Sashe 99
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna shiga bedroom Azaan ya waigo yana aikama Amaar wani kallo cike da tuhuma,Amaar ya d'auke kansa yayi kamar bai ga abunda Azaan yake ba,Azaan yace "har yanzun kana da abun fad'a?" Amaar yayi saurin kallonsa yana squeezing fuskarsa yace "think i didn't get it right" Azaan ya sauke numfashi idanunsa akan Amaar yace "baka gane ba?" Amaar yace "yeah! Me kake son cewa ne?" Azaan yace "kana nufin baka ji maganar da step Mom d'inku take yi ba?" Amaar ya tab'e baki yace "ba wannan ne lokaci na farko da naji irin maganar nan a bakinta ba" Azaan ya d'an zaro idanunsa yace "ohhh! Ka san maganar kenan ni ne ka rainawa hankali?" Amaar ya girgiza masa kai yace "nope!" Azaan yace "uhn! What's up?" Amaar yayi d'an tsaki cike da takaici yace "forget the matter please.. Think bai kamata mu b'ata ma kanmu lokaci akan maganar ba" Azaan yace "ko saboda me za'a barshi?" Amaar yace "because ba shi da wani value" girgiza kai Azaan yayi yace "i want to know me ka sani akan case d'in nan" da sauri Amaar yace "please brother" Azaan yace "baza ka fad'amin ba?" Amaar yace "wai mesa kake son tada ma kanka hankali ne akan maganar?" Azaan yace "just wanted to know,idan baza ka fad'a ba kuma fine" Amaar zai yi wani maganar Azaan yace "please idan baza ka fad'a min abunda nake so ba,just keep quiet.." Kallon Azaan Amaar ya dunga yi da mamaki,he just wish zai iya keeping secret d'in da Aunty tace yayi but yanda Azaan ya damesa da maganar at last dole ya hak'ura yayi exploding masa gaskiyar abunda ya sani,Azaan ya dunga kallonsa and he couldn't take off his eyes on him,can ya ja numshi ya sauke a hankali yace "but me yasa shi Waleed yayi keeping maganar tunda he loves Manar?" Amaar yace "don't u understand maganar Mom d'insa?" Azaan yace "na ji.." Amaar yace "ka san Waleed yana da mugun zurfin ciki,ba komai ne da ya shafesa yake bari a sani ba.. So maybe yayi keeping maganar ne all because of abunda ita Mama take fad'a" Azaan ya dunga gyad'a kai ba tare da ya sake cewa komai ba suka yima juna shiru kowa da tunanin da yake damun ransa. Da dare after isha'a Dadda na zaune tana lazimi Amaar ya shigo parlon yana kallon Dadda dake laziminta yace "ina wuni" ta masa gyaran murya sanda ta kai k'arshe tana washe masa baki tace "lafiya lau d'an fodiyo,hala kaima kaji batun kawo kayan ne ka taho gani? Ai wallahi kai dai baka ga kaya ba kamar za'a bud'e kanti wallahi,takwarata ta yi goshi.." Za ta sauke masa yace "Hjy ai bama sai kin bud'e ba,ni da ba sanin yanda ake yi nayi ba,ki barshi kawai Allah sanya alkhairi ya ba su zaman lafiya" tace "Ameen dai d'an nan dama ganin kaya kam sai mata" shi dai bai ce mata komai ba ya juya zai fita yace "sai da safe" tace "toh! Allah maka albarka,ya kaimu lokacin da zamga na ka auren.." Murmushi yayi ya fita,Dadda ta ci gaba da laziminta. Washe gari da safe wajen k'arfe goma Manar ta shigo b'angaren ta tarar da Dadda suna d'aga kayan da aminiyarta Tasallah,tana ganinsu ta juya za ta koma,Dadda ta kwalo mata kira,ta juya tana kallonta daga bakin k'ofar,Dadda tace "to kuma ki shigo mana kiranki fa nake dan walak'anci kika tsaya nan kina kallona" Manar ta k'arasa fuskarta a d'aure tace "ga ni" sabon wayarta da Amaar ya siya mata k'iran Tecno mai keypads ta mik'a mata tace "maza ki lalubo min zaran da zai had'a ni magana da Mamman" Manar ta kalleta da sauri tace "Yaya?" Dadda ta mata wani kallo tace "to da idan ba shi ba wa nake nufi kuma?" Manar ta shiga contact ta lalubo number sa ta kira mata shi,sai da kiran ya katse kafin Waleed ya kirata,da sauri ta karb'e wayar ta kai kunne without ta yi answering ta fara magana,Manar ta bita da kallo,jin bai yi magana ba Dadda ta d'ago wayar dake ring har lokacin ta kalli Manar tace "to kuma ya haka na ji shiru bai ce komai ba sai kafirin kid'an dake tashi?" Manar tace "to ai baki answering call d'inba kike magana" da sauri Dadda ta mik'a mata wayar tace "to d'an sake lalubo min shi muji" Manar tace "ki danna wajen koren alamar mana" da k'arfi Dadda ta daddage ta danna kamar za ta b'urma button d'in,then ta kai wayar kunnenta,kafin Waleed yayi magana Dadda ta fara cewa "to wai ni kuwa sai yaushe za ka dawo k'asar ne Mamman? Haka kawai ka tafi wata k'asa ka share gindi ka zauna,kai ko kad'an baka ji kewar gida ya dameka ba?" Waleed dake sauraronta yayi Murmushi yace "to ki bari dai har ki had'iye yawu mana,kina ta magana ba coma bare fullstop,sai magana kike kamar an bud'e lalataccen radio" fuska d'aure Dadda tace "ehh lallai Mamman ni kake fad'awa haka? To ka gayama ubanka Yaro ko Asama'u" dariya yayi yace "ba dai haushi kika ji ba ko?" A fusace tace "sai dai kaje ka tambayo uwarka d'an nema" ya d'aure fuskarsa yace "kinga ni idan ba ki da abun fad'a zan kashe wayana,haka kawai kin kira mutum kuma kina masa fad'a,zan tafi masjeed idan kin tuna abunda za ki fad'a later sai ki kira ni" da sauri tace "umm! Dama lefen k'anwarka fa aka kawo nace bari na sanar maka" wani fad'uwa gabansa ya dunga yi yace "lefe?" Ya maimaita,Dadda tace "ehh wallahi kai dai baka ga kayan da suka kawo ba,kamar za'a bud'e kanti,yo abunka da gidan manya,ka san fa gidan sarauta za taje" a fusace yace "don't tell me that.." Da sauri Dadda ta zaro ido tace "inji dai ba zagina kayi ba da wannan kafirin yaren naku da kuka aro gurin yahudu da nasara?" Waleed ya sauke numfashi yana matse forehead d'insa da veins d'in gurin suke harbawa da k'arfi ya d'an girgiza kansa a hankali yace "not at all.." Mitsi² Dadda tayi da ido tace "wallahi to ba da ni kake ba da Yaro kake.." Yadda tayi magana makes Waleed fashewa da wani dariyar da bai shirya ba,yace "to wai ke wa yace maki zaginki nayi ma? Da kike sako Abbana a ciki?" Dadda tace "ohoon maka dai ni ba dani kake ba wallahi kaji in fad'a maka" babu shiri Waleed yace "bari naje masjeed na dawo zan kira ki" tace "to ai shi kenan.." Har za ta katse kiran sai kuma tace "to dama k'asar da kaje d'in suna sallah ne?" Waleed yace "a'a sai kin zo kya koya musu yadda ake yi" yana fad'a ya katse wayar yana dariyar halin grandma d'insu,sanda yaje masjeed ya dawo tuni ya manta da batunta ya shiga wani uzurin,wasa² har ana saura kwanaki uku