← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 158 OF 184

Sashe 158

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Musamman hannunsa da yake d'auke da jaririn da bai ma san me yake faruwa ba,ya nuna ma Diyanah gurin zama saman luntsuma²n royal chairs da akayi decorating parlon yace "zauna Halimatu" Diyanah ta zauna jikinta a sanyaye tana kallon Hjy Aisha ta gaisheta,cikin tsananin tashin hankali,b'acin rai,bak'in kishi gami da rufewar idanu,ba tare da Hjy Aisha ta tsaya bin ta kan Diyanah ba bare ta amsa gaisuwar da take mata,hankalinta kaf a kan mijinta uban y'ay'anta tace "me zan gani haka Alh? Wace ce wannan d'in ka shigo min da ita cikin gidana? Yaron waye a hannunka kuma?" Kallonta kawai Alh Baffanyo yayi ya girgiza kansa,sanin halinta yasa baima tsaya ba ta amsa ba,sai tambayar da ya watso mata yace "ina yaronki?" Hjy Aisha ta bud'a idanu tace "ban gane ba,me wa kake nufi?" Strictly yace "Fahad!" Wani zazzaro idanu tayi kamar za su fita daga socket d'insu tace "me Fahad zai maka?" Alh Baffanyo yace "ina buk'atar ganinsa,duk inda yake kice masa yazo yanzun ya sameni,kada ya b'ata min lokaci" Hjy Aisha dai sai kallon mijin nata take baki sake ta kasa gane kan yanda al'amarin yake,Alh Baffanyo ya zauna saman luntsuma²n royal chairs da suka zagaye parlon,a nutse ba tare da ya sake bin takan irin kallon tuhumar da Hjy Aisha take masa ba ya d'ago jaririn hannunsa ya fara masa khud'uba da addu'o'i,Hjy Aisha ganin bai ce mata komai ba lokaci d'aya ta d'auki waya ta kira d'an nasu,cikin muryar ba da umarni tace "Fahad! Duk inda kake maza kazo gida yanzun mahaifinku yana nemanka.." Basu ji me yace ba,tace "yanzu!" Ta k'ara fad'a then ta katse kiran tana fesar da wani hucin b'acin rai,almost 20 minutes matashin saurayin mai d'an duhun fata,dogo kyakykyawa wanda bazai wuce sa'an Amaar ba,ya shigo ransa kamar a b'ace yayi sallama a ciki,yana tafe yana kad'a car keys,Alh Baffanyo ya bisa da kallo sanda ya k'araso cikin parlon ya zauna saman kujeran yana kallon mahaifiyarsa yace "here i'm Mom" Hjy Aisha ta girgiza masa kai har lokaci zuciyarta bata daina kawo mata zarge² ba,a d'an fusace tace "ka ji na ce maka ni nake kiranka?" Tab'e baki yayi then ya d'an waiga,zai yi magana idanuwansa suka sauka kan Diyanah dake kallonsa,da sauri ya zabura ya mik'e yana k'ara kallonta da idanuwansa da suke a zazzare yace "ke me kike a nan?" K'ala bata ce masa ba ta d'auke kanta,wani tsawa ya mata gaba d'aya yama manta da iyayensa a gurin yace "ba dake nake ba za ki d'auken kai,uban me ya kawo ki gidan mu?" Alh Baffanyo da ya zura masa idanu tun shigowarsa bai ce masa komai ba lokaci d'aya yace "ubanka take yi" saurin kallon mahaifin nasa yayi a d'an dake yace "Daddy!" Da sauri Alh Baffanyo yace "koma ka zauna my friend" fuska babu isashshen walwala,babu shiri ya zauna yana k'unk'uni,Alh Baffanyo ya kalli Diyanah da kanta yake k'asa,then ya kalli d'an nasa,da wani murya ya kira sunansa "Fahad!" Fahad dake kallon Diyanah yana sake² a ransa da sauri yace "na'am" Alh Baffanyo yace "dama ka san Halimatu ne?" D'auke kai Fahad yayi yak'i cewa komai,Alh Baffanyo yace "tambayarka nake kamin shiru?" Da kyar ya gyad'a kai yace "eh Daddy" Alh Baffanyo yace "me ye tsakaninku?" Saurin d'agowa duka su biyu suka yi suna kallon juna,Diyanah ta fara janye idanuwanta