Sashe 138
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kin kashemin yarinya sai kice tsautsayi ne?" Daddy dai kallon mother kawai yake,ganin ya yi shiru ya k'i cewa komai cikin rawar murya Mama tace "dan Allah ku tausayamin ba dan halina ba sai dan darajan y'ay'an da na haifa dan Allah ku yafe min" sai lokacin Daddy ya d'ago ya kalli inda take,sai dai ya k'asa magana,mother dai ganin za su iya yin b'atacciya tayi sauri ta mik'e ta bar gurin,Daddy ya kalleta kawai ya mik'e yabi bayanta zuwa bedroom,Mama tana ganin haka ta k'ara fashewa da kuka dan ta san da wahala su iya yafe mata,can ta mik'e tana waiwayen k'ofar d'akin ta fita daga gidan tana share hawaye. Almost 30 minutes da fitar Mama daga part d'in,Daddy ya fita part d'in ya wuce part d'in Abba,a hankali ya shiga ya zauna yana kallon Abba da yayi shiru idanuwansa a kulle,after few seconds cikin sanyin jiki yace "i'm very sorry about what happened brother,but no one is above mistake,kuskure ne ya riga ya faru,sai dai ko saboda darajan yaranku,ya kamata ka duba abunda zai iya faruwa,i'm really not happy about this gaskiya,ni dai bana goyon bayan ka rabu da matarka,ko ba komai ya kamata taci albarkacin 'ya'yanta,kuyi hak'uri ku barta tayi zaman y'ayanta,we all know sharrin shaid'an ne,babu wanda yafi k'arfin shaid'an ya rud'esa sai wanda Allah ya tsare,ni da iyalina mun yafe mata,na tabbatar basu rik'eta ba,dan Allah ina rok'on ku yafe mata kuma,Allah ya shirye mu gaba d'aya ya raba mu da bin son zuciya da mummunan k'arshe.." Abba ya d'ago ya kalli d'an uwansa cike da k'arfin hali yace "batun aure tsakaninmu ya k'are,igiya biyu da suka yi saura yau na cikasa mata su,babu wani sauran alak'a tsakanin mu kuma,saboda haka ta bar gidana ba na marmari ko son k'ara ganinta.." Shiru Daddy yayi yana kallonsa,jiki a sanyaye ya masa sallama then ya tashi ya fita. Bayan sallar isha'a Mama tana d'aki,har lokacin kuka take tana kallon d'akin ta kasa tafiya,Deejah da Diyanah suna zaune sai kuka suke suna kallon Mama,can dai Mama ta daure tana kallonsu hawaye suna sauka fuskarta tace "i don't really know where to start,but abunda zan fad'a muku shi ne kuyi hak'uri ku zauna gidan mahaifinku,duk abunda kuka ji gaskiya ne babu k'arya,ba komai yasa na aikata haka ba kuma sai k'iyayyar da nake ma Maryam,duk akanta na jefa kaina cikin mugun hali,na dunga sab'ama Allah,abunda nake ta fafutukar na hana faruwarsa sai ga shi Allah ya gwada min ni ban isa nayi komai ba,nayi ta sab'a masa babu dare babu rana,i still can't believe wai d'ana dana haifa ne yake auren y'arta har ya mata cikin da muka zama sanadinsa,sai dai na san babu yanda zanyi,tun farko Allah ya hukunta matarsa ce,abunda ya faru dani a yau na tabbatar hakan ma wani ishara ne Allah ya saukar min,ubangiji yana so na da rahamarsa shisa ya bani chance d'in da zan repenting,na nemi gafaran wanda na cutar,a matsayina na uwa na san bai kamata ace na cutar da d'ana na cikina ba,amma son duniya ya rufe min ido na aikata abunda na aikata,duk abunda zai faru daku na san ni na ja muku,but u have to take heart and pretend kamar babu abunda ya faru,har zuwa sandw Allah zai fito muku da miji kuyi aure,ni dai tawa ta k'are,ina muku wasiyya kada ku sake wani ya rud'e ku ya d'oraku wani hanyar,kubi mahaifinku abunda yace kuyi²,i know ko ba na tare da ku,Waleed bazai barku kuyi maraici ba.." 