Sashe 26
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read
Malam Usman Ibrahim Maji dad'i shi ne asalin head na family'n,asalinsa bafulatanin garin Maiduguri ne,da ya fito daga garin Bama,mutum ne shi mai hak'uri da sanin ya kamata,a bangaren sha'anin iyali kuwa mutum ne mai matuk'ar k'ok'ari wajen ganin ya kyautatawa iyalinsa tare da sauke hak'k'ok'in da suka rataya wuyansa,matarsa d'aya Zainab wanda ake kira *AZUMI* tun auren saurayi da budurwa,sai dai ita Azumi ko kad'an ba ta da hak'uri mace ce ita mai mita musamman idan aka tab'a ta,za ta iya wuni sur tana mitar abu,Allah ya azurtasu da yara uku Ibrahim khaleel shi ne babba wanda kunya irin na Fulani yasa Azumi ba ta iya kiran sunansa sai dai ta kira shi da Yaro,sai mai binsa Muh'd,sai autarsu Hafsah wanda daga kanta ne haihuwa ya tsaya musu,tun suna yara sun taso cikin gata da soyayyar iyaye,mahaifinsu Malam Usman ya kasance manomi,dai² gwargwado ubangiji ya arzuta shi ta inda bai bar iyalinsa sunyi kuka ba da rashin wani abu,haka wanda duk Allah ya had'asa zama da su bakin iyawarsa da abunda Allah ya hore yakan taimaka ma wanda suka fishi buk'atar taimako. Duk da Malam Usman baiyi karatun boko ba lokacin da yaransa suke tasowa cikin hukuncin ubangiji sosai ya kwad'aitu da son ganin yaransa sun samu ilimi both ilimin addini da na zamani (boko),da yake shima malami ne bakin gwargwado yana da nasa sanin akan ilimin addini shi yake karantar da su ta wannan b'angaren,a gefe d'aya kuma ya sasu makarantar primary ta nan garin Bama,lokacin ko da Muh'd ya gama secondary,lokacin da sakamako jarabawar SSCE ya fito kai tsaye ya gwada yana son makarantar sojoji,a nam malam Usman yayi duk shige da ficensa ya sama masa makarantar sojoji ta Biu dake cikin garin Maiduguri,nan fa gida ya rage daga Hafsah sai Yaro,tsayin lokaci suna rayuwarsu a garin Bama ba tare da ko wane irin matsala ya gifta musu ba,rana tsaka sai ga rigimar boko haram ya taso a garin Maiduguri,bayan b'arna gami da kashe²,salwantar rayukan al'umma da dukiyoyinsu,Malam Usman ya kasa samun nutsuwa da zamansu a garin,da yake kuma duka iyayensa Allah ya musu rasuwa da jimawa,ganin ba shi da sauran dangi sai y'an uwa na nesa,wannan dalilin yasa shi tattaro kan iyalinsa da dukiyarsa da tayi saura suka yi hijira zuwa garin Kano,a nan ya samawa kansa matsuguni Hafsah da bata gama secondary ba ya nema mata makarantar gwamnati ta ci gaba da zuwa,tun da suka dawo Kano da yake babu wani sana'a da Malam Usman d'in yake yi sai y'ar dukiyarsa da ya k'ullo,a ita suke ci su sha har ma su biyawa kansu buk'atun yau da kullum. Bahaushe kan ce "zara ba ta barin dami" haka ce ta kasance ga Malam Usman da iyalinsa kasancewar babu wanda suka sani a cikin garin Kano kawai dai suna rayuwa ne daga su sai halinsu,bayan wani lokaci ba tare da sun farga ba,y'an kud'ad'e da duk wasu kaya masu sauk'in kud'i da suka zo da shi duk suka k'are,abincin da za suci ya fara gagararsu samuwa,a nan ne hikima ya zowa Malam d'in inda yasa yaransa maza a gabs suka bazama neman abun yi,sune can yau,idan sunga ba'a