← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 165 OF 184

Sashe 165

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bedroom d'in ya zauna gefenta yake kallonta,lokaci d'aya wasu hawayen farin ciki suka kawo idanuwansa,yayi murmushi mai cike da tsantsar farin ciki,a hankali ya rankwafo kanta yana kallon kyakykyawar fuskarta da tayi wani fresh tana sauke numfashi a hankali² yace "thank u baby girl.. Kin ba ni abu mafi girma da daraja a rayuwata,Allah ya maki albarka.." A hankali pinkish lips d'inta da suka sha cizo saboda tsananin ciwo suka motsa tace "ameen.." Da wani sanyayyan murya mai cike da bacci,Waleed da yaji maganar a bazata yayi sauri ya kalli idanuwanta sanin bacci take,but daga inda maganar ya fito shi ne abun da yafi bashi mamaki ya zuba mata idanuwansa,a hankali ta d'an motsa idanuwanta then ta bud'esu tana kallonsa tana blinking oily idanunta before ta fara yunk'urin tashi,ya taimaka mata ta tashi zaune,ya kaita bathroom ta wanke baki da fuskarta ta k'ara gyara jikinta then suka fito ya zaunar da ita yana kallonta cike da so da tausayi,ya rik'o hannuwanta ya fara jefa mata tambayoyin ina da ina yake mata ciwo,tace cikinta kad'ai ke mata ciwo shima sama²,ya mata sannu yace zai daina in sha Allah shima idan tana sha magunguna akan lokaci,kafin ya fita ya barta a d'akin yaje karb'o yaran saboda kukansu har d'akin ana ji and ya san yunwa ne tunda babu abunda suka ci for almost good 3 hours sai dabino da zamzam,yana fitowa lokacin ya shigo parlon ya tarar da hadimai daga b'angaren Mommella suna shigowa da kayayyaki iri²,su Azaan duk suna ta faman hiran yadda ake surutun kyaun yaran a social media,daga lokacin da suka musu hotuna suka d'ora ake ta cece kuce akan kyaunsu har yanzun,musamman da suka d'ora wani pic d'in Waleed da Manar kuma,here mutane suke cewa ai ba baya ba,gadon kyau yaran suka yi,wasu suna cewa da Waleed suke kama,wasu na musun da Manar suke kama,har sak'on a gaisar musu da parent d'in yaran suke bayarwa,yayin da wasu ke cewa dan Allah a gayyacesu suna,wasu kuma suna cewa suna son yaran acema Mamman su ta basu,kowa dai da irin abunda yake fad'a akansu da yaran,sanda ya karb'i yaransa Azaan na masa tsiya,ya wuce bai kulasu ba yana sakin murmushi,nan suka koma hiran yanda za'ayi taron suna,ni dai nace "ikon Allah daga haihuwa har an fara maganar suna yaran da ko kwana basu yi ba?" Manar na zaune ya shigo d'auke da yaran,ta kallesu tayi murmushi cike da zolaya tace "Pappy! Sannu da aiki,me muka samu ne?" Wani k'ayataccen murmushi ya sakar mata sexy idanuwansa a kanta sanda ya zauna gefenta yace "repeat it again please" yana kafeta da tsumammun idanuwansa,ta sake cewa "Pappy!" Yayi wani special murmushi yace "woah! It's been awhile nake jiran ranar yau ashe dai zai zo?" Ta gyad'a masa kai tace "yeah! Ga shi kuwa har ka karb'i haihuwa ka d'auki kids d'inmu" ya lumshe kyawawan idanuwansa yana k'ara manna yaran a jikinsa yace "Alhamdulillahillaziiy bii ni'imatihi tatimmus'salihaat" Manar dai sai murmushi take sakin masa,ya fara mik'a mata Al'hassan yace "take him kiyi feeding shi ne babba" ta bud'a idanuwanta tana kallon yaron dake tura hannu a bakinsa da sak komai na fuskarsa irin na Waleed ne then ta d'ago tana d'an lek'a fuskar