Sashe 45
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aunty tana gama fad'a masa haka ta juya ta fita cike da jimamin hali irin na Hjy Asama'u,Mama da ta rakata da mugun kallo tayi tsaki ta juya ta kalli inda yake durk'ushe har lokacin cikin rashin tabbas,da kakkausar murya tace "ina fatan ka ji duk maganganuna kuma ka haddace su,kada kayi zaton wasa nake maka,ya zama dole ka rik'e shi a cikin kanka.. Idan har ni na haifeka ba kai ka haifi kanka ba laazim kayi min biyayya.. If not kuma ga fili ga mai doki,ni da kai zan ga wanda zai yi nasara" tana gama fad'a itama ta juya a fusace ta fice had'e da banging masa k'ofar,runtse idanunsa yayi da k'arfi,gaba d'aya ji yake duniyar ta masa zafi,he only wish mafarki yayi duka maganganunta yana farkawa ya fad'a mata tace ta amince,sanda ya bud'e birkitattun idanunsa ya sake tabbatarwa kansa da gaske al'amarin ya faru,da kyar ya d'ago hannuwansa ya rufe fuskarsa da su,ya shafe ak'alla mintuna talatin zaune a gurin ba tare da ya iya motsin kirki ba bare ya san abunda ya kamata yayi,sanda yaji bud'e k'ofarta yayi k'arfin hali ya tashi ko gabansa ba ya iya gani ya nufi hanyar fita daga d'akin. Aunty kam sanda ta fita ta barsu bedroom d'inta ta koma ta zauna bakin gado ta yi shiru tana maimaita kalmar "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" ganin komai take kamar almara,ita gaba d'aya ma bata gane me yake faruwa ba lokacin,Ameerah da ta gani tsaye bakin k'ofa tare da Waleed yana mata magana shi ne dalilin da yasa ko da ta hauro saman tabi bayansa d'akin Hjy Asama'u da taga ya shiga taji me yake faruwa,ko Ameerah ta masa wani laifin ne bai hukuntata ba ya rabu da ita a iya fad'a dan bata ji me suke cewa ba,bisa tsautsayi kuma ko da ta bud'e k'ofar bata kai ga shiga ciki ba ma sai ta tarar da maganar Maman wanda ya ainihin girgiza ta,tsayin lokaci suke zaune gidan suke hak'uri da ita da halinta,duk adadin k'iyayyarta garesu da bata iya b'oyewa ita ko Mother basu tab'a damuwa ba sun fi zaton kishi ke damunta,ashe ita abun dake ranta daban kawai ana zama ne a babu yadda za'ayi, amma ta ciki na ciki,cikin wannan halin Amaar ya turo k'ofar ya shigo da sallama a bakinsa,tsabar yadda tayi zurfi cikin tunani bata ma san ya shigo ba,ya k'arasa kusa da ita ya zauna sanda ya rik'o hannunta cikin nasa ta sauke wani gauron numfashi,a hankali yace "Aunty wani abu ya faru?" K'uri tayi masa da ido ta kasa ce masa komai,hankalin Amaar ya fara tashi ganin yadda take kallonsa tashin hankali kwance k'an fuskarta,a firgice ya jijjigata yace "Aunty please tell me what happened? Me aka miki naga kamar hankalinki a tashe? And yanzun na ga Waleed na yi masa magana bai saurare ni ba ya wuce,na ga kamar kuka yake or something like this,ban dai tantance me yake damunsa ba dan bai ma tsaya ba bare ya kula ni.." Girgiza masa kai Aunty tayi tana sauke wani heavy ajiyar zuciya ta sanar masa kaf abunda ya faru,cikin tsananin tashin hankali Amaar ya fara maimaita kalmar "Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun.." Tsayin mintuna suka yi shiru babu mai magana a tsakaninsu sai can da Aunty tayi k'arfin hali tace "Amaar zan rok'e ka wani alfarma" ya