashe 1
Ragayar Dutse Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
KRBBK:
RDB3P001
Nana Haleema.
#The Battle between love and marriage
#Justice
#Attack
#Reward
#Intense love.
Baffa da sauri ya koma cikin gidan ya samu Saheer a zaune akan kujera ya dafe kansa cikin wani irin yanayi na damuwa da tashin hankali. Baffa ya yi turus, yadda ya ji Mmaa tana ƙwalla ihu ya yi tunanin suma ya yi, amma sai ya gansa a zaune ya dafe kansa da duka hannayensa.
Ya ƙaraso lokacin da Mama take magana cikin faɗa tana cewa, "ƴar gwal ce? Tunda ta zaɓi kuɗi a kan halacci ba sai a ƙyale ta ba? Ita kaɗai ce mace a duniya da za ka kashe kanka saboda ita?. Daga hannun masu garkuwa da mutane ka fito, har yanzu jikinka bai yi daidai ba, in ka kashe kan ka kanka ka yiwa asara ba ita ba, ita ta yi aure a gidan masu kuɗi, ta bar ka a nan cikin tunanin banza da wofi. Ka manta da ita, domin ita matar aure ce a yanzu, ka raini lafiyar jikinka."
A lokacin Baffa ya dafa kafadarsa, Saheer ya ɗago jajayen idanunsa ya kalli Baffa, sai ya riƙe hannun Baffa, muryarsa tana rawa sosai ya ce, "Baffa da gaske ta yi aure?."
Baffa ya yi ajiyar zuciya cikin dubun tausayin Saheer ya riƙe hannunsa ya ce, "ta so mu je ciki."
A hankali ya miƙe tsaye yana ji zuciyarsa tana bugawa kamar zata faɗo daga ƙirjinsa, jiri yana ɗaukarsa kamar zai kifa da kansa. Baffa ya riƙe hannunsa sannan ya juyo ya kalli su Mama ya ce, "kar wanda ya biyo bayan mu" ya faɗa yana kallonsu sannan ya ja hannunsa suka tafi ciki.
Mama ta bi su da kallo sannan ta yi dariya ta ce, "ai na faÉ—a daman, indai ina da rai wallahi wallahi bazai auri wannan yarinyar mai buÉ—aÉ—É—en ido ba. Ko asalin yarinya ba mu sani ba mu haÉ—a jini da ita..? Sai dai in bana raye wallahi." Ita dai Adda bata ce komai ba, tausayin Saheer ya mamaye mata zuciya cikin tsananin tashin hankali. Hanan ce take biyewa Mama sannan suka shiga ciki.
Baffa akan kujera ya zaunar dashi, ya ɗauko masa ruwa ya miƙa masa. Saheer ya karɓa ba tare da ya sha ba, ya bi Baffa da kallo har ya zauna a kusa da shi.
Baffa ganin irin kallon da Saheer yake yi masa ya saka ya ce, "ka sha ruwan Saheer."
Ya girgiza kai ya ce, "Bazan iya ba Baffa. Don Allah ka sanar da ni abinda yake faruwa, na kasa gasgata abinda na gani, na kasa yarda da abinda kunnuwana suka ji. Mafarki nake yi ko a zahiri ne ni na kasa ganewa, abu É—aya nake so na tabbatar, da gaske Islaha ta auri wani ko wasa ake yi min?."
Baffa ya sauke numfashi cikin tausayin ɗansa, ya san Saheer yana matuƙar ƙaunar Islaha, yana sonta so na zahiri kuma na gaskiya, yana yi mata so na aure, yana so ya ɗauke ta ya katange ta a cikin inuwarsa a matsayin matarsa. Ya so ta tun tana gidan marayu, son da yake yi mata ne ya saka shi ɗauko ta ya kawo ta gidansu, ya cigaba da ɗaukar ɗawainiyarta a matsayin Yayanta kuma mijinta na gobe.