Al'hussain,mamaki shimfid'e a fuskarta tace "Yaya amma kai ya akayi ka ganesu ni dai na rikice?" Yayi wani murmushi yace "ni da na karb'i haihuwarsu ya bazan gane wanda na fara d'auka ba?" Ta d'an dame fuskarta tace "tou ni dai wallahi gani nayi they're look alike,ya zan iya ganesu ni?" Dariya yayi ya lakuce mata hanci then ya nuna mata su yace "yeah! They look alike but Al'hassan ya fi girma da nauyi,shi Al'hussain yayi k'arami and ba shi da nauyi" sanda taji yana fad'a mata haka da sauri ta kalli yaran tana sakin murmushi tace "ooohhh! Thanks Pappy" yayi mata murmushi yace "ahan! A basu abincinsu,tun d'azun suke kuka kina bacci" cikin zak'uwa ta gyad'a masa kai tace "tou!" Tana masa murmushi,ta juya tace "sauke min zip d'in tou" da taimakonsa ta cire rigan,a tare suka kalli k'irjinta da suka yi mugun cika kamar za su fad'o,Waleed yayi ajiyar zuciya a hankali ya mayar da idanuwansa kan Al'hussain dake d'an kuka k'asa²,Manar dai sai rawar k'afan za tayi feeding kid d'inta take tana sakin murmushi,sanda ta cire breast d'in ta kai masa bakinsa yayi saurin kamawa yana sauke ajiyar zuciya,yana fara sha tayi wani irin k'ara da sauri ta zare nonon daga bakinsa,Waleed ya tsaya kallonta mamaki shimfid'e a fuskarsa yake kallonta yace "what?" Hawaye har sun cika mata ido ta kalleshi tace "wallahi Yaya a hak'ura da feeding d'in" bud'a idanuwansa yayi da sauri yana mata wani kallo yace "kamar ya a hak'ura? Su da abincinsu za ki hana su ne?" Kallonsa ta tsaya yi tace "tabb' d'i! Ni dai wallahi su hak'ura ka ji kuwa wani azabar da naji?" Kamar zai fashe da dariya saboda yanda tayi,yana kallonta sosai ya danne dariyar yace "c'mon! Ki basu a haka zai daina ne" wani gwalo idanuwa tayi tace "na basu fa kace?" Ya gyad'a mata kai yace "yeah! Haka nace kou baza kiyi ba?" Jujjuya masa kai tayi tace "kuma a haka zan basu su biyun?" Ya sake gyad'a mata kai yana tsareta da idanunsa,babu zato bare tsammani kawai sai gani yayi ta fara kuka,idanuwansa shi dai har sannan a kanta yana mata kallo mai cike da mamaki yace "wai mene ne matsalarki ne?" Tace "matsalata ni bazan iya feeding d'insu ba that's all" yayi wani murmushi yace "wasa kike" tace "ni wallahi ba wasa nake ba" ya kalleta yace "alright! Yanzu ni kike so nayi feeding d'insu ne?" Juyar da kanta tayi bata ce masa komai ba,ya gyara rik'on da yama yaron a jikinsa yace "okay! Idan baza ki feeding d'insu ba why kika haifesu? Shima ai da sai kice baza kiyi ba" a tsiwace tace "ai dai ba ni na bawa kaina ba Allah ne ya d'ora min nauyin haifarsu" ya gyad'a kai yace "yeah! Tunda kin san haka akan haihuwarsu shayar da suma hakki ne akanki" za tayi magana yace "c'mon! 'Daukesa ki bashi ni kina b'atan lokaci" tace "Yaya ni dai bazan iya ba gaskiya" nan da nan ya d'aure fuskarsa babu alamun wasa yace "feed him!" In a serious tone da dole ta kallesa,yanda taga fuskarsa babu alamun dariya yasa ta d'aukesa tana turo baki ta mayar masa nonon da watermark d'in are leaked,da k'arfi ta runtse idanuwanta sanda yake sha hawaye suna zubo mata,ya bita da idanu yana kallon yanda ta rirrik'e beddings d'in,lokaci d'aya yaji ta bashi tausayi but bai nuna mata ba,har yaron ya k'oshi ya karb'esa ya bata d'ayan,shima tayi feeding d'insa tana share hawaye,ya karb'esa yasa shi a