dace ba gobe su nufi can,duk abunda ya kama idan har za su samu to fa babu girman kai za suyi,hatta sharar rumfunan kasuwa zuwa cikin shaguna idan har aka kira su za suje su yi ko aike,d'an abunda suka samu shi za su tattara su sayi abinci,washe gari idan sun samu kwatankwacin abunda ya faeu jiya haka za su sake yi,sun sha zuwa kasuwa a k'afa su koma a k'afa idan sun gaji su samu guri su huta,malam USMAN yakan ce "suyi hak'uri su jurewa duk wani k'unci,hak'ik'a dukkan tsanani yana tare da sauk'i,dan haka wata rana sai labarimm" sau da yawa idan yana fad'an haka yaran sukan yi dariya suce "da wuya wannan lokacin ya riske mu baba" sai yayi murmushi yace da su "kadaku taba yanke tsammani da samun rahamar Ubangiji, kudai ku ci gaba da hakuri,hak'ik'a nasarar Allah tana nan zuwa a kusa.." Da sun ji ya ce haka sai suce "ko yaushe cikin tsammanin zuwanta muke" sai yace "ku dai kuci gaba da addu'ah,ku mik'a dukkan lamuranku ga Allah,hak'ik'a Allah mai ji ne kuma Mao gani.." Kamar yadda yake fad'a,cikin haka Allah ya had'a Malam Usman da wani mutum da ake kira Alh Yakubu Na Abba,kasancewarsa mutum ne sananne a cikin garin Kano ta b'angaren harkar da ya shafi kasuwanci,kusan duk kasuwannin kano da wahala baka ji an ambaci sunansa cikin wad'anda suka mallaki shaguna ba,Allah ya bashi tarin dukiya da ilimi dai² gwargwado,a b'angare guda kuwa duk wannan d'umbin arziki da Allah ya yiwa wannan bawa nasa,tsayin shekaru tun aurensa na faei Allah baisa an tab'a ko da b'atan wata a gidansa ba,da yawan lokaci bisa shawarar da aka basa ya sha auren zawarawa da yaji labarin sun haihu a wani gidan,ba don komai ba sai don yana sa rai akan ko Allah zai sa a dace ya samu k'aruwa ta b'angarensu,sai dai fa da zaran ya aura d'in idan aka shigo sai dai yaji shiru babu wani labarin da zai sake biyowa baya,wannan dalilin yasa Alh Yakubu yake rik'on y'ay'an y'an uwansa,yakea kyautata musu kamar shi ya haifesu,ana cikin haka ya auro wata matan da ake kira Hjy Ladi,ta zo da yaranta biyu duka mata,Asama'u itace babba sai k'anwarta Rabi,Hjy Ladi ta kasance irin matan nan masu shige² da masifar fad'in rai,lokacin da mijinta mahaifin su Asama'u ya rasu ko da labarinta yaje kunnen Alh Na Abba nan take ya nuna yana ra'ayinta,ba tare da tunanin komai ba ya aika magabatansa gidansu,mahaifinta dattijon arziki ya nemi da su ba shu lokaci ya tabbatar idan babu matsala,bayan tafiyarsu Malam Jauro ya kira y'arsa ya tambayeta ko tana son Alh Na Abba,take a nan ta amsa saboda tun kafin lokacin take jin labarin sa,abu na biyu kuma dukiyarsa wanda ita ce ummul'aba'isin da yasa ta amsa ba tare da jinkiri ba,Malam Jauro ya aikawa wakilan Alh Na Abba a nan aka tsayar da lokacin bikinsu,bayan aure ko da ta shiga gidan ta tarar da mata uku inda ta zo a cikon ta hud'u,yadda Alh Na Abba yake sakar musu dukiya komai a wadace ba kamar gidan tsohon mijinta ba da ta rasu,a nan k'arya ta k'aru,ita da y'ay'anta suka fara jin kansu,har ya zama sun fi asalin y'ay'an y'an uwan Alh Na Abba fank'ama da nuna su wasu ne,gurin shige² da yawon Hjy Ladi ta had'u