daga kansa ta sake sunkuyar da kanta tana share zafafan hawayen da suka kwaranyo mata,Alh Baffanyo ya yiwa d'an nasa tsawa yace "kai nake sauraro yallab'ai" in'ina Fahad ya fara ya kasa magana,Alh Baffanyo ya gyad'a kai ya d'ago masa jaririn da ya d'an rufe da babban rigarsa yace "wannan shi ne abunda ya had'a ku,right?" Da sauri Fahad ya zaro idanuwansa,a tsorace yake kallon yaron yana kuma kallon Diyanah,cikin kid'ima bakinsa yana b'ari,gumi duk ya gama wanke masa fuska yace "mesa za ki min haka Diyanah? Dama baki zubar da cikin ba? So kike asirina ya tonu,ki b'atamin suna da iyayena?" Idanun Hjy Aisha a waje take kallonsu da sauraren abunda yake faruwa,cikin b'arin baki da jiki ta mik'e tsaye hawaye suna zubowa fuskarta tace "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Fahad me kake son fad'a ne? Kana nufin kai kama yarinyar nan ciki ta haifa maka yaro?" Sunkuyar da kansa yayi gumi yana keto masa ta ko ina,duk uban sanyin parlon bai hana rigarsa jik'ewa ba,da kyar ya iya bud'a bakinsa cewa "I'm very sorry Mom,this is not intentional,ba halina kenan ba Mom,but i don't know how hakan ya faru" kuka sosai Hjy Aisha take tana girgiza kai tana maimaita fad'in "allahumma ajirnii fii musibatii wa'aklufnii khairan minha.. Alhamdulillahi alaa kulli haliin" ba k'aramin kid'ima Fahad ya shiga ba ganin yanda take kuka,ya sauka daga kujeran da yake jikinsa a mugun sanyaye ya durk'usa kusa da k'afarta hawayen nadama suna saukowa fuskarsa ya rik'e k'afafuwanta yace "Mom ki yafe min,na san na aikata laifi,but believe me Mom wallahi akanta ne kad'ai haka ya tab'a faruwa,na yi k'ok'arin rik'e kaina da tarbiyyan da kuka min,but i can't na kasa Mom,forgive me Mom bazan sake ba" share fuskarta tayi ta d'ago ta kalli Alh Baffanyo tace "ka ga irin abunda na dunga jin tsoro tun farkon,wannan shi ne dalilin da yasa ko da yaron nan yace aure yake so,na baka shawaran ka masa auren nan gudun faruwar wani matsala,shin yanzu wa gari ya waya? Me za muce ma mutane idan labarin ya baza gari?" Jikin Alh Baffanyo yayi sanyi da maganarta a hankali ya sauke numfashi yana gyad'a kai yace "duk wannan ya riga ya faru,babu wanda yafi k'arfin k'addara ya fad'a masa,sai dai mu tari gaba kuma" Hjy Aisha ta gyad'a kai a hankali tana kallon Diyanah tace "tou yanzu Alh ya ake ciki? Ba dai family'nta sun koreta bane kan wannan abun da ya faru?" Alh Baffanyo ya girgiza kai yace "ko kad'an,sai dai na yanke hukuncin da nima naga ya min dai²" not only Hjy Aisha hatta Fahad sai da ya d'ago kansa yana jiran yaji me Daddyn nasa zai ce,Hjy Aisha tace "wane hukunci ka yanke Alh?" Alh Baffanyo yace "na sa an d'aura musu aure yau d'in nan,saboda mu rufawa kanmu da y'ay'an mu asiri.." Numfashi mai mugun nauyi Hjy Aisha ta sauke tana gyad'a kai cike da gamsuwa tace "maa sha Allah.. Alhamdulillah alaa kulli haliin.. Hakan ya yi sosai.. Allah tsare mu da mummunar k'addara" Alh Baffanyo yace "ameen.." Here ya musu nasiha sosai,itama Hjy Aisha ta musu kafin ta kira maids tasa aka d'auke kayan Diyanah zuwa bedroom d'inta,da kanta ta zo ta karb'i jaririn hannun mijinta tana kallon yaron hawayen tausayi suna zubo mata tace "haka Allah ya k'adarta maka na ka rayuwar.. Allah maka albarka,ya albarkaci rayuwarka.." Fahad dai sai kallon Diyanah yake fuskarsa d'auke da farin cikin wai yau shi ne