gyad'a mata yace "ina ji Aunty" a hankali tace "dan Allah ba don ni ba,kamar yadda muka san maganar nan daga ni sai kai,ina rok'onka ka binnesa a zuciyarka,kada ka bari wani mahaluki a cikin gidan nan ya sani.. Musamman kakarku,na tabbatar taji maganar za ta tada rikici a gidan nan,please Amaar ba don ni ba.." Gyad'a mata kai yayi yace "in sha Allah Aunty babu wanda zai sani,na yi miki alk'awari" ta sauke numfashi tana gyad'a masa kai tace "thank u" shiru yayi ya dunga binta da kallo gaba d'aya ita kanta tausayi take bashi yadda yaga ta damu,ina kuma ga Mother idan ta ji? Ita kanta Manar da ba ta da laifin komai cikin abubuwan da suka faru me yasa za'a k'i ta har haka? Shi duk bai tab'a ganin inda laifin wani ya shafi wani ba sai a gurin Mama ita ce kawai ya tab'a ji a tarihi ta k'i wani babu dalili,tabbas ba don ya san Azaan yana son Manar ba,shi a kan kansa baiga dalilin da zai hana baice yana son manar ba,ya jima a d'akin yana kwatarmata hankali kafin ya tashi ya fita yana mai tausayawa d'an uwansa da yake cikin tsaka mai wuyar fita. A b'angaren Waleed kuwa yana fita ya nufi parking space,sanda yake k'ok'arin bud'e motarsa a niyyarsa na barin gidan,yana laluba aljihunsa ya nemi keys d'insa a tare da shi ya rasa,ya waiga yaga ko a hanya ya yar da su amma bai gansu ba,akan ya koma cikin gidan ya duba dan ya fi kyautata zaton a d'akin Mama ya yar da su kawai ya gwammace ya wuce gidan Dadda,sanda ya shiga bai tarar da kowa a parlon ba,ya kwanta kan kujera ya rufe idanunsa,a hankali komai da ya faru ya dunga dawo masa fresh,sai a lokacin yaji zuciyarsa ta karye abunda bai tab'a yi ba tsayin rayuwarsa a hankali yake kuka mara sauti,hawaye suna kwaranyowa daga idanunsa,Manar da zuwa lokacin ta gama gyara jikinta saboda zuwan period d'inta ta fito parlon a niyyarta ta kulle part d'in kasancewar ba'a jima ba Dadda ta fita unguwa y'ar gidan Tasallah k'awarta ta haihu,ta fito rik'e da keys a hannunta tana wasa da su ta gansa kwance kan kujera,ta harari inda yake ta zumb'uro masa baki,har ta d'auke kanta saboda haushin fad'an da ya mata babu jimawa,sai kuma idanunta suka hango mata kamar dai wani abu yana faruwa,da sauri ta sake kallon inda yake kwance,shi kam ko kula da ita ma bai yi ba,ganinsa yana wani irin kuka mai shiga zuciya though babu sauti hawaye kad'ai suke zubowa ta mugun tsorata ta zaro idanu cikin firgici,tsayin rayuwarta da shi bata tab'a ganinsa a irin yanayin ba,da gudu ta k'arasa tana kiransa "Yaya!" Ta tsuguna gabansa da fuskar kuka ta kai hannunta saman fuskarsa tana goge masa hawaye bata san sanda ita kanta ta kece da wani kuka ba,jin sauntinta da k'amshinta a kusa da shi ya sashi zabura ya d'ago yana kallon yadda take kuka ba tare da sanin dalilin kukansa ba,da sauri ya kai hannu ya k'arasa goge hawayensa yana kallonta cike da dauriya yace "me kike ma kuka?" Girgiza masa kai tayi alamun bata sani ba,ya zuba mata jajayen idanunsa yace "tambayarki nake!" Da muryar kuka tace "Yaya nima ban sani ba,gani nayi kawai kana kuka" saurin rik'ota yayi ya zaunar da ita kusa da shi ya kama hannuwanta duka biyu ya k'ank'ame kamar wani zai kwace masa ita,ajiyar zuciya suka dunga