Sashe 4
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
tayi fuska a tsuke tace "yau naji jaraba,mutane sai musun bala'i.. Ni dai na tafi bazan zauna ba aje a cuceni" dariya Ameerah ta fashe da,Manar ta tab'e baki ta d'auke kai,Aunty ta tashi da sauri ta fito,a parlon k'asa ta tarar da matar d'azu ta k'araso tana sakin murmushi tace "sannu da hutawa Hjy" wani kallo matar tayi mata kamar ana mata dole ta amsa "yawwa!" Daga haka ta d'auke kai,Aunty tace "kin san Hjy ta dawo?" Bata kalli direction d'in Aunty ba tace "ehh! Da wani abu ne kuma?" Aunty tace "thought ko bayan ta fita kika sakko" ta girgiza kai tace "not at all.." Gyad'a kai Auntyn tayi itama ta wuce hanyar kitchen da take jin motsi,a bakin k'ofa ta tsaya tayi sallama,maids uku dake ciki suna aiki suka amsa suna gaisar da ita,dattijuwa d'aya sai y'an mata biyu,ta amsa fuskarta a sake tace "idan aikin da kuke yi babu yawa Haulatu ke da Ruqayya kuje b'angaren Hjy ku gyara da sauri" amsawa suka yi suka fito,y'ar dattijuwar ta ci gaba da aikin,Aunty ta juya ta bar gurin matar dake zaune parlor ta bita da wani kallo ta tab'e baki,a k'asa Aunty ta tsaya ta rad'oma Ameerah kira,da sauri ta fito tana daga sama tace "ga ni Aunty" Aunty ta mata wani kallo tace "ni kike so na zo na same ki a nan?" Ta fara sakkowa da sassarfa tace "i'm sorry" Aunty tace "ina Manar d'in take?" Tace "tana sama" tace "maza kira min ita kuzo tare" komawa tayi saman,suka dawo tare da Manar,Aunty tace "maza wuce dining kici abinci" satar kallon matar dake zaune tayi,suna had'a ido ta sunkuyar da kanta da sauri ta girgiza kai tace "a'a na k'oshi" wani kallo Aunty tayi mata tace "na fara miki wasa kou?" Murmushi ta d'ago tana yi,aunty ta had'e rai tace "wuce kafin na sab'a miki" girgiza kai ta sake yi kamar za tayi kuka tace "Allah Aunty ba na jin yunwa,ni gida zanje wajen mother" kallonta Aunty ta dunga yi ta fahimci dalilin k'in cin abincin da bata son yi tace "baki je ba dama?" Ta gyad'a mata kai da sauri tace "nan na fara zuwa" Aunty ta gyad'a kai tace "alright Ameerah maza kuje ki rakata" Ameerah dake tsaye har sannan tace "Aunty kayan fa ban gama ba" tace "kuje zan k'arasa" amsawa suka yi suka juya za su tafi,matar dake zaune tun d'azu bata ce musu komai ba ta tab'e baki tace "son a sani.. Wai gaida uwar miji a kasuwa" tsaf Aunty ta fahimci magana ta yar mata,tayi murmushi ta juyo tana kallonta tace "ai ba wani abu bane dan ka gaisheta ko da a taron arfa ne ba a kasuwa kad'ai ba" tab'e baki Mama tayi tace "a'a ke dai kike ganin ba komai bane yin hakan,amma wannan ai dangin shishshigi ne" wani murmushi Aunty tayi tace "haka ne kam.. Sai dai shi kansa shishshigin ma iyawa ne,idan wani yayi an yaba wani idan yayi shegen duka zai ci.."