Sashe 112
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yace "i’m dripping wet baby kin tayar min da hankali sosai" turo baki tayi tace "ni nayi maka? Ba kai kasa nazo ba?" Yayi murmushi yace "i wish we were at home,so i could do some terrible things to u.." B'ata rai ta k'ara yi tace "ni dai sai da safe bacci zanyi" yace "Uhn! Kiyi bacci yanzu zan kamaki ne.." Sanda ya shiga bedroom d'insa ya kulle k'ofa ya fad'a kan gado,kasa bacci yayi ranan sai juye² yake daga baya ya tashi ya shiga bathroom yayi wanka ya d'auro alwala yazo ya kabbarta sallah. Tun daga ranan gaba d'aya sai bai sake saka Manar a idanunsa ba,gyara na sosai Mommella take musu,yanzun kam ma kulle k'ofa Dadda take ko da rana,idan ba an kwankwasa ba shima sai ta tambayi waye kafin ta bud'e k'ofar,duk saboda Waleed take abun nan,shi kam a nasa gefen tunda ya ga ba ta da niyyar bashi matarsa yasa ma ransa hak'uri ya bar musu gidan,gaba d'aya ya d'auke k'afarsa,kwata² ya daina shigowa sai dai kullum suyi waya. Yau ya kama asabar duka gidan suna ta shirye² kowa na had'a tarkacensa saboda gobe za su wuce Vishakpatnam,around 3pm Waleed ya shigo gidan cikin wani sabon motar da ya siya duk na murnan aurensa da Manar,motar sai kyalli take na sabunta,ya fito daga motar bayan yayi parking ya wuce part d'insu yana sanye da wani shadda light army an masa half jumper mai hannun links,fuskar nan tashi a d'aure har wata y'ar raman dole yayi saboda rashin ganin Manar da baiba cikin satin,d'akin Aunty yayi ya sameta zaune ita da Mommella suna ta tsare²n yadda za'ayi tafiyar gobe,saboda sabon biki za'ayi a can idan anje,kusa da Mommella ya zauna ya gaishesu suka amsa,Aunty ta kalleshi tace "me kake so son" kallon fuskar Aunty yayi a hankali yace "dama ina son Manar ta raka ni mall ne,and za muje ta tayani had'a kaya a can gidan tunda gobe zamu tafi" Aunty ta kalli Mommella,Mommella ta d'auke kai da sauri tana b'oye dariyar da take,Aunty tace "okay! Jira ni ina zuwa son" ta fita da sauri,wani ajiyar zuciya yayi ya lumshe idanunsa,b'angaren Dadda Aunty taje tayi knocking Dadda tace "waye?" Aunty tace "Fatima ce Hjy" Dadda tace "aiho,to ina zuwa jirani na bud'e miki" ta taso ta bud'e,suka gaisa Dadda tace "ya akayi ke da ba zuwa kike ba yau kika lek'o mu?" Aunty ta kalli Manar dake sanye da riga da wando an mata jumpsuit da wani material mint green ta rik'e wayarta tana karanta novel d'in *MAKTOUB* da *REAL SMASHER* ta rubutasa,tsabar dad'in da labarin yake mata bata ma san Aunty ta shigo ba sai da tace "daughter yi sauri ki d'auko hijab d'inki kuzo tare da Ameerah" saurin ajiye wayar tayi ta wuce bedroom d'insu ta d'auki hijab d'inta,tace ma Ameerah "sis kizo Aunty na kiranmu" daga haka bata jira Ameerah ta amsa ba ta fita,Dadda tana kallon Aunty tace "ina za suje?" Aunty tace "Mamansu ce za ta kaisu gyaran wankin kai" daga haka bata tsaya ba tayi gaba suka bita a baya,suna sanye da manyan hijabs d'insu dake sharar k'asa suka wuce part d'in su Aunty,tunda ta shigo yake kallonta ganin yanda fatarta har wani glowing yake ta k'ara haske,duk da hijab d'inta har k'asa ne amma bai hanasa ganin yanda ta wani k'ara cikowa ba tai fresh kaman ka tab'a jini