← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 184

Sashe 146

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ka ci?" D'an murmushi yayi yace "idan kin bani ba" da sauri ta d'auki d'ayan ta mik'a masa tace "ungo kaci tou" girgiza mata kai yayi yana kallon na hannunta yace "na hannunki nake so" ta kallesa ta kalli gutsiren apple d'in hannunta tace "tou ai na cinye wannan" yace "a haka nace sonsa idan baza a bani ba kuma shi kenan na hak'ura" tayi murmushi tace "zan ba ka ai" yace "ba ni tou" mik'a masa sauran tayi tana kallonsa yasa bakinsa ya gutsira dai² inda tasa bakinta then ya mayar mata abunta yace "na gode" tayi dariya tace "tou ka cinya mana ai na bar maka" yace "noo! Karb'i abunki na gode" ta amsa ta ci gaba da cin abunta,shi kuma ya tada mota suka ci gaba da tafiya,a hanya ya kalleta yace "it's better muje gida mu gaida su,kusan 3 month bamu lek'a ba" tace "ai kaine baka ce muje ba,kuma da ba haka kake yi ba" yayi murmushi yace "ya ya nake yi da?" Tace "kullum fa sai ka je,yanzu kuwa ko maganar ma ni bana jin kana yi" yace "da d'inma akwai abunda yake kaini,yanzu kuma abun yana tare da ni shisa ba na zuwa" ta kalleshi tace "mene ne abun?" Yace "baki sani ba?" Tace "ehh!" Ya gyad'a mata kai yace "lallai! Sai dai ki biyani idan kina son ji" tace "tou ni me zan ba ka?" Yace "ke kike da abun bayarwa kuwa" ta dunda kallonsa sai kuma tayi dariya tace "ni dai ka fad'a min tou" yace "da saboda ke nake zuwa yanzu kuma tunda ina tare da ke shisa ba na jin son zuwa" wani k'ayataccen murmushi tayi tace "Mmm! Dama ba gurin Hjy Siyama kake zuwa ba?" Ya girgiza mata kai yace "kawai dai ina shiga mu gaisa amma ni ba gurinta nake zuwa ba" suna hiran ya tsaya wani eatry yace "ina zuwa Madam" tace "uhn!" Ya bud'e motar ya fita,ya d'an jima kafin ya dawo da leda a hannunsa ta kalleshi tace "me ka siyo?" Yace "ba naki bane Hjy" tana jin ya ce haka ta b'ata rai tace "tou nima ai bance nawa bane" ta murgud'a masa baki,d'an murmushi yayi ya tada motar suka bar gurin,har suka k'arasa gidan ko ya yi mata magana ba ta kulasa,yayi murmushi yace "za kiyi bayani idan na kamaki" ta d'auke kai,yana yin parking ta bud'e motar ta fita,bata tsayasa ba ta wuce b'angaren Dadda,a baya ya biyota da ledan a hannunsa,tana jin footsteps d'insa tak'i tsayawa,ta bud'e k'ofar apartment d'in tayi sallama,Dadda na zaune kan dadduma tana lazimi ta juya tace "eheemm!" Manar ta shiga ta zauna kan kujera ta cire hijab d'in jikinta,Waleed ya shigo yana kallon Manar da tayi kicin² ya zauna kusa da ita yace "wai fad'a muka yi kike fushi?" Tace "ohhoo! Nima ban sani ba" yace "tou kiyi hak'uri kina son gani na nuna miki?" Tace "ba na so" fuskarta a d'aure,yayi k'asa da muryarsa yace "please mana" k'in kulasa tayi ya juya ya kalli Dadda,ita kam lazuminta take bata kullesu ba,a hankali yace "i wish we were at home,so i could do some terrible things to u" kallonsa ta dunga yi ta kasa d'auke idanuwanta akansa,ya k'ara k'asa da kansa yana shinshinota yace "if u don’t stop looking at me like that,we’re going to to have to go somewhere private" saurin d'auke kai tayi tana kallon Dadda ta zumb'uro baki tace "tou wai baza ki gama lazumin ba sai mun tafi?" Dadda ta sake cewa "eheemm!" Manar ta kalleta kawai ta mik'e ta d'auki hijab d'inta tace "sai an jima" tayi hanyar fita,Dadda na mata alamar ta tsaya tak'i tayi ficewarta,Waleed yayi murmushi yace "bari muje za mu dawo" ta gyad'a masa kai,yabi Manar da sauri yana fita ya ganta har taje