Sashe 184
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da su saboda makaranta,ranan da za su koma India,bayan sun fito su Mother sun rakosu bakin motoci,suna bankwana da k'ara bawa juna hak'uri,Manar ta waiga ta kalli apartment d'in Dadda,cike da rauni ta nufi part d'in hawaye suna zubo mata,ji take mutuwar ya dawo mata sabo,kamar yanzun take samun labarin mutuwarta,Waleed yaje ya kamo hannunta suka ma su Mother sallama suka tafi,suna hanya ta kwantar da kanta jikinsa tana share hawaye,cikin sanyin maganarta tace "Allah ya miki rahama ya gafarta miki Hajiya.." Waleed ya amsa da "ameen" cikin wannan yanayin mai wuyar fassarawa jirginsu ya d'aga zuwa India,mutuwar Dadda ya girgiza wannan ahali ba kad'an ba,shisa ko bayan komarsu sai da suka d'auki tsayin lokaci kafin suka fara sawa ransu dangana,da lokacin aikin Hajj yayi gaba d'ayansu da suke India da wanda sure Nigeria suka je saudiyya,bayan aikin hajj,lokacin suna shorten tafiya suka je d'awafin bankwana,a nan suka ma Dadda addu'o'in dacewa da rahamar Allah sosai,Manar kam babu ya ita,a lokacin ta dunga tuna zamansu da yanda suka yi rayuwa a saudiyya da Dadda har bayan sun koma Nigeria,daga nan suka wuce Nigeria Waleed yayi zagayen duba hospitals d'insa wanda da taimakon Daddy ya samu ya cimma wannan burin,a nan d'in ne ma Daddy'nta ya tambayi shawaran Waleed game da dukiyarta da Dadda ta bari a hannunsa,Waleed yace ya kamata a fara tambayarta aji ko tana da wani buri akan dukiyarta,Daddy ya bashi damar ya tambayeta suji,ko da yake mata maganar take tace tana son gina islamiyya a wani filinta da sunan Dadda,sannan boreholes a unguwannin da basu da ruwa,lokacin da ta gama masa bayanin yace "shi kenan abunda kike so?" Ta gyad'a masa kai,saboda kuka take lokacin da take masa bayanin,a ranan ya sanarma Daddy yanda suka yi,cikin lokaci k'ank'ani aka fara aikin hak'an boreholes da ginin islamiyyan aka gama,ranan da za ayi launching d'insu ya d'auketa ya zagaya da ita da yake sunzo k'asar taga yadda aikinki ya kasance,yadda bata yi tunani ba haka aka k'awata komai,after then suka koma India cike da farin cikin ganin islamiyyarta da akasa sunan Dadda har an fara karatu,sanda suka koma gida a lokacin cikinta ya tsufa sosai,har ya shiga wata na tara,haihuwa ko yau ko gobe,Ameerah kam kusan watannin y'arta Zainab biyar. Da dare lokacin Waleed ya shigo daga wani aikin gaggawan da ya fitar da shi,ya samu yaransa suna assignment a parlor,yayi murmushi ya zauna sanda yake dubawa yana musu tambayoyi suna ba shi amsa,after yayi correcting d'insu ya tabbatar sun yi dai² then ya wuce bedroom d'insa,ko da ya shiga bai tarar da ita ba,har ya gama shirin kwanciya kuma bata zo ba,ya fito lokacin da yake jin surutun su Little Azaan za su tafi d'akinsu yace "hey friends! Ina Mummy?" Alhussain yace "Daddy tana bedroom fa,tun d'azun ta ce ba ta jin dad'i yau" Waleed yace "alright! Maza muje ku kwanta akwai skul gobe sai da safe kuma" sanda ya rakasu yayi hugging d'insu ya musu addu'o'i yayi kissing d'insu duka,saboda d'abi'arsa ne duk dare daga shi har Manar haka suka sabar musu,ko sunyi bacci kuma ya shigo zai shiga ya gansu ya musu addu'o'i ya musu kiss sannan ya ja musu k'ofar,sanda ya nufi k'ofar fita da sauri yana cewa "bari na duba Mummy,tun safe na kula da yanayinta.." Little dake kan gadonsa gefe da gadon Alhussain yace "Daddy baka ce muzo muje tare ba" da sauri Waleed dake wani tunani a ransa yace "noo! Kuyi mata addu'ah daga nan zai isa gareta" Little yace "tou Daddy za muyi mata,Allah ba ta lafiya" Waleed ya amsa da "ameen" ya fita ya kulle musu k'ofar,a hankali ya tura k'ofar bedroom d'inta yayi sallama,Manar dake durk'ushe k'asa ta rirrik'e beddings zufa duk ya wanke mata fuska da jiki ta d'ago