Daddynsa ya shammata ya yi masa aure,he can't believe al'amarin a gaske yake faruwa,gani yake mafarki ne da ya farka zaiga ba gaskiya bane,kusan shekaru biyar kenan yake ta bin Daddy ya masa aure yak'i yace sai ya yi masters,ya gama ya sake masa maganar yace sai ya yi PhD,after then yace sai ya kama aiki,yanzun haka yana aikin,da ya masa maganar auren yace ya bari sai Yayansa ya yi aure kafin yazo kansa,Allah ma ya sani shi tun tashinsa ya san yana da mugun buk'ata,shisa yayi ta maganar aure²,shi kuma Daddyn ya kasa fahimtarsa,duk sanda ya kalli Yayansa sai yaga kamar baida lafiya ne saboda shi bai wani d'orawa ransa ba,duk abunda Daddyn yace haka yake bi,wani lafiyayyen murmushi ya saki lokacin da Daddyn nasa ya bar parlon,Hjy Aisha dake sakkowa k'asan bayan ta kai Diyanah bedroom d'inta ta kallesa da kyau lokacin da yake mik'ewa fuskarsa d'auke da murmushi zai fita ta kirasa "Fahad!" Da sauri ya waiga yana amsawa,da hannu ta yafitosa tace "zo ka zauna magana nake son yi da kai" babu musu ya dawo ya zauna,nasiha sosai ta sake yi masa mai shiga zuciya akan tsoron Allah da bin dokokinsa,kafin daga k'arshe tace ko da wasa kada ya yarda taji maganar ya fita,tunda anyi komai cikin sirri za su d'ora mutane akan auren sirri yaje yayi ba tare da saninsu ba,ya mata alk'awarin in Allah ya amince bazai fad'awa kowa ba,after then ta sallamesa,da k'arfinsa ya tashi ya fita,babu jimawa ya shigo da uban siyayya nik'i²,tana zaune parlon har lokacin ya shigo,ta d'aga kai ta bisa da kallo cike da tausayin k'addarar da ya fad'a masa. Washe gari da safe suna zaune dining,Yayansa ya fito bedroom d'insa cikin shirin fita office,wani irin fasion men's suit ne a jikinsa mai two piece gray color,ya k'arasa dining ya zauna,sanda ya kalli agogon dake d'aure wrist d'insa a gurguje ya fara cin irish da ketchup sai lafiyayyen tea,yana yi yana danna wayarsa,kukan jaririn da ya karad'e kunnuwansu lokacin yasa Fahad saurin tashi da gudu² yayi sama,da kallo Dr Mahfouz ya bisa yana ajiye fork d'in hannunsa,mamaki ya sashi kasa magana sai kallon hanyar da k'anin nasa ya bi yake,Hjy Aisha ta mik'e ta nufi sama itama,dai² lokacin Fahad ya sauko d'auke da jaririn da Alh Baffanyo ya sama sunansa tun jiyan,yana d'an jijjigasa yana hura masa iska a kunne,Dr Mahfouz dai yayi still ya kasa ci gaba da abunda yake gabansa,sanda Fahad ya wuce parlor da yaronsa,da kyar Dr Mahfouz yayi gathering courage yace "ina muka samu jariri kuma? Afreen sun zo k'asar ne?" Girgiza masa kai Fahad yayi yace "not at all" ya mik'a hannunsa ya karb'i yaron da yayi shiru ya zuba masa idanuwansa,at the same time yana k'ara tambayar Fahad yace "munyi bak'i ne?" Murmushi Fahad yayi yace "a'a" mamaki dai ya k'ara sawa Dr Mahfouz cewa "ha'a! Me kake son na tambayeka kuma? Komai a'a,za mu samu yaro ne haka kawai? To ko dai Mom ta haifar maka k'ani ne ban sani ba?" Wani dariya Hjy Aisha dake sakkowa tayi tace "sannu Mahfouz! Ni kuma kakema fatar na haihu a wannan shekarun nawa?" D'an dariya yayi ya sosa backhead d'insa cikin jin kunya yace "I'm sorry Mom ai ban san kin ji ba" ta girgiza kai tana murmusawa tace "kawo min yaron ka wuce aikin ka,idan ka dawo office kuma ka samu Daddynku yana son magana da kai" yace "tou Mom" then ya mik'a mata yaron da har ransa yaji yana k'aunarsa,yana
Chapter 158 · 0% Book details