da wata hatsabibiyar mata a nan mak'otansu mai suna Hjy Zubaida,a hankali Hjy Ladi ta fara shiga jikin Hjy Zubaida har suka d'an fara sabawa,sanda Hjy ladi taga yadda mijin Hjy Zubaida yake mata rawar jiki,duk abunda tace yana b'arin jiki yake yi,wannan abu ya ja hankalin Hjy Ladi ta k'ara k'aimi wajen shiga jikin Hjyr suka zama k'awaye sosai,ta haka suka san da yawa daga sirrin juna,hatta malaman da suke ma Hjy Zubaida aiki sai da ya zama sun san da zaman Hjy Ladi,Hjy Zubaida ta gabatar da ita a gurinsu,y'ar Hjy Zubaida d'aya Izzatu wadda take tsaran Asama'u,bayan had'uwar Hjy Ladi da mahaifiyar Izzatu Hjy Zubaida,da amincin da ya shiga tsakaninsu yasa suma suka zama k'awaye har ta kaisu ga zama aminai kamar iyayensu,lokacin da Hjy Ladi ta k'wace kambun gidan Alh Na Abba komai da kowa ya dawo k'ark'ashinta,ya zama ita kad'ai take sawa ayi kuma ita take hanawa ak'i yi,gaba d'aya y'ay'an y'an uwan Alh Na Abba da suke gidan sai da ta san yadda tayi duk suka koma gidajen iyayensu,dangi gaba d'aya suka daina zuwa,ta nesanta shi da kowa da komai,hatta matansa da ta shiga ta tarar sai da ta fitar da su,gida ya dawo daga ita sai y'ay'anta kad'ai suke rayuwa suke kuma murza zaren su son ransu. Asalin alak'ar Alh Na Abba da malam Usman wata rana cikin irin ranakun da Alh Na Abba yake zuwa kasuwa duba rumfunansa,a lokacin ana tsanain rana da zafi,shigarsa kasuwa ke da wuya yana kan zagayen shagunansa,ya hangi Malam Usman da yaransa suna shara,bayan wani lokaci ya sake zuwa kasuwar da niyyar duba yadda harkoki suke tafiya ya sake ganin Malam Usman sunyi wujiga² suna zaune,a ranar ko karin safe basu yi ba suka fito,a nan yake tambayar wani yaronsa Malam Usman suka sanar masa y'an gudun hijira ne daga garin Maiduguri,tausayi da son taimako irin na Alh Na Abba lokacin da zai barar kasuwa,ya aika aka kira masa Malam Usman,bayan zuwansa suka gaisa Alh Na Abba yace "Malam shin idan na baka aiki za kayi?" Malam Usman yace "sosai kuwa Alh" Alh Na Abba yace "wane irin alk'awari za ka iya yi min da zai gamsar da ni kai mutumin arziki ne,baza ka ha'ince ni ba?" Malam Usman yace "a'a Alh bazan iya yi maka alk'awari ba,amma dai tabbas zan kula maka da dukiyarka tamkar yadda zan kula da nawa" jin abunda Malam usman ya fad'a Alh Na Abba yayi murmushi yace "Yanzu kam na gamsu da yabon da naji ana yi akan ka,daga yau kai da yaranka za kuna zama cikin shagunan da nake da su cikin kasuwar nan" cikin tsananin farin ciki Malam Usman ya yiwa Alh Na Abba godiya har kamar zai durk'usa masa,Alh Na Abba yace "babu komai,daga yanzu ma kuna iya fara aiki" Malam Usman yace "sai dai wani hanzari ba gudu ba" Alh Na Abba yace "akwai wani matsala ne?" Malam Usman yace "idan babu damuwa ni zan fara zuwa,su yaran su ci gaba da zuwa makaranta,ranakun da suke hutunka k'arshen mako sai su zo" Alh Na Abba yayi murmushi yace "babu damuwa,nima ina da niyyar tambayarka ko suna zuwa makaranta sai kuma ka riga ni" Malam Usman yace "da dai suna zuwa,halin rayuwa da yanayin da muka tsinci kanmu a ciki ya hana su zuwan" a nan Alh Na Abba ya