bikin bai yiwa kowa waya ba kuma ba shi da niyyar dawowa gida,at that same day da dare suna waya da Manar dake d'aki a kwance tace "Yaya sai yaushe za ka dawo?" Yace "babu rana" ta zaro idanunta tace "Kai Yaya yanzu kana nufin baza kai attending event d'in biki na ba?" Waleed da yaji kamar she pours him boiled water ya runtse idanunsa yayi shiru,Manar taji bai ce komai ba ta kirasa a hankali "Yaya!" Still ya kasa amsawa,ta sake kiransa cike da damuwa tace "Yaya what happened?" K'in cewa komai yayi k'arshe kawai ya katse wayar yana sauke numfashi da kyar²,Manar tana jin ya yi cutting kiran ta fara kiransa cike da damuwa,but ya k'i d'auka babu shiri ta tura masa text tace "Yaya! Wai me yake faruwa? Ka san dai hankalina bazai kwanta ba idan ba sanin abunda yake faruwa nayi ba" cike da k'arfin hali Waleed ya bi content d'in lokaci d'aya ya kirata vedio,da sauri tayi picking tana kallonsa a kwance saman lafiyayyen gadon hotel d'in da yake tace "Yaya!" Ya runtse idanunsa yana calming kansa a hankali,Manar ta sake kiransa da muryar kuka tace "tell me please me yake damunka?" Lokaci d'aya ya bud'e idanunsa da suka juye yana kallonta yace "kece" ta zaro idanunta dake cike taf da hawaye tace "ni me nayi maka kuma?" Yace "me yasa kike son tada min hankali ne?" Tace "Yaya me nayi?" Yace "kina min maganar aurenki da wani,do u know how much ur words hurts me?" Ta girgiza masa kai hawaye suna saukowa fuskarta cikin raunin murya tace "I'm very sorry Yaya,ban san ba ka son maganar ba da ban fad'a ba" ya lumshe idanunsa a hankali yace "okay" daga haka hiran na su ya canja. Mama zaune tare da Hjy Izzatu a parlon gidansu Afiyah suna gaisawa da Afiyar da tun bayan barin Waleed k'asar itama ta tattara ta tafi gidansu a cewarta baza ta zauna masa gadin gida ba,su Maman nema suke gaida ta tana amsa musu a wani iri,can dai tana yatsina fuskarta tace "a kawo maku abinci?" Mama tayi murmushi tace "um'um wallahi alhamdullillah! Ai daga gida muke,takanas nace bari dai muzo muganki,sannan mu yi wata magana da ke mai muhimmanci" Afiyah na kallonta tace "okay ina jinki Hjy" Mama ta d'an yi shiru sai kuma tace "hope dai komai lafiya?" Afiyah ta tab'e baki tace "lafiya lao fa though d'anki ya ajiye ni tunda ya tafi ko waya bai min,tunda ya kira nace masa na tafi gidanmu duk sanda ya dawo na koma yake jin haushi na" Mama tace "kayyah! Me isa kika sanar masa ke kuwa?" Afiyah tace "how on earth zan zauna gidansa ina masa gadi? Abunda aka aureni yi masa kenan?" Mama ta girgiza kai tace "ai da baki sanar masa ba,saboda duk shirin da muke yi yanzun na ya dawo ne,ya shaida auren yarinyar can,yanzu kinga kin rusa mana wani plan d'in because duk sanda ya kira ina sanar masa kina gidan tare da su Deejah" Afiyah tana mata wani kallo tace "k'arya kika shirya masa kenan?" Mama da bata ji komai a maganar da Afiyar ta fad'a ba tace "to dama shi wannan mutumin ai sai da k'aryan,wallahi duk fad'i tashin da nake akanki ne naga kin mallakesa ke kad'ai,zuwan da muka yi ma saboda muna son ki kiras ne ki lallab'asa ya dawo,ba yanda banyi da shi ba ya k'i" wani murmushi