saukewa a tare,sai da suka samu nutsuwa kafin da wani murya mai cike da rashin hope yace "Baby kina so na?" Da sauri ta gyad'a masa kai,hawaye suna sake zubowa idonta tace "Ina sonka Yaya,kaima kana so na?" Wani murmushi yayi hawaye sun cika masa ido yace "yeah! I do" b'ata rai tayi saurin yi tana masa wani kallo a shagwab'e tace "me kace?" Bai san sanda murmushi ya kufce masa ba ya zuba mata idanunsa yana kallonta da wani sanyayyan murya yace "ina son ki Baby" murmushin ta mayar masa,yayi shiru sai kallonta yake a hankali ya kai hannunsa ya goge mata guntayen hawayen da suke fuskarta yace "Baby!" Da sauri ta kalleshi bata amsa ba,d'an shiru yayi da farkon kafin ya bud'e bakinsa da kyar yace "ina da muhimmanci a gurinki?" Tace "ehh Yaya" yace "duk abunda nace za ki iya yi min?" Da sauri ta sake cewa "ehh!" Yayi shiru kamar yana tunani kafin yace "da gaske duk abunda nace za kiyi?" Ta gyad'a masa kai cike da tabbatarwa idanunta a kansa,ya sauke numfashi yace "za ki iya killacemin kanki?" Squeezing fuskarta tayi bata gane me yake nufi ba tace "Yaya me kake nufi?" Yayi shiru kamar kada ya fad'a mata because bai san a yadda za ta fahimci maganar ba,and bai ma sani ba ko za ta fad'awa wani,sai da yaji ta d'an girgiza shoulder sa kafin ya dawo hayyacinsa,ta d'aga masa gira tace "mene ne?" Yace "Arhhmm!" Kamar zai fad'a mata kuma sai yace "barshi ma kawai,nan gaba zan fad'a miki" shagwab'e fuskarta tayi kamar za tayi kuka da sauri ya rik'o fuskarta yana girgiza mata kai yace "don't cry.." Sosai tayi fuskar kuka tace "ni sai ka fad'amin abunda kayi niyya" murmushi yayi yana kallon yadda lips d'inta suke fitar da words d'in a nutse ya zuba musu ido yana jin wani abu yana taso masa,waving hannunta tayi a dai² fuskarsa yayi saurin kallonta yana sauke numfashi,ta b'ata rai tace "baka fad'a ba fa" gaba d'aya ya rikice yace "me?" Tace "baka ce komai ba kana ta kallona" girgiza mata kai yayi ya lumshe idanunsa,ta sake tab'a shi fuskarta a had'e tace "ni idan baza ka fad'a na tafi" wani kallo ya mata da har cikin jikinta sai da ta jishi ya mayar da idanunsa ya kulle yace "ina za kije?" Tace "gurin Ameerah za ni,ba zan iya zaunawa ni kad'ai ba" ido d'aya ya bud'e ya kalleta yace "ni aljani ne ko cinye ki zanyi idan kin zauna?" Dariya ta fara masa ya bud'e idanunsa duka ya zuba mata su fuskarsa a d'aure,just in time ta shiga taitayinta,ya girgiza kansa yace "to na sani ko ni ba mutum bane da kike cewa ke kad'ai" d'auke kanta tayi tace "ni dai tafiya zanyi tunda baza ka fad'a ba" yace "me zan fad'a?" Tace "maganar d'azu daka fara" squeezing fuskarsa yayi yace "nace me?" Wani kallo ta dunga binsa da shi ta kasa masa magana,sai da ya tab'ata tayi kicin² za ta matsa daga kusa da shi ya rik'o hannunta,ta kalleshi ta kalli hannunsu da ya sark'e fingers d'insa cikin nata,a hankali yace "don't go.. Stay with me please" b'ata rai tayi tace "ni ka daina min turanci" yayi murmushi yana kallon yadda tayi yace "mene ne matsalarki?" Ta kalleshi tace "haka kace?" Wani dariyar da bai tab'a irinsa ba yayi ta dunga kallonsa ganin how cute he is da yana dariyan,sanda ya daina ta turb'une fuskarta tace "Yaya ka ci gaba"