Sashe 33
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun gari bai gama yin haske ba Dadda ta fita hankali tashe ta isa part d'in ta dunga knocking kamar za ta cire k'ofar tana k'walama Abba kira,haulatu mai aikinsu ta bud'e mata k'ofar,da sauri Dadda ta wuce tana ci gaba da kiran "Yaro!" Jin shiru a fusace kaman za tayi kuka tace "to wai ko Yaron baya jina ne yayi min shiru?" Ta wuce za ta yi sama suka had'u da Abba yana sakkowa cikin sauri sanye da jallabiya,da sauri ta taresa hankali tashe tace "Yaro! Zo maza² muje kaga abunda yake faruwa" shi kansa Abba hankalinsa bai kwanta ba saboda yanayin kiranta da ya jiyo,ya bita da sauri yana tambayarta "Hjy lafiya?" Dadda tace "ina fa lafiya,zo dai muje ka ganewa idanunka" suka fita tare Aunty ta sauko za ta bisu,Mama da ta jiyo kiran ta fito itama tana murtsika idanunta ta tarar Aunty za ta fita tace "lafiya naji muryar tsohuwar nan a nan?" Aunty dai ta yi hanyar fita tace "wallahi ban sani ba,zan je dai na gani" tab'e baki Mama tayi ta nemi guri ta zauna tana jiran su dawo taji kanun labarai. Tsabar saurin da Dadda take har kamar za ta kifa Abba yace "bi a hankali Hjy" bata tsaya kulasa ba ta wuce,suna shiga part d'in ta nufi d'aki Abba yana biye da ita,dai² lokacin sun shigo Manar ta hantsilo daga kan gado,idanun Dadda kamar za su fad'o k'asa tace "A'uzhubillahi! Mene ne haka kuma?" Kafin ta k'arasa Manar ta fara kwara amai,Aunty da tayi shigowar k'arshe ta k'arasa kusa da ita da sauri ta rik'eta tana mata sannu,sympathetically Abba da yayi tsaye bakin k'ofa ya dunga kallonta yana mata sannu,sanda ta gama Aunty tana shafa mata baya tace "sannu daughter" wani kukan ta sake fashewa da shi muryarta ko fita ba ta yi sosai tsabar kukan da ta kwana yi,Aunty ta d'agata tana rarrashinta suka wuce bathroom ta wanke mata jiki,Ameerah dai na gefen gado ta buga tagumi da hannuwa biyu idanunta suna fidda k'wallar tausayin halin da Manar ke ciki,kafin Aunty ta fito da ita Abba ya kalli Dadda yace "Hjy me yake damunta ne?" Da wani muryar takaici Dadda ta fara masa magana "kai dai Yaro wallahi tunda na haifeka baka tab'a zuwa ka d'auko min magana ba,amma wannan d'an naka kullum ne Allah ne da kullum sai ya zo nan ya sa ni dogon magana" Abba dai sai kallonta yake yace "kiyi hak'uri Hjy zan masa fad'a" a fusace ta masa wani kallo tace "wane irin za ka masa fad'a kuma Allah na tuba? Sau nawa yake zuwa ya sani magana,idan naje na fad'a maka a banza,ko sau d'aya ni dai ban tab'a ganin ka zaunar da shi ka masa fad'an ba sai yau ne za kace min haka?" Aunty ta fito da Manar dake kuka har sannan muryarta a dashe ta kaita kan gado ta kwantar da ita,za ta juya Manar tayi saurin rik'o hannunta,kallota Aunty tayi tace "ina zuwa daughter bari na gyara gurin da kika b'ata na dawo" ta gyad'a mata kai a hankali wasu hawayen suna zubowa daga idanunta tace "sss..sanyi nake ji Aunty" k'aton duvet d'in dake kan gadon Aunty taja ta rufeta da shi fuskarta kad'ai ta bari a bud'e,Manar ta k'arasa jan bargon ta rufu dukanta,Aunty ta kalleta cike da tausayi ta wuce ta fara gyara gurin da tayi aman,sanda ta gama tana