Bayan Saheer, in akwai mai son aurensa da Islaha to shine, zai iya cewa ya fi Saheer ɗin murna in ya auri Islaha, saboda ƙaunar da yake yi mata da yadda ya yaba da ɗabi'unta. Shiyasa ya so ya aura masa ita da wuri-wuri, dan bai ɗauki maganar Zulaiha a bakin komai ba, sai tatsuniya. Sai dai kash! Bazai taɓa bari auren ya kasance ba, bazai bar auren ya ba, dan faruwar auren ba ƙaramin masifa bace ga shi kansa da Islahan.
Hukuncin da ya yanke shine yake ganin shine daidai, amma ya san ya yi breaking É—insu shi da ita, ya cutar da rayuwarsu shi da ita, dan dukkansu suna son juna kuma suna burin auren juna.
Amma ya zai yi? Hakan shine ya zama zaɓi da mafita a gare su, hakan da ya yi shine yake ganin ya dace da Saheer da ita kanta Islahan. Tunda ya ke yi mata addu'a akan Allah ya zaɓa mata miji na gari, kuma Allah ya zaɓa mata Rehaan, sai yake ji a ransa Rehaan shine miji na gari a gare ta ba Saheer ba.
Baffa cikin sanyin murya ya ce, "Saheer!."
Saheer da ruwa ya taru a idanunsa, ya É—ago ya kalli Baffa yana jira ya ji me zai ce.
Baffa ya bi sa da kallo tausayi sannan ya ce, "Da gaske ne."
Saheer muryarsa tana cracking ya ce, "Da gaske ne me Baffa?."
Baffa ya zuba masa ido cikin tsananin tausayinsa sannan ya ce, "Da gaske Islaha ta yi aure, tana hanyar zuwa gidan mijinta."
Runtse ido ya yi jin maganar ta da ki zuciyarsa, ta ratsa jijiya da tsoka da ƙasususan jikinsa. Ƙwaawalwarsa ta harba da ƙarfi, ya ja numfashi da ƙarfi yana saukewa a wahalce yana jin zufa tana tsatstsafo masa daga ko ina na jikinsa. Har bayan rigarsa ya jiƙe saboda tashin hankali, goshinsa ya tsatstsafo da gumi yana ɗiga a gaban rigarsa.
Baffa dai kallonsa yake yi cikin tsananin tausayinsa da jin nauyinsa. Allah ya sani ba haka ya yi niya ba, bai yi niyar cutar da ɗansa na cikinsa ba, amma ƙarshe aka kai shi shiyasa ya yi haka. Yana so ya samarwa da Islaha rayuwa mai inganci ne shiyasa ya amince, yana so ta gina kanta akan burukan da suke cikin ranta, ba ya so rayuwarta ta cigaba kasancewa cikin maraici da ƙasƙanci kamar yadda take ciki yanzu.
"Baffa....."
Sai ya kasa ƙarasawa yana kallon Baffa bakinsa yana rawa sosai amma ya kasa magana. Daƙyar ya ce, "Mafarki......"
"Na ke yi......"
"Ko?."
Ya faÉ—a a rarrabe cikin yanayi mai wahalar fassarawa, wanda shi kaÉ—ai ya san girgiÉ—in da zuciyarsa take yi, buri yake yi kunnensa ya ji Baffa ya ce mafarki ne ba gaskiya bane.
Baffa ya ce, "Ba mafarki bane, da gaske ne Saheer."
"Hasbunallahu wani'imal wakil!" Ya faÉ—a yana runtse idanunsa tare da jingina da kujera.
Baffa ya sunkuyar da kansa ya kasa haɗa ido da gudan jinin nasa. Jin sautin kuka ya saka Baffa ya ɗago kansa ya kalli Saheer, ga mamakinsa kuka Saheer yake yi sosai, ya duƙa a gabansa ya ɗora kansa a jikin Baffa yana kuka da yake fita da sauti.
