← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 184

Sashe 79

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwantar da kansa yayi jikin kujeran yana kallon Manar,a hankali yace "yaushe za kizo hutun?" Ta kallesa da sauri tace "waye zaizo hutu?" Yace "ke mana ko kin fasa?" Da sauri ta gyad'a masa kai tace "tabb' d'i yauma kana ganin yanda na wuni bare naje hutu gidanka?" Yace "idan kinje sai ki dunga rakani office" murmushi tayi tace "ni dai a'a ba sai na je ba" yace "why?" Tace "Yaya kana kallo fa matar ka ba ta so na" yace "kema ai kin fad'a min bakya sonta" ta d'aure fuskarta tace "to dama why would i love her? Baka ga irin kallon da take min bama" ya dunga kallonta yana sakin murmushi a hankali yace "so yanzun kin fasa zuwa kenan?" Ta gyad'a masa kai tace "yeah! Idan ka zo gida ai za ka ganni" yace "to girki fa waye zaina min?" Kallon idonsa tayi yanda yayi kamar wani maraya tace "ga matarka nan" yace "bata iya ba wai" dariya ta dunga masa tace "sai ka d'auko muku maids suna yi" ya girgirza kansa yace "ba na son abincin maids" tace "to sai na wa kake so?" Wani kallo yake mata k'asa² a hankali yace "na ki nake so" tayi murmushi tace "to ai idan ka zo zan dunga yi maka" ya lumshe idanunsa a hankali yace "nope! Sai dai ki dawo gida na kina yi min" tace "tabb' ni dai ba zan je ba,ni fa daga yau bazan k'ara zuwa ba ma" kallonta ya dunga yi a hankali yace "saboda me?" Tace "matar ka" tana fad'an haka ta bud'e motar za ta fita yace "wait.." ta juya tana kallonsa tace "what?" Ya sauke wani ajiyar zuciya a hankali yace "I love u" dariya tayi sosai tace "love u too Yayana" murmushin jin dad'i yayi yace "really?" Ta gyad'a masa kai,yana kallon eyeballs d'inta yace "will u marry me?" Zaro ido tayi tace "Yaya.." ya rik'o hannunta da sauri yace "shhhiii.. Tell me please za ki iya aure na?" Girgirza masa kai tayi alamun a'a,yace "why not?" Tace "kai ai Yaya na ne,besides kuma ni Yaya Azaan nake so.." Bai bari ta kai k'arshe ba yace "yeah! I knew shi kike so,but what about me? Ba kya so na baza ki iya aure na ba?" Rau² idanunta suka yi,muryarta yana cracking tace "kai fa Yaya na ne" yace "shi Yaya ba'a aurensa?" Ta gyad'a masa kai da sauri tace "ehh" murmushin takaici yayi yace "alright! Je ki gida za mu k'arasa maganar a waya" tace "toh" ta fita motar ta rufe masa,yana kallonta jikinsa a mugun sanyaye yace "bye" ta d'aga masa hannu ta wuce part d'in Dadda,yana tsaye sai da yaga shigarta gidan then ya juya kan motarsa ya bar gidan. Sanda ta shiga gidan da Dadda ta fara had'uwa tsaye a parlor,tayi sallama za ta wuce Dadda ta bita da ido tace "ina kuma kika tsaya ina ta tsumanki?" Tace "Yaya ne ya tsayar da ni" Dadda tayi mitsi² da ido tana kallonta tace "ince dai bai maki komai ba?" Manar ta kalleta tace "kamar ya?" Dadda tace "ina nufin bai matseki irin na d'azu a gidansa ba?" Wani kallo ta mata ta wuce d'aki k'asa² tace "me yasa baki tsaya kin gani ba za kina tambayata" tayi shigewarta tana turo baki,kayanta ta fara ragewa ta d'aura towel ta shiga wanka,tun tana ciki take jin ring d'in wayarta,sanda ta gama ta fito ta d'auki wayar tana dubawa,taga mafi