kai cikin wahala da azabar ciwo ta sauke idanunta a kansa,da sauri ya k'arasa kusa da ita yana mata wani kallo ya rik'ota yace "sannu Lily" kai kawai ta iya gyad'a masa,yace "za ki haihu yanzu in sha Allah" ita dai addu'o'i kawai take ja,ba ta k'arasawa zai kufce ta kama wani,sanda ya duba yaga haihuwan a kusa ya d'auketa ya wuce bathroom da ita,ya sakata cikin tube,ya durk'usa kusa da ita ya rik'e mata hannu,d'aya hannun kuma yana shafa fuskarta yana mata sannu da k'warar mata guiwa,cikin hukuncin Allah babu jimawa faya da babyn suka taho tare,k'atuwar baby girl jajir da ita tana fitowa ta tsanyara kuka,sai ga mabiyyan ma ya biyota,da sauri ya auna ya yanke cibiyan yasa clip ya mak'ale ya d'ora mata babyn a k'irjinta,ita kam nunfashi take sauke na samun salama tana jero kalmomin godiya ga Allah,ya cire mabiyyan yasa a leda da hand gloves ya nad'esu then ya juyo ya d'auki Babyn ya gogeta da Olive oil,ya had'a ruwa mai d'umi ya mata wanka sannan ya dawo ya gyara uwar y'ar itama,sanda ya gama gyarasu ya d'auko y'arsa yana rik'e da hannun Manar suka fito ya zaunar da ita bak'in gado yana mata sannu ya fita zuwa kitchen,da kansa ya had'o mata lafiyayyen abinci,yana shiga bedroom d'in ya tarar da ita rungume da sai kallonta take tana murmushi,ya zauna gefenta yana kallonsu cike da so da k'auna,da kansa ya dunga bata tana ci,sai da ya tabbatar ta k'oshi ya kyaleta,yace tayi feeding Babyn,babu wanda ya sanarma haihuwar sai da safe,nan su Ameerah suka shigo suka iske ana drama da Waleed da su Alhussain da suke son Manar ta ba su Baby yana cewa kada ta soma,haka kawai su jefar masa da y'a,Ameerah tace "haba Pappy ai kuwa ko dai kowa bai d'auketa ba ya kamata abari 3 brothers su d'auketa" nan duk yaran gidan suka fara murna suna cewa suma a basu,Waleed yace "ai kunji inda matsalar yake,ban amince a bama kowa yarinyata ba.." Ba'a son ran yaran ba,amma babu yanda za suyi dole suka d'auki hak'uri. Ranar suna yarinya ta ci sunan Zainab itama amma za suna kiranta da (Mahasin),bayan anyi hidimar suna,y'an uwa da suka zo suna duk sun koma,aka bar Manar da Baby'nta Mahasin (meanin-Beauty). Bayan wasu watanni da haihuwar,tana zaune tana feeding Mahasin da tayi wayo Waleed ya shigo d'akin da sallama,sanda ta d'aga kai ta kallesa ta amsa tana masa murmushi,ya k'araso yana sauke wani numfashi da k'ureta da kallo,ya zauna gefenta yana kallonsu cike da burgewa har ta gama feeding Mahasin da zuwa lokacin tayi bacci,tana k'ok'arin mayar breast d'inta cikin riga yayi saurin rik'e hannunta yana narke fuskarsa yace "Mummy ki barmin abuna kada ki b'oye min cikin riga,ina so nayi ta sha ina tab'a abuna" zaro idanu tayi a shagwab'e itama tace "ni dai please.." Bai bari ta kai k'arshe ba da sauri ya karb'e Mahasin ya kwantar da ita kan gadonta,sanda ya juyo ya nufo gadonsu,fuskarsa tana bayyanar da wani k'ayataccen murmushi ya k'araso inda take a hankali yace "hey girl.." Tace "hi Man" yayi murmushi yace "What's ur name?" Cikin wani irin kallo da salo tana juya masa idanu tace "my name is Zainab Muh'd Maji Dad'i" want k'ayataccen murmushi ya k'ara yi yana sakin mik'a yace "aaahhh! Lallai yau za ki tabbatar min da sunan maji dad'i.." Dariya ta kyalkyale da shi,sai kuma ta sunkuyo ta d'ora goshinta saman nasa,hancinsu yana gogan na juna tace "zan saka kuka fa" da sauri ya juyata ta koma samansa yana sauke numfashi a hankali yace "abunda nake buk'ata kenan.." Tana masa murmushi tace "ka tara ka samu.." Daga haka tayi saurin had'e bakinsu,tun daga nan har k'arshe ita tai riding d'insa,cike da nishad'i sanda suka samu nutsuwa yana rungume da ita yace "thank u Lilac.." Ta d'aga masa gira tace "alaa shuu?" Yace "for everything.." Nan ya fara lissafo mata,irin jin dad'i da farin