k'arfafawa Malam Usman guiwa,bayan komawar Malam Usman gida da murnansa ya sanar da matarsa labarin yadda suka yi da Alh Na Abba,Azumi ta yi farin ciki dan sosai suke cikin tsananin rayuwa,ita da yaran duka suka yiwa Alh Na Abba addu'ar fatan alkhairi da tsayin rai mai amfani. Tun daga wannan rana Malam Usman ya fara zuwa kasuwa,Alh Na Abba yasa shi cikin yaransa,haka Ibrahim da Muh'd y'ay'ansa ranar da babu makaranta suke binsa kasuwa,a haka rayuwa ya dunga tafiya,Malam Usman ya tsaya kan dukiyar Alh Na Abba tsakani da Allah abu indai ba mallakinsa bane baya tab'a d'auka,ko wani ya gani cikin yaran shagon suna abunda bai dace ba yana tsayawa ya yi musu nasiha,duk cikin yaran Alh Na Abba Malam Usman shi ne mai shekaru sosai,a gefe d'aya kuma kullun labarin kyakykyawar mu'amalarsa da mutane da yadda yake kula da dukiyar uban gidan nasa yasa Alh Na Abba k'ara k'aunarsa har ta kai ya mayar da shi babban yaronsa kuma amintaccensa,duk sauran yaran suka dawo k'ark'ashinsa,cikin tak'aitaccen lokaci rayuwa ya dai²ta a gidan Malam Usman komai bai musu wahala,gabatowar watan ramadhan Alh Na Abba ya yiwa yaransa rabon kayan azumi da na sallah su da iyalinsu,Malam ya dawo gida da sha taran arziki,azumi cikin tsananin mamaki ta tambayesa inda ya samu kud'ad'en da yayi musu siyayya,bai b'oye ba ya sanar mata Alh Na Abba ya musu rabon arziki tare da kujeran umrah,a nan suka shirya zuwa gaisheshi har gida su k'ara yi masa godiya,da yake a lokacin shekaru sun tura sosai Ibrahim ya kusa gama jami'a yana shekarar k'arshe,shi kuma Muh'd lokacin yana level 200,sai auta Hafsah da take zana jarabawar SSCE,bayan sallar Maghreb suka yi kwalliya dukansu,suka d'auki charter taxi bayan sunyi siyayyar kayan marmari suka nufi gidan Alh Na Abba. Kai tsaye aka shigar da su parlon Alh Na Abba,bayan sun gaisa Alh Na Abba yasa aka kira Hjy Ladi da yaranta,ya gabatar da Malam Usman a gurinsu,tun a nan Asama'u ta kyalla idanuta kan Ibrahim gaba d'aya ta kasa nutsuwa,ta kuma zaunawa dai² a haka suka gaisa,lokacin da Malam Usman za su koma har da su aka rakasu bakin motar da ya kawo su,tun daga ranar ta fara bibiyar Ibrahim sai da ta nemo address d'in gidansu,takanas wani lokacin za ta d'auki k'afa taje ba tare da aiken komai ba,sai dan kawai taga Ibrahim,yayin da shi a nasa gefen gaba d'aya baima san tana yi ba,a haka ya kammala makaranta bayan ya yi service Alh Na Abba ya karb'i takardunsa ya nema masa aiki a FIR's (Federal Inland revenue service),cikin d'an lokaci da fara aikinsa kyakykyawan albashin da yake d'auka ya sake sauya akalar rayuwarsu,komai ya sake canjawa a gidan,ba'a d'auki lokaci mai tsayi ba yayi musu gini suka tashi,a lokaci Muh'd ya kammala karatunsa,Alh Na Abba ya tambayesa inda yake son yin aiki,Muh'd yace shi soja yake son zama shi ne burinsa,Alh Na Abba ya karb'i takardunsa ya aikama wani abokinsa,da yake hanyar da suke da ita mai kyau ce cikin hukuncin ubangiji babu jimawa aka kirasu,bayan training da suka yi da duk wasu gwaje² sai ga shi ya fito matsayin sojan ruwa (Navy) aka yi posting d'insa Lagos..