← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 184

Sashe 48

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani washe baki Hjy Asama'u tayi tace "ki bari dan manzo?" Hjy Izzatu tace "wallahi ba maganar wasa nake miki ba,sai ma kinga yarinyar,wayayya uwa uba kuma ga ilimi,ko shi kansa ya ganta bai isa kusheta ba" Mama tace "ai shi kenan an gama magana,ina ga ma kafin naje zan fara yima Sahibar magana idan basu mata miji ba" Hjy Izzatu tace "wane irin ki fara mata waya kuma Allah na tuba,ai kisa shi yaje suga juna shi ne bayani,yadda d'an namu yake tubarkalla duk macen da ta gansa ko bata samu damar masa magana ba ai ta had'iye yawu.." Mama tace "wallahi fa,ai kinsan ba daga nan ba,in dai kyau ne na ce miki gadonsa yayi gurin ubansa,kuma dai kina ganin kakarsu ma,duk da yake ta tsufa ai akwai sauran kyau har yanzu" Hjy Izzatu tayi dariya tace "gaskiya fa,zamanin tana budurwa ina ga samari sun sha fama" Mama tayi dariya tace "to abunki da Fulani kinga kuwa ai ko basu yi gadon komai ba sa yi na kyau" sosai suka yi hira,yayin da maganganun Hjy Izzatu suka yi tasiri a zuciyar Mama ta hau ta zauna,tare da cin alwashi kan lallai za ta aikesa gidan cikin satin,Hjy Izzatu tana mata dariyar yadda taga ta karb'i al'amarin tace "aatooh! Gara dai ki hanzarta dan kinsan hausawa na cewa a bari ya huce shi ke kawo rabon wani.." Bata wani dad'e sosai ba a gidan bayan sun gama shan kan matsalar da suke ganin ita za ta addabesu,Mama ta rakata har bakin mota tasa driver ya mayar da ita gida. Bayan tafiyar Hjy Izzatu Mama ta zauna shiru tana imagining yadda al'amarin zai kasance,bayan wani lokaci ta fito ta lek'a d'akin su Diyanah,cikin sa'a ta gansu su biyun kasancewar tuni Ameerah dana ba ta kwana tare da su,ko da Manar ba ta k'asar ma itakam d'akin Aunty take kwananta,su kuma suka gaje d'akin su biyun,duka suna zaune kan gado kowacce da waya a hannunta,wanda tasa Waleed ya siya musu,ta kallesu tace "Deejah ina Yayanku?" Deejah da ta kafe ear pierce a kunnenta bata ji ba,sai da Mama ta k'arasa ta fizgesa had'e da maka mata tsawa,ta d'ago tana cuna baki tace "kai Mama dan Allah dan banji ba kuma sai kin min tsawa?" Mama ta kafeta da idanu cikin masifa tace "dan ubanki ni kike cema haka?" Deejah ta d'auke kai tace "to me zan miki wai?" Tace "tambayarki nayi Yayanku" cike da jin haushi tace "ni ban gansa ba" Mama tace "je ki duba min idan motarsa na nan,na ga keys d'insa a d'akina d'azun bayan ya fita" a fusace Deejah ta dangwarar da wayar ta mik'e tana k'unk'uni ta fita,Mama ta bita da kallo cikin jin haushi tace "za kici ubanki ne,shegiya da bak'in idonki kamar nawa" ta lek'a taga motarsa na nan ta dawo,Mama tana ganinta tace "ya ya akayi?" Tace "yana nan" gyad'a kai tayi tace "ok! Na san bai yi nisa ba duk inda yake,but je ki part d'in kakarku ki gano min idan yana can" a fusace Deejah tace "haba dan Allah Mama nifa akwai abunda nake kike katse ni,ki aiki Diyanah mana kuma" sakin baki Mama tayi cikin tsantsar mamaki tace "ban isa na aike ki ba ke d'in?" Deejah cikin jin haushi da k'osawa da magana tace "ni bance ba" gyad'a kai Mama tayi tace "tun wuri wallahi ki wuce ki duba