balcony d'insu ya biyota,da sallama ta shiga parlon mother na zaune tana waya da Daddy ta amsa musu,suka k'arasa parlon Manar ta matsa jikinta ta zauna tana murmushi,Waleed ya zauna wani kujeran daban,har mother ta gama waya da fara'arta tace "kune da wannan lokacin?" Waleed yace "ehh! Mother,ina wuni?" Ta amsa sai kallonsu take yanda suka kara k'iba gwanin sha'awa,hakan ya tabbatar mata hankalinsu a kwance yake,Manar ta gaisheta ta amsa tana kallon yanda ta zama kamar wanda aka hurawa iska,sun d'an jima a part d'in suna hira a nan suka yi sallar ishaa sukayi dinner kafin suka mata sallama suka fita,suka shiga gidansu after sun gaisa da Aunty da Abba,Deejah ta sauko har k'asan suka gaisa ya tambayeta Diyanah tace tana bacci,yace tun yanzu? Tayi murmushi bata ce komai ba,suka fita suka je b'angaren Dadda,sun jima sosai suna hira a can,tace da tuni gobe za tazo gidan nasu tana ta cewa za a kaita ma ta dubasu Abba ya hanata yace yaushe ma duka suka bar gidan,sai kuma ga su ma sun zo,Waleed yayi murmushi tabbas badan Abba da ya hanata ba da ta je musu,sai guraren 10pm suka mata sallama suka fito,suna tafiya a hanya motar ya yi shiru Manar ta d'an zuba masa idanuwanta,yana driving yace "wannan kallon fa?" Tace "i want to talk to u" yace "uhn! Ya akayi?" Tace "maganar yana da muhimmanci mu bari muje gida" yace "alright.." Sanda suka k'arasa gida yayi horn get keeper ya bud'e masa yana musu barka da dawowa,ya shiga yana amsa masa ya masa sai da safe,yayi parking k'asan tent ya fito ya bud'e mata ta fito,ya d'auko mata ledan apples d'inta suka wuce ciki,bayan sun yi wanka sun fito ta fara masa maganar yace ta bari ba yanzu ba ta huta,duk yanda taso ta masa maganar k'in bata chance yayi,sanda suka zo kwanciya,dukansu sunyi shiru suna kallon juna tace "Yaya!" Yace "uhn!" Tace "maganar d'azu" yana jin ta ce haka yace "wai wannan wane magana ne kika damu da shi haka?" Tace "ni dai ka bari na fad'a maka ka ji?" Ba don ya so ba yace "uhn! What's it?" Shiru tayi tana tunanin yanda za ta bijiro masa da maganar,ya d'ago kansa ya kalleta yace "kin fasa fad'a ne?" Tace "a'a" yace "uhn! What happened?" Tace "Mmm! Dama maganar Mama ne nake son maka" kallonta ya dunga yi da idanuwansa yana squeezing fuskarsa yace "wace Mama?" Tace "Mama dai" ya tab'e baki yana b'ata rai yace "kinga ni ban san me kike cewa ba ki barmu muyi bacci" tace "amma Yaya.." Yace "shhhiii!" Ya d'ora hannunsa akan lips d'inta da wani murya yace "just keep quiet.. Kiyi bacci maza" ya tokare hannunsa d'aya ya tallafe gefen fuskarsa da shi,yana kallonta ya kai d'ayan hannunsa yana shafa kanta zuwa fuskarta,kamar za tayi kuka tace "Yaya na san ka gane abunda nake nufi fa" yace "uhn! Cewa nayi ki min shiru kiyi bacci" hawaye suka fara kawowa idanuwanta tace "me yasa ba ka son maganar?" Yace "please kimin shiru haka" still bata gaji ba tace "ka fad'a min mesa ba ka son na maka maganar,can't u think ita ta haifeka? Ko me tayi bai kamata ka mata haka ba,bai kamata kak'i zuwa ka dubata ba,me yasa za kayi haka Yaya?" Kallonta ya dunga yi ya kasa mata magana,tace "please ba dan ni ba kaje ka dubata,about 5 month fa ake magana amma ko waya baka mata,why?³" Ta k'arasa da wani murya mai cike da rauni,k'wafa yayi kawai ya juya ya sauka daga gadon ya nufi k'ofa,ta tashi ta zauna ta fashe da wani kuka tace "yanzu ko ni nayi wani laifin za ka iya juya min baya kenan?" Cak ya tsaya a gurin idanunwansa a kulle yana ta calming kansa..
Chapter 146 · 0% Book details