kallon Dadda tace "Hjy wai me ya sameta haka lokaci d'aya?" Bud'e bakin Dadda maimakon ta musu bayani sai ta rushe musu da kuka,Abba dai duk ya kasa magana sai kallonta yake,Aunty tayi k'arfin halin fara rarrashinta tace "dan Allah Hjy ki daure ki mana bayani mu san halin da ake ciki" ta kama gefen zaninta tana share fuska kafin tace "fisabilillahi dama ya lafiyar giwa bare ace tayi hauka,kuna kallo dai ba'a yima yarinyar nan wani abuba ta yi kuka bare anyi" Abba ya daure yace "me aka mata?" Kamar mai jira nan Dadda ta fara rattabo masa bayani "nake fad'a maka Yaro jiya da dare yarinyar nan ta shigo min da murnarta tana fad'a min an kawo mata wayar salula.. Kafin ma nayi magana kawai mutumin nan ni dai muna zaman² lafiya ya shigo min ni na d'auka abun arziki ya kawosa,ai yana jin zancen an kawo wa yaran nan waya shi kenan karka dad'a karka raga mutumin sai cewa yayi lallai illalla sai ta kawo masa" Abba yace "waye ya bada wayar?" Dadda tace "wancan yaro dai d'an uwanta na gurin Hafsatu" Abba ya gyad'a kai yace "Azaan kenan?" Dadda tace "shi fa dai nake nufi,to fa shi kenan tunda ya karb'e ya tafi da waya take ta ratatun kuka,daren nan gaba d'aya abunda taita yi kenan,ni dai ina ga bata ko runtsa ba.. Yo Allah na tuba muma bata bari munyi ba bare ita da take da dalili,shi kenan kuma sai ciwo ya rafketa" ran Abba a b'ace ba tare da ya jira ya gama sauraronta ba ya juya da sauri zai fita,Dadda ta bisa da kallo tace "ina kuma za kaje Yaro?" Bai tsaya ba yace "ina zuwa Hjy" ya fita da sauri daga gidan,Aunty ta kad'a kai tace "sha'anin yaran nan sai dai su d'in" Dadda tayi k'wafa tace "ai karma wancan mutumi yaji labari,ni dai da za'a yarda da abunda zance da sai nace kwata² Yaro yasa ya daina zuwarmin tunda babu arziki,kullum yazo sai ya sa ni yawan magana" Aunty ta d'aga kai ta kalli Dadda tana sakin murmushin tsokana tace "haba Hjy Waleed ne fa" a fusace Dadda tace "shi d'in Allah na tuba Waleed d'in na farko ne?" Aunty ta girgiza kai tace "a'a amma dai a gurinki shi ne na farko" nan da nan Dadda tayi mitsi² da idanu tace "Fatima.!" Kafin tayi wani magana tuni Aunty ta yi sauri ta fita,Dadda tace "wallahi ki fita idanuna na rufe,bar ganin ina d'aga maki k'afa,duk ranar da kuka k'ure ni Allah mutum bazai ji da dad'i ba" Aunty dai tuni ta fice tana murmushi ta wuce kitchen,tana shiga ta zuba ruwa cikin kettle ta jona tana tsaye ya tafasa ta juye cikin flask,ta d'ebo potatoes tana ferewa. Tare Abba suka shigo da Waleed dake binsa a baya,suna zuwa Abba yace "wuce ka dubata kamin bayanin abunda yake faruwa" wani b'oyayyar ajiyar zuciya yayi ya k'arasa inda take,a hankali ya kai hannu ya yaye bargon,ya dunga kallonta da mamaki ganin yadda ta k'udundune jikinta,Abba dake tsaye bakin k'ofa ganin Waleed ya kasa tab'a ta yace "ko dai mu tafi asibiti?" A hankali ya girgiza kansa yace "A'a Abba" ya kai hannunsa goshinta da nerves d'inta suka fito b'aro² then ya kai hannunsa kan wuyanta,har bacci ya fara d'aukarta taji ana tab'ata a hankali ta bud'e idanunta da suka kumbure,tana ganinsa ta janye jikinta za ta matsa ya mata wani kallo a d'an