← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 184

Sashe 76

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya sosai ta basa,tana ganinsa tayi shiru tace "a'a har ka fito Mamman?" Bai amsa ba yace "me za ki yi ne Hjy?" Dadda tace "iiiihhh! Yo bazan tashi na nemawa cikina abunda zan ci ba tunda na kwaso yunwar cikina,ga Manar ma bata karya ba na hana ta zama,da kyar ma fa ta yarda ta biyo ni... Abu dai da raina da lafiya ta,tunda ita wancan matar dake sama uwa tsuntsuwa baza ta kula mu ba,ni ba sai nayi mana ba ai dai babu wanda zai hana ni ko yace don me ko?" Murmushi yayi yana shafa beard d'insa yace "kiyi hak'uri yanzu za ta zo ta had'a maku" da sauri Dadda ta ajiye match d'in tana kallonsa tace "amma anya ka ce mata nice na haifi ubanka kuwa?" Yayi murmushi yace "a'a sai dai yanzu ki fad'a mata tunda kin zo" ya juya ya fita yana murmusawa. Afiya ta sakko parlor ta dunga yiwa Manar wani kallo mai cike da tsana tana tafiya,suna had'a ido Manar tayi tsaki ta d'auke kai,tsayawa Afiyah tayi tana kallonta zuciyarta kamar zai fito waje tace "u had better respect ur self idan ba haka ba wallahi gidana kika zo jikinki ne zai mugun yi miki tsami.. Banza k'aramar y'ar iska" kallonta Manar tayi da sauri tace "gidan ki ko gidan Yayana? Gidan ku na can kin baro sa malama don haka baki isa ki min warning a gidan Yaya ba.." Da sauri Waleed ya k'araso wajen jin muryar Manar,ya tsaya kallonsu da mamaki kafin yace "Lafiya? Me ya faru?" Manar tace "wai ce min take in shiga hankalina nan gidanta ne,kuma fa ba abunda na mata daga sakkowarta ta fara min fad'a tana min warning" baki sake Dadda data fito take kallonsu tace "iiiihhh! Ki shiga hankalinki kuma? Anya Safiyah kin san wace ce ita kuwa? To bari kiji wallahi wannan da kike gani ta fiye ma Mamman kowa a duniyar nan,kaji min zabiyar matar nan dai,ita da gidan Yayanta kice ta shiga hankalinta saboda baki da ta ido? To wallahi akan Manar sai nasa Mamman ya kora ki gidanku yanzun nan,gwara ma ki zageni da ki tab'a min Manar,duk da dai zagin nawa ma kinyi kawai dai ni me hak'uri ce na ja bakina nayi shiru ban tanka maki ba,kaji min shafaffiyar mata dai za ta saka ma jikata ido bayan gidan d'an uwanta tazo" mik'ewa Manar tayi kamar za ta yi kuka ta nufi k'ofa tace "ni dai sai kin taho Hjy,dama sai da nace bazan zo ba tun farko.." Dadda ta saki wani salati tana kallon Waleed da yayi still bai ce komai ba tace "yau ake yinta.. To wai dama Mamman baka zaunar da matarka ka sanar mata matsayin mu bane?" Shi dai bai ce komai ba yabi bayan Manar da sauri seeing that har ta fice parlon,yana fita yaga ta nufi gate ya bita ya rik'ota da sauri yace "ina za ki?" Kamar za ta yi kuka tace "ni dai gida zan tafi me zan zauna yi bayan kana gani matarka ta gama zagina" kallon eyeballs d'inta ya dunga yi,ganin bai ce komai ba ta kwace hannunta,ya kalli gate lokaci d'aya ya jawota ya had'ata da jikinsa murya can k'asa yace "toh kiyi hak'uri mu koma dama ai ba gurinta kika zo ba ko?" Ta turo baki ta k'i cewa komai,yayi murmushi yace "baza