'Dan shiru tayi ta shaki numfashi kafin ta juya ta nufi k'ofa da sauri tana fad'in "Allah ya sada mu da alkhairi.." Daga haka ta fita daga d'akin tana goge idonta ta bar d'akin bata k'ara waiwayensu ba,suka bita da kallo suna kuka sosai suna kiranta,Waleed da ya hauro saman zai je d'akinta a dalilin kiran da Abba yake mata,yana jin maganar da take ya tsaya ya jinginar da kansa a hankali ya lumshe idanuwansa hawaye suna sauka fuskarsa,Mama bata iya kallonsa ba saboda wani kunyarsa da kunyar abubuwan da tayi masa da taji ya kamata,ta wuce tana cewa "ga k'annenka nan ka kula dasu dan Allah,ba su da kowa a duniyar nan da ya wuce kai.. Allah ya k'addara saduwar mu.." Abba yana zaune parlor tare da Aunty Mama ta sakko rik'e da trolley d'inta,bata iya kallonsu ba tayi hanyar k'ofa za ta fita,Aunty ta mik'e da sauri ta bi bayanta,sanda suka kai compound kafin Aunty ta kirata,Mama ta d'an tsaya har Aunty ta isa kusa da ita,ta mik'a mata envelope tace "ga shi Abbansu ya ce a baki" Mama ta sa hannu biyu ta karb'a tana kuka sosai tace "na gode Allah saka da alkahiri" Aunty tace "ameen.. Allah tsare" ta juya da sauri ta koma saboda hawayen da suke zubo mata. Tun bayan fitar Mama gidan haka nan gaba d'aya gidan ya zama wani iri,kowa ya yi jigum² kamar gidan makoki,a dare ranar Abba ya kira Waleed yace ya kamata ya d'auki Manar su koma gidansu tunda jikin ya yi sauk'i,Waleed yayi k'asa da kansa yace "Abba da bari nayi sai ta k'ara samun hutu kafin mu tafi,saboda yanayin jikin nata" Abba yana kallonsa yace "shi kenan babu damuwa,Allah kiyaye gaba" ya amsa,then Abba ya sallamesa ya tashi ya fita. Bangaren Dadda ya wuce kai tsaye ya sameta zaune a parlor,suka gaisa kafin ya tambayeta Manar,ta fito daga d'aki sanye da hijab har k'asa sai zuba k'amshi take tana kallonsa ta k'arasa kusa da shi,tunda ta fito Waleed yake kallonta ya kasa d'auke idanuwansa daga kanta har ta zauna,da ido yayi mata magana ya mik'e ya fita,Dadda ta bisa da kallo bata ce komai ba,can Manar ta tashi za ta bisa,da sauri Dadda ta kalleta tace "tou ke kuma ina za kije da wannan talatainin daren?" Manar bata tanka ta ba ta fita,a balcony ta gansa tsaye leaning his back a jikin wall ya lumshe idanuwansa,ta k'arasa da sauri ta shige jikinsa,tun ranan da incidence d'in ya faru rabon su da had'uwa privately sai yau,ya rungumeta da kyau suka sauke ajiyar zuciya,a hankali ya d'ago yana kallon idanuwanta ya bud'a bakinsa yace "muje part d'inmu?" Ta girgiza masa kai tace "a'a mu zauna a nan" yana kallon eyeballs d'inta da itama shi take kallo yace "Hjy fa?" Tace "to ba d'akinta za ta kwana ba kuma?" Ya d'an gyad'a kai yace "alright! Muje Ina jin bacci" kallonsa ta dunga yi sympathetically,kafin ta rik'o hannunsa suka shiga parlon tare,Dadda ta d'aga kai ta kallesu,tana ganin sun wuce hanyar bedroom ta zaro idanuwa da wani expression tace "ku kuma ina za kuje?" Manar dai ta d'aure fuska bata kalleta ba,Waleed yace "sak'o za ta ba ni" suka wuce suka barta baki sake,can sanda suka shige d'akin tace "ni dai na ga jaraba,har wani sak'o