tsawace yace "stay still" sheshshek'ar kuka ta fara ya bita da kallo cikin tsare gida yace "ina ke miki ciwo?" Ta masa banza tak'i cewa komai,ya gyad'a kai k'asa² yadda ita kad'ai za ta ji yace "saboda na kwace wayar kike ciwo?" Still tak'i kulasa,Abba dake tsaye yana jiran yaji ya yi magana yace "ko dai sai mun je asibitin Muh'd?" Waleed ya girgiza kai yace "a'a Abba ba sai munje ko ina ba,zazzab'i ne kawai a jikinta" kafin Abba yayi magana a fusace Dadda tace "A'uzhubillahi! Zazzab'i kuwa ai ba kawai bane,matar da ta kwana kuka shi ne za kace zazzab'i ne kawai" ya juya ya kalleta ba tare da ya yi magana ba ya nufi k'ofa zai fita Abba yace "where are u going?" yace "zanje na siyo medications" Abba ya gyad'a kai ya ciro ATM a aljihunsa yace "karb'i nan kaje da shi" da sauri Waleed yace "no Abba zan siyo na dawo" ya wuce ya fita,Dadda ta tab'e baki ta k'arasa kusa da ita tace "sannu takwara kinji,Allah zai saka miki" parlor Abba ya koma ya zauna yana jiran dawowar Waleed. Almost 10 minutes ya dawo da leda a hannunsa ya shigo da sallama,Abba dake zaune ya amsa Dadda dai ko kallo bai isheta ba ta ci gaba da cin dankalinta,ya kalleta ya wuce ba tare da ya yi magana ba,a zaune ya ganta Aunty a kusa da ita tana mata fad'an ta daure ko tea d'in ta sha,ita dai sai kuka take ta k'i sha,ya k'arasa ya ajiye ledan hannunsa kan bedside drawer,ya kallesu fuskarsa a d'aure yace "Aunty ajiye kawai ki rabu da ita,idan taji wahala za ta sha" Aunty ta d'aga kai ta kalleshi then ta ajiye cup d'in ta nufi hanyar fita,Manar tana ganin za ta fita ta fara kuka,Waleed dake had'a allura ya mata tsawa yace "hey! Hey!!" Da sauri ta sauke k'afarta k'asa za ta mik'e,ya ajiye syringe d'in hannunsa ya rik'ota,da k'arfi ta kwala wani uban k'ara tana kiran Aunty da Dadda,Allah ya taimakesa muryarta bata fita da tuni ta tara masa jama'ah,ya fizgota ya matse sosai a jikinsa yana fad'in "shhhiii" turesa ta dunga yi tana son k'wacewa,da yaga ta k'i tsayawa ya d'aure fuska ya mata tsawa,babu shiri ta nutsu,ya saketa ya nad'e hannuwansa a k'irji ya zuba mata idanu cikin tsare gida yace "kin wuce kin d'auka kin shanye ko sai na gaura miki mari" yadda taga fuskarsa babu alamun wasa da sauri ta juya ta d'auki cup d'in ta kafa kai,duk zafin shayin bata ajiye ba sai da ta shanye tas ta ajiye cup d'in tana hawaye,ya maka mata harara yace "Oyah! Turn around" jin ya yi magana ta tsaya kallonsa ba tare da ta gane me yace ba,sai da ya sake mata tsawa yace "juya nace.. Ki bar kallona" da sauri ta juya tana runtse idanunta,ya d'auki syringe d'in ya gama had'a alluran ya matsa inda take,tayi masa k'ik'am tak'i d'aga rigar sai da yace "Uhn! Kina jira na d'aga miki rigan?" Idanunta a kulle ta janye rigarta sama da sauri,siraran k'afafunta farare tas masu yalwar gashi suka bayyana,a hankali ya dunga bin jikinta da kallo sanda ya kai idanunsa dai² buttocks d'inta a hankali ya runtse idanunsa ya kai hannunsa da niyyar janye red colour d'in pant d'inta ta saman hannunsa ya tab'a jikinta,kamar wanda wuta ta ja da sauri ya janye hannunsa a gurin yana fitar da wani wahalallen numfashi,ya