min shi kafin na karb'i wayar na fasashi" wani kallo Deejah ta d'ago ta bawa Mama tace "yanzu Mama sai ki fasa min waya akan d'an wannan abun?" A fusace Mama tace "za ki wuce ko sai na b'ata miki rai" Deejah ta gyad'a kai ta wuce cikin fushi,fakam² ta dunga tafiya kamar kamar idan taga abu a gabanta za tayi tafiyar ruwa da shi sanda taje bakin apartment d'in ta tura k'ofar a hankali,dai² lokacin zai fito Manar biye da shi a baya Deejah ta kalleshi da yake shi kad'ai ta gani tace "Yaya kaje inji Mama" ya kalleta fuskarsa a d'aure yace "dan uwarki baki iya gaisuwa ba sai fad'an sak'o?" Sanin halinsa yasa da sauri tace "ina wuni" ya maka tsawa yace "bar nan kafin na illataki dak'ik'iya kawai" tab'e baki tayi ta juya,bata bari ya ji ba tayi k'unk'uninta ta wuce,tana barin gurin ya juya ya kalli Manar yace "u've to stay here,zanje na dawo.." Ta kallesa da sauri tace "to za ka d'auko key d'in?" Yace "yeah! Zan taho da su" tayi murmushi tace "to kayi sauri ka dawo" yayi mata murmushi yace "yanzu za kiga na dawo ma kamar walk'iya" tayi dariya ta koma ciki,yana tafiya ta kira Ameerah,tace "to matsoraciya shi ne kika gudu saboda kada Yaya yayi miki fad'a ko?" Ameerah tace "bayan har nan ya biyo ni!" Manar ta tuntsire da dariya tace "Allah k'ara,ki sauri kizo kiji wani magana" cikin zumud'i Ameerah tace "ta samu?" Manar da mugunta tace "ehh! Kiyi sauri ke dai" tana fad'a ta kashe wayar tana dariya,ko minti biyu ba'ayi ba Ameerah ta shigo,ta zauna kusa da ita tana haki Manar ta kalleta tana mata dariya k'asa² tace "wai gudu kika yi?" Ameerah tace "ehh mana" ta sake kyalkyalewa da dariya tace "saboda tsabar shaida shi ne kike sauri kizo kiji.. To babu wani abun da ya samu kawai dama na gaji da rashin ganinki kusa da ni" saurin kallonta tayi tace "da gaske kike ko wasa?" Tace "ai kin san na saba miki k'arya dole ki tambayeni" Ameerah kamar za tayi kuka tace "wallahi sai Allah ya saka min gudun da kika sa nayi" Manar tace "to ni nace kiyi gudu?" Tsabar haushin da Ameerah taji ko kallonta bata kuma yi ba ta d'auke kanta. Tun kafin ya k'arasa shiga d'akin gabansa yake fad'uwa ya daure ya k'arasa shiga yana runtse idanunsa because bai san wannan karon da me za ta zo masa ba,Mama ta bisa da kallo fuskarta a sake unlike sanda suka rabu d'azun kamar za ta cinyesa d'anye,a door way ya tsaya fuskarsa da wani yanayin damuwa shimfid'e a kai yace "here i'm Mama kin sa a kira ni" tace "ehhh! Aikenka zanyi gidan Sahiba" saurin d'ago kansa yayi not believing abunda yake gani,idan har ba idanunsa suna son masa gizo ba,ya ga kamar murmushi take masa lokacin da take fad'a masa za ta aikeshi ne,ya daure yace "Mama amma yanzu?" A hasale ta d'ago tace "ban isa na aikeka yanzu ba?" Ya girgiza kai yace "not at all" wani uban harara ta banka masa tace "ka d'auki ledar can ka kai mata,kace sauran bayani zan mata a waya" ya gyad'a kai yace "alright!" Har ya juya zai fita ya waiga cikin sanyin jiki yace "but Mama" a tsawace ta tari numfashi "but what? Me za kace min?" Yace "Mama address d'in gidan" wani zaro ido tayi tace "gidan Sahibar ne sai na ba-ka address?" yace "Mama bazan gane ba fa" wani kallo ta dunga binsa