za ka karb'a kuma baza ka tsaya a nan ta shiga d'auko ba sai ka bita yar d'akin?" Ta dunga mita,can da taji shiru ta tashi taje wajen door d'in tayi knocking tana kiransa tana cewa ya fito shi take jira za ta kulle k'ofarta,jin shiru tace "tou kuma tsani da Allah idan ka karb'i sak'on ba sai ka fito ba haka? Ni ina son kwanciya kak'i fitowa gadi zanta zama ina muku?" Manar ta d'aga murya tace "tou ki rufe mana idan zai tafi ba sai na bisa na k'ara rufewa ba" Dadda ta dunga kallon k'ofar kamar za tayi kuka tace "ku dai ku dunga jin tsoron Allah,mutane ku dunga dagewa kuna shararo k'arya,idan kun fad'i gaskiya zan hanaku ne?" D'an dariya Manar tayi tace "tou mu dai ki tafi sai da safe" Dadda ta dunga hararan k'ofan kafin tayi k'wafa ta tafi tana mita. Tana barin gurin Waleed yayi saurin cupping fuskarta yana kissing,kamar za tayi kuka ta dunga kallonsa murya can k'asa tace "Yaya ka bari naga kou ta tafi" da sauri ya d'agota ya zaunar da ita ya jawota jikinsa sosai ya rungumeta yana kallon lips d'inta murya can k'asa yace "think ta tafi tunda kika ji shiru" b'ata rai tayi tana son tashi yak'i sakinta,ta cusa fuskarta a k'irjinsa a hankali tace "ni dai ka bari na duba" k'ara rungumeta yayi ya d'ago kanta da sauri yayi grabbing lips d'inta ya fara sucking,ranan sun gurji juna sosai,duk yanda suka dunga k'ok'arin ganin basu yi surutu ba kasawa suka yi,sanda suka dami Dadda tayi kicin² ta had'e rai tana mita,can da aka jima taji shiru ta koma ta kwanta. A k'alla sai da Manar ta samu 2 month a gida,ranan wani Sunday da safe around 11am suna zaune parlor ita da Dadda suna hira,Daddy suka shigo tare da Waleed,tunda suka shigo idanun Waleed suke kanta har suka zauna,Manar tayi masa murmushi,kafin ta gaisar da Daddy'nta,yana kallonta cikin farin ciki yace "kun k'i tafiya gidanku har yanzu kou Mamana?" Da sauri Dadda tace "ina kuwa za su tafi? Kullum sai dai su lallab'o min nan su sani magana,kuma ma dai maganar Allah,ai ya kamata ace zuwa yanzu Mamman ya yi mata lefe kou ba haka ba? Allah na tuba tunda ya sameta a b'agas babu ko sisin kobonsa da yayi kuka,ai bai kamata ace an yafe masa kud'in akwati ba kuma" Daddy dai murmushi kawai yake yi,ganin Dadda sai mita take yace "shi kenan Hjy za'ayi mata in sha Allah" Dadda ta washe baki tace "tou yanzu naji zance ai.. Auuu tou kuma nace yaushe za'ayo akwatin?" Daddy yace "k'ariiban in sha Allah" Dadda tace "tou Allah ya kaimu,ya kuma hore kud'in" yana kallonta har sannan yace "ina kwana?" Dadda tace "lafiya lao,ya gidan da iyali?" Yace "Alhamdulillah! Kun tashi lafiya,ya gida?" Tace "an gode Allah" ya gyad'a kai,sanda suka tab'a hira kafin ya tashi ya fita tare da Waleed suna magana,kafin Waleed ya fita yama Manar alama zai dawo,ta gyad'a masa kai,can da yamma ya dawo ya tarar da Dadda ita kad'ai parlon,ya zauna ya gaisheta,ta amsa tana kallonsa,yace "ina mata ta?" Wani kallo Dadda ta masa kafin tayi magana Manar ta fito d'aki sanye da gown da ya tsaya mata k'asan guiwa,tana zuwa kusa da shi ta fad'a jikinsa da saurin tana dariya,Dadda tayi saurin tsuke fuska tace "kai ba na son iskanci,ya za kuzo gabana kuna rungume²,idan iskancin da za kuyi kenan maza ku tashi ku b'ace min daga gani.."