cikin da ya samu ta sanadinta,tayi murmushi tace "Pleasing u is my only purpose in life.." Yayi murmushi mai yalwa cike da jin dad'i ya k'ara rungumeta,a haka bacci ya d'auketa,Waleed dake jin zuciyarsa cike taf da k'aunar y'ar uwarsa,jininsa,matarsa kuma uwar y'ay'ansa,it was there ya zuba mata idanu yana kallonta da tunanin lokacin baya sanda suka sha fama da Mama akan soyayyar Manar da ta addabesa,har zuwa lokacin da take fad'a masa bazai auri Manar ba in har tana numfashi,duk irin rigimar da suka yi sai da ya tuno har bakin da ta kusa yi masa,yau gashi komai ya zama tarihi,har da rabon Yara hud'u da suka haifa,wanda gaba kuma bai san nawa za su k'ara samu ba,cikin sanyi da godiya ga Allah abisa ni'imar da yayi agareshi ya sauka daga gadon ya shiga bathroom ya d'aurai alwala,bayan ya fito ya shirya banda k'amshi babu abunda yake ya shimfid'a pray mat,sanda yayi nafila ya k'ara godema Allah,kafin ya haura saman bed d'in ya sake rungumeta yana tuna maganar sayyadina Aliyu (R.A) da yake cewa "Ahbib habibaka haunan maa asaa anyakuna baghidaka yauman maa,wa'abghid baghidaka yauman maa asaa anyakuna habibaka haunan maa..." Cike da jin dad'in yadda al'amura suka daidaita ta kowane b'angare ya lumshe idanunsa yana tasbihi ga Allah da yake da ikon canja dukkan lamura,a haka shina wani irin bacci mai cike da nutsuwa,sukuni da godiyar Allah ya d'aukesa yana kwak'ume da ita a jikinsa...
*_#KARSHE..._*
#Alhamdulillahillazii bii ni'imatihi tatimmus'salihaat.. On this occasion i would like to thank Almighty Allah again for the gift he has bestowed on me,and i extend my heartfelt congratulations to my followers as well,hakur'in saurarona da kuka yi babu dare babu rana,prayers da kullum kuke min sending ina godiya sosai da sosai,and i ask Allah (S.W.T) to forgive me and u for the mistake i made in writing of this story,wad'anda na b'atawa rai kuyi hak'uri ku yafe min this is nothing but human nature,wanda yayi min na sani ko ban sani ba Allah ya zama shaida akai na yafe muku³,yan paid group d'ina,thank u very much for ur patronizing my book,fatan Allah ya sake had'a fuskokinmu da alkhairinsa.. Allah yasa watan ramadhan da za mu shiga,mu yi ibada lafiya,kuma ya zama karb'ab'b'e,Allah yasa ibadar da za muyi ya zama silan shigarmu aljannah,ameen.🤲
Zan yi kewarku sosai mutane na..😪😥
For any other problem/complain/enquiry chat via 08165726609.
*#BISSALAM...👋*
#Ur's Hawwa Muh'd Usman.
#Twitter-Jeeddahmu898.
#Wattpad Real-smasher.
#I.G realsmasher898.
#Asli Smasher.
#Oum Janan.
#Manar.
#End's Wednesday 07/April,2021. @6:10pm GMT.
*_#KARSHE..._*
#Alhamdulillahillazii bii ni'imatihi tatimmus'salihaat.. On this occasion i would like to thank Almighty Allah again for the gift he has bestowed on me,and i extend my heartfelt congratulations to my followers as well,hakur'in saurarona da kuka yi babu dare babu rana,prayers da kullum kuke min sending ina godiya sosai da sosai,and i ask Allah (S.W.T) to forgive me and u for the mistake i made in writing of this story,wad'anda na b'atawa rai kuyi hak'uri ku yafe min this is nothing but human nature,wanda yayi min na sani ko ban sani ba Allah ya zama shaida akai na yafe muku³,yan paid group d'ina,thank u very much for ur patronizing my book,fatan Allah ya sake had'a fuskokinmu da alkhairinsa.. Allah yasa watan ramadhan da za mu shiga,mu yi ibada lafiya,kuma ya zama karb'ab'b'e,Allah yasa ibadar da za muyi ya zama silan shigarmu aljannah,ameen.🤲
Zan yi kewarku sosai mutane na..😪😥
For any other problem/complain/enquiry chat via 08165726609.
*#BISSALAM...👋*
#Ur's Hawwa Muh'd Usman.
#Twitter-Jeeddahmu898.
#Wattpad Real-smasher.
#I.G realsmasher898.
#Asli Smasher.
#Oum Janan.
#Manar.
#End's Wednesday 07/April,2021. @6:10pm GMT.