yawan kiran ma Waleed ne sai na Azaan,tayi murmushi kafin ta fara kiran Waleed,yana ganin call d'inta ya katse ya kirata video dan gaba d'aya kalamanta sun sanyayar masa da jiki,kiran yana connecting yayi ajiyar zuciya a hankali yana kallonta yace "thought kiran nawa ma baza'a k'ara d'auka ba" tace "why not?" Yace "na sani tunda ance ba'a so na hakan yasa an yanke hukuncin dai na min magana" murmushi tayi kawai bata amsa ba,yana kallonta yace "wanka kika yi ne?" Ta kalli jikinta a hankali ta gyad'a masa kai tace "ehh" yace "okay! Bari na kyaleki ki shirya ko?" A hankali tace "toh" yana mata wani kallo yace "za ki min flash idan kin gama?" Tace "ehh" yace "okay! Thanks" suna ajiye wayar kiran Azaan yana sake shigowa,ta d'auka da sauri tace "Yaya!" Yace "My Guddi! How are u?" Tayi ajiyar zuciya tace "i'm fine,u?" Yace "alhamdulillah! But not feeling good" a rikice tace "Yaya me yake damunka?" A hankali yace "kece kike damuna" tace "ni kuma?" Yace "sure" kamar za tayi kuka tace "ni to me nayi maka?" Yace "kin hana zuciyana nutsuwa" wani ajiyar zuciya tayi tace "thought ma wani abun za kace na yi maka" yace "shi wannan ba wani abu bane?" Tace "ehh" yace "really?" Tace "yeah" yace "ke dai kika d'auka haka" tace "ai kowa ma haka zai d'auka" wani murmushi yayi yace "okay! Let's back to serious" tace "uhn" yace "Mujse shaadi karoge? (Will u marry me?)" Da wani irin zumud'i tace "yes³" yayi murmushi yace "really?" Tace "absolutely sure" yace "thank u Guddi,saboda amsan da kika ba ni yanzun nan har na ji ina son zuwa Nigeria na ganki" tace "nima haka" yace "okay! Ki kwanta kiyi bacci,da safe za muyi waya" tace "toh" yace "goodnight love" tace "goodnight.." Tun suna waya kiran Waleed yake shigowa,tana k'ok'arin ajiye wayar wani kiran ya sake shigowa ta d'auka kafin ma tayi magana yace "thank u!" Fad'uwa gabanta yayi tace "me nayi Yaya?" A fusace yace "meye ne ma baki yi ba,saboda kin raina ni ni zan dunga kiraki k'i d'aukan wayana,ko da yake kina waya da wanda kike so ya za'ayi ki saurare ni" yadda yake mata magana cikin fad'a nan da nan hawaye suka kawo idonta,bai saurareta ba yace "shi kenan kiyi yadda kike so zan kyaleki.. Dama na takura maki ko?" Ta girgirza masa kai kamar tana gabansa,kafin tayi magana yace "thank u.. Goodnight" tana shirin yi masa magana k'it ya katse wayarsa,tun daga ranar ko a mafarki bai k'ara kiranta ba,idan ya shigo gidan ma ba ya yarda ta gansa,duk hanyar da yasan zai had'asu duka ya toshe su,ko gaishe da Dadda idan zai zo sai ya daidaici lokacin da ba ta nan zai shigo,kafin ta dawo ya fice abunsa,tun abun bai damunta har dai ta fara shiga damuwa,idan ta kirasa a waya ba ta samunsa yanzun,ko chat ma bata ganinsa,haka nan idan ta tura masa sak'o zai nuna mata ya tafi amma ba ta gane ya gani ko bai gani ba. Shi kam a nasa b'angaren yana sane yayi mata hakan,dan ya gwadata yaga da gasken ba ta sonsa ko kuwa dai fad'a masa hakan kawai take yi,duk hanyar da yasan zai had'a su gaba d'aya ya rufeta,ba iya chat da ya danna mata block ba,hatta contact d'inta ya sa number ta blacklist,shisa ko ta kirasa ba ta samu,text ne kad'ai idan ta masa via