Baffa sai ya ji kamar ya ta ya shi kukan, zuciyarsa ta karye ya ɗora hannunsa a kansa ya ce, "ka yi haƙuri Saheer, ban yanke mu ku wannan hukuncin dan na jefa ɗayan ku a cikin wannan yanayin ba. Itama yanayin da ta shiga kenan da a lokacin da sanar mata da maganar, ta shiga gigicewa fiye da tunanin ka. Ni kuma na yi haka ne saboda bana so rayuwar Islaha ta cigaba da zama jiya e yau, tana buƙatar cigaba. Kai ka san ina son auren ku da ita, tunda ka ga na aikata hakan ka san ina da hujja mai ƙarfi. Ban yi dan na raba ku ta ƙarfi da yaji ba, na yi ne dan hakan shine masalaha a gare ka da ita kanta. Wallahi in dai babar ka tana raye, baza ta taɓa bari auren nan ya yu ba."
Saheer ba ya iya fahimtar abinda Baffa yake faÉ—a, abinda yake hange kawai Islaha ta yi aure tana kan hanyar zuwa gidan wani a matsayin matarsa, shi kaÉ—ai yake yi masa amsa kuwa a kunnensa, ya kasa daina jin maganar a kunnensa tana ratsa jinin jikinsa.
A lokacin Sadik ya shigo da sallama Baffa ya amsa ya ce, "ƙaraso Sadik, zo ka rarrashi ɗan uwanka akan laifin da na yi masa."
Sadik ya tako a sukwane zuwa inda Saheeer yake cikin tausayi, dan ko shi ba Saheer ba, sai yanzu yake jin zafi da haushin auren da Islaha ta yi. Duk da shi ya san dalilin auren, amma ya kasa amfani da sanin nasa, yana jin zafin auren, yana kuma ta ya abokinsa kishi mai yawa.
Ya riƙo Saheer ya miƙe zaune, Baffa ya bisa da kallo ganin yadda fuskarsa ta yi ja, idanunsa sun yi ja sosai kuma sun kumbura, ga shi daman ba shi da lafiya, har lokacin jikinsa bai dawo daidai daga azabar da ya sha a hannun masu garkuwa da mutane ba. Baffa ya ce, "Sadik ku je ɗaki ya huta, zamu yi magana. Yanzu ba ya fahimtar abinda nake faɗa masa."
Sadik a sanyaye cikin raumi ya ce, "To Baffa. Saheer ta so mu je, magrib tana yi." Saheer kamar bai ji ba yana dai zaune ya rufe idonsa ya kasa motsi.
Sadik ya É—an yi gapping shoulder É—insa ya ce, "Tashi mu je."
A lokacin ya buɗe idanunsa ya kalli Sadik, kamar zai yi magana sai ya rufe bakinsa, dan harshensa ya sarƙe bazai iya furta komai ba, miƙe daƙyar suka fita zuwa ɗakinsa.
Baffa ya bi sa da kallo cikin tausayi, amma har lokacin ba ya danasanin aurar da Islaha a inda zata samu abinda zata gina rayuwarta yadda take so.
   Saheer a gefen gadonsa ya zauna, sai kuma ya cire riga ya ajjiye a gefe yana jan numfashi daƙyar kamar mai cutar sarƙewar numfashi. Sadik ya zauna a gefensa yana kallon yadda ya rame, ga tabon dukan da ya ci a hannun masu garkuwa da mutane nan caɓa-caɓa a jikinsa, ga cizon ƙwarukan da bai san ya suke ba, har lokacin jikinsa da dauɗa bata gama fita ba.
ÆŠakin ya yi shiru babu mai magana a cikinsu, sai numfashin da Saheer yake saukewa a hankali kamar wanda ya yi gudu, zuciyarsa tana bugawa a guje, har yana jin sautinta a kunnesa.
Sun jima a haka kafim Saheer ya yi breaking silence É—in ya ce, "Kai ma ka san ta yi auren?."
Sadik ya É—an lumshe ido ya buÉ—e, ya É—ago ido ya kalle sa ya ce, "Ka bari ka samu lafiya sai mu yi maganar, za ka fahimta in sha Allah."
"Kai ma ka san ta yi aure!?" Ya tambaya cikin tsawa yana kallonsa.
Sadik ya kalle sa dan ya san ba ya cikin hayyacinsa, ta É—aga masa kai ce, "Na sani, shiyasa....."