da shi na tsantsar mamakin kalamansa,yace "Mama!" A fusace ta fara masifa "zancen banza zancen wofi,ni za ka kawoma k'ananun iskanci kace min baka san gidan ba.. When last muka je da kai?" Yayi shiru ya sauke kansa k'asa,a fusace tace "idan baza ka ba ka ajiye min kayan zanje na kai mata da kaina,ba sai ka nuna min haka zan san ban isa da kai ba" hak'uri ya fara ba-ta,but ta k'i yin shiru sai da ta tsigaleshi tass kafin ta wurga masa k'aramin takarda mai d'auke da address da house no,yayi ajiyar zuciya ya sunkuya ya d'auka,ya mata sallama ya fita,sanda ya kusa ficewa daga apartment d'in idanunta suka hango masa keys d'insa,da sauri ta bazamo tana kwalo masa kira,ya tsaya bakin entrance yana kallonta gabansa sai fad'uwa yake dan bai san me za ta sake cewa ba,ta k'arasa ta mik'a masa keys d'in tana fad'in "a k'afa za kaje hala da baka tambayi keys d'inba?" Shi dai bai kula maganarta ba yayi b'oyayyen ajiyar zuciya ya karb'a ya mata godiya then ya fita ita kuma ta juya tana tab'e baki. Yana fita ransa a b'ace ya bud'e back seat ya watsa ledar ya shiga ya yima motar key,ransa duk a b'ace ya fizgi motar ya fice,kamar ya san Mama tana kallonsa ta window bedroom d'inta sanda taga fitarsa tayi ajiyar zuciya ta saki curtains d'in ta koma gefen gado ta zauna tana sakin bayananniyar ajiyar zuciya da furucin "wa akhiiraan.." Tayi wani murmushin da ita kad'ai ta san ma'anarsa. Waleed har ya fita ya tuna ya cema Manar zai dawo ta jirasa,yayi parking motar a bakin get ya fita,da k'afa ya dawo cikin gidan yana tafiya yana satar kallon apartment d'insu da fargabar kada Mama ta ganshi ya k'arasa gidan Dadda,yana shiga ya gansu su biyun babu mai magana da wata,bai wani tsaya dogon nazari ba yace "get up muje mu dawo" Manar da kamar dama k'afafunta suna mata k'aik'ayi tayi zaraf tace "Yaya shi ne ka dad'e?" Da sauri yace "d'auko hijab kizo mu tafi" kallon Ameerah tayi tace "taso muje sis" ta girgiza mata kai da sauri tana satar kallon Waleed,Manar ma ta kalleshi,ganin kallon da take masa ta k'i tafiya ta d'auko hijab d'in ya waiga ya kalli Ameerah,tayi saurin d'auke kanta tace "a'a sai kun dawo,zan jira ki ai" Manar ta sake saurin kallonsa za tayi magana ya katseta yace ma Ameerah itama ta d'auko hijab suje tare,da murnarta taje ta d'auko suka fita,ko Dadda basu tsaya yiwa sallama ba tana sallah lokacin suka fice,a mota sanda suka fita Manar a gaba kusa da shi,banda surutu babu abunda take masa shi duk ransa a b'ace yake ba sosai yake gane abunda take fad'a ba,yana driven yace ma Ameerah ta d'auko masa paper a cikin ledar kusa da ita,ta d'auko ta mik'a masa yace "Manar karb'i ki karanta min" karb'a tayi kamar gaske ta zubawa takardar ido,yace "Uhn! Ke nake sauraro" nan fa ta masa dummm,yayi ta mata magana ta kasa bashi amsa,sai da yaji haushinta yayi parking gefen hanya ya fizge takardar ya maka mata mugun kallo ya duba,yana gama karantawa ya cilla mata ya sake tada motar,cikin takaici yana girgiza kansa yace "karatun hausan shima bakya ganewa kenan?" Ta zumb'ura masa baki ta k'i cewa komai,ya waiga kad'an ya kalleta yace "da alamun zansa a mayar dake primary.."
Chapter 48 · 0% Book details