ki hak'ura ba?" B'ata fuska tayi tace "zagina fa tayi kana ji" ya zaro sexy idanunsa still smiling ya ja hancinta yace "banda sharri fa ni ban ji sanda ta zage ki ba" kwace kanta tayi za ta wuce ya sake rik'ota yace "na fa ce kiyi hak'uri ko?" Ta kallesa fuskarta a d'aure kamar za tayi kuka tace "toh baka gaya mata ni wace ce bane?" Dariya sosai tasa yayi seeing that she looks like Dadda da tana magana,ya rik'o hannunta biyu yace "haba na gaya mata mana,but kiyi hak'uri zan sake gaya mata yanzu,mu koma ciki sai ki had'a maku breakfast d'in da kanki mu rabu da ita ko?" Ta turo baki bata ce komai ba,yana mata murmushi yace "idan mun koma kice ma Hjy kin hak'ura don ta daina mitar nan kin ji?" A hankali tace "toh" Yana kallonta har sanan yace "let's go" daga haka suka koma parlon yana rik'e da hannunta,Dadda kad'ai suka tarar a parlon tana kallon stairs tana cewa "banda Allah ya yi ni d'in mai hak'uri ce ma d'azu fa haka kika fito kika gaida ni a tsaye k'ik'am,yo ko uwarki kya yima haka,kuma dan na yi maki shiru bance komai ba,sannan na maki magana bamu karya ba tsabar k'aryar bala'i kince babu komai a gidan,su wancan kaya na cikin d'akin ajiya da firinji kuma fa? Ke kuma irin zaman da za mu yi dake kenan tun ba'a je ko ina ba?" Waleed da ya shigo ya k'arasa kusa da Dadda yace "haba Hjy kiyi hak'uri mana,Manar d'in ma fa ta hak'ura kike mita kuma" da sauri Dadda ta kalli Manar tace "wai haka?" Manar ta gyad'a mata kai a hankali,Dadda ta wani washe baki tace "alhamdulillahi.. Toh ai sai ka ce mata ta sakko ta had'a mana abun karin kumallo ko? Gaskiya dai Mamman baka yi dacen mata ba,tun ba aje ko ina ba ta fara nuna hali,ko da yake ai dama Asama'u ta nemo maka auren dole sai dai muyi ta hak'uri kuma,idan Allah ya yi mai zama tare da mu ce to,idan kuma tafiya za tayi ni sai na nemo maka wacce za kuyi dai² da kaina.." Kallon Manar Waleed yayi ya mata alamar ta tafi kitchen d'in,ta b'ata rai ta rungume hannuwanta a k'irji tace "kuma ni kad'ai zanje?" Dadda ta kalleta da sauri tace "ina za kije ke kad'ai?" Da sauri Waleed ya nufeta yace "mu je tare to" bata masa musu ba ta nufi kitchen d'in ya bi bayanta,tana shiga ta k'arasa gurin gas da Dadda ta bari a kunne ta d'ora musu Lipton,ya mik'a mata kayan k'amshi tasa,ya juya ya d'ebo potatoes ya zube ya d'au wuk'a zai fere da sauri Manar ta karb'a tace "Yaya kawo nayi kada ka yanke" ya mik'a mata yace "okay! But be careful with the knife" bata ce masa komai ba ta fara fere dankalin,ya tsaya jikin kitchen island yana kallonta,duk wanda ta gama ferewa sai ta sa a ruwan da ya kawo mata cikin bowl,shi dai kallonta kawai yake har ta gama,ta kalleshi tace "ai dai wannan ya ishemu ni da Hjy ko?" Ya zaro ido yace "ni kuma fa?" Ta kallesa da sauri tace "za kaci ne?" Ya gyad'a mata kai,ta tab'e baki tace "to ai dai zai ishemu har kai" ta zuba mai cikin fry pan ta d'auki albasa tana yankawa tana masa surutu,lokaci d'aya ta saki wani k'ara ta jefar da wuk'ar kafin Waleed ya mata magana jini har ya fara fitowa,ya rik'eta da sauri yace "Ya