inbox ko tayi mailing nasa yana ganin wannan but ba ya tsayawa ba ta amsa,ana cikin hakan tafiya ya taso masa zuwa India zai je wani course,ranar da zai tafi ya zo gidan suka yi sallama da mutanen gidan a lokacin suna skul,ya gama abunda zai yi Amaar ya kaisu airport shi da Afiyah,though bai yi niyyar zuwa ko ina da ita ba,Mama ta takura masa lallai sai ya tafi da ita tunda ba kwana kusa zai dawo ba,haka nan babu yadda zai yi ya shirya musu tafiya tare,daga bayan ne Manar ta samu labarin ba ya nan,tayi kuka sosai lokacin ta shiga damuwa dan har wani k'aramar jinya tayi,bayan nan kuma ta share komai ta ci gaba da harkokin gabanta,shi kam Waleed sanda suka sauka India a New Delhi suka ya da zango,da suka yi waya da Mommella yake sanar mata suna k'asar ta so sun sauka gurinta so sai akayi rashin sa'a kuma tsakaninsu akwai d'an nisa,hakan yasa dole suka nemi matsuguni nan tunda ita tana yankin vishakpatnam ne,but lokaci² yana Yana zuwa ya kai mata ziyara. Some years later aka fara shirye²n saukan su Manar had'e da graduations d'insu,during this period soyayya mai zafi suke yi da Azaan amma ta waya,gaba d'aya yanzun ba sosai yake zuwa ba,dan kusan tun bayan tafiyar Waleed bai fi sau biyu yazo ba,ta rasa me yasa sai dai suyi chat ko waya ma yanzun sai su d'auki tsayin lokaci basu ji muryar juna ba,while a gefe d'aya kullum zancensa shi dai ji yake kamar ya jawo kwanakin da suka yi saura,though bai fi 3 month ya rage su fara exam d'in waec ba,idan sako zai bayar a kawo mata kuwa dama ta hannun Amaar yake zuwa gareta,ranan wata Sunday ya kama saura sati biyu saukarsu,ranan kuma ya kama 2 and ½ years da tafiyar Waleed India wanda ake saka ran dawowarsa cikin satin,around 4pm suka sauka Nigeria,Amaar kad'ai ya sanar ma yace kada ya fad'awa kowa suna hanya,Amaar ya tura driver yaje d'auko su a airport ya masa gargad'in kada ya fad'awa kowa,ba tare da ya fad'a ba ya d'auki mota ya nufi airport,sanda motar su ya shigo gidan,uban sun lace ne jikin Afiyah sai mayafi da ta sak'ale a wuya hannunta rik'e da handbag sai takalmi mai tsini da ta sa,ta yi kyau har ta gaji,sai k'amshi take bazawa Kamar dai ba itace idan kaje d'akinta za ka gansa kaca² ba,fuskar nan nata ya sha make-up har ba a cewa komai,motar yana yin parking Waleed dake sanye da 3 piece men's suit kalar green mai duhu ya fito,part d'insu ya nufa direct tana biye da shi a baya,su a shiga da ihu Deejah da Diyanah suka tare su,suka yi welcoming d'inta da fara'a ta amsa masu da siririyar muryarta tana murmushi,Ameerah dake shigowa lokacin ta gaishesu ta tafi sama ta kira Aunty,Aunty na sakkowa tace "a'a su Aunty amarya ne a k'asar namu,sannu da zuwa" Afiyah ta kalleta tace "yauwa.." Aunty ta zauna tace "fatan kun dawo lafiya? " Afiyah tace "lafiya lau,ya gida?" Aunty tace "Alhamdulillah,ya hanya?" Afiyah tace "lafiya lau" Aunty tace "maa sha Allah.." Waleed dai sai kallon Afiyah yake jin bata gaisheta ba,bai ce komai ba ya kalli Aunty yace "Abba fa?" Aunty tace "tun safe ya fita" ya mik'e yace "okay! Bari mu gaida Hjy" Aunty tace "toh sai kun dawo" yace "Daddy fa ya dawo?" Aunty tace "a'a
Chapter 79 · 0% Book details