ya fito,gaida Mommella suka yi,Aunty tace "maza kuje son but kada ku zauna,daga can ka wuce da su gyaran kai please ka sa na ma Hjy k'arya" saurin kallonta yayi zai magana ta masa alamun ya wuce kada ya dameta,yayi gaba cike da jin haushin had'osa da Ameerah da tayi yayi k'wafa k'asa² yace "na san me zan muku ai" yayi gaba yana turama Azaan message dan cikin sati d'ayan ba k'aramin alak'a ne ya k'ullu tsakaninsa da Azaan ba wanda duka gidan suke mamaki,Azaan dake d'akin Amaar sai juye² yake yana son yin bacci ya kasa yayi zumbur ya diro daga gadon ya d'auki jallabiya yasa,Amaar ya kallesa yace "hey brother! Where are u going?" Azaan bai sauraresa ba yace "I'm coming" yayi waje har yana had'awa da d'an gudu,dai² lokacin Deejah na fitowa kitchen da bottle water a hannunta taga Waleed zai fita tace "Yaya" waigawa yayi fuskarsa a d'aure yace "what?" Ta d'anyi dum sai kuma tace "nothing.." Harara ya wurga mata yayi tsaki zai fita sai kuma tace "Yaya Mama fa ba ta lafiya" wani juyowa yayi ya kalleta ya d'an tsaya wajen k'ofar ya kalli Manar a hankali yace "ki jirani a mota" ta gyad'a masa kai ta fita,ya mayar da k'ofar ya kulle yana kallon Deejah yace "me yake damunta?" Kwallan da ta taru a idanunta ta share tace "wallahi Yaya muma bamu sani ba,surutai dai kawai take kuma ko bacci take ba ta fasawa" even though ya girgiza da maganan amma bai fasa bud'e k'ofa ba yace "Allah bata lafiya.. Zanje ana jirana idan na dawo zan shigo,ki mata sannu" ya fice da sauri,Deejah ta share kwallar idonta ta wuce sama tana bud'e d'akin taga Mama a zaune tana fad'in "wallahi bazan barsu ba,ko zanyi yawo tsirara sai na rabasu,wallahi Waleed d'ina ba ya sonta" sai kuma ta fashe da kuka,saurin k'arasawa Deejah tayi tana share hawaye tace "Mama yanzu naga Yayanmu" zabura Mama tayi tace "yana ina?" Deejah tace ya fita yanzu" hanyar fita Mama tayi tana fad'in "ku kira min shi" Deejah tayi saurin rik'ota saboda yanzun rufe k'ofar suke da mukulli saboda ita,tace "Mama zai dawo yanzu ya ce zai shigo ya ganki" kallonta Mama ta dunga yi kafin ta koma ta zauna ta had'a kai da guiwa tana rafzar kuka tana fad'in "shi kenan sun mana farrak'u sun raba ni da d'a na.. Wayyo na shiga uku na lalace shi kenan an shiga tsakanina da Waleed d'ina" sai ta k'ara fashewa da kuka. Waleed kam yana fita ya shiga motarsa ya fita daga gidan,slowly yake tafiya a line yana kallon mirror sanda motar Azaan ta fito daga gidan yayi ajiyar zuciya ya tsaya har Azaan ya k'araso gurin ya tsaya,Waleed ya kalleshi ganin yanda ya d'an rame abun ya mugun bashi dariya ya d'auke kansa yana murmusawa yace "ba ka da lafiya ne?" Wani kallo Azaan ya masa yace "ko dai ba mu da lafiya? Kai baka ga yanda kake bane?" Murmushi Waleed yayi yace "ka dai bini a hankali kar na hanaka ita wallahi" Azaan ya d'an lumshe idanunsa yace "sorry brother tana ina ma?" Ta mirror Waleed ya kalli Aneerah yace "ke bi mijinki yana kiranki,daga nan kice ya kaiki saloon dan wallahi ni bazan je kaiki ba" kallonsa tayi sai kuma ta sunkuyar da kanta a hankali tana matsa fingers d'inta,Waleed ya mata tsawa yace "get out malama kina b'atan lokaci" saurin bud'e motarsa Azaan yayi yana fad'in "ya haka