salaam.. Garin ya ya Kika yanke?" Wajen sink ya matsa da ita ya kunna tap ya tsaya bayanta yana wanke mata hannun yana kallon cut d'in da ba wani babba ba,a hankali yace "sorry lil sis" yana gama wanke mata ya juyo da ita,yaga hawaye a idonta,tuni ya rud'e yana tambayarta "yana miki zafi ne?" Jikinsa ta fad'a ta fashe da kuka tana yarfe hannun,a hankali ya d'ago kanta ya kai fingers d'insa ya share mata hawayen yace "sorry" ta wani shagwab'e masa tace "sai dai kayi frying d'in kai kuma ni bazan yi ba" murmushi yayi ya ci gaba da goge mata hawayen a hankali yace "na ji zauna to ki jira na gama" ya d'agata ya d'ora saman kitchen island,ya juya ya kallo man da yayi zafi yace "toh ya za'ayi yanzu?" Wani dariya ta fashe da shi tace "baka sani ba Yaya?" Ya bud'a hannu alamar bai sani ba,ta kallesa tana masa murmushi tace "ka wanke dankalin ya tsane tukun" ya juya da sauri yayi yadda tace,ya sake kallonta yace "sai me?" Dariya ta dunga yi kafin ta gwada masa yadda zaiyi,yana kallonta fuskarsa a d'aure yace "kema fa ba girkin kiki iya ba amma kike min dariya" tayi murmushi tace "kaji Yaya wanda kake sawa nayi maka fa?" Ya tab'e baki yace "ci kawai nake amma ba wani dad'i" zaro idanu tayi tace "haka ma za kace?" Da sauri yace "nope! Ba haka nake son cewa ba,sub'utar baki nayi" ta gyad'a kai tace "gobe ma ai rana ce" yayi dariya daga haka ya koma gurin fry pan d'in albasan har ya yi ja,ya kwashe ya zuba dankali ciki,tana zaune tana kallonsa idan yayi ba dai² ba tace ba haka ba,a haka har ya gama ya juya zai ajiye bowl d'in a sink,ta kallesa tace "saura eggs to" ya zaro ido yace "idan ya k'one fa?" Tayi dariya tace "i'll help bazai k'one ba" yayi murmushi a hankali yace "okay" ya d'ebo eggs cikin few minutes yayi chopping onion ya soya musu,duk tana zaune tana kallonsa tana masa dariya,yana gamawa ya juyo yana mata murmushi yace "yeah! I can cook now ba tare da an koya min ba" dariya ta dunga yi tace "kai Yaya it's just potatoes fa and egg kad'ai kayi kake wani zuzutawa" ya cire apron d'in data d'aura masa ya k'arasa inda take ya jingina kusa da ita a hankali yace "I'm happy! U teach me how to cook something" ita dai bata ce komai ba sai dariyar da take masa,a hankali ya sauke numfashi yana shak'ar k'amshinta mai dad'i,jikinsa a mugun mace saboda closeness da suka samu yaji ya fara saukar masa kasala da sauri ya d'an yi taking steps d'insa backward yace "sakko ki je parlor zan kawo breakfast d'in yanzu" ta gyad'a masa kai tace "sauke ni to" yana sauketa k'asa ta nufi k'ofa ya bita da kallo har ta fita,ya dauk'i flask d'in ruwan zafin ya d'aukar musu cups da spoon ya fita parlon,ya ganta ita kad'ai ya kalleta yace "Hjy fa?" Tace "tana salatudh-dhuha" yayi murmushi yana kallo agogo ganin 11am ya ajiye flask d'in hannunsa,then ya koma ya d'auko plate d'in dankalin ya ajiye,ya d'aga kansa ya kalli stairs kafin ya tashi ya nufi sama Manar ta bisa da kallo ta tab'e baki ta d'auke kai,Afiyah tana d'akinta tana waya da Mummy'nta ta sanar mata duk abunda ya
Chapter 76 · 0% Book details