shoulder d'insa,babu jimawa suka koma bacci,Manar kam zamewa tayi ta kwanta ta lumshe idanuwanta tana sauke ajiyar zuciya a hankali²,a haka wani bacci ya fara fizgarta,Waleed da yaga haka yace "hey! Wake up Lily" turo baki tayi a shagwab'e tace "ni me zan maka kuma?" Lafiyayyan murmushi ya saki ganin cike da rigima tayi maganar,shima cike da tsokana yace "ba cewa zanyi ki feeding d'ina ba bare kice za kimin fad'a,tashi kici abinci sai ki kwanta ki huta" da sauri ta bud'a idanuwanta ta kalleshi sai kuma ta tashi ta zauna tana hararansa,yayi mata murmushi yace "u ask for it" tab'e baki tayi ta kwaikwayesa tace "u ask for it!" Wani k'ayataccen murmushi ya sake saki yace "it's ur time,Allah zai ara mana lokacin da zan rama" tace "kou ka rame ba" yace "whatever!" Daga haka ya kwantar da yaran ya fita yana sakin murmushi. Not too long ya dawo da tray a hannunsa waya mak'ale a kunnensa ya danneta da shoulder d'insa yana magana,ta bisa da kallo har ya ajiye mata tray d'in lafiyayyan tuwon semovita da Mommella ta shiryo mata da miyar kuka da ya ji man shanu sai zuba k'amshi yake da nama,gefe kuma farfesu ne da gashin nama,ya jiye a gabanta da ido ya mata alama taci,ta hararesa tana murgud'a baki tana k'unk'uni tace "ai dai zan ci naga" ya bud'a mata idanuwa still yana magana a wayar yana cewa "in sha Allah.. Zan fad'a mata" tayi saurin kallonsa sai kuma taji yana cewa "ameen ameen,na gode sosai.. Sai an jima" tun bai sauke wayar daga kunnensa ba yake gyad'a kai yana k'ureta da kallo sanda ya zauna yace "me kike cewa?" Bata kallesa ba tace "ni ka ji na yi maka magana ne?" Yace "a'a ai da yake bakya yi ne" tayi wani murmushi mai cike da rainin wayo bata k'ara kallonsa ba har ta d'aga mug dake kan tray d'in ta shanye tea dake ciki then ta fara cin tuwon tana lumshe idanu,sanda ta gama tsaf tayi hamdala,za ta tashi ya rik'ota da sauri yace "ke ina za kije?" Tace "parlor gurin su Ameerah" ya mata wani kallo k'ala bai ce mata ba ta shiga taitayinta ta koma ta zauna,ya d'auke kayan ya fita da su,daga can da yaga su Ameerah sun fita,ya kulle k'ofar gidan ya dawo ya sameta sai kumbura fuska take,ya tab'e baki ya k'araso ya kwanta gefenta ya rungumeta yace "oyah! Sleep maza² ba na son na k'ara jin maganarki" daga haka itama bata sake magana ba ta kulle idanuwanta,a hankali taji ya ce "Mama na gaisheki,ta ce na maki barka kafin ta kira ki" ta gyad'a masa kai tace "ina amsawa,na gode." A haka wani sahihin bacci mai nauyin gaske ya kwasheta ta barsa sai amsa kiran waya yake. To cut the story short sai da akayi kwana biyu da haihuwar kafin Dadda ta iso,ranta duk a b'ace sai masifa take wai duk su Abba suka hanata tahowa tun ranan da akayi haihuwar,dan walak'anci shi ne sai yau,shima sai da suka ga ranta ya b'aci suka hak'ura suka bari ta zo,ko zama bata yiba tace ai sai a kaita ta gano y'ay'anta,Mommella tasa hadimai su rakata ganin za ta tada mata rikici daga zuwanta,suna tafiya a mota saboda d'an tazaran dake in between apartments d'in tana mitar banda rashin sanin darajar haihuwar fari da kuma ita da ba gari d'aya suke ba taya ma za'a bar Manar ita da Waleed salon yaje ya d'irka mata wani cikin da d'anyan jego,su dai hadimai ba jinta suke ba,suna rakata suka dawo tun
Chapter 165 · 0% Book details