kuma za ka tsorata min mata,ka bita a hankali mana har ta fito" Waleed ya masa wani kallo yace "dan Allah janyeta ni kada ku b'atan lokaci,ina da abunyi idan ku kun rasa" da k'arfi yaja murfin motarsa ya rufe yayi gaba ya barsu,Azaan yana ganin wucewarsa yayi dariya ya kirasa,Waleed ya d'auka yace "what?" Azaan yace "daka tafi mu a titi kake so muyi.." sai kuma ya waske yana satar kallon Ameerah yace "a titi kake so mu zauna?" Murmushi Waleed yayi cike da tsokana yace "ohon muku.. Ni dai Allah ya sani bazan jira ba,idan ka ga dama ko a motane ma kuyi tayi,mu had'u anjima a saloon.." yana fad'a bai jira ba ya katse wayar yana dariya yana satan kallon Manar dake gefensa ta wani k'udundune a hijab tun da Azaan ya fito gida tak'i yarda ta kallesa,yayi murmushi har suka k'arasa gidansa,yayi parking yana kallonta yace "let's go" k'in bud'e idanu tayi yaga ba ta da niyyar motsawa ya fita ya zagaya gefenta ya fara nad'e hannun rigarsa ya sunkuya ya d'aukota,mutsu² ta fara a shagwab'e tace "ka sauke ni" yace "ank'i a sauke kin" ya wuce cikin gidan da ita tana ta mutsu²,sai da suka kai sama ya sauketa k'ofar bedroom d'insa ya bud'e yace "oyah muje" nok'e masa kafad'a tayi yace "kada ki bari na d'auke ki na shigar da ke da kaina.. Billah abunda baki tab'a zato ba zai faru" gwalo idanu tayi a cikin hijab d'in tana tura baki tana lek'o fuskarta waje,yayi murmushi yayi ya ya tsaya yana kallonta,a hankali ta tura k'ofar da kyar take iya d'aga k'afa ta shiga,tana kaiwa tsakiyar d'akin ta tsaya,ta waiga a hankali ganin bata ganshi ba ta turo baki,ta baya taji ya rungumeta,sosai ta tsorata ta saki y'ar k'ara saboda bata san ya b'uya a bayanta ba,ya rungumeta firmly a hankali ya kawo bakinsa d'ai² kunnenta yace "i miss u" ya juyo da ita da sauri ya kai hanunsa yayi cupping fuskarta,yana kallon eye balls d'inta yace "did u miss me?" 'Dan murmushi tayi saboda yanda yayi maganar ta girgiza masa kai,ya zaro idanunsa yana kallota yace "what" ta b'oye fuskarta a k'irjinsa tace "ni ban yi ba" gyad'a kai yayi,yana rik'e da ita ya zauna bakin gado,ya d'orata akan cinya yana kallon fuskarta yace "wa na kama?" A d'an rikice ta kallesa tana dafe k'irjinta,ganin yanda yake kallonta yasa ta fara k'ok'arin tashi za ta guda,ya rik'eta sosai yana mata murmushi,rufe fuska tayi tana turo baki tace "ba fa da kai nake ba" sanda ta shammacesa da gudu ta tashi za ta shige bathroom ya rik'ota ta baya tare da cire hijabin jikinta ya matseta a jikin bango yana kallon idanunta yace "wa na kama?" Yana matsota,tayi tsilli² ta kasa cewa komai sai k'ik'k'ifta idanu take,a hankali ya rungumeta ya sauke fuskarsa kan wuyanta yana sauke ajiyar zuciya da wani murya yace "did u miss me?" Dan dariya taji yazo mata,ta d'auke kanta tana kallonsa ta gefen ido tace "sorry!" A hankali ya rik'o hanunta ya zauna a kan gado ya d'orata akan jikinshi yana kallon fuskarta murya can k'asa yace "did u miss me?" Kanta ta kwantar a k'irjinsa a kunyace tace "uhm" sai Kuma ta rufe bakinta da sauri dan bata ma san lokacin da maganar yayi escaping mata ba,ya had'e kansu wuri d'aya ya zagaye ta da hannayensa yana d'an jijjigata akan k'afarsa yana mata murmushi,murya can