← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 184

Sashe 139

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Dariya duka suka yi Manar tace "amma Dadda idan za mu koma gidanmu tare zamu tafi ko?" Haushi yasa Dadda watsa mata wani kallo ta mata dak'uwa tace "k'aniyarki da tafiyar.. Kinga idan baki fita idona ba tamm,dan rashin kunya meye ba kwa yi a gaban idanuna? Tsotse²,ke ce rungumesa,dan ki fad'a kansa kuwa dama ba wani abu bane tun can kin saba, Allah na tuba indai Mamman ne ai gaki nan gashi wataran sai kinyi kamar ki gudu da k'afar ki" turo baki Manar tayi tace "nifa ba ni nake cewa muyi a gabanki ba,ki tambayesa kiji idan ni nake cewa muyi a kan idanunki" ta k'arasa fad'a tana kallonsa tace "Yaya ka fad'a mata,nice nake cewa muyi a gabanta?" Wani karkace kai Waleed yayi yace "a'a ni ban sani ba,ina zaune dai kike zuwa kice na taimaka na k'ara yi miki ciki ko za ta koremu mu tafi gidanmu,ba haka akayi ba?" Nan da nan idanunta suka yi rau²,kan kace me har ta fara zubar da hawaye tana dukansa tana cewa "Allah kuwa ba gaskiya yake fad'a ba,wallahi bazan iya fad'ar haka ba,ai ni ba mara kunya bace.." Lips dinta ya dank'o yana mata wani kallo yace "waye mara kunyar a nan ni ko ke?" Saurin girgiza masa kai tayi tana kuka tace "nifa bance kai ba" dariya yayi ya kai harshensa yana lashe mata hawayen da wani murya yace "Allah ya cece ki yarinya da kinga irin rashin kunyata yanzun nan" da sauri ta fara zamewa daga jikinsa ta rarrafa ta koma k'asa ta zauna tana zumb'uro masa baki...
Chapter 139 · 0% Book details